19

womenofwords/WA

🔏NOT ALL GLITTERS ARE GOLD💫

(BA DUK KYALLI BANE GWAL)✨

     Be with 👇

*𝐴𝑊𝐸-𝐼𝑁𝑆𝑃𝐼𝑅𝐼𝑁𝐺 𝐼𝑁𝐾🥌*

Tagwayen tafiya Mai sihirtattaciyar Ma'ana ta ban Mamaki daga jerin Tawwada d'aya Al-'kalami biyu first series.

*LOKACI.!*

Halish Sultan.

*BA DUK 'KYALLI BANE GWAL.!*

Chuchu jay

https://whatsapp.com/channel/0029VaRpQeUHwXb52H0abb05

Ga masu nema daga farko 👆

Chapter 19

    Kiran da Uncle Saleh Yayi wa Jamal shine abinda ya saka shi bari ɗakin dan yasan kiran Uncle Saleh a yanzu yana nufin Hajiya Saddiqa tazo ,kamar yarda tace tana san ganin shi kuwa zuwan nasa ne,bayan ya gaishe ta a ɗin Office Uncle Saleh ya samu guri ya zauna yana mai bin ta da kallon ƙiyayya baki ɗaya baya ganin mutuncin ta da darajar ta saboda yasan bata da su,ji yake kamar ya tashi ya shaƙe ta musamman idan ya tuna da cewa Jannah na hannun ta koda kuwa basu faɗa masa ba,kallan sa take da wani irin smirk Kafun tace"a gani na na ƙarshe da kai Jamal ka sake girma da kyau,Masha Allah abun sai wanda ya gani,.gyara zama tayi tana mai juya jakar ta dake kan table tace "naji cewa kana da interest kan Nafisa and itace roomy ɗin ka,well I'm happy dan bazan iya Misilta maka irin murnar da nake ciki ba, you're my secret weapon a kasuwanci na,You make amazing designs da duk lokacin da muka yi lunching ɗin su muke samun manyan alherai,I'm aware a yanzu kasan Nafisa jaka ce ta ɓangaren boko babu abinda ta sani,ni kuma i don't keep useless people dan haka yarda kuka kasance tare ɗin nan ina so ka koya mata aiki,i don't care what you do with her amma ina so at the end of the day ya zama na more ta,Jannah ta ƙara kyau".

Murmushi yai jin last sentence ɗin ta na jannah ta ƙara kyau,cike da rashin tsoran ta yace "is that a threat?".ƴar dariya tayi tace"threat?come on young man kana sounding kamar Jannah na hannuna zan mata wani mugun abu,bata hannu na amma nasan inda take and hopely zata dawo hannu na in yaso Kaga you will work at ease har Allah yayi contract ɗin mu ya cika so dan haka dole ne yanzu ka horar da Nafisa ,ban damu ta yarda za kayi ba but just do it"…cike da matuƙar haushin ta yace"when are you going to let her free,I mean yarinyar nan have a life of her own,ba siyan ta kika yi ba ,ba ke kika haife ta ba,ba kuma ke kika hallice ta ba mene amfanin ki daƙile mata enci".tashi tayi tana dariya tace"wannan ba damuwar ka bane ɗan saurayi,ban san mene ta faɗa maka ba amma ina so ka sani kada ka tura hancin ka dan ƙarshe zaka ji ciwo,maganar raba muku ɗaki kuma ka manta ,idan na raba muku ɗaki wane zai na bata lesson ɗin dare,kada ka damu Jannah rayuwa take mai kyau".da haka ta fita a Office ɗin tana dariya wadda Jamal ke jin ta cikin wuyan sa,tana fita Uncle Saleh ya shigo,saboda baya san jin maganar sa ya tashi yana mai cewa"ko mene zaka ce Uncle save it and spare me the bullshit".bai jira wani ƙarin magana ba ya fita yana mai jinsa yana cewa"Ka fito da Nafisa Hajiya tace ayi introducing ɗin ta da sauran ma'aikatan ,.yana fita inda ya saba zama shi kaɗai ya nufa,yana zuwa ya fashe da kuka ko zuciyarsa dake masa zafi zata daina ,ya daɗe a gurin yana mai san Zuciyar sa ta lafa masa Kafun ya tashi dan zuwa kiran Nafisa kamar yarda Hajiya tace ayi introducing ɗin ta,zaiyyi amma fa duk wanda yake ganin zai iya cutar da ita to zai fara ne ta kansa,ille kuwa koda suka je tare da Nafisa kowa kallan ta yake sannan kowa da abinda yake saƙawa a ran sa dan gane da ita.

*******************************************

    Yau ta kasance girkin Hajiya Hadiza ne dan At least Saddiqa kan bar Alhaji yaci abinci ta Musamman idan bata da niyyar ayi abinci a sashen ta,amma fa maganar su ƙwana guri ɗaya babu ita babu kuma wanda ya isa ,kamar kullum Hajiya Hadiza na serving Alhaji abinci wanda ta ɗauka ibada ,tana tsaka da zuba abinci a plate Hajiya saddiqa ta shigo bayan ta biye da yarinya wadda kana kallan ta kasan a tsorace take,kallan ta Hajiya Hadiza tayi ta ɗauke kai dan tasan zuwan bana Alheri bane dan haka tana gama zuba masa abincin ta miƙa masa gaban sa ta juya dan barin falon baki ɗaya ,step ɗaya ta ɗauka daga kan stairs ɗin dining area ɗin Hajiya Saddiqa tace"hold on,na san a zuciyar ki kullum kina mun addu'a mara kyau kina so kiga baya na ,amma kuma matsalar guda ɗaya ce wanda ya fika ya fika,ta ko ina kuma ni Saddiqa na fiki Hadiza,ina da mugunta amma ta wani bangaren ina da zuciya mai kyau,idan na zauna na kalli yarda kike very miserable a gidan nan sai kina bani tausayi kamar cikin chokalin shan shayi shi yasa nake duba ɗan abinda baza a rasa ba wanda nasan kina ɗaukar sa dearly a rayuwar ki na baki musamman idan ya zamana a gurina they don't mean jack,so yanzu ma hakan ne,tunda dai miji ya zaɓi da ya so ni ya bar ki naga bai kamata na bar ki babu tuƙuici ba dan haka yanzu ma na ɗan gutsira Miki wata kyauta".

Yarinyar bayanta ta jawo gaba ta hankaɗa ta gurin Hajiya Hadiza da ƙarfi wanda ba domin Hajiya Hadiza tayi saurin tare ta ba sai ta faɗi tayi rauni,wata irin dariya Hajiya Saddiqa tasa tace"gata nan Ni'ima ce da kika aikin haukan damuwa akai,kin san ina da kuɗi sannan nasan mutane so na daɗe ina cigiyar inda zan ganta lastly dai muka samo ta gidan marayu,zaki iya tattara ta ku fita zan gana da Alhaji na".

Alhaji da ya zama kamar wawa ne ya ture abincin yana mai tasowa yace"da gaske wannan Ni'ima ce? Hajiya what happen garin yaya aka samo ta ,ya akai kika gane ta naga tun jarirantaka ta ɓace"...wani banza kallo ta bawa Alhaji Bukar kafin tace"zaka ja da magana ta kenan Alhaji?,tunda nace Ni'ima ce itace mana idan kuma baka yarda bane ai zamanin yanzu yazo da abubuwa kala kala a asibiti ma za'a gane,kada kasa fa Nayi dana sanin nemo ta after all ka faɗa mun riba ta ,bana san iskanci".

"Ni'ima ce,i can feel it,I'm her mother and the bond and connection cannot be wrong"hannun ramarmiyar Yarinyar Hajiya Hadiza ta kama ba tare da ta sake furta wani abu ba ta jata suka bar ɗakin..

Dogon tsaki Hajiya Saddiqa ta buga tace"Shegiya wadda bata iya godewa Alheri ba,atleast ta nuna ,ta mun godiya ai,amma ta wani jata ita ala dole uwa ,yen yen yen yen,ni dallah me ta dafa?,Kamar bindi Alhaji Bukar ya bita yana mai cewa,tuwan shinkafa ne miyar Vegetable nasan kina so kuwa muje na saka miki,haka ya zuba mata abincin ta fara ci duk da kuwa daɗin da yayi mata bai hana ta duk loma ɗaya ba ta zagi Hajiya Hadiza.

    Straight Hajiya Hadiza taja hannun Yarinyar zuwa sashen ta zuciyar ta nayi mata mugun bugu da wani irin zafi da ta kasa misaltawa ,suna shiga Sultan dake koyawa Saima assignment ya taso yana mai cewa"Ummu lafiya nagan ki kamar kinyi kuka?wannan ɗin wace?"..dan goge hawayen dake gefen idanunta tayi tace“Ni'ima ce ƙanwar ka data ɓata Allah ya bayyana and Ina yin kuka ne saboda daɗin haɗuwa da ita".cike da Mamaki Sultan yace "Ni'ima kuma?wane ya gano ta and ba tun tana jaririya ta ɓace ba ya akayi aka gane ta da sauri haka?anya Ummu i can't see the resemblance ƙwata ƙwata".Cije haƙora Hajiya Hadiza tayi tace"Sultan nace Ni'ima ce ƙanwar ka da ta ɓata ta bayyana shin kana buƙatar karin bayani ne? she's your sister, she's your sister don't you understand?why are you asking me questions?"Wani irin kuka ya ƙwace mata a ƙarshen maganar ta da yasa ta saki hannun Found Ni'ima ta nufi ɗakin ta da saurin tana mai zubar hawaye,kallan ƙofar ɗakin nata Sultan yayi "yace Ummu na yarda ,i was just confused and happy ne"sai kuma ya dawo da kallan sa kan Ni'ima wadda kana kallan ta kasan yunwa tayi mata mugun kamu saboda ramar dake tattare da ita,ɗan murmushi yayi yace"welcome back home sis"Saima dake gefen sa ne ta rungume ta tana mai cewa"duk da we don't know you amma mu na ta Miki addu'a ashe kina hanyar dawowa gare mu"murmushi kawai Ni'ima keyi ta kasa faɗin komai, hankali ta baki ɗaya yana kan Ummu da ta shiga ɗaki tana kuka.

Kallan su Sultan yayi for the last time Kafun yace"Saimah ki kaita ɗakin ki daga gani she needs hot shower bari naje na samu Ummu".daga haka ya juya ya nufi ɗakin Ummun nasu yana mai jin tsoron shiga, Kamar munafiki yayi knocking inda ta basa izini ya shiga,saurin goge idanun ta tayi tace"ka biyo ni ka cigaba da mun jamb questions ɗin ne ko kuwa yaya,and farin cikin ma baza ka barni nayi cikin ƙwanciyar hankali ba"?

Sosa kan sa yayi yace"kiyi haƙuri Ummu abun ne kawai na jisa wani irin shi yasa,Kiyi haƙuri...Sniffing tayi tace "ko yaya zaka jisa Sultan bana san tambaya,anga Ni'ima an gan ta sai mu gode wa Allah,i was just lost in emotion kaga na shigo na bar ta"tashi tayi har tana mai haɗa kafafu.

"Na saka Saima ta kaita ɗakin ta tayi wanka cos with the way she's stinking tana buƙatar wanka da ruwa mai zafi,I'm just sad for her yarda na ganta daga gani she have story to tell"ɗan shiru yayi da ya kai Aya baya son ya sake faɗar wani Abu Ummu tayi kuka amma deep down Abunda yake ji kaɗan ne,ka mata yayi ace yayi farin ciki,amma neither shi ko Ummu babu wani farin ciki a wannan baƙon al'amarin.

Shiru Ummu tayi ita bata fita ba kuma bata zauna ba,haka nan taji tana san sanin halin da Nafisa ke ciki,cike da damuwa yace"har yanzu dai labarin Nafisa shiru dai ko?...ajiyar zuciya Sultan yayi yace"Wallahi Ummu abun Ni har ya fara bani tsoro,Allah yasa dai Aunty gidan da ta ɗaukota ta mayar da ita ba wani abu ta mata ba.

Murɗa handle ɗin ƙofar Hajiya Hadiza tayi tace"babu abinda zai same ta domin Allah ba azzalimin bawan sa bane".bin bayan ta yayi yana mai faɗin insha Allah Ummu.

    Hannu Biyu Hajiya Hadiza ta ƙarbi Ni'ima ta nuna mata gida tazo cikin danginta ta saki jikin ta sannan ta ƙwantar da hankalin ta komai ya zo ƙarshe,murna sosai Ni'ima ta ringa yi musamman da ya zamana tana samun abincin da a Rayuwar ta ta cire ran zata samu,ga kuma kulawa da barin uƙuba a baya,iya azabar da ta gani a rayuwar ta bata fatan komawa koda kuwa maƙiyi ne bata masa fatan faɗawa halin da ta fito daga ciki,babu wanda ya takura mata kan ta faɗi daga inda ta fito wanda hakan yayi mata daɗi,daga Ummu har yaranta kuwa kowa tunani ta hanyar da zai daɗaɗa mata yake ,Kafun kace mene jikin ta ya fara kyau, lokacin da ta cika sati biyu gidan Hajiya Hadiza ta kira ta ɗakin ta ,cike da sakewa da sabon sabo da ta ɗan fara dasu taje tana mai zama ƙasa tace"ina wuni Ummu"murmushi Hajiya Hadiza tayi tace"lafiya lau yarinyar Ummu fatan kina jin daɗin kasancewa damu ko?.da sauri ta ɗaga kanta tace"sosai Ummu,ina jin daɗi sosai ina kuma farin ciki da ya zamana na samu dangina.

ɗan shiru Ummu tayi kafin tace"bana san tambayar ki,amma Ni'ima zan so ki bani labarin inda kika zauna da kuma yarda Saddiqa ta samo ki".shiru Ni'ima tayi kafin tace"gidan Marayu"sai kuma ta fashe da kuka,ganin hakan ba ƙaramun tadawa Hajiya Hadiza hankali yayi ba dan haka tace"ya isa yi shiru,duk dai inda kika baro ƙarshen sa kinzo gida Alhamdulillah,and insha Allahu wahala ta ƙare,ki shirya Monday zan enrolling ɗin ki a school,hope dai gidan Marayun suna baku ilimi?

Kaɗa kai tayi tace"js1 na tsaya.

"To Alhamdulillah insha Allahu zamu san yarda za'ayi yanzu ki tashi kije ku gama tsifar kan anjima sai muje a gyara muku ".Ummu ta faɗa tana mai Bin ta da kallan tausayi,tashi Ni'ima tayi ta bar ɗakin tana mata Godiya,lastly ta fito daga hell ɗin da bata taɓa tunanin zata fito ba ko da wasa.

•••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••

    Gurin Nafisa kuwa tun ranar da Jamal Yayi introducing ɗinta ta fara zuwa ma'aikata dashi,bangare guda kuma ya cigaba da ɗora mata lesson na turanci da take so a free time ɗin su, dukkan idanun kanta suke amma Jamal ya kanainaye babu wanda ya isa ya tunkaro ta, Kamar kullum yarda suke fita break tare haka suka fita tana ta faman cicije baki,Kallan ta yayi yace"Fee,nasan dai wannan sabon halin shiru shiru ɗin da kike akwai wani abu , menene talk to me"Cije Leben ta tayi tace"Nephew wallahi kunya nake ji kuma ina san ka sake faɗa mun dan na fara Sallah kar Allah ya ƙona ni".buɗe ɗakinsu yayi ya shiga tana mai bin sa a baya,zama yayi kan couch yace"ina jinki yar ƙanwata ,kada kiji kunya ta a duk wani abu da ya shige miki duhu,just ask me"zama tayi bakin gado tace"wallahi jinin nan ya ɗauke min tun da safe ni kuma na manta yarda kace mun ana wanka ƙwata ƙwata"..

Murmushi yayi yace"idan kin manta sai na tuna muki yarda ake wanka na faɗa miki abinda zaki fara da fari shine Niyya (A zuciya)sai kiyi Bismillah,sannan sai ki wanke hannunki sau uku,Sai kiyi tsarki ki wanke duk inda Jinin haila ko janaba ta sauka  sau uku, idan baki aski akai-akai wato kana barin gashi anaso ki cuccuɗa gashin gabanki domin janaba zata iya ɓuya ko ta bushe ba tare da kin sani ba,Sai kiyi alwala irin yadda kike alwala idan zaki yi sallah ,ana iyayin alwala so daya daya,ma’ana ba sai kin wanke koh ina sau uku ba,amma ba zaki wanke kafa ba sai ki  kammala wankan,Sai ki diba ruwa a tafin hannunki guda biyu ki mummurza gashin kan ki sosai sau uku saboda ana so duk ƙofofin gashin ka da suka bude a yayin fitar   Jinin haila ko sha'awa su koma daidai. Malamai sunce anfiso ka diba ruwan da tafukan hannayen ka maimakon ka kwara ruwan a kan ka saboda kwara ruwa akai yayin wankan janaba koh Jinin haila yakan sa ciwon kai domin kofofin gashi suna budewa a lokacin fitar da najasar..

Sai ki raba jikin ki gida biyu, ki fara wanke bangaren dama tun daga kafadar ki har zuwa kasa. Sannan shima ɗaya bangaren na hagu sai ki wanke ko ina tun daga kafadarki har zuwa kasa.. Daga karshe sai ki wanke ƙafafun ki suma ki fara da dama sannan hagu.

Idan kikayi haka kin gama wankan hai'la ko jannaba .Kuma  zaki iya yin sallah da wannan alwala da ki ka yi a lokacin wankan tsarki ba sai kin sake wata alwalar ba.Wannan wankan shi akeyi a wankan Janaba, Wankan Haila, Wankan  Biƙi. Wankan Mamaci, Wankan Musuluntar Kafiri,. Banbancin su kawai shine niyya, kowanne idan zakayi sai ka Kudirta a zuciyarka kayi niyyar yin "wankan abinda kakeso kayi kamar,Janaba,Biki,ko kuma Haila".sannan muddin kika ga jini ya ɗauke kada kice zaki jinkirta,maza Kiyi wanka kiyi alwala,gangacine kace zaka jinkirta ko wani zai dawo,dan haka yanzu zakiyi wanka ki rama salolin da ake binki.

Dan shiru tayi kafin tace"yanzu dai na gane amma shi biƙin da janaba ɗin mene,tunda ni dai Hai'la nayi kuma shi na sani". Murmushi yayi dan a yanzu ya daina kunyar amsa mata tambayoyi tunda idan bai faɗa mata ba Babu mai faɗa mata,"shi biƙi jini ne da mace ke yi idan ta haihu, shine bayan haihuwa za ta fitar dashi iya kwanakin da Allah ya tsara mata,wasu sati biyu,wasu uku wasu har kwana arba'in,shi kuma wankan janaba Yana faruwa ne idan mace da namiji suna haɗu wuri ɗaya sun yi jima'i"

Rufe fuska tayi tace"iskanci kawai,dama ni Allah yasa bazan yi ba tunda Ni ba ƴar iska bace".dariya yayi sosai kafin yace"Naji idan lokacin ki yazo zaki gane banbancin Iskanci da kuma abinda Allah ya halatta yanzu dai maza tashi kije kiyi wanka kizo ki rama sallolinki Kafun nan bari ni kuma na haɗa mana Abunda za muci and ya kamata kema ki na koya na huta da aikin mata.dariya tayi ta tashi tana mai cewa na gode Sannan ta shiga bathroom,ajiyar zuciya ya sauka yace"Jamal sannu da ƙokari"Kafun shima ya tashi ya shiga kitchen dan sama musu abuna zasu ci.

°°°

    Daga gurin su Akram kuwa tunda Salman ya shigo rayuwar sa ya samu sassauci Safiyya musamman da ya zamana tana shakkar Salman,shi mutun ne mara ɗaukar raini shi yasa a fili ma ya sakewa wanda jinin sa bai haɗu da ba abune babba,tunda ya fahimci Safiyya da kuma rashin san takurar ta da Akram baya so ya ɗaura ɗamarar ci mata duk space ɗin da ya samu shi yasa basu shiri ko kaɗan dan haka ta ɗan ɗauke kafar ta duk da kuwa takan jaddadawa Akram shi ba mai cikin alƙawari bane,dan haka ya faɗa mata duk abinda ya taso na alƙawarin da ya dauka ba zai ƙasa a gwiwa ba wajen ganin ya mata tunda shi har yanzu a zuciyar sa yar uwa ya ɗauke ta,babu inda take samun damar sa kamar aji tunda shi da Salman ba department ɗaya suke ba shi yana chan bangaren quantity survey.

Kowa yayi settling ya cigaba da rayuwa wadda ke zuwar ma wasu da daɗi wani bangaren kuma akasin haka amma a hakan kowa ya dage wajen ganin ya cimma burin sa na rayuwa..

Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top