29
womenofwords/WA
🔏NOT ALL GLITTERS ARE GOLD💫
(BA DUK KYALLI BANE GWAL)✨
Be with 👇
*𝐴𝑊𝐸-𝐼𝑁𝑆𝑃𝐼𝑅𝐼𝑁𝐺 𝐼𝑁𝐾🥌*
Tagwayen tafiya Mai sihirtattaciyar Ma'ana ta ban Mamaki daga jerin Tawwada d'aya Al-'kalami biyu first series.
*LOKACI.!*
Halish Sultan.
*BA DUK 'KYALLI BANE GWAL.!*
Amina Jamil Adam (Chuchu jay)
https://whatsapp.com/channel/0029VaRpQeUHwXb52H0abb05
Ga masu nema daga farko
Chapter 29
Bayan fitar su Hajiya babu daɗewa Nafisa ma ta shirya ta fita tana mai zumuɗin ganin Akram,daga chan gefen gidan ta samu guri ta tsaya tana mai mayyar da Kallanta ga ƙofar gate ɗin .
"I'm just pleased da ya zamana wannan kyakyawar tsaleliyar budurwar ni take jira"
Juyowa tayi tana kallan sa kafin tayin ƙasa da idanun ta cike da kunya,.Ƴar dariya yayi ganin abin da tayi kafin yace mata" Bismillah ya kamata mu bar area ɗin nan kafin wani daga cikin yaran Alhaji su fito su kai rahoto duk da ban san yarda kuke dasu ba.Bata ce komai ba ta fara takawa yana biye da ita a gefe,babu wanda yace da wani komai haka suke tafiyar har suka isa ƙaramin titin dake kan Area ɗin,Cab ɗin da ya kira already tana standby tana jiran su ,Haka ride ɗin ya kasance babu wanda yace wani abu sai shi dake aikin satar kallanta , imagining abubuwa da dama yake akan sa he can't believe wai yau Nafisan sa ce ta chanja ba kamar yarda ya san ta da ba,idan rayuwa ta buga maka wani juyin sai ka daɗe da tagumi a fuskarka baka cire ba,lokacin da ya tafi karatu bai taɓa tunanin komai zai chanja ba baya ga Nafisa da yake fatan dama ta chanza,a tunaninsa bayan ya gama karatu ya dawo gida Nigeria zai fara sauka a gidan da yafi masa ko wanne gida,a ƙofa zai tarar da Nafisa fuskarta ɗauke da wannan murmushin nata mai kyau wanda idan tayi side cheek ɗinta guda ɗaya yake lomawa,zai fito mata da gifts ɗin da ya siyo mata ,zasu zauna ya bata labarin Turai yayin da zata bashi labarin yarda tayi faɗa da wancan ,ta daina ma wancan magana,yarda Big Mummy tayi mata hukunci akan laifin da bata yarda ta aikata ba,zai bata tabbacin zasuyi rayuwa mai kyau dan ya dawo da labarin da take san taji a yarintar ta na zai Aure ta,yana santa,bai taɓa san wata ba bayan ita,.He was expecting everything to be perfect ,yarda zasuyi Aure ace yau ga Nafisa ta ɗauki Babynsa tana mai shagwaɓar bata ita saka pampers ba a gefe guda yana taya ta Big Mummy na Scolding ɗin su,that was the life , exactly irin life ɗin da ya tafi yana mafarki akai amma sai aka samu akasarin haka ta hanyar lalacewar komai,a yanzu a gaban sa broken Nafisa ce wadda baya kallan soyayya a gabanta apart from damuwa duk da kuwa bai san mene aynayin damuwar Tata ba baya ga kukan da take jiya tana mai faɗa masa su suka kashe Big Mummy,idan kuma tunaninsa ya kai inda ya kamata ,abin yana da dangantaka da su Hajiya Sakina.
Dai dai location ɗin da ya bawa Driver ɗin ya tsaya,daga motar ta ɗaga kai tana mai kallan inda suka zo kafin tayi Murmushi ta kallesa,shima murmushin yayi ya fita ya zaga bangarenta ya buɗe mata door ɗin.."nasan kina mamakin zuwan mu park ba sai kin faɗa mun ba cos da kallo kawai zan iya chamkar abin da ke zuciyar ki dan na yarda da cewa i know you best".Ba tare da ta kallesa ba ta amsa masa da"well maybe that was then,but sha kayi guessing dai dai,I mean I can't believe ka kawo ni park".Buɗe baki yayi lokacin da ta kai karshen maganarta yana mai zama speechless,finger ɗin sa guda ɗaya ya ɗaga yana mai rage idon sa guda ɗaya ya sha gabanta"do you just speak English?".
Tsayawa tayi da tafiyar da take tana mai kallan fuskarsa kafin ta saka dariya,shima dariya ya taya ta dan idan yace bai mamaki ba ƙarya yake,"something enter yanzu kenan?"cigaba da tafiya inda yake ta cigaba yayin da shi kuma yake takawa da baya yana kallon ta."well wani abu wai shi Yaren turanci ya shiga ,amma nan da kake kallo na a js1 ɗin da kasanni wanda na maimaita sau uku na tsaya daga nan ban yi gaba ba, but zan godewa Allah domin bai bani ta wani gurin ba ya bani ta wani gurin,cos a yanzu kana magana ne da extra ordinary Being used poor designer,watch out zaka bige mutum". saurin matsawa yayi yana mai bawa yaran da ya kusa bigewa da mamansa haƙuri kafin ya dawo gefenta suka cigaba da tafiya yana mai cewa"so kina san kice mun you're a designer?,I mean what can you design".
"Bags, Shoe's, kaya etc zan iya zuwa da ideas na ko wanne yazo kaina,but sadly ana amfani da ƙwaƙwalwata a yanzu ba tawa bace, after all ka kalleni I'm just someone who's struggling,kada ka bari appearance ɗina ya yaudare ka".
Ƙarasawa ciki sukayi inda ta samu guri ta zauna a build chairs,gefenta ya zauna yana mai ce mata"tell more about this new you, saboda I'm curious na san sanin abin da ya mayar mun da cheerful ,free spirit Feenah na matured haka".Kallan sa tayi na wani lokacin kafin ta fara basa labarin abubuwan da suka faru da ita tun daga kan mutuwar su Big Mummy har yanzu da take gabansa,abin da ya bata mamaki shine ganin hawaye a idanunsa dan ita ko hawayen ma yanzu ta daina,cike da matuƙar damuwa yace da ita"Nafisa,kizo na ɗaukeki mu bar garin nan,infact zan iya barin ƙasar nan dake we can start a family tare,zan iya barin komai domin ke,we will start from scratch, saboda wannan matar is very dangerous,bazan iya zuba ido ta kashe ki ba ko wani abu makamancin na Jannah ya faru dake,I feel bad for her ta yarda da ace ke makamancin hakan ya sama bazan iya kallan kaina ba saboda ban kula dake yarda ya kamata ace nayi ba,we can leave everything behind,the sad memories,the pain,and everything,Ina da ke kina dani ina ganin shi kaɗai ya isa,zamu iya zuwa inda za'a darajata talent ɗin ki babu wanda zai damu da kina da kwallin degree ko baki dashi ,i don't have enough Amma abin da na karanta pays alot,with time Ina samun wani bangare da zan riƙe shikenan,i can be a developer,and much more,Insha Allahu baza kiyi dana sanin bani dama ba Nafisa,I can't even phantom the thought of losing you,kinji? Please "
Ta jima bata ɗauke idanun ta daga kansa ba ,jin hawaye na san fitowa a idanunta yasa tayi saurin ɗauke idanun ta tana mai cewa"yanzu da baka ganni bafa,Saffiyya fa sai kayi yaya da ita cos naga relationship ɗin ku ya ɗauki wani step".
"Ina kan neman ki dan ko ranar da na ganki ina tare da Isma'il wanda ya sanar Dani kina Nassarawa a binciken da na saka shi,Feenah trust me da ace ban ganki ba bazan taɓa hutawa ba har sai na ganki,Saffiyya kuma she's nothing , she's a friend dana taimakawa, that's All Babu wani abu dake tsakanina da ita,I loved you since day one har na tafi ban daina ba,i always do,I think of you,and I still do love you,Dan Allah ki bani dama na ɗauke ki daga rayuwar ƙunci da baƙin ciki wadda babu komai a cikin ta sai pain,let me heal you with my love, affection and care ".
Yar ƙaramar dariya tayi in between hawayen dake zuba a yanzu kan kumatun ta,hannun ta tasa ta share su tana mai kallan gefe guda"I can't believe yau Kaine gabana kake faɗa mun maganganun da na daɗe ina mafarki,Boda Akram yana cewa he's in love with Nafi, literally he can't live without her,duk yarda wannan offer ɗin taka ta saka na ƙwaɗaitu Naji ina san rufe idanuna na ƙarba amma bazan iya ba,wannan rayuwar da kake gani ina cikin ta tsundum idan nace yau zan cire kaina banyiwa mutane da yawa adalci ba ,ciki harda Ya Jamal,shi ɗin ya zamar mun wata katanga wadda idan da ace bani da ita ƙila abin da ya samu Jannah sai yafi nawa muni,ya taka babbar rawa akan rayuwata ,a yanzu da fansar sa ke kusa idan nace na zare kaina na zama butulu,maganar ma na cire kaina bai taso ba,matar nan kamar yarda ta faɗa ina cikin tafin hannunta ,kaga itace tasan iyayena ,ita ta kashe Big Mummy da Mummy Nadiya,duk yarda zan so na bar komai a wannan gurin da aka kai bazan iya ba,idan ni ina da kai da zaka riƙeni ka kula dani kayi duk wani abu possible da zai cire ni a damuwa sauran ɗaruruwan yaran da aka kama da kuma ake shirin kamawa fa?.Wannan matar fa Hajiya Saddiqa have to fall down on her tummy kuma ni kaɗai zan iya zama sanadin hakan,at this point bai damuna ƙwata ƙwata ko gudun wai zai shafi rayuwa ta,kawai na yarda da kalmomi guda uku na"just do it"bazan so kaina ba duk yarda nake so na kai...Sauke ajiyar Zuwa yayi yana mai juya maganganunta,tabbas shi kansa yasan babu abin da Nafisa zata yi ta biya Jamal akan abubuwan da yayi mata,sanin cewa shima yaso kansa yasa shi faɗa mata cewa "ina tare dake duk wani step da zaki ɗauka,ko mene kike yi dole ki Saka ni I want to be involve,beside Kinga daga nan kina shiga Nassarawa ina shiga baza barki ki sake minti ɗaya garin nan babu ni a cikin sa ba ,i will be your protecting shield ,duk lokacin da kika kirani zan kasance a gabanki,we will see the end of this together,yarda na sameki yanzu Bazan yarda ki kuɓuce mun ba,Kinga har na samu na yiwa Jamal Godiya I'm very sure yasan da Boda Akram"..Wani irin kunya taji ga Maganar sa karshe,ƴar dariya tayi tace"ni bana so Boda Akram,and I'm very greatful Kuma bazan ƙi san kaina nace ka zauna ba ,i will snatch ɗan Alhaji away from this place,so tell me about ɗan Alhaji.
Ɗaga gira guda ɗaya yayi"wane ɗan Alhaji"?."Kai mana dodon Hajiya Sakina "Murmushi yayi yana mai shafa gashin kansa da yayiwa aski mai kyau kafin ya fara bata labarin sa a takaice,yana tsaka da magana ne wayarsa ta hau ƙara,a tare suka kalli wayar cos tan tsakiyarsu ,da Mamaki take kallan hoton Salman dake yawo akan screen ɗin,bata ce komai ba ya ɗauki wayar yana mai masa Sallama kafin ya ƙara da "Bukar Jnr, Babban ɗa a gidan Alhaji Bukar."
Tsaki Salman yayi yana mai cewa "daɗina da kai iskanci da nacin abin da mutum bai so,ni dallah na tura maka wani document ta email ɗin ka ka duba mun dan wani jargons ne naku na haɗu dashi thank God Ina da Mayen Computer ".."Well kazo inda za'a sosa maka Baya da ice,so bros ya Ummu da mutanen Gidan? ".Kafin Salman ya basa amsa ta matsa yarda Zaiji tace"Ya Salman Barka".
Cire wayar Salman yayi daga kunne ya kalli wanda yake magana dashi sannan ya juya gefe da gefensa dan tabbatar da ba a cikin wayar bane,ganin babu kowa a gurin ya saka ya mayar da wayar kunnen sa yana mai cewa"Nafisa?". Dariya tayi tace"ita ce dai so kaga dai ta tabbata Akram abokin ka na ƙasar waje shine Boda Akram ɗin wanda kace ni ba kalarsa bace,well here you are Gani ga Boda Akram a zaune".Da mutuƙar mamaki Akram ke tambayar ta in tasan shi yayin da Salman ke faɗin"Bro zan kamka for this tunda ko da wasa baka taɓa faɗa mun cewa kana da ɓatacciyar Nafisa ba mai faɗawa kowa kafi su kyau,guy really?nine dan banza mai zama na buɗe maka cikina ko?.
Kasa daina Fara'a Akram yana mai cewa"Calm down dude,ka kwantar da hankalin ka i will explain,ɗiff Salman ya kashe wayarsa,Dariya Akram yayi yace"wannan guy ɗin nawa sa shi well zan basa mamaki idan ya ganni a Nassarawa,so a ina kika san Salman?
"Yaran kishiyar Hajiya Saddiqa ne a na baka labari, never thought zaku zama frnds haka".
"Flat mate ɗin ne sannan a shekarun da muka yi mun zama kaman brother dan Salman mutumin kirki ne,sannan dodon Saffiyya shi ke mun maganin ta".
"Well ban taɓa zatan akwai wanda Safiya zata ji tsoro ba"kallan agogon hannunta tayi tana tana mai saurin miƙewa,"mun daɗe fa kada Hajiya ta koma taga ban dawo ba".Tashin shima yayi yana mai cewa"okay so har yanzu dai ana sona kuma ni kaɗai za'a Aura ko?".Cike da kunya tace"zamu gani"kafin ta juya ta fara tafiya tana murmushi,it been long da ta jita cikin nashaɗi haka,bata yi tunanin sabon grown up Akram zai taso mata da childhood love ɗinta lokaci ɗaya ba,.a haka suka jera yan ta tsokanar ta tana ta sumi sumi da fuska musamman da yake tuno mata da wautar ta ta da.a hanya yake bata labarin su Khadija inda yake faɗa mata Khadija tayi Aure,Asiya ma ta Auri Yusuf saurayin ta,Yayin da akayi adopting Sa'adatu zuwa Canada,Suwaiba kuma har yanzu tana gidan,duk da dai gidan ba kamar da ba amma a haka suke rayuwar da daɗi ba daɗi.
Kuyi manage,in San gama book ɗin nan Insha Allahu kafin December taƙare dan haka kuyi expecting update a kullum Insha Allah.
Xx
Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top