34

womenofwords/WA

🔏NOT ALL GLITTERS ARE GOLD💫

(BA DUK KYALLI BANE GWAL)✨

     Be with 👇

*𝐴𝑊𝐸-𝐼𝑁𝑆𝑃𝐼𝑅𝐼𝑁𝐺 𝐼𝑁𝐾🥌*

Tagwayen tafiya Mai sihirtattaciyar Ma'ana ta ban Mamaki daga jerin Tawwada d'aya Al-'kalami biyu first series.

*LOKACI.!*

Halish Sultan.

*BA DUK 'KYALLI BANE GWAL.!*

Amina Jamil Adam (Chuchu jay)
Chapter 34

    Bayan an saka Nafisa cikin ambulance ɗaya daga cikin Nurses ɗin da suka zo ta nufi gurin Hajiya Saddiqa dan feeling pulse ɗin ta duk da kuwa kowa ya saka ran ta mutu duba da yarda Rodi ɗin ya fasa ta although gefen ciki ne,hannunta ta kama ta saka yatsunta guda biyu ta nutsu,jin weak pulse yasa ta kiran Wani Nurse da sauri tana mai faɗa masa akwai Pulse,ɗaya daga cikin jami'an tsaron ne yace "ko da akwai Pulse wannan ai ta gama yawo dama ƙyaleta kukayi ta ƙarasa muje muyi detaining gawarta ".

Kuka sosai Khafilat ta fashe dashi jin abin da ya faɗa Khalid yana mai lallashin ta,kula da ita da ɗayan yayi yasa salin alin ya Ciro handcuffs ɗin dake jikin wandosa ,bai ce komai ba ya ɓama mata a lokaci ta a kare da cewa she's on a run,kuka ta fashe da shi domin ba dan Amah ta haife ta ba babu abin da zai saka ta tsaya,duk wani abu da tayi masu mara kyau baya counting a wannan lokacin ,abu guda ɗaya ta sani wanda shine mahaifiyarsu na buƙatarsu.,da wata azabar gwara mutuwa haka kawai take ayyana wa a ranta dan tasan idan Allah ya bar Amah da rai ba ƙaramar azaba zata sha ba,a sanin ta kuma da ita muddin yau akace ta rayu Allah ya bata talala tayi imani da Allah baza ta chanza munanan Ayyukanta ba,idan kuma ta tafi a haka baki ɗayan su sun san babu sauran Rahma dan sa ran Rahma yana ga mutum mai Aikata Alheri duk da tsakanin bawa da Ubangijinsa wani baya shiga.

Baki ɗaya aka ƙwasheta da Rodin Aka ɗungunzuma Asibiti tare da yan sanda dan already Nafisa sun wuce,.Babu abin da Akram da Jamal suke a zuciyoyinsu baya ga Addu'a dan babu wanda karaya bata kawowa ziyara ba duk da yarda ɗaya daga cikin ma'aikata lafiyan ke basu Assurance na insha Allahu za'a kamo bakin zaren domin sun riga da sun bata taimakon gaggawa ,bayan isar su asibitin direct OR aka wuce da ita ,sunata aikin jeka ka dawo wani likita ya fito yana mai neman Family ɗin ta ,a tare suka haɗa baki wajen amsawa,Takarda ya nuna musu akan sai sun cike saboda zasu mata aiki wajen hana poising ɗin yaɗuwa dan a halin da ake ciki ya fara taɓa Hajinta,faɗuwa gaban Akram yayi  jin abin da likitan ke faɗi,A sanyaye ya ƙarbi takardar zai saka hannu,har ya dora pen akai ya maida kallonsa kan Jamal wanda kana kallon fuskarsa kasan shima cikin muguwar damuwa yake,Miƙa masa pen ɗin yayi akan ya saka hannu cos ya lura da yayi bankan-bankan a al'amarin Nafisa wanda hakan yana neman shatawa Jamal layi.

Kamar wanda laka ta fashewa haka ya karɓi Pen ɗin ya saka Hannu,then ya maida ga Doctor ɗin wanda ya karba ya koma ciki,.

"Na kira Familyn Nafisa na faɗa musu halin da take ciki,hope ban laifi ba,naga kamar ya kamata su sani duk da basu san su ɗin Family ɗinta bane ".

Takawa Akram yayi yaje ya zauna akan bench ɗin da ke gefe ,biyosa Jamal yayi shima ya zauna yana mai mayar da ajiyar zuciya.

"Ya kamata ace sun sani,Jamal ina jin farin ciki sosai da ya zamana Nafisa ta samu danginta na aynayi,wallahi naji daɗi sosai Fatana kawai shine ta tsallake wannan jarabawar cikin Aminci,ko kasan cewa koda tana yarinya bata taɓa kawo danginta a kanta ba cos ta tashi da wannan fushin na cewa sun banzantar da ita,ta gurin da mukayi kamanceceniya kenan,saɓanin fahimta,family ɗin Nafisa abin ka nuna ne dan mutanen kirki ne,Salman is my frnd and was my roommate saninsa ya tabbatar mun family ɗin sa mutanen kirki ne".

Goge ƴar ƙwallar dake kurmin idanunsa yayi yana mai kallan Jamal.

"Dan Adam baya iya tsara abu amma naso ace Big Mummy na raye taga Nafisa a yau ,ka manta da wahalar da tasha, ni bana ɗaukar wahalar da tasha wahala saboda ka tsaya mata har ta samu skills ɗin da take dashi a yanzu,babu irin godiyar da zan maka ta isa,I won't hide it gare ka,ina san Nafisa so mai girma tun ƙuruciya,I'm just hoping a zuciyar ka baka mata soyayyar namiji da mace dan Bazan iya maka wannan sadaukarwar ba duk da nasa zan fito a cikin mutane masu san zuciya ,ina san kulawa da Nafisa a wannan Karan kuma bana san competition ya shiga hanya ta,bani da wani abu mai amfani yanzu da ya wuce Nafisa."

Dafa kafaɗarsa Jamal yayi yana mai jin wani irin a zuciyarsa,yasan yana san Nafisa ba zai ƙarya ba dan a kanta ya fara sanin menene ma soyayyar,sun shaƙu ta yarda yake jinta kamar ahalinsa,bai taɓa planning faɗa mata ba saboda gudun ɓata abin da ke tsakaninsu,shi kansa yasan Akram ya dace da Nafisa ba shi ba domin baya da rayuwar da zai iya bata,a kullum fatan sa shine ta sami rayuwa wadda take so wato rayuwa mai inganci,da fara'arsa ya ce"wanene zai shiga tsakanin Nasifa da Boda Akram?,duk wani wanda zai san Nafisa tun yarinta da Boda Akram a bakinta ,no matter the distance Babu Wanda zai iya cire ka a rayuwar Nafisa kuma na gamsu da cewa kaine kaɗai zaka iya bawa Nafisa rayuwar da ya kamata a matsayin miji,so calm down ka ƙwantar da hankalinka kayi abin da yake wuyan ka,tsakanina da Nafisa Soyayyace irin ta yaya da ƙanwarsa ,dan har a raina ina jinta,but duk ranar da ka Sakata kuka ka shirya ƙarbar hukunci na,fatan mu yanzu shine lafiyarta".

"I'm scared "

"Don't be Akram nayi imani da Allah akan cewa zata cinye wannan jarabawar ".

    Bayan wani lokaci Akram ya hangi Salman da tawagar gidan su ,duk da basu san matsayin Nafisa garesu ba hakan bai hana su tahowa baki ɗaya ba lokacin da Jannah ta sanar da Ummu Nafisa na asibiti Hajiya Saddiqa tayi poisoning ɗin ta,Akram yaje ya taho dasu inda suke yayin da Ummu ke tambayarsa Nafisa cike da damuwa,sanar da ita tana operation Room har a lokacin yasa ta zauna jiki duk a sanyaye tana karanto dukkan wata addu'a da tazo zuciyarta,.

Dawowa kusa da ita Jamal yayi yana auna ta yarda zai fara sanar da Ummu dan ya kamata ace ta sani tun kafin Nafisan ta fito,nemo ƙwarin gwiwar fuskantarta yayi kafin ya ce."Ummu Ni'imah ba itace aynayin Ni'imah ba, wannan Jannah sunanta ,kuma ƙanwatace Hajiya Saddiqa ta kawo ta dole,Nafisa dake ɗakin chan a kwance itace Ni'imah addu'ar ki nada matukar Muhimmancin gareta a yanzu".

Da mamaki Saimah tace"Nafisa dai?so kana so kace ita Ya Ni'imah wannan spy ce?".

"Yanzu ba lokaci Bayani bane ,lokacin na yiwa Nafisa addu'a ne everything will be in place mu fara ganinta lafiya tukunna"cewar Sultan wanda baki ɗaya nutsuwa ta gagara zuwar masa .

Wani hawaye ke bin kuncin Umma kafin ta ke faɗin"tun ranar da jannah ta saka ƙafa gurina nasan ba Ni'imah ta bace,duk da cewa tun tana wata daya na rabu da ita amma zuciyata zata faɗa mun itace koda kuwa ina wasi wasi,nasan cewa Saddiqa ta aiko jannah amma ita ɗin yarinya ce mai hankali mai zuciya mai kyau shi yasa na jata jikina duk da nayi bakin ciki na rashin sanin Halin da Ni'ima take ,Tun ranar da na fara saka ido kan Nafisa naji wani abu da uwa kanji dangane da ɗanta,I felt it but I just don't know what to say or how to think,Ya Allah Protect this child and bless her with your miracles".Kuka ta fashe dashi a ƙarshen maganar ta wanda yasa Salman fara lallashinta sanin ba ƙaramin abu zai saka Ummu hawaye ba.

Bayan wasu awanni likitan ya fito biye da waɗanda suka mata aikin tare ,a tare dukkansu suka yi gurinsa suna tambayar Nafisa,

"In sha Allah surgery ɗin anyi Nasara,yanzu haka za a kaita ɗakin hutu ne ,zata kai 2 hour kafin tayi regaining conscious"likitan ya faɗa musu yana mai Umartar da wani yaje ya cike abubuwa dake necessary,baki ɗayan su haka suka zauna jiran tashin Nafisa yayin da Saimah ta koma gida dan kawo masu abinci ,.

Zaune Ummu ke gaban gadon Nafisa tana aikin Kallanta yayin da hannunta ke rike da na Nafisa guda,ita ta sani tuni yarda take jin Nafisa a zuciyarta ba wai kawai Irin soyayyar ɗan adam da ɗan adam bace ita tasan akwai wata daban duk da baza tace gata ba,tana tsaka da zantukan zuciys hannun Nafisa dake riƙe da nata yayi motsi,da sauri ta kalli hannun tana mai kiran sunanta gently,sake motsa hannun da tayi yasa Ummu tashi tsaye tana mai sake kiran sunanta , ƙoƙarin tashi Nafisa take tayi saurin komawa sakamakon ciwan da taji daga ƙasan cikinta ,buɗe idanunta tayi amma sai ya zama ta buɗesu ne cikin duhu dan haka tace"dan Allah a kunna haske duhu".

"duhu kuma Nafisa ?"Ummu ta faɗa hankalinta tashe ganin a lokacin duk da gari ya fara duhu amma ɗakin kamar rana ,ganin hakan yasa ta fita ta ce da ɗaya daga cikin su yaje ya kira likita Nafisa ta tashi tana ganin duhu,baki ɗaya sukayi ƙoƙarin shiga ɗakin suna masu maida maganar duhu kuma , Salman ne yayi karfin halin zuwa kiran doctor ,. Bayan shigar su kowa da tambayar da yake mata, jin muryoyinsu baki ɗaya yasa ta fashewa da kuka tana mai faɗin "i don't want to lose my eyes,dan Allah Ku kunna fitila,bana san duhun nan,bana san na zama makaunyi lokacin da nake buƙàtar ido fiye da ko wanne lokaci,ina san na kalli Family ɗina,I want to look at my Ummu, please I don't want to get blind ".

Kuka kawai Ummu ta fashe dashi Samrat dake gefenta tana taya ta,su kansu mazan ƙarfin hali ya hana su zama su ta rusa kukan,rungume ta Ummu tayi tana mai kasa faɗin komai tausayin Nafisan ya cika mata ciki ,.shigowar likitan yasa baki ɗayan su fita,bayan ya duba lafiyar idanun ya gano tayi losing sight ɗinta ne,dan haka ya fito jikinsa a sanyaye ya nemi magana da mahaifinta ,kafin kowa ya bashi Amsa Ummu ta bisa sanin hankalinta ba zai taɓa ƙwanciya ba muddin ba ita ta bisa ba yayin da mazan suka shiga gurin Nafisa wadda a lokacin ta koma ta ƙwanta ta rufe idanunta kamar mai bacci.

    Bayan isar Ummu da Likitan Office ɗin sa ne yake mai shaida mata Gubar ta taɓa mata idanu amma baya ga wanann babu wani complication.

"Likita makanta Complication ce mana ,yanzu babu wani abu da za a iya yi?"Ummu ta tambaya cike da karyewar zuciya.

Aje pen ɗin dake hannunsa yayi "Gaskiya Hajiya bana tunanin akwai wani abu da za a iya yi ɗan already idanunta sun zama damage duba da ta ɗauki lokaci da wannan Gubar a jikinta ,amma zamu gwada duk da ba zance ga Assurance ba".

Godiya kawai ta iya masa ta fita ,bakin Office ɗin ta tsaya tana mai jin wani irin hawaye na zubo mata,a hankali taji ƙafafunta sun kasa ɗaukarta dan haka ta silale ta durƙusa tana mai ambaton Allah da yi masa godiya da ya bar Nafisa da rayuwa,duk da cewa abin da wahalar ɗauka amma abin ka godewa Ubangiji ne a duk halin da ka tsinci kanka,.Sai da taji nutsuwa ta ɗanzo mata kafin ta koma ɗakin lokacin Saimah ta dawo,baki ɗayan su suke san sanin Abin da likita ya faɗa dan haka bata boye musu ba ta faɗa har ga Nafisan tana ji, kujerar dake bakin gadon ta zauna tana mai kiran sunanta.

Bata amsa ta ba amma tana jinta dan haka ta fara bata baki inda take faɗin"nasan dai ke musulumace Nafisa and komai ya faru da bawa ƙaddararsa ce ,sai mu gode masa ya taƙaita ya rangwanta miki,doctor yace da kin kara Awa guda ba a kawo ki asibiti ba hatta aikin da suka Miki bazai iyu ba,sun tsayar da spreading ɗin Gubar sannan sun yanke hanjin da ya taɓo an dasa,aikin ki yayi kyau babu complications sannan sun ce zasu duba idan da abin da zasu ma idanunki,idan ma ba suyi ba zamu samu wata hanyar Insha Allah idan idanunki masu buɗewane zasu buɗe ,kiyi haƙuri Nafisa kada ki saka wannan a ranki abin farin cikin guda ɗaya ne ,we are all here for you,me Salman,Sultan , Saimah,Samrat,kalla ga Nan Jamal,ga Akram ga jannah,we are one family and zamu tsaya tare har iyakar rayuwar mu Insha Allah,dan Allah kada ki bari wannan ƙaddarar ta zamar Miki sanadin shiga wata cutar,indai Saddiqa ce cutar da ta miki zata girbeta babu barin koda gefe ɗaya.

Cikin kuka ta ce"Ummu abin da ta mun bai kai wanda ta yiwa Jannah ba,that woman ta kashe masu iyaye ta saceta ,ta kaita ta siyar she was raped over and over again ,after that ta cire mata ƙoda ,idan har ta tsira bayan abin da ta mun ta sha da yawa Ummu"

Buɗe baki Ummu tayi jin abin da ta faɗa dangane da jannah,Kallanta ta mayar gare ta ,saurin sunkuyar da kai ƙasa tayi hawaye na bin kuncinta dan tuna Wannan mummunar rayuwar da ta fuskanta kawai abu ne mai nauyi, alamu Ummu tayi mata da hannu kan tazo,babu musu tazo cos a zaman da tayi da Ummu she felt that warmth of a mother,ganin hawaye a idanun Ummu yasa ta rushe da kuka, jawota Ummu tayi ta rungume tana mai shafa mata baya a hankali.

"I'm sorry Jannah ban San abin da kika yi facing kenan ba I would have treat you better,I'm sorry Amma Ina so ki sani daga yau zan zamar Miki mahaifiyar da baki da ,daga ke har Jamal daga yau ina san ku ɗauke ni uwa su Salman yan uwanku,we are going to live together as one family,and Insha Allahu we will be happy".

Ummu bata sake firgita da Saddiqa ba sai da ta ji labarin abubuwan da ya faru kaf,tasan Saddiqa bata da imani amma ba tayi tunanin rashin imanin ta ya kai ƙololuwa har haka ba,amma a yanzu ko haka aka barta ai tana cikin azaba.

Suna wannan zaman ɗan sanda guda ya shigo akan yana san ganin Akram,bai masa musu ba ya bisa,gurin ogan su ya kaisa inda yake tambayar sa yarda zasu Samu Sakina dan a binciken da sukayi sun ji yana da alaka da ita,baiyyi mamaki ba dan haka yace dasu tana hanya sanin cewa duk abin da ya samu Hajiya Saddiqa baza ta taɓa nannaɗe hannayenta ba sai ta zo,ille kuwa bayan wasu lokuta ta shigo ward ɗin kamar wata zarrar tana mai ɗaura dan kwalinta da yake kuncewa Nana A'ishah na biye da hannunta riƙe da jakarta Hashim kuma da warin takalmin ta ,kuka kawai take tana faɗin ta shiga uku dan a bayanin da Khafilat ta bata ta ce mata kamar Saddiqa ta mutu,kallan Hashim tayi tana mai basa umarni da ya kira wayar khafilat suji ɗakin da take,turus tayi ganin Akram tsaye gefen sa yan sanda,yan sandan na ganin ta suka gane ta ɗan suna da details nata,juyawa Akram yayi yana mai cewa officer ɗin "yallabai dan Allah kada ayi ram da ita a bari ta fara ganawa da yar uwarta".

"Ai yar uwar tana nan har yanzu babu wanda yasan halin da take ciki dan ba a shiga ma inda take ,kai dai bari yarda ta shigo tarkon nan mu ɓame ta".

Ganin sun nufo inda take yasa ta fara ja da baya duk da kuwa tasan bata da laifin da zasu kamata amma a rayuwarta ta tsani yan sanda ,inda kuma aka samu matsala bata san aynayin abin da ya kawo Hajiya Saddiqa asibiti ba.

Mace daga cikin yan sanda ce tayi zafin Nama waje kamo hannunta tana mai saka mata handcuff tare da faɗin "you're under arrest ,for murder, kidnapping, conspiracy and other illegal crimes,you have the right to remain silent because everything you do or say can be testify against you in the court of law ".

08130229878.

Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top