2


    A hankali Nafisa ta aje Hijab ɗin dake hannun ta juyo tana mai bawa Suwaiba wani irin banzan kallo kafin tace"Dan uwar ki kina so kice ko mene ya ɓata a ɗakin nan nice wato gani ɓera bugu da ƙari ma na rasa Abinda zan sata sai jambaki,jambakin ma na rasa na wane zan ɗauka sai na Khadijah wadda basir duk ya cinyewa baki,wallahi Suwaiba ki fita harka ta ,babu wani abu da kika iya bayan munafirci,to wallahi Ni cimmiki zanyi,ai kin san hali na ba wai baki sani ba,kal bura ubaki nakan ci na zauna lafiya,ina cewa nan da na ɗauki ɗan kunne ki kinsan cewa Ara nayi amma saboda tsabar kina san haɗani da uwata kika je kika faɗi mata wai na satar miki,to wallahi ta Allah ba taki ba,tsakanina da big mummy sai ta Allah bata mutum ba idan kuma kina ganin ƙarya nake to muje zuwa shege ka fasa".juyawa tayi dan ɗaukan Hijab ɗin ta,saka hannunta kai ke da wuya Muryar Suwaiba ta tsayar da ita inda take faɗin"yo uwarki ta gidan Marayu dai, babu wanda bai san tsintar ki tayi ba,cikin gidan nan wane bai san labarin yarda ta tsince ki ba ". A fusace Nafisa ta juyo ta nuna ta da yatsa tace"ki nuna mun wanda yake mai cikaken asali gidan nan,kece matsiyaciya sannan waɗan da basu san ke munafuka bace zaki yaudara amma bani ba ,duk taran tsintattu ne kilan ma ke cikin shegu kika fito"charaf Suwaiba ta kama inda take cewa"kila ke kuma ana karuwai duk inda akaje aka dawo kin haɗa iri dasu musamman yarda ki ke maƙalewa Brother AKRAM Allah kilan a karuwaci aka samu cikin ki shi yasa aka zo bakin gidan nan aka cillar dake duk da ruwan da ake sheƙawa,Allah ma ya temakeshi ƙasar zai bari ,kilan kuma sai ki nemi wani kibi tunda muna da yalwar mazan"bakin ta na rufuwa Hannun Nafisa na sauka kan fuskar ta,ai kafin kace ƙwabo faɗa ya kece tsakanin su ,sosai suke kaiwa juna duka wanda Suwaiba tafi dakuwa,a haka suna kan kokawar suka fita har ƙofar ɗakin su inda hakan ya jawo hankalin mutane suka fara zuwa kafin aka samu waɗan da suka shige tsakani domin raba su,zage zage suka cigaba tsakanin su,wata sister ɗinsu ce ta riƙe Nafisa wadda ke faman cilla ƙafa tana cewa a rabu da ita ta illata Suwaiba yayi da ita kuma Suwaiba ke kuka duba da raunin da Nafisa tayi mata a ƙasan ido.muryar Big mommy dake faɗin "ku sake ta"shine Abinda ya dawo da Nafisa ciki hankalin ta ,sai a wannan lokacin ta farga da cewa wai faɗa take,cike da mutuƙar takaici big mummy tasa aka kai Suwaiba sick Bay domin a mata dressing ciwan da Nafisa ta ji mata,Kallanta ta mayar kan Nafisa tace"idan na riga ki zuwa inda ya dace kije Wannan lokacin wallahi baza kiji daɗi na ba,sai nayi mutuƙar saɓa miki fiye da tunani".tana juyawa Nafisa ta kwasa da gudu tana kuka dan tasan ta kaɗe ne kawai,ta riga Big Mommy zuwa ɗakin horo wanda tana zuwa ta zube kan gwiwowinta ta ɗaga hannunta sama ta rufe idanu tana furta duk wata Addu'a da tazo mata baki,jin Muryar Big mommy data sargent ya  saka tayi saurin buɗe idanunta tana mai cewa"Na shiga uku Ni Nafisa".Baki kai ga shiga uku ba tukunna ai,maza Sargent fara dukan ta har sai nace ka bari.murmushi dattijon yayi yana mai gyara kan dorinar dake hannun sa sharfefiya,dama yana jin Haushi Nafisa duk da kuwa babu abun da ya taɓa haɗa su amma jin kowa na koƙen ta yake fatan wani abu ya haɗa shi da ita ya tafarfasa ta,cikin zumuɗi ya ɗaga bulalar ya fara dukkan Nafisa Wadda guda ɗaya na shigarta ta hau kururuwa tana ihu,runtse ido Big mommy dake zaune tayi tana jin ihun Nafisa har cikin ranta,amma dole ne ta mata hukunci dan ta lura idan ta cigaba da sake da Nafisa za'a samu Babbar damuwa dole ne ta ringa nuna mata kurenta idan tayi ba dai dai ba.Duka Sargent ya cigaba da yiwa Nafisa Wadda ke faman ihun domin kuwa dukan baki ɗaya ya zautar da ita,yana ƙoƙarin sake ɗagawa  ya zuba mata wata mai shegen zafin Akram ya shigo gurin da sauri ya saka hannun sa ya tare dukkan,sosai ta shige sa,cikin yanayi na jin zafin dukan sosai yace"Baba Idi duka akace kayi mata ba wai ka kashe ta ba,haba dan Allah wanne irin duka ne wannan".cike da jin kunya Baba Idi yace"wannan yarinyar bata jin magana Akram horo shine dai dai da ita".a hankali Big mummy dake gefen su tace"zaka iya tafiya Nagode".babu musu ya fita yana sake kallan Nafisa Wadda ke aikin kuka kamar an yanka ta,sallamar khadija da Suwaiba ne ya katse dukkan su daga yunƙurin yin Magana,Kallan Khadijah Big mommy tayi tace"ya ciwan nata?".kafin Khadijah tace wani Abu Suwaiba tace"wallahi Big mummy baki ji ba kamar ido na zai cire".cike da takaicin ta Akram yace"shin tukunna ma mene ya haɗa ku?wani kukan Munafirci Suwaiba ta ƙaƙalo ganin yarda Nafisa ke kuka gudun itama Kada a chasa tafara bada Abunda ya haɗa su tana mai cire Part ɗin da ta faɗawa Nafisa jinin Karuwai". tambayar Big mummy Khadija tayi shin Nafisa ta satar mata jambaki tace ta duba ne bata gan sa ba amma daga baya kuma ta gani cikin kaya, Nafisa na jin haka ta tashi ta fita a gurin da gudu dan idan ta tsaya wani damban zasu sake da Suwaiba bugu da ƙari kuma baza ta iya kare kanta ba saboda takaici.Nasiha Big mommy tayi musu tana mai sake tuna musu su ɗin Yan uwan juna ne kuma dole ne su koyi hakuri da juna.

    Bayan fitar su Big mummy ta samu guri ta zauna tana mai dafe kan ta ,zama Akram ma yayi yace"Big mommy duka bazai gyara. Nafisa ba ,sai dai ma ya sake lalata ta, wannan dukan da Baba Idi Kuma yayi mata yayi yawa a matsayin ta na mace,beside kina Kallan yanzun Bata da laifi kan Abun da ake zargin nata ma"Ajiyar zuciya Big Mommy ta sauke tace"Akram ban san yaya zanyi da Nafisa ba duniya,bata jin magana ko na sule ɗaya yanzu da ace da tausayi ta cire wa Suwaiba ido fa, komai na Nafisa na damu na,ita Baga nutsuwa ba sannan Baga ilimin ba,idan na zauna damuwa kullum yawa take mun dan ina mutuƙar san Nafisa ta samu rayuwa mai kyau fiye da kowa,amma a yanzu bata bani dalilin haka  ban san kwatakwata ina ta dosa a rayuwa ba,wa kake ganin zai Aure ta a haka,na farko baka da Background Mai kyau sannan baka da hali mai kyau,Ni dai nasan ko cikin gida nan babu namijin da zai so ya Auri Nafisa ballantana kuma wani daga waje abun na mutuƙar damu na".ɗan murmushi Akram yayi yace"Kuruciyar ka bashi ne zai nuna wane kai nan gaba ba mommy ni jikina Yana bani tana da future mai kyau kuma insha Allahu zakiyi alfahari da ita,it doesn't matter bata da wani ƙoƙarin a yanzun gaba zata yi ".cikin damuwa Big mommy tace"gaba yaushe Akram,sai yaushe,kullum fa ƙara girma take,wane ya sani wannan karan ma ta sake repeating who knows Dan baki ɗaya bata taimakon kanta balle ta taimaki masu taimakon ta,gashi kaima tafiya zaka yi kaga sai Abunda yayi gaba, yaushe ne ma zaka wuce?"sosa Ƙeyarsa yayi yace"next two weeks insha Allahu amma kafin na wuce nama Ismai'l magana zai cigaba da Bata lesson,and least I forget a Taya ni yiwa Babana Alhaji godiya dan ta gurin ki kawai ake samun sa,dan Allah ki faɗa masa bazan basa kunya ba Kuma bazan manta Abunda yayi mun a Rayuwa ba dan haka ma shi zan fara kawo wa takardar sakamakon tura Ni Yankee da yayi,ya shirya  tarbata".shiru Big mummy tayi na Wani lokacin tana mai shan jinin jikinta kafin tace"Baban ka kuma?"tashi yayi daga zaunen da yake yana mai yin murmushi mai ɗaci yace"Alhaji Muhammad Tukur ,kin san shi ɗin Baban kowa ne muddin kana cikin gidan nan,bari naje na duba yar ƙanwata".fita Yayi Big mummy na binsa da kallo zuciyar ta nayi mata ɗari ɗari tana mai jin tsoron ko Akram yasan Sirrin da ita kaɗai ta sani kuma take ɓoyo shekara goma sha biyar kenan,saurin kawar da tunanin tayi tana mai sake jadadawa a ranta kan cewa ita kaɗai ta sani kuma baza ta tona ba har sai mai Sirrin ya nemi a faɗa.shin wanene Akram?

    Akram kamar kowa yake cikin gidan marayun amma nashi salon shigo gidan ya banbanta dana kowa,yana da shekaru Bakwai aka kawo sa ,a cewar waɗanda suka kawo sa ɗin iyayen sa sun mutu a hatsarin mota shi kaɗai ya tsira sannan yace bai san kowa nasa ba dan haka suka kawo sa gidan Marayu,a dukkannin al'amarin zaka gane akwai sake domin kuwa ya kamata ace sun bada cigiya,a maganar da suke yaji suna cewa ya manta shekaru baƙwai da yayi duba da hatsarin da ya samu wanda duk da yarintar sa hakan ya bashi mamaki domin kuwa babu wani nasa ko wata rayuwar sa da ya manta ,shi dai yasan yayi hatsarin a hayar su ta zuwa makaranta shi da driver ɗin Babansa bayan nan kuma ya farka ya ganshi a Asibiti da baƙin fuskar da suka kawo sa gidan Marayu,yasan cewa mahaifiyar sa ta mutu wajen haihuwar sa a yarda ake faɗa masa,sannan mahaifin sa na raye hasali ma a ranar kafin ya fita domin tafiya makaranta yaje gurinsa har ya basa kuɗin break,fahimta da yayi na cewa buƙatar sane ba ayi yasa ya ƙi magana illa sunan sa kawai da aka tambaya ya faɗa wanda babu wanda yayi mamaki inda ya kamata kuma ace sunyi.zafin fansa da ita Akram ya girma dan ya yarda da cewa mahaifin sa ya wulaƙantar dashi ne saboda matar sa wadda ko kaɗan bata ƙaunar sa sannan a gaban sa zata ci zarafin sa tayi masa ƙeta iya ƙeta amma mahaifin sa baya iya faɗin komai haka nan yana kallon su zai wuce, abun na nan zuciyar Akram yana ganin sa kamar sabo,suna,guri,gida babu wanda ya yarda ya manta haka yake ta bitar su har ya zuwa girman sa,a da baya da wata sake wa da kowa sai Big Mommy ita ma ba sosai ba sai daga baya da Nafisa tazo ,shaƙuwa sosai suke da ita tsakanin su dan kullum yana maƙale gurin Big mummy yanawa Nafisa wasa,bangare na karatun ta kuwa duk da yarda bata ja baya gajiya da yi mata lesson a cewar sa idan bata ɗauka yau ba gobe zata ɗauka,Tafiyar sa Yankee yaƙi sanar mata ne dan yasan baza su zauna lafiya ba,ya zaɓi Yankee ne domin samun karatu mai kyau ,bai san tafiya ya bar Nafisa amma ya zama dole muddin yana san itama yaga ya bata rayuwa mai kyau amma dole ne ya fara samarwa kansa yanci da Future Mai kyau tukunna.

    Kai tsaye bayan fitar sa inda yasan zai samu Nafisa ya nufa, definitely yasan dama idan tana da damuwa gurin take zuwa tasha kukanta ta ƙoshi ,zaune ya tarar da ita tana ta sharɓar kuka kamar ranta zai fita,zama yaje yayi kusa da ita rasa abinda zai fara faɗa mata yayi ganin yarda take kukan haiƙan da gaske,gyara murya yayi yace"Feenah kukan nan ya isa haka dan Allah kiyi haƙuri".kamar jira take ta sake fashewa da kuka tana mai cewa"Yanzu tafiya Zaka yi shine baka faɗa mun ba sai a bakin waccan munafukar Suwaiba ɗin nake ji, wallahi ƙafata ƙafar ka nima bazan zauna ba".da Mamaki ya kalle ta yace"Abinda kike wa kuka kenan ba dukan da aka miki ba?"cikin kukan ta ƙara da cewa"Ni wannan duk bai dame ni ba kamar yarda tafiyan ka ta dame ni,duk waɗan nan zan iya magananin su daga Suwaiba ɗin har mai dukan nawa Amma tafiyar ka fa,Allah in ka tafi Kabar Ni zan gudu daga gidan nan "dafe saitin ƙirjin ta tayi tace"baka ji nan yarda yake mun ciwo bama idan na tuna wai zaka bar gidan nan Ni ina ciki, Allah bazan yarda ba ko mene za'ayi"dariyar dake neman ƙwace masa ya gumtse kafin yace"oya juyo ki kalle Ni nan Feenah ta mai kyau"ƴar dariya tayi sannan ya juyo fuskar nan tayi jawur idanun nan kuwa shaɓe shaɓe da hawaye, hannun sa yasa yana mai goge mata hawayen yace"maza ki saurare Ni,wannan kukan bana san shi a kan fuskar ki mai kyau,da farko kuma ina san ki sani tafiyan da zanyi dan ni dake zanyi ta,ina so naje na dawo nayi kuɗi yarda zan kula dake sosai,ba dai Ni zaki Aura ba?to ki kwantar da hankalin ki ina dawowa zan Aure ki na ɗauke ki gidan nan,amma fa sai kin mun alƙawari zaki dage a karatu".ɗa gyatsine tayi da fuska kafin tace"kai Ni wallahi maganar karatun nan bana san ta kwatakwata, wallahi babu abinda ke hawa kaina sai ma sauka dan zaka ga kamar na kama ina komawa na kwanta nayi bacci na tashi sai kaga wani ikon Allah nutsuwa ta tafi dashi,amma dai in dai zaka riƙe alƙawarin ka na Aure na zanyi ƙoƙari ko ɗan turancin nan na iya tunda yare ne".ƴar dariya yayi yace"naji Isma'il zai na miki bita,dan Allah matar kada ki bashi hard time".wani sunkuyar da kai tayi tana murmushi jin ya kirata matar ita a dole kunya kafin tace"baza kaji matsala daga gurin na ba duk abinda kaji ya faru Allah shine yaja ,ka ja masa kunne sai mu zauna lafiya Kuma ka faɗa masa kada ma ya fara tunanin so na dan Ni bana kasuwa dan nasan ba lallai ya iya ɗauke kai ma kyau na ba". dariya yayi sosai kafin yace naji kyakkyawata zan ja masa kunne yanzu dai yarda abun nan yazo da haka ba karatu sai gobe,yanzu kije ki huta and Allah idan naji wani abu ya haɗa ki da suwaiba zamu ɓata.kaɗa kai tayi ta ɗaya yatsun ta guda biyu tace Nayi alƙawari indai bata shiga harka ta ba.

TBC

Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top