31
Tsaye Hajiya Saddiqa take kan Safiyya da gaba ɗayan bata cikin hankalinta ,kallan guy ɗin da tayi inviting tayi "shaho,naso aje ayi mun harvesting Organs ɗinta amma sai na sake shawara,duk da cewa zata yi kuɗi amma kasan at this point na samu abin da yafi enough a harkar nan ta harvesting Organs,duba da abin da tayi kana kallon ta ba wata babba ba amma wai tana da zarra,well ina san yanke fukafukanta da suke ƙokarin tashi sama,ka tafi da ita a sakata cikin Babban brothel ɗina idan na shigo garin nan da kwana biyu zan san yarda zanyi ayi shifting ɗin ta inda ya kamata taje ta girbi abin da ta shuka".
"Amma Hajiya babu dai matsala wajen fita da ita daga gidan nan ko?"
"Kamar yarda babu matsala wajen shigowa da kai haka babu matsala wajen fitar da ita,after all yanzu karfe Biyu na dare kowa ya hau gado,kayi aikin ka kawai ,idan ta isa gurin da ya dace zan maka transfer na 500k,ka faɗawa ƙyalli uwar gida kada ta bata abinci bayan ruwa har sai na shigo gari".
"Yarda kika ce haka za'ayi hajjaju".
Kamar kayan wanki ya saɓa Safiyya a kafaɗarsa ya bi bayan Hajiya dake gane masa gaba,ta bayan gida inda emergency door wadda shi kansa mai gidan mantawa yake da ita suka fita ,sai da tabbatar sun fita kafin ta dawo cikin gidan kamar wata munafuka ,tana ƙoƙarin shiga gidan aka haskota da ƙatuwar torch light,hannu tasa tana mai ƙare fuskar ta tana faɗin"lafiya?wane haka yake haske ni?"..Ƙarasowa Chief security ɗin yayi ,ganin ta yasa yayi saurin ɗauke hasken daga fuskarta.
"Kiyi haƙuri Hajiya,ban san ke bace,lafiya dai kika fito karfe 2 na dare haka."
"Tunda karfe biyu na dare ne kada na fito,abeg matsa a gabana bana san ɗiban Albarka".
Bai sake cewa komai ba ya matsa mata ta wuce tana mita ,kallo kawai ya bita da shi yana mamakin abin da ya fito da ita domin idan kunnuwan sa sunji masa daidai ba Muryarta kawai yaji ba,bin inda ta fito yayi yana haskawa amma bai ga komai ba .
Da asuba Akram zai fita sallar asuba ,yana buɗe kofar ɗakinsa wata takarda da aka saƙala a gurin ta faɗo ,duƙawa yayi ya ɗauka , murmushi yayi tunanin ko Nafisa ce,buɗewa yayi yana mai faɗin ,yau love Message ɗin asuba na samu kenan.
"Na tafi kada kayi ƙokarin nemana dan baza ka ganni ba,naje dan yin rayuwar da nake ganin ita ce, Nagode da komai."
Safiyyah..
Naɗe Paper ɗin yayi ya cilla cikin ɗakinsa,God knows yayi mata iya ƙokarinsa,idan haka ta zaɓa Allah yasa shine mafi Alheri,..Bayan sun idar da sallar asuba cikin masallacin gidan tare da securities ɗin su inda Alhaji Muhammad ne yake jan su Sallah normally,bayan idarwa kamar kullum ya ɗauki Alqur'ani ya fara karantawa kamar yarda mahaifinsa yake yi a kullum har zuwa ƙarfe shida,yana ƙoƙarin tashi ya tsayar dashi ta hanyar faɗin"kasan abin da ya faru kuwa a gidan nan jiya da rana"?.ɗan kallan sa yayi kafin yace "a'a Daddy ban sani ba,abu ne da ya kamata na sani?".
Zayyana masa abin da ya faru yayi wanda yasa Akram shiga matuƙar mamaki,so abun har ya kai nan, tafiyar Saffiyya ta faɗo masa,wannan ne kenan dalilin barin ta gidan,haka kawai sai yaji babu daɗi,dama ya gama yanke shawarar bin Nafisa wanda yana ganin shine dai dai , shaida masa yayi da akwai gurin da zaije idan ya gama sorting gidansa ya dawo,sosai baiji daɗin jin hakan ba amma da yayi tunanin sai ya amince masa tare da cewa zai bashi Black card idan zai wuce,kamar bazai karɓa ba amma sai yaga idan yayi hakan ya nuna masa kamar bai manta abin da ya wuce ba dan haka ya amince akan zai karɓa ɗin,after all shima yasan rayuwar zatayi tsauri idan babu kuɗi duk da kuwa bai shirya ƙin neman nasa ba a duk inda zaije dan a rayuwarsa bai da niyyar taƙama da kuɗin ubansa muddin ba nasa bane.
Bayan sunƙume Saffiyya komawa ɗaki Hajiya Saddiqa tayi ta ƙwanta ta shaƙi baccinta hankalinta ƙwance sun kauda wani matsalar ,da safiya suna zaune Dinning suna shirin karyawa ta kalli sakina da baki ɗaya bata da walwala,zuba ketchup tayi a gefen plate ɗin da ta zuba irish potato da fried plantain still hankalita na kan sakina dan tasan akwai abin da ke damunta,kasa haƙuri tayi dan haka ta tambaya dan san jin damuwarta.
"Wai lafiya Sakina duk kika bi Kika damu kan ki?,ina fatan dai ba maganar waccan yarinyar bace dan raina zai ɓaci sosai idan kika faɗa mun akan ta kika faɗa kogin tunani"
"Ni yaya ba a kanta nake tunanin ba ,ai nasan ita ta zama labari,wallahi kan Daddyn su hashim ne,wallahi duk bana jin dadin yarda baice mun komai ba kan batun Akram,abinci ma a part ɗin sa yake ci".
"So that's it?,ki ƙwantar da Hankali ki,ni kina bani mamaki wallahi idan naga kina shiga wani hali saboda abin da bai kai ya kawo ba,baki san saka yardar ki ga Malaman tsubbu kuma mutanen nan na amanar mu ne dan suna biya mana buƙatu so mene kike tantama,ya faɗa Miki da ƙafafunsa zai kawo kansa gareki ,maganar Akram kuma kamar ba'a yi ta ba , mene Kike wahalar da rayuwarki a banza?".
"Amma yaya."ɗaga mata hannu tayi "bana san Amma,kici abincin ki ,ina nan har ƙwana biyu masu zuwa".
"Favourite Amah e don happen o,kasala don burst, everywhere don scatter"faɗin Hashim wanda yake saukowa da gudu daga Upstairs hannunsa riƙe da wayarsa yana kallo,a tare suke binsa da kallo kafun ta tambaye sa 'lafiya?.
"Aikuwa ba lafiya ba ,na faɗa Miki everywhere don scatter dan Khaffy na trending ".
Tsaki tayi ta cigaba da cin abincin ta tana mai cewa"dama ai na haife ta ne dan tayi trending bana tunanin sabon abu ne".Wayar ya kawo saitin fuskar ta yana mai faɗin aikuwa wannan sabo ne dan kama su akayi Suna sex party,Ganin headline ɗin dake ɗauke da "young Talented daughter of the wealthy business woman Hajiya Saddiqa, caught by the police at a nasty sex party location ".dankallin da tasa bakinta ta yiwa wata muguwar haɗiya wanda ya koma daidai magowaranta ya tsaya,take jikinta ya fara karkarawa ko ina na neman tsaya mata,wani irin juwa taji ta kawo mata ziyara lokaci guda ta fara ganin dishi dishi,magana guda ke ɗauke a bakin ta ta ƙarshe wadda ita ce"my reputation"kafin komai ya zamar mata Blank,.Da gudu Hashim yayi kanta yana kiran sunanta ganin zata faɗi yayin da Hajiya Sakina ma ta tashi tana mai saka ihu wanda ya jawo hankali duk wani mai rai a sashen nasu,zuciyar Musulunci kawai tasa Akram da ya kula da suma tayi ɗauko Ruwa dan yayyafa mata yayin da Nafisa ke aikin faɗin "Mene ya samu Amah ta,dan Allah kuyi sauri kada ta mutu".jawota Nana A'ishah tayi tana mai cewa"baki ganin you're over acting?we all know you don't care",ƙwace hannunta tayi tana mai bata amsa da"ku kuke ganin komai acting ne".
Bayan farfaɗowar Hajiya Saddiqa wayarta ta fara nema hankalita a mutuƙar tashe tana kuka dan tasan Wannan Bala'in ba ƙaramin asara zai jawo mata ba,Khafilat ta kashe ta,duk wani connection da tasan zata samu a lokacin gagara yayi,cike da tashin hankali take faɗin,sakina maza yi mun booking Flight yau zamu bar garin nan,asirina a rufe yar iskar yarinyar nan ta tona mun meye ne wani Sex party.
"Ai fav amah party ne da ake ƙarɓa Tatata, everywhere Naked sounds kawai da aiki kike ji cool sex music na tashi ,mostly kuma a buge suke Kinsan in kana hayyacinka abin baya nishaɗi,but nasu khaffy ma naga wasu a comment section na cewa Lesbian party ne and irin su wasu ke sponsoring ɗin su,abu shock me oo that innocent khaffy Ashe badgirl ce omoh that's a show off Ina da cousin jan wuya"
"Will You shut up you stupid boy "Hajiya Sakina ta buga masa tsawa ganin yarda Yayarta ta sake shiga kogin badibafar tana nutso daf da kadar da ta buɗe baki.
Tashi tayi tana mai faɗin"na shiga uku Ni Saddiqa ,Allah yasa babu ƙwaya,idan da ƙwaya ta kashe ni,kawai ku binne ni,maza ke tashi muje ,sakina mu tafi airport".
Babu musu Nafisa ta haura sama ɗan dauko kayansu,duk da cewa abu ne da ya kamata ace tayi murna,amma ganin Hajiya Saddiqa cikin wannan yanayin sai take jin wani irin, conscience ɗin ta yana dawowa,jin ana knocking yasa tayi saurin goge hawayenta ta buɗe kofar,ganin Akram yasa tayi saurin matsa masa tace ya shigo,ganin yana Kallanta yasa ta fashe da kuka tana ma cewa"i caused this,Wani irin nake ji a raina".
Yatsansa yasa ka lips ɗinta ya kaɗa mata kai alamun tayi shiru kafin ya fara goge mata hawayenta ."kina kuka akan wannan ɗan ƙaramin abun ina ga lokacin da babba zai zo,a abubuwan da matar nan tayi dan an mata wannan ba komai bane,yanzu kiyi tunanin Jannah da duk abin da tayi facing ,kina ganin ta chan-chan-ci haka?she doesn't deserved it they ruined her Kuma wannan matar da kike tausayawa ce ,she did All that babu wani regards balle tausayi,idan munce karma ne mahaifinsu was bad amma su ai they are not bad,amma ta bangaren Khafilat fa?she's bad and she need to stop,kisa haka kamar taimakonta da taimakon al'umma,dan haka ki share hawayen nan bana san su,I'm very proud of you"..Ji tayi hankalinta ya ƙwanta wani karfin gwiwa yana zuwar mata yana danne wannan feeling ɗin na guilt,jakarta da batayi unpacking ba ta ɗauko ta mayar da abin da baza a rasa ba sannan ta maida Kallanta gareshi tana mai tambayar sa sai yaushe'
Murmushi yayi ya gyara tsayuwar sa yana mai saka hannunsa kan haɓarsa ya kashe ido guda ɗaya yana mai cewa"har an fara missing ɗina kenan,well anjima zanbi afternoon flight,nima Bazan iya zama inda babu hayati ɗina ba".
"Who's your hayati "ta faɗa tana mai buga babban ɗan yatsan ta na ƙafa a ƙasa tana blushing..Knocking da akayi yasa ta sanin she needs to go.
"Abeg ke ake jira kina ɓatawa mutane lokaci "Nana A'isha ta faɗa daga waje kafin ta wuce,ɗaga mata hannu Akram yayi kafin ta fita ,bayan wani lokaci shima ya fito ya wuce ɗakinsa domin yin shirin tafiya shima .
*****
Suna isa Nassarawa babu ɓata lokaci Hajiya ta cewa Driver ɗinta ya kaita station ɗin da suke ,.a Bakin state CID na garin paparazzo's ne haƙe suna jiran zuwan su dan Nafisa ta faɗawa Jamal suna zuwa yayi leaking information ɗin,cikin tashin hankali ganinsu tace"oooohh Allah ya tsinewa paparazi ɗin nan yan bura uban matsiyata,taya suke san na shiga gurin nan danni bana san ganin fuska ta a jaridu da Mujallu kan wannan case ɗin I can't risk it".
"Amma Amah idan baki shiga ba yanzu Kinsan dai Khaffy ba iya ɗaukar uƙubar cell zatayi ba na ƙwana ɗaya".
Kallan nafisa da tayi maganar tayi,kafin tace muje to,Babu musu Nafisa ta buɗe kofar ta fita yayin da Hajiya Saddiqa ta fito ta ɗaya bangaren,tana fitowa ta kama Nafisa da tazo saitinta ,kafin ta farga ta kamota ta sakata gabanta ta Kare kanta,aikuwa paparazzi na ganin su suka yo kansu,haske flashes kawai kake ji kamar tashin hankali wanda yasa Nafisa saka hannunta ta kare idanunta da Haske yayiwa yawa,a haka suka shiga cikin station ɗin,wani irin ƙululun baƙin ciki ne yazo wuyan Nafisa ya tsaya,ji take kamar ta kamata tayi ta dukanta har sai ta daina koda Motsi,Office ɗin Babbansu Hajiya ta shiga tana mai dana sanin rashin ɗauko shade ,haɗe rai sosai tayi lokacin da ya taso yana mai gaisheta cike da girmamawa,ɗaga masa hannu tayi.
"Kaga Ƙassim kada ka cika mun kunne da fake gaishe gaishenka,kai yanzu dan bana gari shikenan sai a kama Khafilat kana ji kana kallo?haba dan Allah ni ai gani nake koda bana gari ku da nake daku masu dukan kirjine su fito mun da Khafilat".
"Wallahi Hajiya abin ne yafi karfina,amma ai ta samu treatment mai kyau,maganar fa daga chan sama take I'm even scared Gobe zasu shiga court dan har cocaine aka kama su dashi,da sauran kayan maye na tashin Hankali".
Jin haka yasa tayi saurin cewa"ai faɗuwa dai tazo dai dai da zama na kawo muku wadda ta haɗa party ɗin sai ku sakar mun ƴata,da kanta ta leƙa ta kirawo Nafisa,bata mata musu ba duk da tasan cewa kiran ba alheri bane,guri aka bata ta zauna kafin Hajiya Saddiqa tace"Yauwa Nafisa maza ki faɗa musu kece kika haɗa party ɗin nan sai su saki Khafilat,Kinga dai ƙanwarkice kada kisa ta hau kan laifin ki wanda bata ji bata gani ba,Ƙassim gata nan ita ta shigo musu da cocaine ɗin"zumbur Nafisa ta tashi daga zaunen da take tana mai dafe kirji tace"Ni kuma ,yaushe?,Hajiya duka yaushe muka shigo garin nan ni dake?sir Ina da masu min Shaidar cewa i have nothing to do with this,I won't take this big Fall"ta mayar da maganar gurin jami'in tsaron..Kallan Hajiya yayi wanda yasan cewa karya take san haɗawa Nafisa.
Cike da yar damuwa yake faɗa mata",Hajiya case ɗin nan fa ya wuce tunaninki sosai,dan yaran nan Kamasu akayi ƙuruƙuru wanda yanzu haka ba sai na faɗa Miki ba its all over the media,ban San me zan Miki ba".
"Ni na sani"ta faɗa ta tashi tana mai watsawa Nafisa wani mugun kallo kafin ta fita tana mai ƙoƙarin kiran lawyer ɗinta wanda tunda yake kiranta taƙi dauka tunanin ta zata iya fita da khafilat a ranar,bayan sun gama magana ne yace ta jira sa zai zo da takardun bail, komawa Office ɗin Ƙassim tayi tana aikin safa da marwa shi kuma yana aikin bata haƙuri.
"Kasan dai nice na ɗauki nauyin aikin da aka yiwa yaranka na ƙwaƙwalwa ko?"
"Na sani Hajiya kiyi haƙuri ".
"Nice na baka taimako a lokacin da commissioner shedrack ya saka ka tsaka mai wahala ko?"
"Na sani Hajiya shi yasa naso shi ki ka kira"
"Ni da shi mun Samu gagarumar Rigima can't you see that,bantaɓa tunanin zan shiga matsalar jami'an tsaro ba ,God damn it"dukan table ɗinsa da tayi karshen maganar Tata yasa yayi saurin matsawa yana mai sake bata haƙuri.
Nunasa tayi da yatsa kafin ta ɗauke kamar ta tuna wani abu tace"yanzu ai ka saka a fito da ita na ganta"
"Bazai iyu ba Hajiya sai an kawo takardun bail".
Bata tanka shi ba ta cigaba da aikin safa da marwa tana tunanin kala kala,dole ne Nafisa ta ɗauki lefin nan ko tana so ko bata so ba zai iyu rayuwar khafilat ta lalace ba a wannan lokacin da ta fara tashi tauraruwarta kuma na haskawa,tasan cewa zata samu wani wanda zai mata zane ɗin amma khafilat kuwa idan ta tafi prison yanzu rayuwarta ta lalace wanda abu ne da baza ta taɓa bari ya iyu ba,dole ne Amfanin Nafisa ya ƙaru ta wannan hanyar .
08130229878
Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top