36
womenofwords/WA
🔏NOT ALL GLITTERS ARE GOLD💫
(BA DUK KYALLI BANE GWAL)
chapter 36
A hankali komai yake tafiya cikin aminci da yardar Allah,Tun kwanciyar Hajiya Saddiqa da Nafisa yanzu sati guda kenan,bangaren Nafisa a yau da suka cika sati aka basu sallama yayin da Hajiya Saddiqa ta farka a ranar ,tana buɗe idanunta ta ganta cikin dakin Asibiti,a hankali ta fara Kallan ko ina,ƙokarin tashi tayi amma ta kasa dalilin wani irin raɗaɗi da ya zo mata a ba zata,Shigowar Nanny muna kenan tana ganin halin da take ciki, da sauri ta isa gare ta tayi mata sama da gadon yarda zai ɗago da ita zaune ,Cike da zafin Nama Hajiya Saddiqa ta kama hannunta tana mai cewa.
"Ina Nafisa?,ta mutu ko?Hadiza ma ta bita ko?,dama ni na sani, wallahi duk wanda yace zai ja Dani zai mutu ne".
Cike da mamaki Nanny Muna ke Binta da kallo kafin tace"yanzu Hajiya tunanin Nafisa kike daga tashin ki?babu wanda daga cikin mu yayi tunanin zaki tashi fa ,a tunani na abu na farko da zaki fara tambaya bayan tashin ki shine halin da Khafilat take ciki,mene ya faru da ita ko yarda Khalid ke Coping,yaran nan yana nan kullum yana tunanin yarda zaiyyi ki tashi,baya duba kansa, all he think about shine halin da ƙanwarsa ke ciki da kuma lokacin da zaki farka,amma sai kike tambayar abin da bai kamata ace yana ranki ba duba da inda abin ya kusa kaiki"
"Kin kusa mutuwa fa sati guda babu wanda yayi tunanin zaki buɗe idanunki".
Da mamaki take kallan Nanny Muna kafin ta ce"Sai kuma gashi ba,hakan na nufin Allah ya bani wata dama ne na taka duk wani wanda ya shigar mun gaba,beside idan ban kashe su ba ni zasu kashe,ina zuwa ma tukunna yaushe muka fara musayar yawo dake Muna?,dan kawai na bar ki Kinsan wani abu nawa ba shine yake nufin zaki iya kallona kina faɗa mun maganganun da baki da right na faɗan su ba,wannan ya zama na ƙarshe,an binne Hadiza da ɗiyar ta?cikin su kuma wane ya sake bin su?".
Da mugun takaicinta Nanny Muna ta bata amsa da"babu wanda ya mutu a cikinsu Nafisa ce kawai ta makance,amma a yanzu da muke magana dake makantarta ba abu bane da zai mugun ɗaga mata hankali duba da a yawan dangin Hajiya Hadiza sun ƙaru dan a yanzu akwai Akram yaran mijin Hajiya Sakina ga kuma Jamal da jannah,ban faɗa Miki ba,Hajiya Sakina Tazo amma yan sanda sun kamata kafin ta Iskoki,suna zargin ta da murder wanda Naji sunce tare kukayi da kuma wai conspiracy ban dai san sauran ba amma cikin ayyukan ki aka gane tana da kama so".
Cikin wani irin tashin hankali ta yi yunkuri ta sauko daga gadon tana mai furta.
"Hala dai Muna kin manta cewa kina da masaniyar duk abin nake yi idan kuma na faɗi kin faɗi. "
"A'a Hajiya da gyara a maganar ki dan Ni bansan kina kwakule cikin yaran mutane ba, tunanin na gidan karuwa kawai kike dashi sai sanin da nayi ke kika sace Ni'imah amma bayan nan babu abin da na sani dangane dake kada ki watsan tsaba Kaji su bini,yanzu ma maganar da nake miki na gama haɗa kayana jira nake ki farka shima wai Saboda humanity,amma yanzu da kika tashi da wannan mugun abin a ranki nasan cewa duk wanda ya biki sai kin kai sa ƙasa,Ni Kinga tafiya ta".
Juyawa Nanny Muna tayi dan barin asibitin dan dama ta gama shirinta sanin cewa Hajiya Saddiqa ta gama yawo muddin kuma ta zauna tare da ita zasu rusa ne wanwar,tana Jiyo ashar ɗin da hajiya Saddiqa ke gundumar mata amma bata juyo ba ,tana fita yan sandar dake gadinta suka faɗa dakin jin hargowarta.Tana ganinsu ta fara kaɗa kai alamun A'a,ja da baya ta fara kafin ta ce"kun san wacece ni kuwa ku ka shigo mun kai tsaye?,ina da mugun kuɗi sannan ina da mugun hatsari" .
Dariya yar sandar mace tayi kana ta ce"mun sani,amma a yanzu ke ba kowa bace face Criminal wadda tayi surviving dan ta karbi hukuncin ta ,ta ina kika samu kuɗin?kowa ya sani ta hanyar yashe cikin yayan jama'a ne kina siyarwa da kuma miyagun kwayoyi,yanzu maganar da nake Miki duk wani gidan jaridu da kike tunanin suna binki suna lashe Miki takashi yanzu sun dawo su suke yaɗa aika aikan ki,babu inda labarin ki bai je ba haka zalika babu wanda ba zai kalle ki ba bai tsine Miki ba,kina tunanin LGs ko?to duk wani mai aiki da ke bincike yabi ta kansa wanda dukkan su sun janye hannun jarin dake tattare dake bugu da ƙari duk wata kadarar ki a yanzu tana hannu dan haka ki kiyaye kafun na chanza Miki kamanin wannan mummunar fuskar taki."
Tana kai karshen maganarta tana mai kama hannun Hajiya Saddiqa ta saka mata handcuffs kana ta saka guda ɗayan jikin gadon da take tana mai karawa da cewa"za muji idan likita yace za a iya sallamar ki domin ki koma Cell ki zauna da ƙanwar ki kafin ku gurfana gaban Alƙali".
Kokarin fizge hannunta take yar sandar ta ɗaga hannu ta ƙwaɗa mata mari,zata sake magana ta ƙara mata wanda yafi na farkon lafiya kafin ta zaunar da ita ta fita karamin dan sandan na bin ta a baya,.wani irin ihu Hajiya Saddiqa ta saka kamar ranta zai fita,kamar sabon kamun hauka ta fara cewa"duk sai na kashe ku,baku san wace ni ba ,dukkan ku sai kun mutu,duk sai na zama ajalin ku na muku alƙawari,tana wannan ihun likitan da ke duba ta ya shigo dan duba ta,kamar zararra haka ta tashi tayo kansa tana yin wani abu kamar haushi tana zage zage akan babu wanda ya isa ,ganin haka yasa ya kira aka riƙe masa ita yayi mata wata allura,kafin kace kwabo ta koma luu ta kwanta,yar sandar da ta shigo dan taimaka musu ne ta ce"Doctor fatan ba hauka take ba dan last abin da zan so yanzu shine matar nan ta haukace,.
Murmumshi yayi ya bata Amsa.
"Lafiyar ta ƙalau ba wani hauka abubuwan da suka faru sukayi hitting ɗinta amma ko a yanzu za'a iya sallamarta,amma zamu sake duba ta".
"Yauwa likita a duba ta idan babu wata matsala zuwa gobe zamu wuce da ita ya zama dai tana cikin hankalin ta,it's just sad a matsayin ka na likita ka ceto ta da taimakon Allah ,sadly kuma zata rasa rayuwar da take mutuƙar so dan wannan matar I'm very sure hukuncin ta na kisa ne,dan wannan jininta ya hallata kawai ".
A tare suka fita inda yake faɗa mata wani family member ɗin ta sai yazo ya saka hannu tukuna,abin da yake basu mamaki shine yarda tana da miji amma har a lokacin bai zo ba gurin duka both related marasa lafiyan dake ƙarƙashin sa.
A hankali Nafisa ke lalube da crutch idanunta ɗauke da Bakin Glasses wanda aka bata a asibitin,sosai suka sha daru kafin ta yarda ta saka ,ta sha kuka sosai ganin wai yau itace ke ɗauke da glass ɗin makafi hannun ta ɗauke da sanda,sun gama haɗa komai nasu Jamal da Sultan suka zo ɗaukan su yayin da Sauran ke gida suna jiran su,riƙe hannun Ummu tayi lokacin da zasu fita a ɗakin,.
"Ummu Har yanzu Hajiya Saddiqa na asibitin nan?"
Kallan Sultan Ummu tayi dan bata damu da sanin tana nan ko tana wane hali ba dan ita ta ƴarta take ,ta yarda da cewa abin da ka shuka shine zaka girba,a iya zamansu tare sosai Saddiqa ta cutar da ita fiye da tunanin mutum amma koda sau ɗaya bata taɓa tunanin ramawa ba,babu wani tunani na ta gwada cutar da ita sanin cewa Ubangiji baya bacci,ko da ace ya ara maka lokaci idan ka duba da idanun basira zaka ga ƙalilan ne.
"Kamar fa tana nan har yanzu dan jiya da na biyo ta inda aka kwantar da ita naga Khalid da kuma police dake gadin ta".
"Ka kaini mana Ya Sultan "ta faɗa a takaice tana mai juyawa saitin da taji Muryar Sultan .Bai mata musu ba yace muje yana mai kama hannunta guda ɗaya,kamar Ummu baza ta bisu ba lokaci guda kuma taji tana mai san Ganin Saddiqan,.
Koda suka je shiga da fari jami'an tsaron basu yarda da su shiga ba sai da suka gabatar masu da kan su kafin suka aminci musu akan kada su daɗe dan likitan ya riga da ya basu tabbacin zasu iya tafiya da ita Khalid kawai suke jira wanda ya bi Doctor ɗin ya dawo,shine babban mutunci da suka mata so far.
Ta riga ta gama ihuce ihucenta da zage zagenta ta zauna kawai tayi shiru tana buga lissafin yarda zata kubuta , babban abin haushin shine yarda Lawyer ɗin ta yaƙi daukar wayar Khalid,karshe ma yayi blocking ɗin sa, tunanin yarda zata samu Wani leader na German Mafia da suka taɓa harƙallar yara ta ke, sanin sun gina alaƙa mai kyau dan baza ta manta yarda tayi hosting nasa ba da har Anal sex ya nema ta bashi wanda haka ya kara musu danƙon zumunci inda a lokacin yayi mata alƙawarin duk abin da ya taso mata na matsala sanin cewa abin da suke akwai haɗari to kawai ta nemesa,takaicinta Wayarta na hannun matsiyatan ya sandan chan Gashi babu numbern sa akan ta ,tunowa da tayi na ta rubuta Number ɗin sa a wani Mini Note book da takan aje ƙananun abubuwa yasa taji wani irin Salama,buɗe kofa da akayi yasa ba tare da ta juyo ba take mai cewa.
"Maza Khalid ka fara haɗa kayan ka zamu wuce Germany,bari na aika ka gida ". juyowa tayi,turus tayi ganin Waɗan da bata taɓa tunanin zata gani ba ,wata irin dariya ta saka lokacin da ta kula da sandar dake hannun Nafisa da glasses ɗin idanun ta kafin tace .
"Na kasa yarda da yarinyar nan karshe ta makance,shima yana daga cikin nasara,wallahi ku godewa Allah hannuna ɗauke yake da wannan abin da babu mai fita"kallan Ummu tayi wadda ke Binta itama da ido.
"Nifa Hadiza yarda na tsaneki da yaranki zan iya bada rayuwata muddin zaku hallaka,zan iya mallaka wa sheɗan ruhi na muddin zaku wahala,bana da burin ganin ku cikin farin ciki ko na misƙala zarratun,tunda Allah ya barni da raina kuwa wallahi wasan bai ƙare ba".
Wani irin tausayin ta Ummu taji maimakon taji haushin ta,kamar tana tsoran magana tace.
"Yanzu Saddiqa baki gaji ba?,ba kowa bane zaiyi irin faɗowar da kikayi da mugun raunin a kikayi ya rayu,hatta ke kanki babu wanda ya taba tunanin zaki rayu,amma Ubangiji ya ara miki rana ya baki rayuwa domin ki san inda kika kuskure amma Saddiqan tunanin ki kenan har a yau?kaico".
Cike da kumfar baki ta nuna ta da yatsa.
"Naci kan bura ubanki dake da abun da kika haifa,Ni zaki zo kina faɗawa Allah?Tunda kika ga na rayu Allah na yasan tsakanina dake bata ƙare ba shi yasa na rayu dan na kashe ki,kuma wallahi indai ina raye sai naga bayan ki da duk wani abu da Bukar ya ke taƙama da shi,menene ƙarshe ace zan mutu na shiga wuta ko?to indai Bukatata zata biya a duniya na shirya nutso tare da shedan"(wa'iyazubillah 😭 Allah kamana tsari da ayyuka makamantan na yan wuta,Ya Allah kada ka bari mu ga koda irin wutar jahannama ne ameen).
Baki ɗayansu sukayi haɗaka wajen furta "innalillahi waina ilaihir rajiun "har da Khalid wanda shigowarsa kenan,cike da tashin hankali ya zo gaban ta ya kama hannu ta dake free yana kuka.
"Amah wutar jahannama kike wa kanki fata?kina kallo nan ga Ummu ga Nafisa kamata yayi kin nemi yafiyar su tunda suka baki dama amma kike faɗan Abu mafi muni daga bakin ki?"
Hannun sa ta buge da ƙarfi.
"Sai mene idan naje wuta?ba abin da kowa ke faɗa ba ,Nima nasan na aikata aikin yan wutan ta abarni mana".
"Amah kin aikata ,amma yafiyar Ubangiji da waɗanda kika zalunta ya kamata ,ga Ummu nan tazo ta baki dama nefa ki nemawa kanki sassauci,ga nan Nafisa kin Cutar da ita fiye da kowa,ask for forgiveness koda akan gwiwanki ne,wannan dama Allah ya baki ki gyara".
Ya faɗa hawaye na bi masa kuncinsa domin duk inda lalacewa ta kai ,duk yarda girman abin da ta aikata suke mahaifiyar sa ce baya mata mugun fata.
Kallan sa tayi na wani lokaci kamar zata yi mubaya'a kafin ta hakaɗe hannunsa da ƙarfi tace.""idan ka zabi Hadiza ne Khalid kaje kada ka sake zuwa koda inda nake, mene iyakacin ku ƙi yafe mun dan na haife ku da boka ,to sai mene?hanyar samun ku bata dameni ba muddin zaku zama silar samun abin da nake mafarki,inace na muku ƙokari?i was there ,I was the rich mother da kowa zai so,na barku kuyi abin da kuke so da rayuwar ku so mene kuke so?"
Nuna Ummu tayi da yatsa.
"Wannan?wannan bazan taɓa durƙusa mata ba,mijinta kuma har abada baza ta sake ganin sa ba,ki fara irga ranakun takaba,idan ban sameshi ba kema wallahi kin rasa ,muddin kuma ina numfashi sai na farauci rayuwar ku koda zan dawwama ina tara shegun yara."
Dariya ta saka kafin kuma ta fashe da kuka tana mai cewa"my Little Baby Halisa,ita kaɗai na haifa da Bukar wadda nake tunanin zata zamar mun komai nawa , although babu wanda nayi niyar sanarwa da cewa sauran yaran ba nasa bane Bafa,but wadda na ɗauka dearly na riƙe sai tazo ta tafi,how dare you Hadiza how dare you ki zama kece mai yara da Bukar yara har nawa?I can't stand it ,idea ɗin kawai sawa yake naji kamar zan mutu,sai kuma dan tsabagen san zuciya kice na bar ki kiji daɗi?wallahi uwar da ta haife ki ma tayi mugun kaɗan,ki jirani kaɗan na fita daga rikicin da nake ".
Juyawa Khalid yayi ya fita a ɗakin yana kuka ,ya kasa yarda da duk wani abu da kunnuwansa suka jiye masa,ji yake kamar ya gudu ya tafi chan wani gari mai nisa inda babu wanda zai kuma jin labarinsa har ya ƙare rayuwarsa .
Rashin abin faɗa ko wannen su yayi karma Nafisa da ta shigo da batu kala kala,amma jin maganganun jahilci daga bakin Amah sai ta tsinci kanta rasa duk wani abu da ta ƙunso a bakinta baya ga.
"Duk abin da kika shuka sai kin girba,ki bar ganin kinyi Nasara na makance ke taki faɗuwar kenan,ki duba gefe da gefe mene kike dashi a yanzu bayan hannu da Handcuffs bakin ɗaki dauke da jami'an tsaro dake jira suyi gaba dake zuwa ɗakin da baki taɓa sawa a ranki zaki je ba,yar uwarki na chan tana jiran ki ku girbi abin da kuka shuka,Allah ya Ji dake kamar yarda ya dace dake".
Da taimakon Sandarta ta samu ta juya yayin da Ummu tayi saurin kamata tana mai ce mata ta bari ta kama ta su fita,haka suka juya baki ɗayan su suka fita,zama Hajiya Saddiqa tayi kan gadonta ta fashe da wani irin kuka tana mai jin mugun baƙin cikin rashin nasararta ,duk da abin da ya samu Nafisa bata gamsu ba,so take ya zamana komai ya ƙare musu,so take ace Ita da uwarta sunyi mutuwar wulaƙanci ta yarda dukkan dangin su kowa zai rasa nutsuwa ya shiga cikin mugun tashin hankali,amma kash sai Komai ya dawo kanta,daɗi guda wanda take ji shine salwantar da Alhaji Bukar da tayi cos kafin ta saka ya bar ƙasar ta ringa feeding ɗinsa silent poison da kaɗan da kaɗan wanda zai kashesa slowly,babu ɗogon dana sani a tattare da ita domin koda yau za'a sake bata chance zata yi ƙoƙarin taga bata bar ɓarakar da zata saka wani a ɗakin Hajiya Hadiza tsira ba.
A ranar aka bawa ya sanda ita suka wuce da ita,Khalid na daga chan nesa yana kallo aka saka ta cikin mota aka yi gaba da ita,a wannan gaɓar yana mai sake bawa kansa tabbacin Amah kanta ta sani,da ace kuma za a bata zaɓi kanta zata zaɓa, tausayin kansa da na ƴar uwarsa ne ya cika masa ciki,yanzu ta ina zasu fara kamo bakin zaren cigaba da rayuwa?musamman ma shi dake waje bai san inda zai nufa ba,har gwanda Khafilat tasan ina ta dosa dan prison ne sai taje,At least zai zamar mata wata katanga duk da bata san abin da zata tarar a chan ɗin ba.
Koda suka isa station ɗin inda aka saka Khafilat da Sakina aka watsa ta ,.
"Gashi nan kwa yi zumunci kafin ranar Monday kuje ku kalli alƙali cikin ido ya kalle ku"cewar police ɗin dake kulle gurin.
Bayan ya wuce ne hajja Sakina ta rarrafa gareta tana mai kama hannunta cike da damuwa idanu cike da ƙwalla.
"Yaya garin yaya muka ƙare a nan?,i can't die yaya ki san yarda zamu fita a nan,kina ji Alhaji yace ya sake ni har uku fa,sannan ya san Nana A'isha da Hashim ba nashi bane ,ina zasu saka kansu ni Sakina, gashi yan iskan yaran tunda aka kamani suka gudu,ko ubayen su na faɗa musu ai na mutu da sauƙi,Shi Hashim yaran Boka na gangare da muka Saba zuwa dake ne,Nana A'isha kuma ɗiyar wannan tsohon malamin na patiskum da ya taɓa buga mun ƙasa ne baiyi ba,na shiga uku yaya yanzu da baki ce a kashe Matar nan ta gidan marayu ba da tuni asirina rufe cikin ɗakina,amma ki kalla inda kika kaimu ".
Wani irin kallo Hajjiya Saddiqa ta bata kafin ta lailoya mata wani ashar tana mai cewa"Ni zaki ware wa kai?da nace a kashe su ubanki yasa ki yarda,ko kuwa a'a idan nace zo Sakina ki faɗa wuta zaki faɗa dan uwarki"
Take suka fara chachar baki wannan yace wannan,wannan yace wannan..Dariyar da Khafilat ta saka ya sa baki ɗayansu kallan ta,.
"Abun ba na mamaki bane ,two sisters with same mindset,wato duka yaranku yaran bokaye ne,ba abun mamaki bane da kuka zama sisters masu baƙar zuciya a tare ".
"Dan kutumar ubanki who caused all this? Wane ya tona mana asiri?gashi ai kema naki asirin ya tonu ,yar bura uba Shegiya,duk wahalar da nayi domin ku baku gani".Hajiya Saddiqa ta faɗa kamar zata shaƙe Khafilat.
Tashi tayi ta nufa bakin cell ɗin tana mai kallan waje kafin ta juyo ta kallesu tana mai cewa"Bazan je kotu ba ballantana na mutu,bazan mutu ba sai Hadiza ta mutu tukunna."
Xx
Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top