21
womenofwords/WA
🔏NOT ALL GLITTERS ARE GOLD💫
(BA DUK KYALLI BANE GWAL)✨
Be with 👇
*𝐴𝑊𝐸-𝐼𝑁𝑆𝑃𝐼𝑅𝐼𝑁𝐺 𝐼𝑁𝐾🥌*
Tagwayen tafiya Mai sihirtattaciyar Ma'ana ta ban Mamaki daga jerin Tawwada d'aya Al-'kalami biyu first series.
*LOKACI.!*
Halish Sultan.
*BA DUK 'KYALLI BANE GWAL.!*
Amina Jamil Adam (Chuchu jay)
https://whatsapp.com/channel/0029VaRpQeUHwXb52H0abb05
Ga masu nema daga farko 👆
Chapter 21
A hankali Nafisa ke haɗa kayan ta cikin traveling bag tana mai jin wasu irin zafafan hawaye na bi mata kunci,bata da niyyar tare su domin kuwa sun chan-chan-ci su zuba , ta kasa yarda cewa yau ita ce ta ɗaga hannun ta ga Jamal,Shi ɗin bai chan-chan-ci haka daga gare ta ba koda kuwa yaya ne,Jamal shine ya yi mata komai ya maye mata gurbi mafi girma a rayuwar ta,hatta Bra da ta fara sawa a rayuwar ta Jamal ya siyan mata.baza ta taɓa manta wa da hakan ba..A ranar sun fita aiki tana da shekaru sha biyar lokacin,tun da suka isa cikin ma'aikatar da suke aiki a ciki Halilu ɗaya daga cikin ma'aikatan ke Kallan ƙirjin Nafisa duk da ta yafa gyale,kula da haka da Jamal yayi yasa ya fara tunanin Abin da ya kamata ya yi .Bras ɗin da ya siyo mata sun mata yawa amma haka ta yi ta sawa,kunya kuwa babu irin wadda bata sha ba,idan tana tuna abubuwan da Jamal yayi mata sai taji kamar ƙasa ta tsage ta shige ,a wani bangare guda kuwa tana jin sa kamar uwa a gare ta domin kuwa duk ɗumin da za ta samu ga mahaifiya Jamal ya bata,idan tana tare da shi ta kan ji ƙwanciyar hankali da nutsuwa suna ratsa ta ta ko ina,Jin shigowar Jamal yasa ta yi saurin juyowa idanun ta ɗauke da ƙwalla,alamu ya yi ma ta da hannu akan kada ta ce komai,kafin ya nuna mata ƙofa .
Kuka ta fashe da shi mara sauti,Murmushi yayi mata kafun ya yi mata alamu da hannun sa akan za su yi waya, a zahiri kuwa sai cewa ya yi"Amma Nafisa kin ba ni Mamaki ,ban san cewa ke mutum ce mai manta Alheri ba saboda kawai san abin Duniya,kin yi disappointing ɗina, mene ban miki ba?duk wani abu da kike taƙama da shi a yau sanadin wane?na koya miki komai babu ƙeta ko mugun ta ,shin kina ganin abin da kika mun kin kyauta?mun yi maganar nan tare,zamu zauna tare ,ni da ke da Jannah,we will look for Jannah together,idan ma kina ƙwaɗayin iyayen ki da ta ce zata nemo mi ki duk zan miki idan ki ka yi haƙuri amma mene ,sai ki ka zabi ki chaka mun wuƙa a baya kuma wai duk dan san duniya,Why?" .
Koƙarin saita kan ta ta yi Kafun ta ce"Jamal ke nan,shekarun ka ashirin da takwas amma kamar har yanzu baka san karatun rayuwa ba,wane kai da bazan yaudare ka ba?shin kai uba na ne ko kuwa mun haɗa wata alaƙa da zata saka na zabeka sama da rayuwa ta,ka kalle ni da kyau ka kuma karanci lebena da kyau,duk wani abu da ka ke tunanin muna da shi tare ƙarya ce,jannah kuma matsalar ka ce ba tawa ba,tunda ƙanwar ka ce ba ƙanwa ta ba,ina san kasa a ran ka kai ɗin ba komai bane face tsanin dana taka ya Kai ni inda ya kama ta ya kaini,ka kalle ka da kyau ba ka da komai ba ka da wani abu da zaka iya bani so Please ka ji da rayuwar ka."
Alamu ya yi mata da yatsa na ta yi dai dai kafin kuma ya ce "za ki gani idan abin da ki ka zaɓa dai dai ne".jakar ta ta gyara ta na mai cewa"to Kafin na gani ka fara bin wancan munafikin kawun na ka dake aikin laɓe ya taimaka maka da gurin zama dan a yanzu dai baka da komai sai dattin Aljihu".
Da sauri Uncle Saleh ya Matsa a gurin yana mamakin yarda Nafisa ta yaudari Jamal haka,gaskiya ya yarda da aka ce ka ji tsoran mata ,yanzu duk abin da yaran nan ya yi mata ?da ya sani tun tana yarinya ya kama ta ya danne yar banza ya ji daɗin sa da ya san cewa wannan ranar zata zo,.Fitowa ta yi a ɗakin ,wani Kallan banza ta bashi kafin ta yi gaba ya bi ta a baya dan kaita gidan Hajiya Saddiqa .
A harabar gidan Alhaji Mamman tsaye kawai Nafisa tayi tana mai ƙarewa gidan kallo, ko mai yana nan yarda ta san shi sai dai ta tabbata kowa na gidan ya chanza kamar yarda ita ma tazo a chanze,ita da Jamal sun gama tsara abin da za suyi tun tuni idan suka samu yanci ,ba su taɓa tunanin abin zai zo da wuri ba amma sakamakon abin da Hajiya Saddiqa tayi suka matso da komai nasu kusa,a wata majiya Jamal ke jin cewa Hajiya Saddiqa tana aikin ƙwayoyi na gaske sannan akwai kila wa ƙala na Safarar yan mata da take yi,baki ɗaya dai sun kasa saka hannun su a abu guda ɗaya dan haka Nafisa ta ce zata shigo gidan,da farko Jamal bai amince ba amma da ta kashe masa gwiwa da maganar Jannah sai ya yarda amma ya yi mata kashedin ta bi a hankali sannan idan damuwa ta tashi ta kira sa,hoton Jannah ya bata tun tana shekaru 12 tasan a duk inda za ta gan ta baza ta kasa gane ta ba,ta yi alƙawarin bawa Hajiya Saddiqa kashin ta a hannu,sai ta saka ta yi asara mai girma ,sai ta saka ta yi dana sanin saka ƙafar ta a Gashuwa har ta ɗauko ta ta shigo da ita rayuwar ta .Kallan sashen Hajiya Hadiza ta yi tana mai jin wani irin yanayi dangane da gurin,tana san Hajiya Hadiza dan ta yi mata alherai da taji daɗin su ,a iya ɗan sanin ta da tayi da yaran ta babu sharrin su da zata faɗa,ta yarda da cewa wannan abu da za ta yi har da su zata taimakawa dan kuwa Hajiya Saddiqa guba ce wadda idan ta taɓa abu sai ta ɓata shi duka.
Ƙokarin ɗauke idanun ta tayi daga gurin lokaci guda kuma ta mayar ganin 17 years old Saimah ta fito tana dariya ,gefen ta kuma wata budurwa ce doguwa mai kyau ita ma tana dariyar,daga bayan su Salman ya fito ya na dariya shima ya ce"ba na faɗa muku Ummu ta fara tsufa ba"dariya suka sake Ni'ima na cewa "Allah ya Salman ku daina tsokanar mun Ummu na". Kafin ya sake magana idanun sa suka sauka kan Nafisa,da Mamaki ya ce"kamar Nafisa ce waccan Saimah ko ido na ne"?.
A tare Saimah da Ni'imah suka maida kallan su kan Nafisa,ganin haka yasa ta barin gurin ta nufi sashen Hajiya Saddiqa dan baza ta yi abin da zai saka Hajiya Saddiqa ƙin yarda da ita ba,kula su Salman kuma a ranar farkon ta kamar wargatsawa kan ta komai ne,she can't risk it.
Da mamaki Saimah ta ce"anya Ya Salman,idan Nafisa ce baza ta taɓa wuce mu haka ba". sunglasses ɗin sa ya sa yace"Well yanzu dai mu je kafin Ummu taji bamu tafi ba ,kun san Nene na jin shiru zata fara ƙwaɗa Mata kira,maganar Nafisa kuwa idan ita ce nasan zamu dawo mu same ta gidan nan ".A tare su ka jera dan zuwa kaiwa Nene ziyarar dawowar sa daga ƙasar waje karatu".
Da sallama Nafisa ta shiga sashen Hajiya Saddiqa,da sauri Khalid dake ƙwance kan doguwar kujera ya juyo yana mai cire headphone ɗaya ya ce"kai!?wa nake ji kamar Muryar Nafisa the Stinky girl?.tasowa ya yi da saurin sa ya ce"kai wallahi ita ce,zagaye ta ya fara kafun ya ce"wallahi ke ce ,kuma komai zan zan".
Wani irin takaicin sa ta ji,dama ta san in dai Khalid ne za a rina, already ta san baza a shuka abun arziƙi da shi ba,ƙare masa kallo ta yi,zahiri ya yi kama da mai shekaru ashirin da biyu da ya kamata ya yi Amma kana masa kallo ɗaya ba sai an faɗa maka cewa yana Shaye Shaye ba dan ta nuna sa.
"Useless girl mara zuciya ,nayi tunanin ai ko Kallan mu baza ki kuma ba ,inda kika fito chan cikin lion den ɗin nan shine ya dace da ke amma ba gidan nan ba ,but ko ma mene nan ɗin ma zaki san matsayin ki ,shegiya".Khafilat da ke tsaye kan staircase ta faɗa tana mai turowa Nafisa wuƙaƙe da idanun ta.
Wata irin dariyar ƙeta Khalid ya sa,cikin dariyar ya ke faɗin"Sis!?easy mana mene na sheganta ta?".Daga bayan ta Nanny Muna ta ce"to ranka ya daɗe ai shegiyar ce dan galibin su na gidan Marayun nan shegu ne aka tara ,tunda dai babu ɗan halak ɗin da za'a a haifa a wullar,yawancin su wannan tambarin cillarwa ɗin yana nan har abada".
Abin ya yi wa Nafisa zafi amma hango Hajiya ta gefen ido da tayi ya sa ta saka dariya ta ce"nagode sosai,and Ina San wannan hanyar nuna ƙewa ta ɗin da ku ka yi,wallahi ni ma na yi kewar ku kamar babu gobe ,shin ina Amah ɗin mu ne?ni ita na fi san na gani ma fiye da kowa ".Jin haka yasa Hajiya Saddiqa sakkowa dan dama ita ce ta aiko Nanny Muna da Khafilat dan ta gwada juriyar Nafisa..Tana saukowa ta wani washe baki tace "my baby Welcome back,ku da ku ka tsaya mata sharhi hala ba ku ga a gajiya take ba,maza Muna abincin nan da na haɗa mata je ki ɗauko ki biyo ta da shi ɗaki ,bari na nuna ma ta ɗakin ta ko ta ɗan yi wanka ta huta.
"Ai yanzu na ji bata wari Amah dan ni wani ƙamshi da ta ke ne ma yake ratsa ni"Khalid ya faɗa ya na mai watsawa Nafisa wani kallo.ba tare da bi ta kan Khalid ba Amah ta jata ta na faɗin"welcome back daughter".
Sashen Nanny muna dake bayan bangaren ta su ka ɗauka,abin bai ba ta mamaki ba dan a yanzu Hajiya Saddiqa ta daina ba ta mamaki.Kallan ɗakin ta yi lokacin da suka shiga, everything is plain ,wani tsohon gado ne mai ɗauke da wata lamushashshiyar katifa ,babu wardrobe a ɗakin babu Ac ga fankar dake ciki ba wani iska take ba sai shegiyar ƙara kamar tsohon mashin,gefe guda kuwa daga kan tebur su cardboard papers ne ,laptop,sketching sets , pens,da iyayen papers,ganin tana Kallan gurin yasa Hajiya Saddiqa murmushi ta ce"komai da zaki buƙata yana nan,Hard drive ne kawai ban aje Miki ba but Khalid zai kawo,yanzu abin da za a yi ,ki Huta Muna za ta kawo miki abinci in yaso idan kika ƙoshi sai ki fara aiki,And yes idan kina buƙatar iska you're free Zaki iya fita waje after all kema Nan ɗin gidan ku ne".
Kuka kawai Nafisa ta saka tana mai aikin Zubawa Hajiya Saddiqa godiya kamar ta saka ta a aljanna,cike da makirci Hajiya Saddiqa ta rungume ta ,tace"mu gama gina Khafilat tukunna bayan nan na miki alƙwarin introducing ɗin ki ga manyan mutane ".jin ta kawai Nafisa take amma ita tasan babu wanda ta zo gina wa illa ma rusawa da ta zo yi kuma sai ta rusa ɗin da ikon Allah .
Kai tsaye Hajiya Saddiqa na fita a ɗakin ta nufi falo,wani banzan kallo ta bawa Khalid kafin ta ce"kai kuma ina san ka sani,ko wacce yarinya ka ke san bi kaje ka bi tunda ka sakawa kan ka masifa da jaraba,amma ka sani Nafisa off limit ce ,dan na kula da kallon da ka ke mata ,wallahi tallahi ka ji na rantse maka ,ko da wasa na ji labarin ka wa Nafisa wani abu da yayi kama da lalata wallahi sai ka koma rehab ɗin da ka fito,tunda kai ka rantse baza ka shiryu ba,to ka sani a faɗin duniyar nan ban da Nafisa ,indai kuma ba so kake ka fi haka lalacewa ba".
Bari gurin tayi tana mai jin Haushin halayyar Khalid,yaran da take so ta ƙarfi da yaji su lalace sun ƙi sai nata wanda tasan Hajiya Hadiza ke saka mata hannu..Kallan Khafilat dake aikin danna waya Khalid ya yi ya ce"dan Allah sis kinga nayi wani abu?na rasa wa zan nema sai Nafisa?
Wani banzan kallo ta bashi kafin ta ce"kai dai ka sani wallahi Ya Khalid ,ka ji kuma abin da Amah ta faɗa sai ka gyara tazugen ka.
_______________________________________
YOBE STATE.
Yau ta kasance safiyar Monday,cikin gidan Alhaji Muhammad Tukur Gashuwa baki ɗaya iyalan ke zaune kan teburin cin abinci domin yin karin kumallo, Matar sa Hajiya Sakina ce ta tashi lokacin da professional cook Radiya ta gama jera abincin da ke time table na safiyar ,gaban Alhaji Muhammad ta isa ta buɗe plate ta fara zuba masa plaintain mossa bakin ta na san magana.
Kula da hakan da mai gidan na ta ya yi ne yasa ya ce"Mummyn Hashim hala ki na da magana".
Zama tayi kujerar kusa da shi ta ce"Wallahi Honey ina da ita,alƙawarin da ka mun na five million ɗin nan ya kamata ace ka cika,ina buƙatar wannan kuɗin wanda nasan ka fi ƙarfin su dan in ka cire so kamar baka taɓa komai bane so Please ka mun transfer ".Kallan ta ya yi kafin ya yi murmushi ya ce"ban san abin da kike yi da kuɗi ba, business na ce kiyi kin ƙi kin fi gane ki ci kuɗin da baki nema ba,last week 8million na baki amma kice cikin sati guda ba ki san inda kika kai su ba,ina da mabuƙata ƙasa na fa ,dukiya ta kuma dan su nake nema ,kullum sake karuwa suke so Please ki san yarda za kina kashe kuɗi,ina sane da cewa ƙaramar Sallah kin tauye su ,nawa na baki?20 Million domin a yi masu kayan sallah da abubuwan da baza a rasa ba amma 2.5million kika kashe masu,ki sani siyayyar su ta Babbar Sallah ke za kiyi and Ina so ki sani idanuna na kan ki"
Taɓe bakinta tayi tace"tunda kai ka haife su ai sai ka yi ta yi,su iyayen da suka haife su ai ba su damu da su ba suka yasar kai ka ɗauka kasa a kai bayan ga naka iyalin,ni dai ina jiran 5 million".
Bai sake tanka ta ba dan ya san kula ta ɗin bashi da amfani .
"Wai Mummy mai yasa kike san shegen san a saka mana parsley cikin Avocado juice ne,why can't it be only avocado".Hashim babban yaran Hajiya Sakina ya faɗa lokacin da ya aje cup ɗin juice ɗin da ya kurɓa..Wani Banza kallo Hajiya Sakina ta bashi.
"Ka tashi ka dake ni Hashim sai na san ka kai matsayin da ya kamata ace ka kai"
Hannayen sa ya ɗaga cikin surrender"ni nace zan dake ki Mummy ,kice dai kina Neman haɗa ni da Daddy,Nana A'isha ko kin ji na ce zan daki Mummy?".
"Ni ban ji ba ,kawai dai dan an hanata five mila ne"Nana A'isha ta faɗa tana mai gumtse dariyar ta.Dariyar shima Hashim yasa kafin yace"dey calm down mommah , idan Daddy ya mutu aka raba mana gado nasan na takaba kawai zaki samu Ni da Nana Aisha zamu kwashe komai ,zan kula da ke dan nine zan kulawa da Nana Aisha nata ,kafin ta sake wayau,Kinga a yanzu she's just 20"
Cike da fitina Nana A'isha ta kalle sa tana mai aje fork ɗin da ta ke cin abinci dashi"kai ɗin shekarar ka nawa?you're just 23 yarda kake ganin zaka iya kulawa da Akalar maƙudan kuɗi Nima zan iya har na fika ma , Wallahi baka isa kace kaine zaka kula mun da gado ba".
Kallansu kawai Alhaji Muhammad yake yana mai jin wani irin abu ya tokare masa ƙirjin sa,yaran da ya haifa yau sune suke zaune gabansa suke maganar gadon sa,kenan sun ƙosa ma ya mutu su huta ,mene amfanin Auren mace mara tarbiyya?tabbas da yasan cewa Sakina bata da tarbiyya har haka bazai taɓa ƙwaɗayin haɗa zuri'a da ita ba,amma tayi masa shigo-shigo ba zurfi shi yasa har suke a wannan gejin a yanzu,abubuwa da dama da take mara sa kyau yana sane ,kama da asirin da take masa duk ya sani,sannan a daren jiya ya jita tana waya akan zata koma gurin boka dan tana ganin aikin da tayi ya karye tunda har yanzu yana iya mayar mata magana dan ya raina ta,yasan nanne inda kuɗin ta ke tafiya bugu da ƙari kuma yana sane da abin da za tayi da 5mill ɗin da take nema ya bata,abu guda ne bata sani ba bin ta yake kamar Gara a katako ,a baya ta ci nasara amma a yanzu kuwa aikin hofi take.
"Idan bakuyi wasa ba dukkan dukiya ta zata tafi gidan Marayun Alheri dan Wallahi sun fiku sau dubu,da na bar maku dukiya ta gwara na bar masu na san su zasu mutunta abin da suka samu kamar rayuwa"
Haɗe rai sosai Hashim yayi yace"wallahi Daddy da an mutu kuwa dan wallahi sai na sakawa gidan wuta kowa ya mutu a duniyar nan ba ka da masu cin gadon ka bayan Ni da Nana Aisha".
Goge baki Alhaji Muhammad yayi da tissue ya tashi dan barin gurin.
"Ni ɗin fa dan uban ka ayi yaya dani"Hajiya Sakina ta faɗa tana mai watsawa Hashim wani irin banzan kallo.Shiru kawai Alhaji Muhammad yayi ,shi bai juyo ya kalle su ba shi bai ce musu uffan ba ,wasu hawaye ya ji suna neman sauko masa ,ya yarda da cewa wannan ƙaddarar tasa hakki ne ke bin sa ,amma da ace za'a dawo masa da hannun agogo baya Abin da yayi a bayan shi zai sake a yanzu.ya fara tafiya kenan cook ɗin su ta shigo daga waje ,da Murmushin ta ta karaso ta ce"Sir kana da baƙi,gasu chan da securities a first gate basu bar su sun shigo ba akan ba ka faɗa musu za kayi baƙi ba .
Da Mamaki ya ce "baƙi kuma?ya ya su ke?"
"Eh sir Saurayi ne da budurwa, saurayin very handsome haka dan idan ba wai ido na ba to naga yanayin ka da shi,kilan dai ko relatives".sanin bashi da kowa yasa abun ya ba shi mamaki sosai,dan haka ya sauko ya je ya zauna kan couch ya kira head of securities ɗin ya ce a bar su za su iya shigowa .
08130229878
Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top