28
womenofwords/WA
🔏NOT ALL GLITTERS ARE GOLD💫
(BA DUK KYALLI BANE GWAL)✨
Be with 👇
*𝐴𝑊𝐸-𝐼𝑁𝑆𝑃𝐼𝑅𝐼𝑁𝐺 𝐼𝑁𝐾🥌*
Tagwayen tafiya Mai sihirtattaciyar Ma'ana ta ban Mamaki daga jerin Tawwada d'aya Al-'kalami biyu first series.
*LOKACI.!*
Halish Sultan.
*BA DUK 'KYALLI BANE GWAL.!*
Amina Jamil Adam (Chuchu jay)
https://whatsapp.com/channel/0029VaRpQeUHwXb52H0abb05
Ga masu nema daga farko
Chapter 28
Dube dube Hajiya Sakina keyi tana mai faɗin taji motsi, kallan flower base ɗin dake ƙasa tayi tana mai cewa .Na faɗa Miki wani yazo gurin nan.
"To koma wane kilan wucewa yazo yi abeg manta bari naje na ƙwanta,kada ki manta fa da abin da na faɗa Miki ".wucewa Hajiya Saddiqa tayi dan zuwa dakinta ta ƙwanta yayin da Hajiya Sakina ta ɗan yi kalle kallenta ta koma ɗaki,ganin ta wuce yasa Nafisa dake maƙale bayan gurin hannu rufe a bakinta ta fara kiciniyar ƙwacewa,ganin haka yasa ya saketa ya matsa gefe yana mai cewa "yi haƙuri"ɗagowa tayi ta kallesa,duk da a cikin duhu ne bata kasa gane shi ba ,kuka ta fashe dashi mai sauti wanda hakan yasa yayi saurin jan hannunta zuwa ɗakin sa dake daga chan karshe ta baya ,bata masa musu ba dan a yarda take jinta ko ina ne zata je,koda suka shiga zaunar da ita yayi har a lokacin bata daina kuka ba,kuka sosai take komai yana dawo mata sabo,sai da taji dama bata fito ba har taji maganar da suke,dawo mata maganganun suke kamar lokacin take jinsu inda Hajiya sakina ke cewa."yanzu yaya baki tunanin Nafisa zata baki matsala nan gaba?Ni wallahi ina tsoran yarinyar nan haka kawai jikina ke bani ba abin kirki za a shuka da ita ba,bugu da ƙari kina ji dai Akram ya san ta,duk wanda Akram ya sani kuma ni ina tantama".Yar dariya Hajiya Saddiqa tayi kafin tace"yo ni Sakina mene zai tsoratani da Nafisa yarinyar da komai nata a hannuna suke tun haihuwa,yar da na raba ta da iyayen ta ni mai iya rabata da rayuwa ne, yanzu kawai dan tana da amfani gareni ne, kada ki manta komai is under control,kafin mu rabata da gidan Marayun Nan yaya muka saka aka ƙone wannan mai shegen katsalandan ɗin,to Allah yasa Kinga ita da ƙawarta ajalinsu a haɗe yake , bari kiji wallahi yarda nayi sanadin mutuwar wadda Nafisa ke kira uwa haka zan kashe duk wanda yace zai kawo min cikas,kuma......."ƙokarin ƙara maganar ta yayi daidai da tashin hankalin da Nafisa ta shiga da motsinta da sukaji sakamakon kasa riƙe gangar jikinta da tayi.
Cikin wani irin matsanancin kuka take faɗin "su suka kashe Big Mummy da mummy Nadiya,sune Babu abin da suka yi musu fa , idan ni suke so mai yasa zasu raba su da rayuwarsu,why?"ganin irin kukan da take yasa Akram shiga tashin hankali bugu da ƙari ga maganar dake fita a bakin ta na su suka kashesu,.Ya fito ne yana tunanin ta inda zai fara ganin ta ,koda ya hangota ta kara kunneta ƙofar ɗakin Hajiya sakina,kafin ya farga yaga tana neman faɗuwa wanda dalilin haka yasa yayi saurin zuwa ya janye ta.
Ruwan da ya aje saboda shan dare ya ɗauko ya buɗe mata ya bata yace tasha,bata masa musu ba ta karɓa tasha kaɗan ta basa tana mai cigaba da kuka da a yanzu hawaye kawai ke fita,ya ma rasa ta inda zai fara dan haka yace da ita zai raka ta ɗaki ta ƙwanta idan yaso gobe zasuyi magana,bata bari ya bita ba gudun kada wani ya gansu tare duk da cewa kowa na ɗakin amma dai still ,a yanayin da take jin ta a lokacin kuwa tana buƙatar kasancewa ita kaɗai,kwanciya tayi kan gado ta cigaba da kukan ta wanda a ɗan lokacin ya fara haifar mata da ciwon kai,ita kanta akan kanta bata san yaya zatayi da maganar da taji ba, dama ta daɗe tana mamakin yarda gobara ta fara a ɗakin Big Mummy,abin abu ne na dubuwa duba domin a wannan daren wutar da suka kwanta da ita solar ce sannan ɗakin babu wani abu da za'ace yayi causing wutar ,saninta da Big mummy hatta ɗakunan yara sai ta bi ta kashe abubuwan wuta balle a kai ga nata ,tasan something was off Wanda bata taɓa kawo menene ba bata kuma cigaba da tunanin menene ba ashe Waɗannan kafiran masu zuciyar firaune ne ke da saka hannu,sai a yanzu dalilin zaɓarta da sukayi ya fara dawo mata,ashe dama mafarin komai nata sune, Ashe Hajiya Saddiqa ta san iyayenta, sannan ita ta rabata da gida ta kawota ,ta yar a wulaƙance,shin su wane iyayenta?.
Wani irin zafi zuciyarta ke yi mata kamar zata fasa kirjinta ta fito,ta rasa abin da zatayi ,ganin bacci yaƙi zuwa ga damuwa da tunani fal zuciyarta yasa ta tashi ta ɗauro alwala dan kaiwa Allah kukanta dan shi kaɗai zai iya mata magani.
Washe gari yan uwan sheɗan guda biyu suka gama yanke shawarar matakin da zasu fara ɗauka wanda shine satar takardun gidajen Alhaji da wasu kadarorinsa masu amfani su saka a ɗakin Akram sannan su tada tarzoma,samu dukkan documents ɗin bai masu wata wahala ba tunda a Office ɗinsa na gida yake aje irin waɗannan sanin shi kaɗai yake da access da gurin,amma da yake Allah ya haɗasa da shaiɗanu sai da suka san yarda suka samu mukuli suka binciko,juya documents ɗin Hajiya sakina tayi fuskanta ɗauke da Murmushi tace"Yaya ji nake kamar na gudu kawai da komai,amma sanin cewa abin da zan samu idan ba Alhaji sunfi haka dole na hakura na kora wancan la'anannen yaron.
"Shine kawai mafita,idan ma hakan bai faru ba sai mu salwantar dashi ya tafi gurin da idan yaje bazai dawo ba,so nake komai ya faru cikin saurin na koma gida dan Kinsan fa na bar kasuwanci na,yanzu dai ki zo muje a aje sai mu tafi gurin sabon mutumin da kika samu dan Nima na gwadasa duk da kuwa Alhaji yanzu yana tafin hannuna ,har faɗa mun yake zai dawo daga Cairo ɗin dana hankaɗasa nace ya zauna sai na nemesa".
Dariya sosai Hajiya Sakina ta saka tana mai jin daɗin kasancewar zuciyarsu iri ɗaya ce ita da yayarta,duk da ita ta fara ɗorata a hanya amma yanzu itama tayi nisan da muddin a kace ta dawo za'a samu matsala, menene yafi rayuwar juya mutum daɗi?a ganin ta babu domin a duk lokacin da ta saka Alhaji yayi wani abu yayi mata kai tsaye ji take kamar komai na duniya zata iya ji dashi.
A tare suka zauna dan yin breakfast kafin su fita,tun daga nesa Nafisa ke kallansu tana tunani kala kala dangane dasu,a daren jiya ta shiga tashin Hankali sosai bayan ta daɗe tana kaiwa Allah kukanta sosai ta samu sassauci cikin ranta,safiya nayi ta kira Jamal ta shaida masa abin da ke faru,shima a lokacin ji yake kamar yayi tsuntsuwa yazo garin ayi duk mai iyuwa ,amma sanin cewa shi yaƙi dan dabara ne ya saka ya taushe ta akan kada ta bari haka ya zama silar ƙaryarta, insha Allahu nasara a gurinsu take .
Takowa tayi tana mai washe haƙoranta ta gaishe su cikin yanayi na fara'a,Hajiya Saddiqa ce kawai ta Amsa banda Sakina wadda ta mayar da hankalinta kan abincin da ta ke ci,.A baya ta tsani Nafisa haka kawai bata santa amma sanin cewa akwai possiblity ɗin alaƙa ta sanayya tsakaninta da Akram sai taji ta sake tsanar ta sosai,ganin har a lokacin Nafisa bata bar gurin ba yasa ta kalleta cike da Bala'i.
"Hala sai mun ƙware zaki bar gurin nan ko?abeg idan yunwa kike ji nan gidan Akwai abincin da Bama kisan yarda zakiyi da shi ba kije ki nema, mayunwaciya kawai".
"Kina nufin ni nawa gidan da yunwa ko Sakina,"
"Kai yaya !kema Kinsan ba haka nake nufi ba dan Allah ,kawai yarinyar ce akwai ta da abin haushi wallahi,kina kallo har yanzu bata bar nan ɗin ba".
Jin abinda ta faɗa yasa Hajiya Saddiqa kallan Nafisa wadda ita kanta bata san abin da ya tsayar da ita ba,haka kawai taji tana san sake ƙare musu kallo,sosai tana mamaki idan ta tuna su biyun mutane ne da Allah ya halitta sannan sun san da cewa zasu mutu kuma akwai hisabi,amma ko a jikinsu,sun mayar da shirka kamar saka riga da cirewa,mugunta kuwa itace abincin su,to dama duk wanda zaiyyi shirka ai yayiwa Ubangijin da ya hallicesa ƙeta ina ga ɗan Adam?dukkan wani sauran rashin mutunci babu wanda baza su iya ba .
Murmushi tayi tana mai cewa"Wallahi Amah pad nake so ban san ya zanyi ba".
"Ya kike so nace kiyi?tunda Kinsan cewa watanki yazo da na faɗa Miki zamu yi tafiya ki shirya mana,kada ki batan rai akan wanda ke damuna Please kije duk yarda zakiyi kiyi".
"And please idan kin tashi kunzugu kiyi mai kyau kada kiyi mun stain a Gida muna Sallah "Hajiya Sakina ta faɗa tana mai cigaba da cin abincin ta.
Juyawa Nafisa tayi tana san tayi dariya jin wai suna Sallah,ko ta ina zata karbu kana zuwa gurin wani ya baka Sa'a tayaya bangare guda kuma zaka yaudari kanka wajen yin Sallah?.Hanyar komawa sama ta ɗauka dan dama rasa abin faɗa yasa tace pad take buƙata,.Hange take ta inda zata ga Akram,tuna daren jiya sai taji duk bata ji daɗi ba dan bata so a ce bayan shekarun nan a cikin wannan yanayin suka haɗu ba,so take ta gan shi tayi magana dashi koda kuwa basu maida alaƙarsu kamar ta da ba,ta san komai ya faru ne saboda yarinyanta,duk da bata daina yaudarar kanta ba a shekarun amma abin yayi mata sassauci dangane dashi,ganin Saffiyya kuma ya sake tabbatar mata da cewa bata da wani chance dashi,dama bata saka high hope Akai ba musamman a yanzu da komai ya canza,sun tashi daga marayu biyu da suka tashi guri ɗaya ,a yanzu kowa akwai rayuwar da yake kokawa da shi baza taso kuma ace akan matsalarta ta ƙara masa wata ba,tsakaninta da Jamal kuwa dama suna cikin wannan abin ne tare dan haka dole su riƙe hannun juna,.A lokacin da suke a tare kowa da Maganar da yake na soyayya suke,tabbas tana ganin girma da martabar Jamal,ta sani a duk rayuwarta babu abin da zata masa ta biya sa irin abubuwan da yayi mata a rayuwa amma bangare nayi masa soyayyar dake tsakanin mace da namiji bata jin haka dangane dashi musamman idan ta hangi cewa shi Zaman soyayya da Aure ya gaji sabani,Sabani kuma shine abu na farko da baza ta so ya shiga tsakanin ta da Jamal ba ,duk da cewa a yanzu ma zasu iya samu matsayin yan adam,amma ta saka aranta gwanda wannan atleast zata kiyaye tasan kuma shima a nashi bangaren abin da yake ransa kenan.
Jin Hajiya Saddiqa na ƙwala mata kira yasa ta tsaya dan tabbatarwa da ita ɗin take kira,sake ambatar sunanta da ta kuma yasa ta juya dan jin kiran me take mata,tana zuwa ta watsa mata dubu biyu tana mai cewa"gashi kije ki siya pad ɗin ,ki godewa Allah zuciyar musulunci ta taɓani ,idan kuma kin fita bana san ki je ko ina,kin sanni ai muddin kika je wanna tsinannan gidan zaki gane Kuranki,in kina ganin karya nake kuma kije ki gani".
Ɗaukar kuɗin tayi tana mai yi mata Godiya kafin ta bata tabbacin daga siyo pad baza ta sake koda taku ɗaya ba.
Da murna ta haura sama sanin zata fita waje ,at least koda bata je inda take san zuwa ba zata gana da Akram,notepad ta cire cikin jakarta ta rubuta masa zata fita ,yana jin fitar su Hajiya ya fito,kamar munafuka haka ta zaga ta tura Note ɗin karkashin kofar sa,ta juya zata bar gurin Saffiyya ta danno kai,raɓawa tayi zata wuce ta ɗan tasan haɗuwarsu ba Alheri bace, kafin ta gifta ta ta kamo hannunta ta dawo da ita baya.
"Lafiya?"ta tambaya tana mai kallanta cike da rashin tsoro,a da ma bata ji tsoran ta ba inaga yanzu .
"Lafiya?"Safiyya ta maimaita kafin ta ƙara da faɗin"idan naje na faɗawa Uwar ɗakin ki daga inda naga kina fitowa na tabbata baza ki mun wannan tambayar ba,har yanzu dai ba a daina wannan ƙwaƙwar ta mugun san rijalu ba,na san ke ba makaunyi bace nasan kuma Kinsan cewa Akram yanzu ba tsarar ki bane"
Kallan bakin ta kawai Nafisa take kafin ta fashe da dariya sosai,.Dube Dube Safiyya ta fara tana san sanin abin da take wa dariya,hannu Nafisa tasa ta nuna bakinta.
"Ba jikin ki nake kallo ba wawulo ɗinki da aka gyara ne wallahi ya bani dariya sosai,wai ke cika ba a san haƙoran roba ne a gaban bakin ki ba,kike wani buɗe su kike magana kamar wata Akuya,to bari kiji,wallahi bayan girma har rayuwa na sake gogewa akai ,idan baki fita gonata ba sai na saka hannu na na fincike wannan haƙoran da aka liƙa Miki na haɗa da na gefen su na cire Kinga sai a saka Miki huɗu,banza ko wanke su baki iya da kyau ba dan ga shi nan bakin ki yana wari".
Bangazar ta tayi ta wuce,mutuwar tsaye Safiyya tayi tana mai jin wasu hawaye na name zuba mata,saurin mayar dasu tayi dan ba girmanta bane ace ta yiwa Nafisa kuka,lokacin da ta juya already Nafisa ta ɓace da ganin ta,.
Buɗe kofa Akram yayi dan ganin ko Nafisa na gurin sakamakon Note ɗin ta da ya tsinta,yana ganin Saffiyya yayi ƙoƙarin komawa Amma kafin ya shiga ta cimasa ta hanyar faɗin"idan baka riƙe linzamin waccan karyar taka ba da kyau wallahi zai na yaga sa" .fuu ta juya ta bar gurin,taɓe baki yayi a zuciyarsa yace"kyaji da shi".wani irin daɗin yake ji da ya saka shi komawa ya shirya ya fita daga gidan dan ganin fitar su Hajiya Saddiqa da jiran fitowar Nafisa.
Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top