33

    Ja da baya Khalid ya fara yana mai kaɗa kai lokaci guda idanun sa na kawo ruwa,sakin baki tayi tana kallon sa cike da Mamaki.

"Me kake nufi Khalid?kana san ka watsa mun ƙasa a ido ne?,ina so ka sani duk duniya baka da gatan da ya wuce nawa,dan haka ko kayi abun da na saka ka ko kana ji kana kallo zaka mutu."

"Amma Amah a yarda kike faɗa yanzu Nafisa ƙanwa tace, nasan Ni ba na kirki bane ,ba kullum nake Sallar ba,i smoke,I get high,ina ɗauka Miki kuɗi ba tare da saninki ba amma nasan cewa Raping Nafisa ba abu bane mai kyau,ba zan ƙaryata ba akan cewa nayi sha'awarta,amma a lokacin bansan wacece ba,yanzu Kuma da nasani Bazan iya commiting abin da yafi karfin na bayana ba,Amah I can't ,ki rabu da ita,tana buƙatar ganin Doctor"..

Wani mari ta ɗaukesa da shi wanda ya saka ya kusa tuntsirawa,nunasa tayi da yatsa"You ungrateful human being,na haifeka ,i clothe You,fed you, schooled you,na baka rayuwa mai kyau,ka faɗa mun abin da useless mahaifinka ya taɓa maka ,yanzu dan ina san aran jikinka domin cimma burina zaka mun rashin biyayya,Kalli nan Khalid,duk abin nan dake faruwa uwarta ce sila,asiri tayi muku kai da Khafilat kuka shiga halin da kuke ciki yanzu ,ko baka gani,dole ne ka ɗauki fansa,idan kai baza ka iya ba ni zan ɗauka kuma babu wanda ya isa ya hana ni, duk asirin da Hadiza take muku baka gani ko?"

"Ko kuma wanda kike masu ya dawo kan mu ba,Amah na san reputation ɗin ki da kuɗinki ya fi Miki komai a rayuwa,da za'ace ki zaɓemu ni da Khafilat kan ki za ki zaɓa, you're selfish and greedy Dan haka babu abin da zan sake yi wanda yake ba daidai ba,can you even hear your self ?Ina ɗan ki wanda yake helpless,dying amma ke ta fansa kike,Amah I'm dying for God sake a matsayinki na mahaifiyarta wannan ba shine abin da ya kamata kina tunani a kai ba,Khafilat na chan a kulle Kinsan kuma prison zata dole ,ni gani nan I'm dying amma tunanin ki nayi raping Nafisa?kina saurarar conscience ɗinki kuwa?that is Idan kina dashi".

Wata irin dariya mai azaba Nafisa ta saka,duk yarda ta ke jin Bala'in ciwan kai kamar zai dare haka tayi ƙoƙarin wajen ganin ta buɗe idanunta domin ganin Hajiya Saddiqa a hali na faɗuwa,.wani irin mari Hajiya Saddiqa ta ɗauke ta dashi kafin ta kama tufkar gashinta ta damƙe da ƙarfi tace"akwai abin da ban faɗa Miki ba wanda ya kamata ki sani,waccan tsohuwar mattaciyar dake ƙasa nice na saka aka ƙone mun ita har lahira so I can do more evil than you never imagine".

Dariya Nafisa ta sake sakawa kafin ta furta"na sani,kuma zaki biya,ko kina tunanin duk abin da kike ke kaɗai kike sane dasu,i know exactly who you are ,nasan cewa ke drug dealer ce,kina Harvesting Organs ɗin mutane,baki da imani,ke muguwa ce, azzaluma ce,kina cinikayyar ɗan adam,ga garkuwa da mutane kina Safarar su,nasan duk wani abu da kika yiwa Jannah,ta dade da daina miki aiki,and guess what ita da ƴaƴanta Jamal sunyi reuniting kece dai Fool a cikin wasan,nasan cewa kina da gidan ƙaruwai wanda kike sato yara kina forcing ɗin su dan ki samu kuɗi,amma akwai ƙarin abu wanda na sani baki sani ba,ki manta da cewa kin yi poisoning ɗina,ban damu da na mutu ba muddin burina zai cika,ke ga yaranki ma baki da imani,kina tunanin ban san cewa San fitar da khafilat da kike ta haukan yi ba dan kada sunanki ya lalace bane,yanzu kuma kina san using helpless yaranki da ya kamata ace kulawarki ce gaban sa ,lokacin da suke buƙatar ki ke wani abu daban ke gabanki saboda baki da imani,kuma a haka kike kiran kankii mutum ɗan Adam,kuma uwa,shame on you,you disgust me"yawo ta tofa mata a fuska da ta kai ƙarshen zancenta ,a fusace Hajiya Saddiqa ta fara marinta tana cewa sai ta kashe ta.

"Amah!! ".

Juyawa tayi tana mai sakin Nafisa jin Muryar Khafilat,da sauri ta isa gare ta tana mai ambatar sunanta tare da kokarin kai hannunta fuskarta,buge hannu khafilat tayi idanunta cike da hawaye Kafun tace"a maganar Nafisa wanene ba gaskiya ba,amfani kawai kike yi damu You dont even regard us ,I mean Mai yasa zakiyi regarding ɗin mu bayan hanyar da kika same mu ma ƙazama ce,Shin kinsan mafarin lalacewa ta?ba komai bane sai da na tsinci maganarki a waya da bokan da kike zuwa kina ƙwana dashi dan ya biya Miki bukata,har gobe na kasa yarda ni da Khalid ba yaran babanmu bane,Amah me kike nemah da baki dashi da har zaki haife mu da mutum wanda yafi kowa ƙazanta,boka fa?duk yarda naso na boye damuwata nayi dan nima bana so yau a wayi gari ace mu yan Zina ne kuma babanmu Boka ne,I started smoking Weed , Amah har Cult na shiga but you Never care,Baki damu da cewa Muna yin abubuwa mara sa kyau ba all You care about is money and Fame,ya Kike tunanin zamu rayu da batun wani Shege shine uban mu,?duk lalacewar mu muna so muma yau muna da uba na gari  komai lalacewarsa,i don't care about Nafisa cos I never like her and I will never do Abu Guda ɗaya na yarda dashi wanda shine i will expose you,I'm taking you down with me Amah,shine dalilin da yasa na gudo daga Station,ja da baya ta fara Khafilat na ja da baya,hannayenta biyu ta ɗaga tana mai faɗin"Baby we can sort this out,wallahi na damu da ku, kune rayuwata ,komai kuma inayi ne domin ku,i will do anything domin Bukar ya karbeku, ya so ku fiye da kowa, babu wanda yasan maganar nan ,daga Ni sai ke sai Khalid sai Nafisa and she's dying, she's going to die ,she have to die,Amma mu zamu rayu tare babu wanda zai san sirrin nan, it's a mistake idan kuka rufa min asiri nima zan rufa muku."

"Indeed "shine kawai abin da Khalid ya iya furtawa ya fita a gurin Khafilat ta mara masa baya,da gudu Hajiya Saddiqa ta bisu tana mai san dole sai ta ƙwace abin da ta gani hannun Khafilat dan ko ba'a faɗa mata ba tasan yana da nasaba da faɗin da take na zata kaita ƙasa which she can't risk,Ganin tayo kanta da gudu zata ƙwaci abin yasa Khafilat saurin Matsawa inda hakan yayi daidai da taka kataƙon da Hajiya Saddiqa ta yi, kafin ƙiftawar ido ta zame ta faɗa ta gefen ginin da baya da tsayi kasancewar gurin Rooftop ,wani irin ihu suka saka baki ɗayansu a tare inda itama ta ƙwantsama wani irin ihu ganin tana faɗowa daga saman Rooftop ɗin gini mai hawa Uku,kamar ka ɗauki abu ka jefar haka al'amarin ya faru,kan wani fiƙakken rodi dake ƙasan gurin ta faɗa wanda ya ɓulamata bayanta ya fasa zuwa cikinta,a take komai dake gurin ya tsaya chak,bata koda sake shurawa ba,wani irin ƙuruƙuruwar ihu Khafilat da Khalid suke ,inda a tare suka nemi hanyar sauka ƙasan,. a yarda abun ya faru kamar ka rufe idanunka ka buɗe.

Faɗawarta yayi dai dai da Isowar Jami'an tsaro da Jamal da Akram,duk wani abin da ke faruwa suna jin ta camera ɗin da ke jikin Nafisa,tashin Hankalin da Akram da Jamal suka shiga ba ƙarami bane musamman da sukaji maganar da Hajiya Saddiqa keyi na poisoning ɗin Nafisa ga kuma demand ɗin ta na Khalid yayi Raping ɗin ta,tun a motar Akram ke kuka yana mai blaming Jamal da ya barta taje, Muddin abu indai kan Nafisa ne baya da wata Jaruma,shi kansa Jamal ɗin wani irin dana sanin amince mata ne ya fara dawo masa,da ace zai ji kukan shima yi zaiyyi amma zuciyarsa ta ƙafe ta hanyar da kuka suka barranta.

Cikin su babu wanda ya tsaya bi ta kan wata Hajiya Saddiqa suka Nufi inda suka ga Khalid da Khafilat sun fito ,a yarda suka ga Nafisa cikin halin da bata san ina take ba shine babban abin da ya tada musu hankali kada ma ace Akram da ke jin wani irin karayar zuciya,ya kasa yarda da irin ƙarfin rashin imanin Hajiya Saddiqa,jikinsa rawa kawai yake yana mai kallon Jamal yana mai faɗin"mene zamuyi?do something Jamal idan na rasa Nafisa zan iya mutuwa,i can't do without her do something Please"

Igiyar Jamal ya nufa ya fara kunce mata yana mai cewa she's going to be okay.ganin baki ɗaya jikinta ya saki yasa Akram saurin tare ta kafin ya ɗauketa a hannunsa kamar jaririya ya fita gurin gudu gudu ,dama already sun kira ambulance,abu guda yake Nanatawa "ya rabbi kada ka bari wani abu ya samu Nafisa".

Da gudu Jamal ya mara masa baya shima yana addu'ar Allah yasa kada wani abu ya sameta ,dan muddin wani abu ya samu Nafisa bazai taɓa yafewa kansa ba,da ace bai amince mata ba da haka duk bai faru ba, atleast zasu shirya ma wani plan ɗin.

Short But worth chapter.

Allah kasa mu mutu muna masu aikata abin Alheri.

Amen

Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top