23
womenofwords/WA
🔏NOT ALL GLITTERS ARE GOLD💫
(BA DUK KYALLI BANE GWAL)✨
Be with 👇
*𝐴𝑊𝐸-𝐼𝑁𝑆𝑃𝐼𝑅𝐼𝑁𝐺 𝐼𝑁𝐾🥌*
Tagwayen tafiya Mai sihirtattaciyar Ma'ana ta ban Mamaki daga jerin Tawwada d'aya Al-'kalami biyu first series.
*LOKACI.!*
Halish Sultan.
*BA DUK 'KYALLI BANE GWAL.!*
Amina Jamil Adam (Chuchu jay)
https://whatsapp.com/channel/0029VaRpQeUHwXb52H0abb05
Ga masu nema daga farko 👆
Chapter 23
"Wato ke kin yi wuya da a yanzu Ban isa kizo inda nake ba sai na biyo dare na nemo ki ko?,mene lokaci yanzu dan ubanki?"
"2:00am"ta faɗa tana kuka saboda zafin riƙe mata shukun da Hajiya Saddiqa tayi"
Kamar a Mafarki Nafisa ke jin Ƙananun maganganu da ƙananun kuka,tashi tayi zaune ta jawo wayar ta dan duba time,hamma tayi ta koma ta ƙwanta ganin biyu na dare ,ta iyu ma mafarki take, lumshe idanun ta ke da wuya ta jiyo Muryar Hajiya Saddiqa na cewa.
"Ban kai ki Bangare Hadiza dan ki huta ba , na kai ki ne domin ki zama kunne na da idanuwa,shekara wurin hudu ba shine yake nufin kin zama ƴar Alhaji Bukar ba,going to school ,fancy clothes, expensive phone, kada ki bari dukkan wannan ya ruɗeki ki manta wacece ke,Kada ki manta idan kika yi wasa Jamal zai mutu".
Kuka sosai tasa ta zuɓe a kasa tana mai neman gafarar ta,.Jin Maganar Nafisa tayi kamar a mafarki ,a Hankali ta miƙe ta yaye labulen window ɗinta kaɗan yarda zata na hangen waje,Hajiya Saddiqa ce da yarinyar da ta gani tare da Saimah ,duk da gurin babu hasken wuta sai na wayar Hajiya Saddiqa wanda shima ba kuna Flash light ɗin tayi ba hasken gaban wayar ne ,Amma duk da hakan tana iya Kallan fuskar wadda ke tsugunne ɗin.
Ganin ta tashi Amah ta juya dan komawa ciki yasa Nafisa zaunawa a Hankali tana mai san ƙwaƙwalwarta ta marƙaɗa mata abin da taji
"Idan ki kayi wasa Jamal zai mutu"?.indai lissafin ta ya bata dai dai Jamal ɗin ta Hajiya Saddiqa ke magana,idan kuma Jamal da ta sani ne then definitely yarinyar dake tare da Hajiya Jannah ce.
Hannu tasa ta rufe bakin ta,so all this while Jannah na cikin gidan Alhaji Bukar sashen Ummu a matsayin yar leƙen Asirin Amah,idan haka ne to taya akayi Hajiya Hadiza da yaranta suka ƙarɓe ta?.Tabbas akwai wanda zai amsa mata wannan tambayoyin,ba dan dare ba a lokacin zata kira Jamal ,amma zata bari sai da safe,.
Tana aikin wannan saƙa da warwara ɗin taji alamun sake fitar Hajiya Saddiqa ,sake buɗe labulen ta tayi ko gurin Jannah ta sake zuwa amma ga mamakinta sai jin tashin motar ta tayi."duk yarda Akayi matar nan na chudanya da Aljanu"ta faɗa a hankali,ji take kamar ta jawo safiya domin sanin amsoshin tambayar ta..
Washe gari da safe ta je gaida Hajiya Saddiqa dan san sanin ko ta kwana gida,ga mamakinta sai ganinta tayi zaune kan dinning table tana shan coffee kamar ba itace ta fita daga gida ba ƙarfe biyu na dare,"shin yaushe ma ta dawo?,dan ita bata ji wani motsin ta ba"da Fara'a fuskar ta ta ƙarasa tana mai cewa"Good morning Amah". Sipping coffee ɗin ta tayi tana mai Kallan ta "how was your night,har ina cewa Muna ta kai Miki breakfast ashe kina hanyar fitowa ".
Zama Nafisa tayi."Wallahi Amah Naji ina san zuwa na haɗa Miki breakfast da kaina ne bansan ya akayi ban tashi da wuri ba ,kuma da abin na kwana a raina".
"Well bana having breakfast Mai Nauyi da safe,amma tunda kinyi niyya and it's weekend Mai zai hana ki shiga ki making wa su Khalid dan ni zan fita ne,Hope dai kin iya girkin. "
Cike da takaici da dana sanin tayin yi mata Girkin Nafisa ta washe haƙora tana mai cewa"aikuwa Amah na iya girki,bari na shiga na haɗa musu ,na so dai ki taɓa"
"No I'm in a hurry,amma i will be okay with dinner Dan sai dare zan dawo"Key ɗin motarta ta ɗauka ta aje cup ɗin tana mai sake kallon Nafisa kafin ta ƙara da cewa"i hope you will behave".Bata jira amsa ba ta fara tafiya dan barin gurin.Ɗaukar cup ɗin da ta aje tayi ta kurbi coffee ɗin tace"yau zata kasance rana mai tsayi.Ganin tare suka fita da Nanny Muna Su Khalid kuma na aikin baccin da bata tunanin ma sunyi Sallar Asuba.
Sai da ta bada tazara sosai da Fitar su kafin ta fita a sashen ta nufi bangaren Hajiya Hadiza,da sallama ɗauke a bakinta ta shiga ,a tare dukkannin su suka juyo suna kallanta kafin lokaci guda yanayi na fuskar kowa ya chanza daga Mamaki zuwa murnar ganin ta,aje Plate da Ummu ta ɗauko tayi ta tako inda Nafi take,ba tayi wata wata ba ta rungume ta tsam kamar wani zai ƙwace ta,take kuma sai jin hawaye tayi a idanun ta suna neman sauka kan kuncin ta,ta fi dangana wannan hawaye da na farin ciki,a duk yanayin da take bata san abin da yasa ba bata wasa da yiwa Nafisa Addu'a,"ina kika shiga Nafisa?,".ta faɗa tana mai raba jikin ta da nata, Goge hawaye Nafisa tayi wanda bata san da zuwan sa ba sai ɗuminsu Murmushin ƙarfin hali tayi "abin da yafi muhimmanci shine dai yanzu na dawo cikin Aminci Ubangiji,Duk da babu wani abu da na haɗa daku na jini wallahi ina jin ku har raina".
Gyara zama Sultan yayi yace"Fatan dai kin koyo turanci dan ni abin da ya dameni kenan ba yanzu ki saka ni lesson ɗin da ban shirya ba ya Salman ya shigar miki".Dariya dukkan su suka saka banda Ni'imah (Jannah)wadda ke bin Nafisa da ido tana tunanin yarda zata fara sanarwa Hajiya cewa ta shigo,domin ta ja mata kunne akan duk ranar da taga Nafisa ta shiga sashen Hajiya Hadiza ko taga ta kula wani daga cikin yaranta ta faɗa mata.
"Maza saimah ki matsa kujerar kusa da Samrat Nafisa ta zauna kusa dani muyi breakfast"Ummu tace tana mai jin wani irin daɗi da baza ta iya misaltawa ba.Buɗe baki Salman yayi yace"Su Ummu anga Nafi mun bani dama ni tun ganin da nayi mata nasan muddin idan har itace zata shigo.
Kamar zata ƙi tayin breakfast ɗin amma ganin yarda Beautiful family ɗin nan ke murnar zuwan ta baza ta taɓa iya faɗa musu a'a ba ,bayan sun gama cin abincin ne ta kalli Ni'imah (Jannah ) tayi Murmushi,itama murmushi tayi mata amma nata na rashin sakewa da kallon da take mata ne,
"Baƙuwa kuka yi Ummu?mai kyau da ita"
"Ai dama idan ka daɗe baka ga mutum ba koda shekaru dubu ne kawai ka tambayi sa ya yake kada ka tambayi halin sa,kana ji ya Salman Nafi dai bata daina san masu kyau ba".cewan Sultan yana mai zama kan Kujera .
Dariya Salman yasa yana tuna yarintar Nafisa da yarda take aikin ƙoda kyansu,.Kafin kowa ya bada amsa Ni'imah tace"sunana Ni'imah Bukar ,Ni yarinyar Ummu ne wadda ta ɓata .
Buɗe baki Nafisa tayi"wow shine aka ganki?well ina taya ki farin ciki,nima ki taya ni Addu'a aga nawa iyayen ,Ya Jamal ya mun alƙawari zamu nemesu tare,nima na masa alƙawarin zamu nemi ƙanwarsa janna tare".Tashi tayi tana kai ayar zancenta gudun kada su mata tambayoyi "Ummu bari naje Amah ta fita shi yasan shigo,Kinsan Halin ta idan tasan nazo nan bala'i ne,".
"Kada ki damu yarinya ta na fahimta ,Allah ya shiga tsakanin na gari da mugu, muna nan duk Muna Addu'ar Allah ya kawo mana sassauci,idan nayi abincin rana kizo kici in zaki iya,rice and stew ɗin nan nawa da kike so na dafa".
"Idan ma bata samu zuwa ba zan aje mata a gurin da na aje mata gyaɗa,yarinya kuma akwai story ke dai sai mun zauna zan baki labarin Turai da abokina mai sunan saurayin ki,amma dai nasan ba shi bane dan wannan classy ne baya da bataçciyar budurwa mai shekaru sha uku "
Dariya kawai tayi tace "zamu gani ya Salman, wane ma ya sani ko shi ɗinne bai faɗa maka yana da budurwa yar sha uku ba,ni kam bari naje kafin su Khafilat su farka,na gode sosai nayi farin cikin sake haɗuwa daku".murmushi tayi ta juya tana mai karawa da "Ya Salman,sai mun haɗu nasan bakin ka kyaikayi yake kaban labarin ƙasar waje."
Dariya kawai yayi bayan fitar ta yayin da Ummu ke bin ƙofar da ta fita da ido tana mai addu'ar Allah ya kawo mata sauki a rayuwa ,ita koda bata da iyaye zata riƙe ta muddin Tabar hannun Saddiqa,tana Jin Nafisa sosai har cikin ranta.
Kallon yarda take ta murmushi Saimah tayi tace"Ummu zaki bani kuɗin na siyo Pouch ɗin ?"
"Zan Miki transfer har na takalmin nan ki siya,dauko mun wayata"
Tafi Saimah tayi ta tashi tana murna "lallai Nafisa lucky star ɗina ce omo,Allah ya biya Ummun mu"...Koda Nafisa ta fita bata shiga ciki ba ,tsaye tayi Daga bayan gurin tana jiran fitowar Ni'ima da tasan tabbas zata fito,bangare guda kuma tafara tunanin Akram,sau tari yakan faɗo mata a rai,sanin babu yarda zata iya yasa take yawan yi masa addu'a,bangaren childhood obsession ɗin ta kuwa ya rage sosai ba kamar da ba,idan Jamal na tsokanar ta kunya ke kamata sosai musamman idan tana tuna yarda take faɗin babu wanda ta kai Akram kyau,tasan a yanzu ya ƙara kyau fiyeda da,ta saka a ranta insha Allahu tana samun yancin kanta zata koma Gashuwa sanin cewa duk inda yaje a faɗin duniya nan zai koma tunda nan ya sani Gida a yanzu.
Ganin fitowar Ni'imah tana Waige Waige ya saka ta yin karamin murmushi,tasan dama dole zata neme ta,hannu ta daga mata,cike da haɗe rai Ni'imah ta ƙaraso inda take "mene wannan ki kayi pulling a ciki,how dare you zaki sako yaya na a maganar ki,nasan ni da ke puppets ne ,it doesn't matter Wanda yafi wani bai Kuma dameni da hajiya ta faɗa Miki sunan yaya na ba,ina so kowa ya tsaya a matsayin sa yayi abin da ke gabansa ".
Kallanta kawai Nafisa takeyi ganin irin kamar da tayi da Jamal sosai,ba sai an faɗa mata jinin sa bace,hannun ta tasa ta shafa gefen fuskar ta"Ni da ke munyi kamanceceniya a fannin ƙaddara,amma kowa da nasa labari da zai bada,idan kika yarda dani naki labarin wahalar yazo karshe,amma fa sai da yardarki,da waya ɗaya zan haɗaki da Jamal wanda ke aikin cigiyar ki da dukkan rayuwarsa,amma sai kin faɗa mun abin da kike yi a sashen Ummu da kuma inda kike kafin nan, Jannah".
Sosai Jannah ke san gasgata Nafisa amma sanin cewa mayaudara kamar Hajiya Saddiqa nada yawa a duniya yasa tace"mai zai saka na yarda da cewa ba Hajiya Saddiqa ta saka ki bibiyata ba?"
Kunna waya Nafisa tayi ta ciro hoton Jamal ta haska mata a fuskar ta,saurin saka hannu Jannah tayi zata karba Nafisa ta ɗauke tana mai cewa"nope sai kin faɗa mun abin da nake san sani,ni kuma zan kira miki Jamal a waya kuyi Magana.
"Amma ai Kinsan magana a nan bazata iyu ba ko?"
"Haka ne ina da inda zamuyi magana babu wanda ya ganmu balle ma yasan munyi,so ki biyo ni zan buɗe Miki ƙofar ɗakina ta baya ki shiga ,inda kuka tsaya jiya tsakar dare ke da Hajiya Saddiqa ki jirani gurin"
Tana kai karshen maganarta ta juya ta shiga sashen Amah,ganin babu motsin su Khafilat abin ya bata mamaki,duk da bata ji su ba baza tayi risk ba dan haka ta nufa ɗakunan su domin dubawa,tun daga bakin ɗakin Khalid minsharin da yake ƙarfe goma saura na safe ya tabbatar mata yana aikin bacci kamar jaki,ɗakin Khafilat kuwa har kasadar tura ƙofar tayi amma ga mamakinta bata cikin gadon ta ko alamun wani ya kwanta bai nuna ba,kenan ba gida ta kwana ba,taɓe baki tayi ta koma ɗaki ta buɗewa Jannah ta shigo.
Bayan ta zauna ta kalli Nafisa"dan Allah ki kira mun Brother Naji Muryar sa zan faɗa Miki komai"
Murmushi Nafisa tayi ta dafata"idan kika faɗa mun komai har ganinsa za kiyi ba jin Muryar sa kawai ba".
Ajiyar zuciya tayi tana mai bawa Nafisa yardar ta.
"Abin da ya faru shine".
Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top