30
Kallan Alhaji Muhammad Hajiya Sakina take zuciyar ta nayi mata ƙuna da maganar da yayi mata na cewa Akram zai fara zuwa Office ,abin da ba zai taɓa iyuwa ba kenan ace suna zaune ita da yaranta Akram ya fara zuwa Office da sunan aiki.
"Amma dai Alhaji kaji abin da na faɗa maka kan yaran nan ko?, Akram fa ba wai ya dawo gidan nan bane dan ku gina wata alaƙa da kake tunanin zaku gina,Akram ya zo gidan nan ne domin ya ɗauki fansa kan abin da yake tunanin kayi masa ,amma tunda baza ka yarda ba bari na tabbatar maka"tashi tayi daga zaunen da take da niyyar zuwa ɗakin Akram ta fito da files ɗin da suka saka masa,ta tabbata Alhaji na saka idanunsa kan dukkan wasu takardunsa da yake ɗauka da muhimmanci to kashin Akram ya bushe,minti guda ba zai ƙara cikin gidan ba,.
"Hajiya wannan takardun kika tashi zaki ɗauko a ɗakin Akram?,well I'm sorry to disappoint you dan na rigaki".Da mutuƙar Mamaki take kalla Saffiyya wadda ke tafe tana aikin rangwaɗa cikin shigar Atampa riga da skirt wanda skirt ɗin yayi masifar kamata ,ga wani mugun ɗauri ta kashe fuskar nan tasha ƙwalli,a fusace Hajiya Sakina tayi kanta da Niyar Fizge takardun amma ta faskara saboda yarda Saffiya ta ankara da zuwan ta tayi wani mugun matsawa,ganin ta kusa faɗuwa yasa Safiyya cewa "kije a banza ki fasa bakin ki ni babu wani abu da ya dameni".gaban Alhaji Muhammad da ya zuba musu ido dukkan su taje tana wata rangwaɗa da wasu fari fari kamar wata tsohuwar jezebel ta zauna tana mai yin wani sumi sumi da fuska kafin ta saka wani irin kuka kissa tana mai cewa"Alhaji waɗannan takardun kane masu muhimmanci waɗan da dukkan wani abu da takardun suka ƙunsa ba wai a ƙasa ka haƙosu ba,takardun kadarorin ka ne da gidaje Hajiya ta ɗauko ɗazu a Office ɗinka ta saka ɗakin Akram dan kawai su yi masa sharri ita da yayarta da tazo,wallahi Alhaji su biyu ɗin nan babu wani abin Alheri da suke shukawa banda sharri da tunanin yarda zasu ga bayan Akram,bawan Allah ,tun tashi nasan Akram,duk da cewa ban isa ko na kai haihuwarsa ba amma ina bada Motherly Advice kuma yana ɗauka sosai,har faɗamun yayi cewa wani lokaci duk da yarintata he use to see a mother figure in me ,he find peace and comfort, Daddyn Akram ina tsoran wani abu ya same shi har raina"ƙarasa maganar tayi da ɗan fashewa da kuka,ganin haka yasa Hajiya sakina da Mamaki ya kusa karwa cewa"to dan bura uban ki sai ki Aure sa,ni zaki kawowa makirici cikin Gida?".
"Bazan iya Auren Akram ba Hajiya dan yarda yake mun kallan mother figure Nima ta wani bangaren ina jin hakan a tattare dashi,kuma sai inda karfina ya ƙare wallahi muddin kika ce baza ki bar Akram ya sha iska ba,kina kallona haka rayuwata ma zan iya bayarwa akan Akram ba kuruciya ba,idan kince kuma sharri na Miki thank God na ɗauki video lokacin da kuke boye files ɗin a ɗakin sa "wayar ta ta kunna tana mai nunawa Daddyn Akram,karɓan files ɗin yayi bayan ya gama kallan video ɗin yayi mata Godiya ya tashi bai koda sparing wa matarsa kallo guda ɗaya ba.Murmushi tayi ganin Abin da ya faru wanda ya tabbatar mata da Sallamar nasararta,hannu tasa ta goge hawayenta a zuciyarta tana ayyana yanzu aka fara wasan,Fincikota Hajiya Sakina tayi tana mai kallanta cikin ido mamaki yaƙi barin fuskarta .
"Ba dai abin da zuciyata ke faɗa mun bane a cikin zuciyarki"ta tambaye ta zuciyarta na wani irin harbawa,. Dariya Saffiyya tasa ta tashi tana mai fizge riƙon da tayi mata ta bata amsa da"well tunda har zuciyarki ta fara baki hint sai ki shirya kafin waccan yayar taki ta wuce ki haɗa jakarki ki bita,dan muddin ina gidan nan kina ciki a yarda zaki barsa kare ma sai ya fiki daraja,abin da kike so da taƙama nima shi nake so kuma ina mai tabbatar miki da cewa sai na samu, besides kamar na ma samu ne,babu boka babu malam".hannu tasa a gefen kafaɗar Hajiya Sakina ta turata gefe kafin ta wuce tana mai kaɗa mata jiki ta hanyar wata irin tafiya kamar wata hawainiya.
Sai a wannan lokacin hajiya Sakina ta samu ikon haɗe bakinta dake buɗe ,kamar wata mahaukaciya ta fashe da wata irin dariya kafin itama ta nufi hanyar saman da sauri gudu har ta wuce Saffiyya,kai tsaye ɗakin Saddiqa ta nufa jikin ta na aikin karkarawa ,sai a lokacin wasu irin hawaye suka fara bin kuncinta ga tsoro fal ranta,ganin yanayin da ta shigo yasa Hajiya Saddiqa tashi daga kwancen da take ta riƙe ta tana tambayar ta" lafiya? Menene Alhajin yace?".kuka kawai ta fashe da shi bata iya bata exact amsan tambayar da tayi mata ba illa faɗin "na shiga uku"da take ."ki zauna ki nutsu Sakina ki faɗa mun menene musan ta inda zamu fara ba wai ki zauna kina maganar kin shiga uku ba".
"Yaya Yarinyar da Akram ya Kawo gidan nan rayuwata take nema, baki ɗaya plan ɗin mu ta rusa ,ashe shegiyar na laɓe tana kallan duk abin da muke har da making na video,worst part ɗin ma Yaya ni duka wannan ba shi ya dameni ba,Yaya baki da baki ta faɗa mun sai ta fitar dani daga gidan nan ta shiga ,wallahi Aunty tsoro nake ji da ban taɓa jin irin sa ba,Aunty Kinga abin da ya faru kuwa" rushewa da kuka ta ƙara wanda yasa Hajiya Saddiqa jin abin har ranta,yo dan uban Safiyya me akayi aka yi ta,kamo hannun ta tayi ta zaunar kusa da ita kafin ta rungume ta tana mai shafa mata baya a hankali tana mai faɗin"ki kwantar da hankalin ki,komai is in place,abin da Bazan iya ba akan duk wanda zai saka ki kuka Sakina babu shi,ke jini nace kuma ke ɗaya kika rage mun wadda nake kalla naji daɗi,tayaya zan ga Rigima tattare dake na naɗe hannu na? gobe da daddare sai dai ki tuna labarin Abin da Safiyya tayi Niyar Miki ba wai ita ba ,Shi kansa Akram ɗin ina da dukkan hanyoyin da zan salwantar dashi ke kin sani amma san buga komai cool da kuma rashin san a zargeki yasa nake san abi komai nashi a hankali,kin manta mai boka yace jiya ne?da ƙafar sa zai bar gidan nan idan wannan tuggun bai ci ba,sai mene dan wannan ya rushe?Ni nayi imani da maganar bokan nan Kan Akram da ƙafafunsa zai bar gidan nan ,idan hakan ma bai iyu ba ki kwantar da hankalin ki komai will be in place,ki bar mun komai a hannuna".
Ajiyar zuci kawai take saukewa lokaci guda kuma nutsuwa ta fara saukar mata ,tana jin daɗin kasancewar Saddiqa yar uwarta dan babu wani abu da yafi karfinta dan haka ta ɗauki maganar Saffiyya ta saka a bayan zuciyarta tasan tunda Saddiqa tasa baki kamar yanka wuƙane,tana da sa'a da yawa.
*****
Safiyya....
Koda ta koma ɗakin ta kan gado ta faɗa tana mai kyalkyacewa da dariya,kallan da Hajiya Sakina ta bata take tunawa da yarda ta hango tsoro a tattare da ita,bata taɓa tunanin cewa wai weak point ɗin ta shine ƙokarin rabata da dukkan abin da take da shi ba,shima sa a ne duk da kuwa baza tace ga taƙamaimai abin da ke zuciyar Daddyn Akram ba,amma koma dai mene tasan cewa a sannu zata karbi zuciyarsa ta hanyar amfani da Akram dan taga abin na kaiwa,so take ta fara saka zuciyarsa jin wani abu na godiya dangane da ita kafin ta fara fito masa da kuɗirin ta fili ,after all a yarda yake da mata mai ƙokarin raba sa da ɗansa da yake masifar so ta tabbata ba zai ƙi tayin wadda take taya sa Masifar san ɗan nasa ba, besides gata yarinya mai jini a jiki,gata da kyanta,tasan ba zai iya watsi da tayin ta ba musamman da ya zamana ta tsara komai da yarda zatayi Blackmailing ɗin sa emotionally ta hanyar wasa da tunaninsa tare da jawosa gare ta,Sai ta tare ko ina ta share gidan ya zama babu kowa daga ita sai Daddyn Akram sai Akram sannan ta fara neman hanyar da zata watsar da Akram a gidan ko duniyar ta yarda babu wanda zai zargeta,daga nan duniya ta zama tata da yaran da zata haifa da Daddyn Akram.Tunanin kawai saka ta shiga wani irin nishaɗi yake ,baza ta taɓa hutawa ba har sai taga ta cimma burin ta ta kai matsayin da babu wanda zai nuna mata yatsa bata karya ba,she can't stop imagining yarda Orphanage na Alheri zai dawo at her mercy, akwai tsare tsare da yawa da zata chanza dan ita da ta fito daga cikin gidan tasan cewa daɗi ya yiwa yaran da bai kamata ace suna da wannan jin daɗin ba,babu wanda zai sake fita waje karatu,babu kuma wanda za a sake kashewa mugun kuɗi,dukkan wanda ke gidan sai ta tabbata yasan matsayin sa ,babu yarda za a yi a cigaba da kai su ƙasar waje su dawo suna ganin zasu iya haɗa kafaɗa da kowa in dai kuma ta samu wannan burin nata ya ciki tayiwa kanta alƙawarin ganin hakan ya iyu.
****
Nafisa...
Kai tsaye bayan ta dawo gida ɗaki wuce tana mai jin ta a wani irin sama,tunda suka shigo unguwar dama suka raba tafiya,babu kowa falon dan haka ta wuce daki kai tsaye,bata san cewa cook ta ga dawowar ta ba sai abinci taga ta biyo ta dashi ta karba tayi mata Godiya ta koma ɗaki ta cigaba da aiki exchanging text messages da Akram wanda ke ta aikin tsokanar ta,tana cikin aikin hawa kan tarkon ƙauna system ɗin ta ta fara blinking tare da sound na shigowar abu,da sauri ta jawo tana mai dubawa,da mamaki taga party ɗin su Khafilat zai faru a daren ranar ,cike da tashin hankalin rasa abin da zata yi ta kira Jamal ta faɗa masa,karshe suka yanke shawarar leaking location ɗin ma jami'an tsaro,bayan ta kashe wayar tayi wani murmushi,at least koda za'ayi bail ɗin su zasu ɗanɗana zaman cell kafin Uwarta ta koma tayi bailing ta,har ta hango yarda jikin ta zai ruɗue ruɗu da cizan sauro,har ta koma ta kwanta ta sake kiran Jamal,yana ɗauka tace"yauwa nephew yanzu wani idea yazo mun,kaga dai khafilat yanzu mutane ƙalilan ne basu santa ba duba da launching day ɗin da a kayi introducing ɗin ta ,why not yarda tayi blowing da taimakon Amah ɗinta da gidajen jaridu da mujallu,mai zai hana mu duba waɗannan same mutanen da suka ɗaga ta su kawo ta kasa,i mean nasan cewa za'a kamo su very dirty kaga mun jefi tsuntsu biyu da dutse ɗaya, immediately ana kamo su yan jarida su zo kasan su akwai san samun mai zafi ,so we can use that nasan you can locate them ko through email ɗin su ne".
Dan shiru yayi kafin yasa dariya yana mai cewa"who corrupt my little pumpkin mind?come here daga ina kika samu idea ɗin nan?".
Kamar tana gabansa tayi saurin kulle fuska tana mai cewa "kai Nephew",Dariya yayi yace "naji that is a very Good idea and I will see to it ,kada ki damu gobe da safe da labari mai daɗi zakiyi breakfast,just sleep soundly and take care".
**
Jamal......
Kamar yarda yayi wa Nafisa alƙawari tun 6 yake area ɗin gurin da zasuyi party ɗin ,ga mamakinsa Guest house ne wanda ko ba'a faɗa masa ba yasan na Hajiya Saddiqa ne ,already dama ya riga yayi hitting up police lokacin fara biɗalar kawai suke jira wanda zasu fara karfe bakwai na dare amma still kafin time ɗin sun fara hallarta,abin da yake basa mamaki mutum Huɗu da yaga sun shiga gidan dukkan su yan shekaru sha bakwai sha shida ne wai har sun san su haɗa sex party,sex party fa,Allah dai ya shirya zuri'a,tun 6:30 kiɗa ya fara tashi a cikin gidan,7:30.police suka hallarci gurin,yana ganin isowar su ya ɗan boye daga bayan wani pillar,basu daɗe da shiga ba sai ga mota guda biyu wadda ba sai an faɗa maka daga gidan jarida bane duba da jikin motocin da logo na gidajen su,kafin kace kwabo sun yi ready na fara ɗaukar bidiyo dan an tabbatar masu da cewa a cikin wannan gidan ne ,ɗaya daga cikin yan jaridar ne ya kalli wanda suka zo tare yace"Habibu baza mu shiga ciki ba kuwa?dan Ni wallahi a tsayen nan da nake na ƙosa naga na fara ɗaukan Rahoto nan,i just can't believe yarinyar da a shekaru 17 ta saka mahaifiyarta ke alfahari da ita a bangare guda kuma suna bayan fage suna lalata sauran yaran jama'a,this is so disheartening,dole mu watsa yarda kowa zai taƙatsantsan da yaransa".
Wanda aka kira da Habibu ne yace"Ni da kaga ni nan Bala ,wallahi ba dan Manager yace muje mu ɗauko rahoton nan ba babu abin da zai kawo ni,shi nema amfanin yaɗa su,yarinyar nan babu wanda bai san uwarta mutuniyae arziƙi bace,kuma yar kasuwa wadda bata rabo da alheri,to mene zai saka dan kawai yarinyarta tayi kuskure guda ɗaya a jawo ta ƙasa?kai kasan wannan labarin will bring her down ""
Haɗe rai Bala yayi sosai yana mai gyara Camera ɗin dake hannunsa kafin yace"kai ka san wannan karatun amma wallahi mu sai mun cigaba da tonawa gurbatattun yara Asiri a duk inda suke in yaso daga nan sai su gyara ,kai kasan guda nawa suka yi paryi irin wannan ɗin?.abeg move idan baza kayi ba mu ka bamu guri..
Jin abin da suke tattauna yasa Jamal yaji wani iri yana ma tunanin shin step ɗin da suka ɗauka mai kyau ne ko akasin haka?
Yana wannan tsayen ya fara jin hayaniya wadda ta tabbatar masa da an fito dasu ne,da sauri ya fito daga maɓoyarsa dan ganin abin da ke wakana,.yan mata biyar ne Khafilat ta shida sai maza biyu waɗanda jikin su babu riga sai gajeren wanduna yayin da mata ke sanyi da wasu yan iskan Lingeries suna masu ƙokarin kakkare jikin su,kafin kace kwabo hasken Flash ya fara tashi a gurin yayin da ruwan tambayoyi ya ke tashi daga yan jaridun da suka samu hallarta.,tare da taimakon yan sandan suka dakatar da yan jaridar kana aka zuba su a mota ,kafin kace kwabo abu ya tafi live da mad streamers .
08130229878.
Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top