25
womenofwords/WA
🔏NOT ALL GLITTERS ARE GOLD💫
(BA DUK KYALLI BANE GWAL)✨
Be with 👇
*𝐴𝑊𝐸-𝐼𝑁𝑆𝑃𝐼𝑅𝐼𝑁𝐺 𝐼𝑁𝐾🥌*
Tagwayen tafiya Mai sihirtattaciyar Ma'ana ta ban Mamaki daga jerin Tawwada d'aya Al-'kalami biyu first series.
*LOKACI.!*
Halish Sultan.
*BA DUK 'KYALLI BANE GWAL.!*
Amina Jamil Adam (Chuchu jay)
https://whatsapp.com/channel/0029VaRpQeUHwXb52H0abb05
Ga masu nema daga farko 👆
Chapter 25
Tashin hankali mara misaltuwa Jamal ya tsinci kan sa lokacin da ya ke samun labarin cewa Mahaifin su aikin Siyyar da sassan jikin ɗan Adam yake ,hatta tsayuwa kasawa ya yi ,zaunawa ya yi a dandaryar ƙasa yana mai jin dukkan duniyar na juya masa,a hankali yake furta innalillahi waina ilaihir rajiun ko zai ji sassauci ,Jannah dake aikin kukan halin da Jamal ya shiga ce ta zauna kusa da shi itama tana kukan ,a nata bangaren ta riga ta san zancen,tayi kuka tayi ƙunci har ta zo ta saba da shi ya bi jikinta.
Tausayinsu Mutuƙa Nafisa taji yana saukar mata ,a da tayi tunanin cewa tafi kuwa Labari mara daɗi,gani take duk duniya babu wanda a kayiwa ba dai dai ba sama da ita ,ashe na ta Zuma ne babu ɗaci, ganin kukan nasu yaƙi karewa yasa ta goge nata hawayen cikin yanayi na tausayi.
"Nephew ba kuka za ka zauna kana yi Jannah na taya ka ba,nasan cewa abin da zafi ,akwai ciwo amma abu ne da ya wuce, gaba zamu kalla da yarda zamu rusa Hajiya Saddiqa,abin da ta yiwa Jannah dama sauran yara zata biya cikin rashin zato,we should plan it Time is not waiting".
Dafe saitin zuciyarsa yayi yana duka a hankali hawaye na sauka daga idanunsa,a duk sanin Nafisa dashi bata taɓa ganin sa a yanayin irin wannan ba,broken, betrayed and hurt,ganin sa a hakan ba ƙaramun karya mata zuciya yayi ba,da akwai abin da zatayi ya rage musu damuwa zatayi amma ta san cewa babu abin da zata iya ita kaɗai sai dasu.
"Nafisa a yarda muka girma bamu san babu ba,babu abin da muke nema gurin mahaifinmu mu ka rasa , he's always there financially,a makaranta har kwatance ake damu yaran Doctor mai kuɗi, babban abin takaicin shine yarda hakan ke mana daɗi,ashe kuɗin haram ne dana jini,wannan jikin namu da Haram aka gina sa,ta yaya zan iya rayuwa da hakan?,abin da ya faru da Jannah fa?shi ya tafi ya bar mu muna biyan bashin abin da ya aikata,da yana nan yaji labarin Abin da ya faru da Jannah sai ya ji abin da iyayen wasu ke ji,it hurts me so much musamman idan na tuna har ɗazu da safe shi nake kallo nake ƙwaikwayo nake fatan na zama kamar sa,mai yasa zaiyyi mana haka?"
Hawaye kawai ke fita a idanunsu su ukun babu mai lallashin wani, Nafisa bata sake yunƙurin basu baki ba dan tasan babu abin da zata ce yayi tasiri,dan haka ta barsu su zubar da baƙin cikin su,bayan wasu ɗaƙiƙun lokuta da suka ɗauka Jamal ya tashi ya goge idanunsa domin kuka ba zai masa magani ko ya kawo masa mafita ba ,cikin ƙarfin hali ya kama hannun Jannah wadda ke jin komai na dawo mata sabo,hannunsa ya sa ya goge hawayen dake fita a idanunta.
"Nasan dole zamuyi kuka kullum muka tuna labarin mu da asalin mu ,amma ina so ki sani ba shine lagwan mu ba ,ina so wannan ya zama karfin mu da kwarin gwiwar mu,abin da bai kashe mu ba shi ke ƙara mana ƙarfi,we will fight this woman,we will take her down ta hanyar da bata zato,kisa a ranki zamuyi haka domin ke ,sauran yara dake wajen ,Mummy da Jameel,i don't care about Dad anymore domin duk abin nan dake faruwa sanadinsa ne ,da ace bai saka kansa a hanyar da yasan zai biya ba da yanzu ba wannann labarin muke ba,amma it's okay abin da ya faru ya faru".
"Nafisa yarda muka shirya haka zamu cigaba ,ki cigaba da fitar mata fake blueprint ni kuma zan cigaba da hacking system na Kanfanin da take adawa dasu ina tura Miki desgings ɗin su na next year,yanzu akwai Wurin months 7 kafin a shiga sabuwar shekara,a yarda nasan wannan Sheɗaniyar matar zatayi duk abin da zata yi tayi launching kafun next year,maybe ending or,Amma dai koma menene ina san ki fitar mata komai da wuri yarda zamu saka ta faɗa trap ɗin da ba tayi zato ba".
Kallan Jannah yayi wadda idanunta sukayi luhu luhu saboda kuka,shi kaɗai yasan abin da yake ji a cikin zuciyarsa ,ya kasa yarda cewa wai little pumpkin ɗinsa was raped ,abused ga kidney guda ɗaya an cire mata,ya kasa yarda cewa mahaifisa shine ya jefe su cikin wannan Bala'in,Amma koma mene Allah yana gani kuma shi yasan dalilin da yasa hakan ya faru.
"Jannah kamar yarda take tsammanin ki zamar mata spy ki cigaba kada ki nuna mata wani hint da zai saka tayi zargin wani abu,keep calm and keep playing along".
Kaɗa masa kai tayi a zuciyar tana anticipating faɗuwar Hajiya Saddiqa,so take ta wulaƙanta ,so take ta zama duk wani abu da ta tara take taƙama da shi su zama ba nata ba kafin ta farga.
"Yaushe zamu sake haɗuwa brother? ".
"Ba yanzu ba Jannah just keep acting ,na karɓa numbern ki gurin Nafisa zamu ringa waya ,amma haduwa bazai iyu ba saboda kada Hajiya ta fara zargin wani abu,idan komai ya ƙare zamu fara sabuwar rayuwa,Nasan banzan iya maida Miki da duk wani abu da kika rasa ba ,amma na Miki alƙawarin rayuwa mai kyau,".
Daɗi sosai Jannah taji tana fatan zuwan wannan sabuwar rayuwar da zasu gina ita da ɗan uwan ta.
Koda zasu koma gida daban daban suka koma kasancewar Hajiya Saddiqa bata nan yasa Nafisa komawa babu wanda yaji ko ya gani tunda dai zaman Khalid da Khafilat a gidan kamar hoto ne kowa yana iskancin gaban sa.
______________________________
Kamar munafuka haka Khafilat ta shiga ɗakin Khalid safiyar Monday,kalle kalle take tana neman gurin da zata saka hannun ta akan abin da take nema,sanin cewa muddin yasan tana nema za suyi faɗa sosai yasa sai da ta bari ya fita tazo nema, bincike ta fara tana Addu'ar Allah yasa taga abin da take nema ɗin cikin gaggawa tayi ta fita.
"Kai uban me kike nema mun cikin ɗaki da sanyin safiyar nan?"
Saurin juyowa tayi a kiɗime jin Muryar Khalid wanda ba tayi zaton zai shigo yanzu ba"har ka gama cin abincin"ta tambaya tana mai aikin rarraba ido,.takowa yayi inda take ya kama hannun ta yana kallon ta da kyau.
"Tambayar ki nayi uban da kike nema cikin ɗakina har kike da guts ɗin yi mun bincike,baki aje ba zaki ɗauka ".
Kwace hannun ta tayi daga riƙon da yayi mata ta rumtse idanun ta "okay fine Naji Weed nake so ka sanmun nawa ya ƙare Nasan kuma idan na faɗa maka baza ka ban ba shi yasa na zo dan ɗauka da kaina"
Sakin baki yayi da mutukar mamaki dan abin ya jisa ne wani irin,Sniffing yayi yana mai lumshe idanu ya buɗe ya ɗaga yatsun sa guda biyu.
"Kinga idan ma Amah ce ta aiko ki I'm sorry to disappoint dan ni bana smoking Wiwi zaki wani zo da wani ƙaton leɓen ki kice mun Weed zan san miki,zo ki fice mun a ɗakina kije ki faɗawa wadda ta aiko ki mission failed"
Hannunsa yasa a bayan Finapore ɗinta da ta cire hannu guda ya fara janta,buge hannun sa tayi da karfi ranta na fara ɓaci.
"Kaga idan zaka samun weed ka sanmun I'm losing my mind Kuma na san kana da ita ɗan jiya na ji warinta na tashi a ɗakin ka,indai ba kuma so kake na faɗawa Amah kana bin sugar mummies ba".
"Ke wa yasan iskancin da kike,idan kika faɗa mata ina bin sugar mummies kina tunanin ni shiru zanyi?yanzu nan Wiwi kika zo nema amma da yake munafurci na cinki wata magana daban kike yi".hannunsa yasa ya ɗaya katifar sa ya Ciro kullin Weed da cocaine powder yayi ya buɗe weed ɗin ya diɓa mata cikin tissue ya mika mata,tura kanta take tana san sanin abin da ke cikin ɗaya kullin.
"Shi farin mene?"
"Bukar Mamman ne"ya bata amsa a taƙaice yana mai mayar da Kayan sa inda ya ɗauke,taɓe baki tayi tace "kai dai ka sani munafuki".ƙofa ya nuna mata alamun ta fita,ba tayi masa musu ba ta fita tunda ta samu abin da take so.
Koda ta isa makaranta kai tsaye lungun da suke buya taje ta kafin ta kira yan korarta Hayfa da Kwaise ,tun kafin su zo har tayi rolling Wiwi ɗinta ta bata wuta ta zuga tana aikin kaɗa kafa,ta ko ina kaimata take tana jin babu wani abu da bazata iya Achieving ba a yanayin da take.
"A'a Boss lady yau mai early weed ce,hope dai akwai tawa da ta Kwaise ".
Cije leɓe tayi tana mai bin Kwaise da kallo kafin ta saka dariya ta buɗe purse ɗinta ta raba musu,zama sukayi suna zuga kamar sun samu sweet bangare guda kuma suna hailing Khafilat.A hankali Kwaise ke aikin zugar tata tana mai zurfafa cikin tunanin kafin tayi ajiyar zuciya.
"Guys Ina da idea fa kwana biyu babu wani motsi babu wani chilling babu wani abu mai ɗan daɗi daɗi,mai zai hana mu haɗa sex party,I mean just us da friends ɗin mu na Bright future ,shateema yayi mun introducing Nose candy and na shaƙa sau ɗaya Allah sai da na tafi cloud nine na dawo to kuyi imagining ga Nose candy ga sex?".
Shirusu kayi suna kallon ta kafin Khafilat ta kwashe da dariya tana nuna ta da yatsa"mene wani nose candy da zaki ce zai tafi da sex?girl you're just talking about Candy and sex mene ya haɗa?just give me that sex party ki manta da wani nose candy,mene location".
"Shine batu kawai"Hayfa ta faɗa tana mai goyan bayan zancen Khafilat.
"Well guys I'm not talking about any Candy Ina Magana ne akan cocaine,idan kukaji ance Nose candy to street name ɗin cocaine kenan,idan kuka zuƙa sau ɗaya, innalillahi ji zakuyi wani karfi ya zo muku,lokacin da naja mantawa nayi Code ɗin mu lesbianism ne cos i had a mad sex with Sharif ".
Kafin wani daga cikinsu ya sake faɗin wata magana Nafisa da ke tsaye a bakin gurin ta shigo ta jawo Lunch box ɗin da ta kawowa Khafilat ta ɗora kan cinyar ta,ba tace komai ba ta juya zata tafi,da zafin Nama Khafilat ta tashi ta kamo hannun ta.
"Ke uban me kike yi a makarantar mu,kuma uban wa ya nuna Miki inda nake ,uban mene kika ji?"
Wani irin murmushi Nafisa tayi ta kalli hannunta da tasa ta riƙe ta,cire wa tayi da ɗaya hannunta tana mai yi mata Kallan kyama kafin ta kalli su Hayfa da kana Kallan su tsoro zaka gani cikin fuskar su,fashewa da Dariya Nafisa tayi.
"Abin da ya kawo ni makarantar ku shine ɗan na kawo Miki abincin da kika manta dan har yanzu Amah kallon yarinya take Miki bata san cewa kina bayan wani tsohon gini a cikin makarantar ku ba hannunki riƙe da hayaƙi kina zuƙa gefe guda kuma ke da ƙawayenki kuna maganar Sexparty,Cocaine ,wanda ya nuna min inda kike kuma kin san bazan san wane ba tunda ba makarantar nake ba da zan gane kowa ,hope bayanina ya amsa dukkan tambayar ki".
Juyawa tayi dan tafiya Khafilat ta sake shan gaban ta tana mai faɗin"idan kika faɗawa Amah abin da kika gani kika ji i can kill you Kuma I'm not bluffing,ba cika baki nake ba".
"Na sani , you're not bluffing ai ba abin mamaki bane,if you like Khaffy ki sha Abin mayen da yafi ko wanne muni a duniya i seriously don't give a flying fuck,now if you will excuse me".Ba ta jira wani karin bayani ba ta bar gurin tana mai jinjinawa Khafilat,ko ɗaya bata ji wani iri a ranta ba ,after all dama ance idan zaka suka ramin mugunta ka shuka kaɗan,a yarda Hajiya Saddiqa take jin Khafilat labarin nan rusa ta zai ,ita kuma bata so ya rusata ta fiso sai yafi haka muni tukunna.
Allah ne yasa zata zo makarantar har ta tsinci Khaffy cikin wannan halin,da fari da Nanny muna tace ta kawo abinci har ranta taji haushi tunda ba aikinta bane amma ganin abin da ya faranta mata yasa ta kira Jamal tace yayi hacking wayar Khafilat dan ya kamata su yiwa Hajiya Saddiqa babbar kyauta cikin tsukukun nan.
Kasancewar bata san Tsoro yasa su khafilat su fasa wannan party yasa da dare bayan kowa ya shiga ɗakin sa ta nufi daƙin khafilat,Khaffy na ganinta ta haɗe rai tana tambayar abin da tazo mata ɗaki dan bata tunanin akwai wani sauran zance tsakanin su,jin haka yasa Nafisa maraicewa ta fara jerawa Khafilat ban haƙuri akan cewa baza ta faɗawa kowa ba tunda in ta faɗa ɗin ma babu mai yarda ,karshe ma dan Khaffy ta sake faɗawa har faɗa mata tayi itama ba virgin bace da ace kuma tana da freedom wannan sex party da ita za'ayi,jin haka yasa Khaffy sakin jiki suka cigaba da planning wannan mummunan party.
Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top