35

womenofwords/WA

🔏NOT ALL GLITTERS ARE GOLD💫

(BA DUK KYALLI BANE GWAL)✨

     Be with 👇

*𝐴𝑊𝐸-𝐼𝑁𝑆𝑃𝐼𝑅𝐼𝑁𝐺 𝐼𝑁𝐾🥌*

Tagwayen tafiya Mai sihirtattaciyar Ma'ana ta ban Mamaki daga jerin Tawwada d'aya Al-'kalami biyu first series.

*LOKACI.!*

Halish Sultan.

*BA DUK 'KYALLI BANE GWAL.!*

Amina Jamil Adam (Chuchu jay)

https://whatsapp.com/channel/0029VaRpQeUHwXb52H0abb05

Ga masu nema daga farko

Chapter 35

    Duk wani abu da Hajiya Saddiqa bata taɓa tunanin wani zai saka hannunsa a kai ba bincike sai da yabi ta kai,gidajen Karuwanta Goma ,yayin da Ɓoyayyan mansion da take harƙallarta guda ɗaya wanda nan suke aje Yan mata da yaran da suka sata domin yin Harvesting musu Organs ko kuma su siyar dasu, warehouse ɗinta da take adana kayan business ɗin ta nan aka kama store guda na kayan maye,within 48 hours komai nata ya shiga ƙarkashin Hukuma,a yara mata da aka ƙubutar sun kai kimanin mutum talatin,maza ashirin,yayin da yaran da take sakawa karuwanci Sai da akayi detaining mutum goma sha biyar, ajiyayyu waɗan da basu shiga harka ba saboda taurin kai mutum biyar harda Safiyya wadda ta galabaita iya galabaita duk da cewa it's ajiyarta hajiya Saddiqa ta bayar da sunan kafin ta dawo.

Cikin su idan kana da detail na yan uwa zaka Bayar a shaida musu halin da kake ciki,duk da kunyar Akram da Safiyyah take haka nan ta bayar da numbern sa duba da shi kadai take da,. fitowar su kenan shi da sultan da Jamal zasu je asibiti a rana ta uku wayarsa ta hau Kara,duba mai kiran sa yayi,ya sha mamaki ganin officer din da sukayi exchanging number ranar da aka Kama Hajiya Sakina akan zasu nemesa idan da damuwa duk da kuwa ya fada musu Either su Kira mijinta ko yaranta.

Kamar ba zai daga ba da fari sai Kuma ya chanza zuciya ya daga bakinsa dauke da sallama,amsa masa yayi daga dayan bangaren kafin ya Kara da cewa.

"Malam Akram mun sake kiran ka dai ,idan babu damuwa muna San ganin ka a station Mana".

"Yallabai indai akan matar da kuka Kamane bana tunanin Ina da hurumi da ita".

"Eh to gaskiya ba kanta bane wata maganar ce daban dangane da matan da muka kamo daga gidan karuwan ita Babbar Criminal din,to sai ya zamana ɗaya daga cikin su ta bada layin ka shi yasa muke bukatar ka".

Yayi mamaki amma sai bai tsaya neman wani Karin bayani ba yace yana zuwa, Bayan ya kashe wayar ne yake kallan su Wanda suma din shi suke kallo jin maganar da yake Dan haka ya fada musu abin da yake faruwa.

"So mu fara zuwa chan Mana"Salman ya faɗa Yana mai buɗe bayan mota ya shiga".

Wani irin kallo Akram ya bashi ganin abin da yayi kafin yace wani Abu Jamal ma ya bude bangaren mai zaman banza ya shiga, duƙawa yayi yana mai cewa"Yan uwana ban gane mai kuke nufi ba,Kai ka koma baya ka harde, Kai Kuma ka shiga gefen mai zaman banza ,shin wane zai shiga gurin driver,abeg make una make me understand dan na Bata batt".

Dariya suka saka a tare inda Jamal ke cewa.

"Ni dama ban iya mota ba ,dama dai Bike ne yauwa daga nan har birnin sin so count me out in dai ba wai duniyar ce ta ishe ku ba".

"Uhum Kai kuma fa oga sir mene uzirinka?"

Akram ya mayar da tambayarsa ga Salman Wanda ke aikin gumtse dariyar dake san sake kwace mishi,ya sani sarai Akram har yanzu Bai kware da tuki ba.

Ganin yaki amsa shi ya mayar ma da hankalinsa kan wayarsa yasa yayi kwafa Yana mai kallan Jamal Yana fadin.

"Idan na kashe ku jininka Yana hannun wannan Dan iskan na Baya".

"Point of correction,Naga kanka Yana kokari barin gangar jikin ka,ka fa iya bakin ka dan daga ni har Jamal babu sa an ka ,kada ka manta kanwar mu kake so ,wallahi ka shiga hankalin ka".

Kallan window yayi ganin irin Expression din Akram dake ji Kamar yayi masa dan iskan duka.

Bai sake fadin wani Abu ba ya shiga driver seat ya yi wa motar key yana tunanin ta yarda zai ciwa Salman.

Station din suka fara zuwa, a tare suka shiga office din Officer din su ukun,bayan sun zauna sun gaisa ne yake tambayar jikin Nafisa sannan ya Kara da.

"Wallahi wannan matar Saddiqa Bata da Imani ko kadan,Nasha ganin azzaluman mutane amma kaga wannan ,ita ce babbar shaɗaniya dana taɓa cin Karo da".

"Ai gashi chan Tana girbar abin da ta shuka ,har yanzu babu Wanda ya san ina ta dosa ,ballantana ma asan halin da take ciki,Kuma wallahi ba shine zai hana Tana warkewa mu gurfanar da ita ba". ɗaya jami'in tsaron ya faɗa a kufule da Hajjaju uwar Khaffy da Khalid.

Su dai su Akram babu wanda ya tofa albarkacin bakin sa Dan da ace wani daga cikinsu zai bude baki sai kowa ya razana, Akram ne yayi kokarin katse su.

"officer sir ni kam wacece ta bada number na cikin Victims din nan cos abin ya bani mamaki musamman da ya kasance bani da wani da ya bata".

"Tace sunanta Safiyyah,Bari yanzu a kawo ta kilan kan gane ta idan ka ganta".

Da mamaki Salman ya ce"Safiyyah Kuma?tot kace min ta tafi ta maka lefting note?".

"Hmm baka san Makircin matar nan ba,kasan shekara nawa Tana mun wasa da hankali kan Jannah?,last da Naji abin da tayi mata ji nayi na rasa inda zan saka kaina naji dadi, that woman ko mene za a yi mata wallahi ba zai biya irin mugayen Sharrin da tayi ba"cewar Jamal.

Officern ke cigaba da alhinin abubuwan Yana Mai tuna lokacin da Jannah ke rubuta complain,wannan matar ai ya tabbata koda ta rayu alkali hukuncin kisa zai yanke mata babu wani tunani.

  Koda Safiyyah ta shigo babu wanda Bai ji tsoran ganin yarda ta koma ba har Jamal Wanda a yau yake saninta ,idanun ta na sauka Kan Akram ta fashe da wani irin kuka Mai tsuma zuciya kari Kuma da dana sanin Abubuwan da suka hadu guri guda suka Mata tsaye,babu Wanda ya ce da ita komai cikin su cike cike kawai sukayi bayan tabbatar da sun santa kafin aka basu ita.

Sun fito da zummar wucewa inda Officer din ke sake tambayar Akram ba zai ga Hajiya Sakina ba, kafin ya bashi amsa Yan sanda suka shigo da Uncle Saleh da wasu maza guda biyu Yana ta aikin bala'in mene yayi da zasu kamasa duk da kuwa yasan abin da ke faruwa.

Turus yayi ya bar kokawar lokacin da yaga Jamal,gurin sa ya nufa Yana mai cewa.

"Alhamdulillah,ai ya yaro na nan sanin kun je kun taho dani ya riga ku zuwa,Jamal ka basu bail papers,Allah na gode maka har na fara tunanin sauran da zan tarar".

"Aikuwa Uncle ka cigaba da tunanin sauran da zaka tarar,bayan Nan Kuma Ka fada tunanin makomar ka idan Alkali ya yanke maka hakunci, courtesy na karshe tsakanina da Kai shine kiran ka uncle da nayi yanzu,wallahi Kai ba Dan Adam bane,idan kana tunanin idan duk abin da kayi bana da masaniya then you're a fool and FYI,Ina nufin for your information nine na bada kararka bincike Kuma ya kawo ka Nan".

Har ya nufa hanyar fita ya tsinci Muryar Saleh na faɗin .

"Duk abin da na aikata ai ban kai mahaifinka ba."

Juyowa yayi yana kallansa kafin yayi murmushi yana mai cewa"da ace shima yana raye a yanzu ai ya karbi hukunci dai dai da abin a ya aikata,yanzu tunda ya riga mu tafiya Ni Ko kai babu wanda zai ce ga gaibu nan ya santa shari'arsa tana hannun ubangiji amma kai da kake raye yanzu ka fara girbar abin da ka shuka".yana kai karshen maganar sa ya fita su Akram suka bi bayan sa suna masu jin babu daɗi,.

Tunda suka dauki hanya babu wanda ya ce uffan ga Safiyyah, ko Salman dake baya tare da ita bai iya faɗa mata komai ba,kamar kuma an zingule sa sai cewa yayi"amma dai Safiyya hatta wanka basu barin ki kuyi ko?".

Kuka tasa lokaci guda kamar an ƙwaɗa Mata Mari,ganin haka yasa Akram dake tuki cewa.

"Mene haka Salman".

"Kada na tambaya kuma?ko ina Yana oozing sai ace nayi shiru,na me and Safiyyah dey this back oo,kada kasa nayi sounding like a bad person ni da kai mun san akwai dalilin da yasa Safiyyah shiga cikin wannan halin,ni a yarda nasa Safiyyah definitely she bite more than she can chew Wanda shi ya kawo mu yau".

Ƙaramun tsaki Akram yayi kafin yace"mun ji,ki daina wannan kukan dan Allah Safiyya kafin ayi tunanin mun sato ki ne Kinga mun kusa check point".

Cikin kuka take cewa."i deserved duk abin da ya dameni,I'm a very bad person Dan Allah Akram ka yafe mun,and kamar yarda Salman ya faɗa Ni na jawa kaina da na nuna interest kan Dad ɗin ka , naso ya Aure Ni saboda kuɗin sa and i wanted to chase matar sa da yaransa,I'm being honest with you har kai banyi niyyar sparing ba,and I confronted Hajiya Sakina washe kawai na tashi na ganni gidan ƙaruwai,wallahi I've learnt a lesson Kuma nayi nadama".sake fashewa tayi da kuka.

"Ahap I said it!I said it,Idan ba san zuciya ba mene zai kai ki tunanin Auren Daddyn Akram har ki fara tunanin tarwatsa masa gida ,kalli nan Saffiyya someone needs to tell you the truth,Akram shine mutum na farko da ya fara Miki karamci,this guy was there for you,babu abinda kike nema gurin sa ya gagara Miki, he's always there babu abin da kike nema ya gagara Miki,You even tie this guy with a year promise and he fulfill kafin ki fara nuna masa ɗabi'ar banza ,and bayan nan fa bai tsaya ba bayan kin masa tuban karya ya ɗauke ki ya kai gidan su duk da kashedin da na masa sanin halayyarki amma da yake shi mutumin kirki ne da ya ɗauke ki yar uwarsa bai ji ba,lastly kika so tarwatsa masa rayuwa, you're very Evil wallahi Saffiya and abin da ya same ki serves you right ".

"I know Salman and nayi dana sani,wallahi wannan karan da gaske nake nayi nadama cos abin da na gani baki ba zai iya lissafa shi ba,babu irin duka da ban sha ba,ga yunwa,ruwa kawai nake sha shima cikin cokalin Hudu idan na sunga dama ne ake karan ɗaya ya zama biyar,zuwan mu station ɗin nan ne suka bamu abinci".

"Aikuwa gashi ya nuna a jikin ki,wannan da kinyi wata gawar ki ma baza a gane ba"Salman ya sake faɗa yana mai mayar da hankalinsa kan wayar sa.

Shi dai Akram bai ce komai ba haka zalika Jamal wanda shima ke ganin rashin kyautawar Safiyyah,koda suka je asibiti tare suka tarar da Nafisa da Ummu suna hira Nafisa na dariya kadan kadan ,yayin da Saimah ke bata abinci baki saboda drip ɗin da aka saka Mata.

Koda suka sanar da Ummu Abin da ya samu Safiyyah bata nuna mata ba ko a fuska illa ma tausayin ta da taji a cewar ta kuskure ne na ƙuruciya,kasancewar zata tafi gida taje tayi wanka yasa tace Jannah ta zauna zata je da Safiyya gida tayi wanka taci abinci .

"Aikuwa ya kamata dan dakin nan wallahi har ya fara chanza yanayi".Salman ya faɗa .

Kallansa Ummu tayi tace"ya isa Salman idan baka tausaya mata ba baza ka musguna mata ba,maza kazo ka kaimu gida.

Dan turus yayi kafin yace."Ummu dan Allah Sultan yaje ni Kinga yanzu nazo ina san ganawa da yar kanwata".

Bata tilasta sa ba ta saka Sultan ya kaisu.

Sosai halin da Safiyyah taga Nafisa ya tsorata ta,duk da kuwa taji kishinta duba da yarda rundunar danginta ke kanta.

*******************

    Wai shin wane hali Hajiya Saddiqa take a yanzu?

Anyi mata aikin da aka cire karfen dake jikin ta duk wani abu da ya kamata a bata Medically anyi amma har a lokacin bata farka ba amma numfashi yana nan tattare da ita,abin da ke bawa likitan Tsoro shine yarda ga dai komai yayi amma she's still unconscious..

Khalid dake zuwa duba ta ne ya kalli Nanny Muna yace"wai ni Muna yaushe Amah zata farka ne,ni duk abin nan ya dameni bana da nutsuwa,bangare guda ina tunanin Khafilat gefe guda kuma hankalina na nan,ban san ya akayi family ɗin mu ya watse haka ba,i can't Believe har Aunty Sakina na da sa hannu a abun da Amah take,abun takaicin kuma shine yarda yaranta duka suka gudu suka ƙi tsayawa,Daddyn Akram kuma an kira sa yace shi ba mijinta bane dan yana samun labarin an kamata ya turo mata da tarakdarta cikin envelope, dukkan wani tie ya yanke da ita har yaranta wanda ya tabbatar da ba nashi bane...

A/N

Nace shin su kuma su Hashim yaran wane jama'a?

Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top