27
womenofwords/WA
🔏NOT ALL GLITTERS ARE GOLD💫
(BA DUK KYALLI BANE GWAL)✨
Be with 👇
*𝐴𝑊𝐸-𝐼𝑁𝑆𝑃𝐼𝑅𝐼𝑁𝐺 𝐼𝑁𝐾🥌*
Tagwayen tafiya Mai sihirtattaciyar Ma'ana ta ban Mamaki daga jerin Tawwada d'aya Al-'kalami biyu first series.
*LOKACI.!*
Halish Sultan.
*BA DUK 'KYALLI BANE GWAL.!*
Amina Jamil Adam (Chuchu jay)
https://whatsapp.com/channel/0029VaRpQeUHwXb52H0abb05
Ga masu nema daga farko 👆
Chapter 27
Koda suka isa gidan kamar za suyi maganin abin a dai dai wannan lokacin haka suka shiga ciki ,fitowa Nafisa tayi ta ɗauko jakarta da ta hajiya Saddiqa ta bi bayan su,lokacin da ta shiga falon sun riga sun haura sama,tsaki tayi ta zauna kan Kujera tana mitar dalilin da yasa ta ƙwasota,da ace ta bar ta a chan ai da ta samu damar zuwa sashen Hajiya Hadiza ko hira ne sa sha ita da Salman ,tunda yace zai bata labari basu zauna ba ,abubuwa bisa abubuwa ga case ɗin Jannah ƙwataƙwata bai barta ta nutsu ba,Wayarta ta jawo tana mai duba saƙon da ya shigo mata daga Jamal dangane da Muphida,ɗiyar macece Zafira Adam,ita ɗin yar kasuwa ce mai fita ƙasashe tana saro kaya, mahaifinta ya rasu ita kaɗai ce ƴar su, mahaifiyar Muphida a kullum bata da time ɗinta dan a wata sau ɗaya suke cin abinci a tare.
Tsaki Nafisa tayi."ba dole yarinya ta shiga matsala ba babu wanda zata zauna ta faɗawa,".Aje wayar tayi a cinyar ta tayi relaxing kan Kujerar tana mai lumshe ido,dole case ɗin Muphida sai ta koma Nassarawa,tana da yaƙinin party ɗin su Khafilat in a week time ne wanda tasan kafin nan sun koma gida.
Tunda Hashim ya shigo falon idanun sa suka sauka kan Nafisa wadda idanun ta ke a rufe kamar mai bacci,leɓensa na ƙasa ya ciza yana mai shiga tsakiyar falon yana Kallanta bai tsaya a nan ba har sai da ya isa gabanta ya durƙusa yana mai ƙare mata kallo yana murmusawa,jin kamar ana kallanta yasa ta buɗe idanun ta a hankali,Washe mata haƙora yayi inda nata bangaren ba tayi wata wata ba wajen saka hannunta a fuskarsa ta hankaɗesa kafin ta tashi tsaye tana tambayar sa lafiya yake mata kallan ƙurilla?
Dariyar Nana A'ishah data riskesu ce yasa Nafisa kallan ta ,nuna Hashim take tana dariya kamar mahaukaciya kafin ta nuna Nafisa then ta sake nuna sa.
"Kai wai mayen mata ko,daga ganin mace zaune kaje kana kallonta kamar zaka lashe,naso ta cire maka ido ai".
"Dan ubanki da ni kike?,waye mayan matan?".Ya faɗa a fusace yana mai shafa inda Nafisa ta karcesa da farcenta.
"Sai dai in uban ka ba nawa,banza ɗan iska an faɗa mayen mata ,idanun ka idan mata me zaka iya ,zaka dake ni ne?".
Kafin ya amsa mata aka buɗe kofar falon,a tare suka kalli mai shigowa kafin Nana A'ishah ta haɗe rai.
"Ga wanda yafi ka maita ai,ni tunda nasan maitar ka banyi tunanin wani zai Fika ba,jarabbabe Mayen dukiya".
Dariya sosai Hashim yasa ga furucin ƙanwarsa yana mai manta cewa faɗa suke,da ace Akram bai shigo ba da yanzu suna ƙokawa da juna,.Ko takansu Akram bai bi ba,yana ƙokarin wucewa dan haurawa sama idanun sa suka gano masa gefen fuskar ta,har ya wuce ya dawo da baya jin wani irin faduwar gaba da yaji ya ziyarce sa,gaban ta ya isa wanda yin hakan yayi dai dai da ɗago idanunta ta saka cikin nasa,da mamaki suke kallan juna dan yau koda kuwa shekaru ɗari sukayi ba tare da saka juna a ido ba babu yarda za'ayi su kasa gane juna,take idanun Nafisa suka ciko da ƙwalla lokaci guda kuma baƙinta ya fara karkarawa,ji tayi harshen ta kamar ya karye duba da yarda take neman magana amma ta gagara samu ta furta.
"Ashe dai bani kaɗai bane mayan mata har da ɗan uwan mu na bogi Akram,kina kallo ko Nana A'ishah yarda ta jawo sa kamar magnet?lallai yarinyar nan hot cake ce dan ni wallahi sai da ta tashi naga ɗuwawu iya ɗuwawu ba irin naki kamar an taka leda ba".
"Daɗinta na Mummy ma haka yake kaga ba a banza yake a shafe ba na uwar ka ma haka yake banza kawai mai ƙaton baki duk hayaƙi ya gama ƙona sa".
"Mene ke faruwa anan gurin?"Muryar Hajiya Sakina ta katse musu chachar bakin da suke yi tsakanin su,juyowa Nana A'isha tayi tana mai ƙaƙalo kuka tana faɗin ai Hashim ke zagin mata Hallita ,saukowa Hajiya Sakina tayi Hajiya Saddiqa biye da ita kafin tace"to dan uban shi ya Miki wata,ko kuma ya kashe ki ,yauwa yaya kinga shegen Allah yayi ya shigo,ni ban ma ta gilmawar tsinaniyar yarinyar da yazo da ita ba duka tun safe "ta mayar da maganar kan Hajiya saddiqa wadda baki ɗaya hankalin ta na kan Akram dake gaban Nafisa,duk da Nafisa ta juyo tana kallansu amma shi nashi idanun na kanta ,ya kasa gasgata abin da yake gani,amma duk wanda zai faɗa masa wannan ba Nafisan sa bace zai ƙaryata sa ,dan babu yarda za'ayi ya kasa gane Nafisa duk da girma da kyan da ta ƙara.
"Wannan ne ɗan Alhajin?"
Juyowa Akram yayi karan farko yana mai kallansu kafin ya mayar mata da amsar tambayar ta da.Eh shine zakiyi wani abu a kai ne?.
Takowa gaban sa tayi ta kama hannun sa bakin na kumfar bala'i take faɗin , Akwai abinda zanyi,yau sai ka bar gidan nan,baza kazo ana zaman lafiya ba ka lalata sa,gidan nan na Sakina ne da yaranta wallahi babu wani Shege da zai zo rana tsaka yace shima ɗa ne sai dai muna ɗa,tun Muna mutunta juna kazo ka tattara tsummokaran rayuwar ka kayi gaba".
Hannunsa da ta riƙe yayiwa ƙwacewar da har sai da ta kusa faɗuwa kafin ya kalleta da kyau."To dama ai ni a ganin ki banga alamun mutunci ba ballantana na mutunta ki,it's okay idan kin mutuntani tunda dama ni ai irin mutunci ne ,amma daga ke har ƙanwar taki ko yaranta banga irin mutunci ba,dan Allah hajiya Kinga magana ake ta Family kada kisa bakin ki nazo na aje tarbiyya ta nayi abin da babu wanda zai mamakin nayi ,Kinsan a ɗan zaman da nayi da Mummy ta lasa mun rashin mutunci,ki kiyaye ".
"Kada ka sake kirana Mummy "Hajiya Sakina ta faɗa tana mai jin kamar ta kashe sa a lokacin kowa ya huta.
"Matar babana ai mahaifiya tace,kuma kada ki manta farkon zuwan ki gidan nan ke kikace na kira ki da mummy dan wallahi sai na faɗa,bari ni na shiga daga ciki nayi wanka".gittawa yayi ta gefen su ya wuce duk da kuwa zuciyar sa na jan sa ya koma ga Nafisa amma a yarda ya karanci yanayin yi mata magana a yanzu ba dabara bane, Tambayoyi ne a kansa da yawa wanda ya san ita kaɗa zata bashi amsar su.
Tafi Hajiya saddiqa tasa bayan wucewar Akram kafin ta kalli Nafisa da kallan tuhuma,idan idanunta sun gano mata dai dai kallan sani take masa?to a ina ta san sa ,shin daga ina ya fito ,ina yake duk tsawon wannan shekarun,.Sauke ido Nafisa tayi ganin irin kallon ƙurilla da take mata,rasa abin faɗa tayi ta kuma rasa inda zata kai tunanin ta,so Akram shine ɗan Alhaji?bata gane tayi missing ɗin sa ba sai da ya kasance a gaban ta bata da ikon yi masa magana,kashe tension ɗin dake gurin tayi ta hanyar tambayar ɗakin ta,sai da tayi tambayar itama taga wautar ta.
"Tunda gidan uban ki ne a baki ɗaki mana Shegiya,Ni yaya ban san larurar da yasa kika taho da wannan ba ake maganar gaban ta ba".
Gumtse baki Nafisa tayi dan dariya ke neman ƙwace mata ,muddin kuma ta bari ta fito a yanayin nan to kafin a watsar da ɗan Alhaji waje za'a watsa ta.
Banko ƙofa da a kayi yasa baki ɗayan su kallan ƙofar falon ,Safiyya ce ta shigo da izzarta ,tana ƙoƙarin wuce su Hajiya Sakina ta kamota ta dawo da ita baya tana mai faɗin."yaya Kinga matsiyaciyar da ya kawo wadda ke nema ta fisa gadara".Fincikewa Saffiyya tayi tana huci tana mai kankarawa Hajiya Saddiqa ta hanyar kaɗa mata yatsa akan kada ta sake ƙwatantawa,kwasam idanunta suka sauka kan Nafisa,ganin kamar gizo idanunta Kemata yasa ta ƙarasa gurin da take tsaye ta kama hannun ta ,da mutuƙar mamaki ta ambaci sunanta dan wannan ta wuce kama .
Fizgewa tayi tana mai Binta da kallo mamakin kasancewar ta a gida fal cikinta,wani tunani zuciyarta ta faɗa na shin ko ita da Akram sunyi Aure ne.
"Dama ni a yarda munafukar yarinyar na ke kalla Akram jikina ya bani Akwai wata magana,ashe kuma da akwai ɗin,dan ubanki ina kika san su??"..Kallan Hajiya Saddiqa Saffiyya tayi kafin ta saka dariya tace"Wai Nafisa?ta haɗu da Akram kenan,to Nafi dai wata sheɗaniyar yarinya ce da ta adabi kowa a cikin gida Marayun Alhaji,duk wanda zaka tambaya halayyar ta babu mai faɗa maka alheri ta adabi kowa ta hana kowa rawar gaban hantsi,a bangare guda kuma Babu wanda bai san ta ba waje obsession na Akram,duk inda yasa ƙafa zata saka tata,to ni da ba Aikin jarida nayi ba da zan cigaba da zuba ba, abin ya saka na fesa muku kaɗan kuwa ba komai bane face ƙiyayya,ina cikin masu bada bad testimony akan ta ,duk wanda ya ƙwashe ta sai ta tarwatsa sa ta hargiza masa ƙwanciyar hankali dan wannan yarinyar ƙanwar shaiɗance,yafi ku samu gurin da ya dace da sheɗanu ku aje ta, it's a friendly advice.
Tana kai aya ta bar musu gurin tana tunanin dalilin zuwan Nafisa gidan,last abin da take so shine a kawo mata cikas cikin al'amuran ta,.
"Yanzu ki fara mun bayani ko na shaƙeki menene gaskiyar abin da waccan ta faɗa a nan gurin,bana san kuma ki mun karya".
"Amah bana tunanin ina da wani lafi dan na san su,kowa da abin da zai faɗa dangane da kai idan kace Kuma zancen da wani zai bi shi zai dameka kullum a baya kake,tabbas na sansu ,tare muka tashi gidan marayu,amma ba hakan ke nufin ina da Alaƙa da su ba ,idan ma ina da ita alaƙar a dane wadda a yanzu da ita da babu duk ɗaya ce,loyalty ɗina ke na bawa babu wanda ke gaba dake guri na a duniyar nan,waccan kuma kawai tana zancen ta saboda abin da ya sha giftwa tsakanin mu na yarinyata,bayan shi babu wani abu,Akram kuma shine mutum na karshe da zan so nayi mu'amala da".duk wannan maganar da take kan kunnen Akram da ya fito daga ɗakinsa dan ganin ko sun wuce.
"Ni yaya ba fa maganar Akram da wata Nafisa ke gaba na ba,yarda za a kamo bakin zaren nan shi ya dame ni"cewar Hajiya Sakina wadda ta ƙosa ayi mai iyuwa..Dariya Hashim dake zaune gefen Nana A'ishah yayi yana mai faɗin "Ni wallahi komai daɗi yake mun ,ayi ta tashin hankali kar a bari as far as dukiyar mu na tsare,Nasan kuma idan da mummy da babbar Hajiya komai a tsare yake ko ƙanwata?"
"Aikuwa wallahi".
Ajiyar zuciya Hajiya Saddiqa ta sauke tace da Nana A'ishah ta kai Nafisa guest room kafin ta ja hannun Hajiya Sakina suka fita a falon.
Kai kawo kawai Akram keyi a ɗakin sa yana tunanin yarda zai ga Nafisa ,yasan cewa maganar da ta faɗa ba har zuciyar ta bane ,so yake ya ganta yaji ina take duk shekarun nan sannan mene haɗinta da waɗan nan sheɗanun,a hirar da sukayi da Isma'il earlier ya faɗa masa tana Nasarawa karkashin wata mata amma information ɗin ta is close, dawowarsa gida yana tunanin yarda zai shawo kan lamarin ya fara nemanta ,a duk yarda yake imagining abubuwa bai taɓa tunanin zai shigo gidan yana tunanin ta ba kwasam kuma ya ganta cikin gidan a falo tare da su Hashim,san sanin abin da yake faruwa shine abu guda da yake neman tarwatsa masa ƙwaƙwalwa,yana wannan Safa da marwa ɗin Safiyyah ta buɗe ɗakin sa ta shigo,ɗago kai yayi ya kalleta."ba na hanaki shigo mun ɗaki kai tsaye ba?mene yake damun ki,ki nemi izini idan an baki sai ki shigo idan ba'a baki ba ki juya,shine abin da matured mutane keyi".
Murmushi tayi ta samu gefen gadonsa ta zauna tana mai faɗin"congratulations,Allah ya haɗaka da Nafisa,I'm impressed da yarda na ganta,ta haɗu amma batun improvement na ƙwaƙwalwar bana tunanin an samu cigaba dan once jaki is always a jaki,amma kana tunanin cewa dawowar wannan yarinyar rayuwarka ba Anoba bace?Ni dai a yarda na hanga annoba ce dan tana tare da Mutanen da suke nema duk wata hanya da zasu bi dan suga bayanka ,ka dai bi a hankali shawara ce "tashi tayi bayan ta gama zubar ta zata fita,baice mata uffan ba har ta fita a ɗakin, komawa yayi kan gadon sa ya ƙwanta yana mai jin zuciyar sa babu daɗi,ko yaya ne yau dole ya ga Nafisa koda kuwa ba suyi magana mai tsayi ba.
Da dare babu wanda yazo dinner dan tun zuwan Akram komai ya tsaya chak,babu mai haɗuwa da kai gurin cin abinci,Akram na zaune yana duba wayarsa yaji ana masa knocking,tasowa yayi ya buɗe,cook zaliha ce tsaye tana ma yi masa fara'a yayin da ya gaida ta cikin mutunci,Sanar masa da kiran da Alhaji ke masa a Office ɗinsa na gida tayi sannan ta bashi abincin darensa,godiya yayi mata ciki da girmamawa kafin ya koma ɗakin yana tunanin yaje kiran Alhajin ko kada yaje,daga bisani ya amsam tayi zuciyar tasa na zuwa yaji dalilin kiran nasa.
Koda ya shiga Office ɗin yana zaune kan Office chair ɗinsa Yana duba wasu files,zama yayi yana mai kallansa kafin yace "ina wuni".kamar a mafarki haka yaji gaisuwar,aje file ɗin da ya buɗe yayi ya amsa shi kafin ya ƙara da cewa"wasu aikin ne baka samun damar yinsu a waje sai a gida ,yanzu haka wani ƙaramin aiki nake san ƙarasawa,abin ne sai a hankali, software engineering ka karanta ko?
"Eh"ya bashi amsa a taƙaice kamar baya san yayi maganar dan har ga Allah baya san doguwar hira shi muddin ba bayani zai bashi kan abin da ya faru ba.
Kula da haka yasa shi cewa"kayi haƙuri Akram,duk abin da zan faɗa maka bayan haƙuri ne ,ina san kuma ka sani duk wani abu da ya faru gata nayi maka,kaga Sakina ƙwata ƙwata ba mutuniyar arziƙi bace,idan kuma ka haɗa su guri ɗaya da Saddiqa to komai ya lalace,da fari da na Aure ta mutuniyar kirki ce,a baya da mahaifiyar ka ta rasu na daɗe ban fita daga Alhinin mutuwarta ba musamman idan na kalleka naga ƙarancin shekarun ka ,shine babban dalilin da ya Saka na sake aure,a yarda ta nuna kai nata ne sai hankalina ya fara ƙwanciya,ban farga ba har sai a aka kai lokacin da ta fara azabtar da kai da yunwa,ina kallo zata dakeka tayi mai horo Wanda hankali bazai ɗauka ba,bana iya ɗaukar mataki a lokacin ba dan bazan yi bane saboda bazan iya ba sakamakon Asiri da take mun wani kan wani,duk da yana kamani amma wani lokacin yakan sakeni duba da bana wasa da addu'a da neman tsari".
"Sakina nada sharri fiye da yarda kake tunani,Wata rana tana ɗakina muna bacci aka Kirata a waya,a ranar Naji tana maganar kashe ka,Ni ba mazauni bane,idan ma na zauna bani da ƙarfin yin katabus,sanin bazan iya zama na rasaka ba yasa na haɗa labarin mutuwar ka lokacin ta Saka ancire brake ɗin motar da kake ciki,da kyar na samu aka cire ka a motar dan saura kiris na rasa ka,koda aka kaika asibiti likita ya sanar Dani ka samu memory problem da naga haka yasa na ɗauke ka na kaika gidan Marayun Alheri domin ka sake rayuwa sabuwa,a lokacin na damƙaka hannun Hafsatu(big mummy) wadda ita kaɗai tasan kai wane kuma ta rufe sirrin hakan Allah yayi musu rahma, "
Akram na kaika ne amma ban manta da kai ba ,duk wani motsin ka ina sane dashi,lokaci kawai nake jira na dawo da kai gida,na maka alƙawari babu wani abu da nayi dan watsar da kai, Hashim da Nana A'ishah yarana ne amma ba dan a gaban ka bane ,bana jin su kamar yarda nake jin ka zuciya ta ,kayi mun hakuri Akram ka bani damar gyara lokacin da muka rasa duk da baza mu maimaita su ba.
Shiru Akram yayi lokacin da ya gama jin bayanan mahaifin sa,ba wai bai yarda dasu bane amma ya rasa inda zai aka su a zuciyarsa ko zaiji sanyi,shin idan har yasan Asiri take masa sannan ta a neman rayuwar sa da ya gane mai yasa yake tare da ita har yanzu?
Kasa riƙe abin yayi a zuciyar sa har sai da ya tambaya,cike da kulawa yace masa "bana jin dadin zama da sakina amma a hange da tunani da nayi rabuwa a ita ɗin ba shine mafita ba, after all mun haɗa zuri'a idan kuma nace zan rabu da ita a yanzu sai taje ina?na aure ta tun tana da iyaye yanzu babu su bai kamata ace na sake ta gejin nan ba ".
"Well kayi haƙuri Daddy ba bazan ƙi faɗa maka gaskiyar muddin har yanzu baka ji a zuciyar ka zaka rabu da ita ba to tabbas har yanzu baka warke daga duk wani abu take maka ba,a labarina kuma abu ɗaya nake san faɗa maka wanda shine babu wani losing memory da nayi,koma was intact,shine dalilina na zuwa dan na ɗauki fansa,amma da na zauna nayi tunani sai naga menene zan ɗauka fansa duka a ciki?babu i just need my home ,my Father and my identity, kayi hakuri idan a yarda nazo maka ya ɓata maka rai,komai kuma ya wuce a guri na".
Wasu hawaye Alhaji Muhammad yaji suna Zarya kumatun sa ,bai taɓa tunanin samun yafiyar Akram nan kusa ba,tasowa yayi ya kamosa daga zaunen da yake ya rungumesa yana mai yi masa godiya, murmushi Akram yayi jin ɗumin mahaifinsa a jikin sa ,abune wanda ya gama cire tsammanin zai samu.
Da dare Nafisa na zaune wuraren karfe Goma tana mai Tunani kala kala,so take taga Akram amma bata san ta yarda zata fara ba,dan haka wurin shaɗaya da taji gidan yai shiru ta fito a dakin ta ko Allah zai sa ta yi arba dashi sanin cewa duk inda yake a yanzu shima hankalinsa yana kan ta,tana ƙoƙarin wuce wata ƙofa taji alamun ana magana a ɗakin,Waige Waige ta fara,ganin babu giftawa kowa a gurin ga dim light yasa ta kara kunneta bakin ƙofar dan jin abin dake faruwa a ciki,.tashin hankali na maganar da ta tsinta yasa taji juwa ta kawo mata ziyar,bata san lokacin a bayanta ya daki flower base Dake kan table a gurin ba ya faɗi,tambayar da akayi na Wane karfi yayi daidai da janye ta da akayi cikin duhun gurin inda ƙofar ɗakin ta buɗe Hajiya Saddiqa da Sakina suka bayyana.
Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top