26

womenofwords/WA

🔏NOT ALL GLITTERS ARE GOLD💫

(BA DUK KYALLI BANE GWAL)✨

     Be with 👇

*𝐴𝑊𝐸-𝐼𝑁𝑆𝑃𝐼𝑅𝐼𝑁𝐺 𝐼𝑁𝐾🥌*

Tagwayen tafiya Mai sihirtattaciyar Ma'ana ta ban Mamaki daga jerin Tawwada d'aya Al-'kalami biyu first series.

*LOKACI.!*

Halish Sultan.

*BA DUK 'KYALLI BANE GWAL.!*

Amina Jamil Adam (Chuchu jay)

https://whatsapp.com/channel/0029VaRpQeUHwXb52H0abb05

Ga masu nema daga farko 👆

Chapter 26

   Yau ya kasance kwana huɗu kenan tunda Akram ya dawo gidan Alhaji Muhammad,babu abinda ke shaƙawa Hajiya Sakina kamar yarda Alhaji ya ƙi cewa komai dangane da batun gudan ma kada ta cikasa da tambayoyi a kwanakin ƙwata ƙwata bata sanin dawowarsa gida sai dai taji fitar sa,ganin haka yasa yau karfe 3 na dare ta shiga ɗakin sa dan tuhumar sa,ta daɗe tsaye kan sa tana shawara da zuciyarta akan ta tashe sa ko kar ta tashe sa,da yake bala'i ke cinta ba tayi wani tunani ba ta fara dukan ƙafar sa.

"Alhaji ka tashi muyi Magana, Alhaji,ka tashi" .

Cike da baccin dake kansa sosai ya buɗe ido yana kallanta , glasses ɗin sa dake taimaka masa wajen gani ya laluba yasa kafin ya kunna wutar gefen gadon sa yana mai tambayar ta lafiya.

"Zaka tambayeni Lafiya mana idan ka gama aikin guje gujen ka , maganar Akram ce ,Kasan dai banzan zauna inuwa ɗaya dashi ba, wallahi a san mafita dan bazai taɓa saɓuwa bane ".

"Me kike so ki faɗa mun?shin Bazai taɓa saɓuwa ba ta yaya,kina so kice mun kin Cire Akram daga sahun yara na ne zaki shigo mun ɗaki ki tasheni tsakar dare kin mun maganar banza".

"Aw maganar banza ce ma Alhaji,to wallahi Ni dai na faɗa maka nawa ,da ace tunda shegen yazo Baka fara was buya dani ba ai babu abin da zai saka na bi dare , wallahi kaji kunyar ƙarya Alhaji,da girman ka ashe kaina makaryaci ne,to wallahi lahirar da kayi ikirarin Akram na can sai ya koma" .

Cire Glasses ɗin sa yayi ya kashe fital ya kwanta yana mai faɗa mata ta mayar dashi idan zata iya amma kafin nan ta fitar masa daga ɗaki,cike da kumfar baki ta juya ta fita tana faɗin zata mayar dashi ɗin ne idan bai wasa ba,.Haka nan ta koma ɗakin ta duniya tayi mata matukar zafi,wayar ta da ɗauki tayi dialing number ɗin Hajiya Saddiqa cike da damuwa ,sai da ta mata kira wajen huɗu tukunna ta ɗauka.

"Mena haka Sakina kin duba lokaci kuwa zaki kirani da wanann daren?"

Kuka sosai ta fashe dashi tana mai zayyana mata abin da ya faru,kamar tana Kallan ta take mai taɓa saitin zuciyarta tana cewa .

"Wallahi Yaya bazan iya raba dukiyar Alhaji da Akram ba,kuɗin Alhaji da duk abin da ya mallaka nawa ne da yarana dan mene rana tsaka kawai Akram zai dawo,inace he's suppose to be dead to me yake a duniya a cikin gidan mu,Allah Yaya sai ya koma".

"Naji zai koma amma ki samu kiyi bacci yanzu gobe da safe zanzo Yoben sai musan yaya za'ayi dashi amma dan Allah Sakina ki barni nayi bacci tukunna"bata jira abin da zata ce ba ta kashe wayarta ta koma ta ƙwanta dan kwana biyu bata samun isasshen bacci.

Haka nan Hajiya Sakina ta ƙarasa daren ta tana aikin kuka,Sabon bokan ta ya mata hangen gaba kuma ya shaida mata muddin Akram na raye ita da yaranta babu Abin da zasu samu,bugu da ƙari ga sirrin da take aikin boyewa wanda aka tabbatar mata idan Akram ya dawo jikin Alhaji cikin lokaci kaɗan zai tarwatsa mata komai sirrin ta ya fallasa , wannan kuma shine abin da baza ta taɓa bari ya faru ba dole ne ta ɗauki mataki na gaba ɗaya.

    Washe gari da safe tunda ta tashi take kiran Hajiya Saddiqa taji ko ta taho,tana wannan Alhinin zaune a falo Saffiyya ta sakko tana mai ƙwalawa Mai share share su Ramma kira kamar zata fasa kunnen kowa,ignoring ɗin ta Hajiya Sakina tayi dan last abin da take buƙata a yanzu shine damuwa bisa kan damuwar dake tattare da ita ,.Da gudu Ramma da Saffiyya ke kira ta fito daga ɗakin baki na kasa da take gyarawa,kafin tace tak Saffiyya ta ɗauke ta da mari,buɗe baki tayi da mutuƙar mamaki dan bata tuna yiwa Saffiyya laifi ba ,idan ma tayi mata bata tunanin dacewa ne Saffiyya ta ɗaga hannu ta ɗauke ta da mari haka tunda tasan cewa a haife ta haifi irin Safiyya biyar.

"Wannan shine na karshe da zaki kuma gyara min ɗaki ki fesa mun room freshener ɗin da kika saka mun ,idan hakan ya sake maimaita kansa wallahi ki kuka da kanki,iskancin banza kai ,ki rasa wane irin room freshener Zaki saka mun sai irin wanda ke tashi a asibiti ko ɗakin talakawa ,ki kiyaye ,dan wallahi zan iya korarki ".

Mamaki ne ya cika Hajiya Sakina dake zaune a falo ganin abin da ya faru,tasowa tayi ta nuna Safiyya da hannu.

"Come ke har kina da Audacity ɗin kiran mai aiki na ki mareta har kike ikirarin korarta?,"dariya tasa ta takaici kafin ta ƙara da cewa"Gaskiya ne dama Kinsan ance idan tsintacce ya samu guri bai iya ba, wato zaki kore ta?"

Hannayen Saffiyya ta haɗe a kirji tana mai girgiza ƙafa da murguɗa baki.

"Ta kuma ki gani,last da na tuna Akram shine babban yaran gidan nan kuma shi ta kawo ni ɗan haka ina da dukkan wani right da dukkan wani kasƙantace dake cikin gidan nan duk tsufan sa".

Bata jira jin ta bakin Hajiya Sakina ba ta koma tana ma faman kaɗa mata jiki kamar wata mazari,mutuwar tsaye kawai Hajiya Sakina tayi kafin ta iya faɗin"this is amazing".Bata Kalli inda Ramma take ba ta haura saman dan zuwa ɗakinta ta ɗauki car keys ɗin ta dan zuwa airport ta jira zuwan yayar ta ,baza ta iya ɗaukar abin da ke faruwa ba ,no this can't be happening.

Safiyya kuwa koda ta shiga ɗakin ta gadonta ta faɗa tana mai mayar a ajiyar zuciya,dole zata yi wani abu da rayuwar ta ,ta fahimci cewa babu Abin da zatayi Akram ya fahimci inda ta dosa,babu yarda za'ayi ta koma rayuwar gidan Marayu ta kasanci sannan babu yarda za'ayi ta yarda ta zauna a talauci da wulaƙanci,ranar da Akram ya kawo ta gidan bai sanar mata gidan mahaifin sa zasu je ba amma ta da duk inda zai kaita yafi wanann shegen gidan Marayun,bata gama shan mamaki ba sai da taji wai Alhaji Muhammad Mahaifinsa ne,tunda take bata taɓa tunanin zata taɓa ganin Alhaji Muhammad ba sai gata karshe cikin gidan sa tare da ɗansa ,wannan kaɗai ya isa ya tabbatar mata da cewa baza ta sake komawa slum ba ,iskar Turai da abincin gurin da rayuwa a chan ya mata taɓawar da baza ta taɓa yarda ta koma inda bata da maganar karshe ba,a rayuwarta tana so taga mutane a ƙarkashinta tana yagasu suna bin ƙasar da take takawa sun lasa ,a Kallan rayuwa ta bangare mai kyau kuwa bataga cewa Akram zai iya bata ba,ko zai iya bata baya da niyya ,da fari Rayuwar Nana A'ishah take san taga tana irin ta,mahaifi mai kuɗi,gida mai kyau ga mota ga waya mai tsada ga uwa mai izza amma da ta zauna tayi tunani sai taga itama izzar take so,bata sake ƙwaɗaituwa da hakan ba sai a ta hangi ɗakin Hajiya Sakina daga nesa ,ga wata arniyat mota a take ja,a yarda ta tsinci tana magana da Hashim ma ita ke kulawa da gidan Marayun da suka fito,shin yaya zai kasance ace yau itace ke da mukullin asusun Alheri orphanage?,tunani kawai nishadi yake saka ta inaga hakan ya tabbata?,muddin kuwa tana san haka su ta samu Alhaji Muhammad Tukur a hannunta ta hanyar Aurensa tunda ba Haramun bane a musulunci sai dai Akram ya ga kamar tayi masa butulci amma a nata bangaren tana kiran hakan a gyara rayuwa.

Murmushi kawai take kamar wata wawuya kafin ta ɗaga wayar ta da kiran ƙawar da tayi a Ohio muheeba, ringing ɗaya ta ɗauka tana mai hailing ɗinta kamar yarda ta saba.

"Hajiya ta mayyar Akram,mai tsoran Salman,talauci kauce arziƙi taso ".

Dariya tana kafin ta tashi ta sakawa ƙofar ta key ta dawo ta zauna tana faɗin "ki daina tuna mun da Salman wanann tsinanen da ya hanani rawar gaban hanci ,and guess what ta wani bangare ya kyauta mun dan a ace ya barni dana ɗauki wuƙa na daɓawa kaina da kaina,girl talauci kauce ,arziki zo,ko Kinsan a yanzu haka ina cikin gidan su Akram?and a yanzu haka maganar da nake Miki Har gobe mahaifin Akram yana cikin Mayun masu kuɗi a ƙasar nan"

"Ke bari dan Allah?yanzu haka kina gidan su fa kikace mun,Omo kaini mana maye plan ɗin ki dan nasan ke mayya ce wajen haɗa tuggu".

Dariya sosai Saffiyya tasa tana mai faɗin,ki ƙara ki sake faɗa ta waje na yanzu ba gama batun Akram na uban sa nake ,kin sanni idan na saka kaina guri ɗaya sai na cusa ,to a yanzu ma sai na kai sai dai kiji Akram na kira na Aunty.

Dariya suka saka tare suna masu Sharing idea ɗin yarda zasu kamo bakin zaren,tana wannan iya shegen Akram ya ƙwankwasa mata ƙofa,kamar baza ta buɗe masa ba amma sai ta buɗe ɗin tana mai tambayar sa lafiya?da mamaki ya maimaita tambayar Tata yana mai cewa"idan na tuna ni da ke yau zamu gida Alheri we talked about this so mene Kike tambaya ta lafiya?.

Juya masa baya tayi dan ita iskar dake cikin gidan ma ba san shaƙa take ba ballantana har akai ga tayi mu'amala da mutanen gidan,."Ni bazan ja ba Akram kai dai a ka rantse sai ka komawa bayan ka kaje kace ina gaishe da kowa da kowa,beside bana jin daɗi baza iya fita ba ".

Mamaki bai barsa ya sake cewa komai ba ya juya ya fita yana mai jinjina ɗabiun Saffiyya,anya yayi wa kansa dabara kuwa da yake ƙokarin taimaka mata? maganganun Salman yake tunawa inda yake ce masa ya kiyaye jan Saffiyya jikinsa ba Alheri bace,sau da dama idan ya faɗa masa haka sai dai yace masa suyi tunani mai kyau a kanta ,bazai manta Alheran Saffiyya a gare shi ba tare suka tashi tsakanin su akwai fahimta mai kyau a da sannan ita ta tsaya masa lokacin da yake cikin yanayi na rashin sabo da damuwa she was there dan haka yake tunanin bata rayuwa mai kyau shine kawai abin da zaiyyi ya biya ta dan bazai karya ba sosai Saffiyya ta taimaka wajen saita a emotionally amma wannan saffiyar dake gabansa yana nema ya kasa gane ta.

Tsaki tayi baya ya fita tana mai faɗin kaɗan ma ka fara gani yanzu da na san inda alƙibikata ta nufa".

______

    Kamar yarda Nafisa ta buƙaci Akram yayi hacking wayar Khafilat hakance ta kasance ,sosai Nafisa ta shiga cikin mugun mamaki lokacin da ta shiga chats ɗin Khafilat,ta kasa yarda da cewa yarinyar nan yar shekara goma sha bakwai ce,at that age har ta iya ayi connecting ɗinta da manyan hajiyoyi ko manyan mata marasa kuɗi da iskanci tana biyansa ta hanyar satar wa Hajiya Saddiqa kuɗi.

Abun bai sake shocking ɗinta ba sai da taga last transaction receipts ɗinta ta turawa wata mata Dubu ɗari shida dan kawai tayi lalata da ita,da tabi chats ɗin su tana karantawa abin shock her sosai da sosai,wani group chat da akayi naming da IFgirls ta shiga,ta mutu zaune da taga yarda suke Sharing nudes ɗin su da chats na ƙazanta da suke tsakanin su,she just can't believe cewa khafilat is beyond tunaninta ,Ganin last chats ɗin su suna magana akan exploiting wata yarinya ma suna Muphida ranar party ɗin su yasa ta sake shiga damuwa ,she needs to know more about wannan Muphida ɗin da a yarda ta fusknci chats ɗin nasu yarinyar a school ɗin su take and ita victim ce ta molesting and bully acts ɗinsu,Haka ta cigaba da bin chats ɗin nasu har ta faɗa wani group chat da ke da tabrin kan ƙwarangwal da ƙafafu,sosai hankalin ta ya tashi da taga Cult ne na lesbians da suke baka Charms na dukkan macen da kake nema in ruturn ka bada wani abu,hannu tasa a bakin ta ,jin an buɗe kofar ta yasa tayi saurin kulle Mini system ɗin ta Akram ya siyan mata tana mai Kallan ƙofar,binta da Kallo Hajiya Saddiqa tayi kafin ta tambaye ta ko tayi missing wani abu da ya kamata sani?

Saurin kaɗa kai Nafisa tayi tana mai cewa"a'a ina kan aikine ,wanann system ɗin kuma da dashi nake amfani so ina creating wani designs na tashin sense ne,

Kallan ta kawai Hajiya saddiqa take kafin ta kalli system ɗin .

"Zan so na gani amma yanzu bani da lokaci,ki ɗauki kayan ki na guda Biyar da ita zamu je Yobe bazan kuma iya risking barin ki a nan gidan ba har ba kwana biyar,ban maki wannan yardar ba,kafin kuma ki tambayeni ba za kije wannan ƙazamin gurin da kike kira gida ba get ready yanzu zamu wuce ".

Ta wani bangaren taji daɗi zata je yobe amma ta wani bangaren guda kuma tana jin takaicin zata shiga garin amma baza a barta taje taga yan uwanta ba,tana mutuƙar kewarsu musamman Khadija,Hamama ,Sa'adatu da Suwaiba,Baza tayi karya ba Hatta Asiya tayi missing ɗin ta,rayuwarta baki ɗaya tana gurin,bakin cikinta guda ɗaya ne shine na rashin sake Saka big mummy da mummy Nadiya a idanunta.

    Koda suka sauka a filin jirgi already Hajiya Sakina na jiran su,suna zawu inda take ta taso da kukanta ta rungume Hajiya Saddiqa tana mai bare bakin ta kamar kwano.

"Yaya"

Ganin haka yasa Nafisa taɓe baki tana mai tuna furucinta da take faɗa mata ita muguwa ce ,ko mene ya saka muguwa kuka?.Kamar bata so ta gaishe ta,bata amsa mata ba hasalima ko inda take bata kalla ba.Tunda suka ɗauki hanya babu wani zancen kirki da suke illa yarda za'ayi da dan Alhaji,a zuciya Nafisa tace "kai kuwa ɗan Alhaji ka shiga uku ,na ƙosa naje naganka, naga wanda ya razana muguwa har sai da ta nemo ɗaukin yayar ta".

A/N

Assalamu alaikum fatan kuna cikin ƙoshin lafiya,kuyi hakuri kunji ni shiru amma na muku ƙoƙarin two pages,so I went through writer's block,😂but I'm over and Insha Allahu I will give you guys a better ending,the romance is about to start,fr I know wannan yana cikin litattafina na farko da yayi lacking Romance, but Insha Allah the message will be meaningful .

Not edited

Xx♥️

Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top