18
womenofwords/WA
🔏NOT ALL GLITTERS ARE GOLD💫
(BA DUK KYALLI BANE GWAL)✨
Be with 👇
*𝐴𝑊𝐸-𝐼𝑁𝑆𝑃𝐼𝑅𝐼𝑁𝐺 𝐼𝑁𝐾🥌*
Tagwayen tafiya Mai sihirtattaciyar Ma'ana ta ban Mamaki daga jerin Tawwada d'aya Al-'kalami biyu first series.
*LOKACI.!*
Halish Sultan.
*BA DUK 'KYALLI BANE GWAL.!*
Chuchu jay
https://whatsapp.com/channel/0029VaRpQeUHwXb52H0abb05
Ga masu nema daga farko 👆
Chapter 18
A Hankali Nafisa ta fara rayuwa cikin masarrafa da ma'ajiyar na LGs wadda sosai Jamal yayi mata ƙokari cikin satin da tayi ,tunda tazo babu abinda take illa tayi bacci ,taci Abinci sai kuma tayi game ko kallo a tab ɗin Jamal,bata sanin fitar sa asubar fari yake barin ɗakin ba zai dawo ba sai rana shima dan yayi mata fixing abinda zata ci,yana gamawa zai koma gurin Aiki sai kuma dare ,idan ya dawo yayi making abincin dare baya zama ɗakin sai tayi bacci yakan dawo wanda hakan ya kara saka Nafisa miƙe ƙafa..kamar kullum ya dawo bayan fitar sa ta safe wanda koda ya fita Nafisa na Aikin bacci tun Sallar Asuba da ya tashe ta tayi ta koma,sau da dama sai dai ya dawo daga Sallah ya ganta ƙwance inda tayi sallah tana bacci,koda ya shiga ɗakin cikin matuƙar tashin hankali ya ƙara sa ga Nafisa wadda ke duƙe a ƙasa tana Aikin kuka hannun ta bisa Marar ta tana faɗin wayyo zata mutu,cike da damuwa yace"Nafisa mene yake damun ki?"jin Muryar sa ya saka ta sake rushewa da Wani irin matsanancin kuka tana cewa"Na shiga uku Nephew ƙasan cikina kamar zai tsage kuma tun ɗazu nake Sake pant amma kamar marar tawa ta fashe ne jini sai zuba yake ga ciwo kamar zan mutu dan Allah ka Kaini Asibi"cike da ƙiɗimewa yace"marar kice ta fashe?mun shiga uku garin yaya and.."shiru yayi lokacin da idanun sa suka sauka kan stain na jinin dake inda ta matsa bugu da ƙari kuma wani irin mummunar faɗuwar gaba ta saukar masa lokaci guda ,bai san lokacin da ya kamo hannun ta ba ya ɗago da ita tana kallan sa yace"wane yazo gurin ki?,wani ya Miki wani abu,ki faɗa mun wanene"
"Ni babu wanda yazo guri na,Kuma Ni babu wanda yayi mun wani abu,kawai fa ina bacci naji Marata na murɗa mun kaɗan kaɗan to shine ya ringa ƙaruwa da kaɗan kaɗan shine fa lokaci ɗaya ta fashe jini ya fara fitowa"rushewa tayi da kuka a ƙarshen maganar ta da mutuƙar gaske.,fahimtar inda batun ya nufa yasa Jamal zama a ƙasa yana mai shafa kansa yace "Shit"for a moment yayi tunanin wani yazo yayi raping ɗin ta amma da ya fahimci cewa period ta fara wanda it's very obvious na farkon ta ne sai yaji hankalin sa ya ƙwanta duk da kuwa bai san ta inda zai fara ba,wani irin tausayin ta da a kullum yake ji ne ya sake saukar masa ,a wannan yanayin ya kamata ace tana tare da mahaifiyar ta wadda zata ƙwantar mata da hankali tayi guiding ɗinta ta nuna mata ta hau step ne na girma,idan babu mahaifiya kuma ya kama ta ace tana gaban wata mother figure da zata ɗora ta a hanya amma kash tata ƙaddarar da Girman gaban wani Namiji wanda bata da alaƙa dashi yazo,shi mutumin Kirki ne ko na banza?tambayar da yakan yawan yiwa kan sa kenan,tabbas koda ace shi yana da tawaya ta wani halin wanda yasan ba zai rasa ba tunda babu mutum ɗari bisa ɗari yana Fatan ya zamar wa Nafisa Family ,ya zamar mata madafa ya taimaka mata a duk hanyar da zai samu dan duk ta inda ya duba ya zaga rayuwar ta bata da maraba da tasa ,bai Tsammani ba yaji hawaye a kuncin sa ,idan Nafisa tana gurin sa yasan she's safe amma Jannah fa?ina take yaya zatayi lokacin da nata al'adar ya sauka ɗan she's just as clueless as Nafisa ,sautin kukan Nafisa da ta cigaba ne ya fito dashi daga tunanin da ya faɗa ,cikin wani irin kuka tace"ta fashe ɗin ko Nephew shi yasa kaima kake kuka?ai na sani Nikam na shiga uku zan mutu"rumtse idanun sa yayi yace"ki saurareni nan Nafisa ki daina wannan kukan,ba marar kine ya fashe ba,Kin taɓa yin islamiyya?".kaɗa masa kai tayi tace"Eh nayi Islamiyya a chan gidan mu"
"Good,nasan At Least an koya muku Karatun haila and wannan jinin shine ki keyi".a tsorace tace"na shiga uku,yanzu kana so kace min na fara jini haila?na girma kenan fa kuma zan iya samun ciki ,na shiga uku ni Nafisa,kuka ta sake fashewa dashi wanda yasa Jamal rasa inda zai saka kansa,tashi yayi yace "ina zuwa yanzu zan dawo "yana fita ta sake duba gurin jinin ta fashe da matsanancin kuka Zuciyar ta kuma na mata wani irin duka dan idan bata manta ba akwai ranar da taji su Khadija na hirar hai'la har suke faɗin mace na farawa zata iya ɗaukar ciki gashi tana tare da Namiji kuma taji ance idan namiji ya fiye taɓaka zaka samu ciki gashi da Jamal ya shigo ya taɓa mata hannu,dafe kirjin ta tayi tace"shikenan na shiga uku Ya min ciki shikenan ya zanyi da raina?mene Boda Akram zai ce idan yasan ina da ciki?".haka nan ta zauna tana ta aikin rusar kuka .
Kai da kawowa Jamal keyi bakin ƙofar Office ɗin Uncle Saleh yana tunanin ta inda zai fara faɗa masa zai fita cos fitar sa ma sai da sanin sa ,farcen sa yake ciza da haƙora yana mai saƙa da warwarar Abunda zai faɗa masa ya fita,yana wannan tunanin Uncle Saleh ya fito,kallon sa yayi yace"Ah Nephew lafiya kake ta Safa da marwa a nan gurin hope I'm safe ?dama kuma kaga ina neman ka Hajiya na shigowa yanzu za kuyi magana kan Nafisa".licking lips Jamal yayi yace"kafin tazo ina san zan ɗan fita na siya abu".
"Kaci Sa'a kuwa fitar zanyi nima ,mene za'a siyo maka in yaso sai na taho maka dashi".
Haɗe rai sosai Jamal yayi yace"Uncle Ni ba yaro bane for God sake ,nace maka zan je na siyo abu ba shine yake nufin nace maka ka taimaka ka siyo mun ba,shin shikenan ni a kullum sai dai na faɗi abinda nake so a siya mun kamar wani yaro? nasan mene nake kuma bazan gudu ba ka sani "..dafa kafaɗar sa Uncle Saleh yayi yace"yi haƙuri calm down ,kaje amma kada ka daɗe".bai jira ƙarin wata maganar ba ya juya ya bar gurin,.kai tsaye bayan ya fita ya tsari machine yace ya kaisa cikin gari ,Allah yasa Hajiya Saddiqa na biyan sa 20 thousand duk wata wanda saboda tsabar takaici bai taɓawa ,hannun sa da abinda yake making makes millions amma take basa 20k wai ya kula da kansa,yana da savings ada wanda mahaifinsa yayi masu shi da Jannah shine abinda kaɗai ya tsira dasu ya zuba su guri mai amfani saboda gaba..
Bayan isar sa Cikin Garin wani shopping mall yaje ,ya daɗe a side ɗin Toiletry yana tunanin Abunda zai ɗauka,ga dai pad yana kallo amma sai yake ganin kamar shi ake kallo,wata budurwa da ta kula dashi ne ta tako tana mai murmushi dan tana kallo idan ya kai hannu kan pad ɗin yaga kamar shi ake kallo sai aje,basket ɗin hannun ta ta gyara ta saka hannunta ta ɗauki pad mai 36 ,then ta ɗauko Shaving foam ta saka ciki ,murmushi tayi ta kalli Jamal tace"nasan nauyin ɗauka kake and it seems ko sister ko wife kazo siyawa ,it's even obvious wife ne and she most be very lucky,muje zan riƙe maka sai kayi payment ɗin,hannunsa yasa a kan sa ya shafa a ransa yana mai faɗin "Abeg see embarrassment "kamar tasan abinda yake tunanin tace"calm down yana faruwa haka musamman gaka young with a wife to take care of dole ne zaka ji kunya amma trust me it's nothing,do you need a new pant muje sashin panties?.kamar bai san maganar yace"ina san siyan mata Toiletry tukunna hope you won't mind helping me".murmushi tayi tace of course , Antiperspirant,deodorant ,bathsalt, emollient ,hair oil, spray , ointment, perfume,Lotion.,tasa hannu zata ɗauka powder ne yace "No banda powder"murmushi tayi tace idan ka kai mata ita tasan amfanin da zata yi dashi".sanin cewa sai ya sani Nafisa zata sani gashi shi kuma bai sani ba kuma bazai iya tambayar wannan baiwar Allah ɗin ba yasa yace"ai tana da ita"gyara Basket ɗin tayi tace,well I guess ba sai an ɗauka panties ba kenan,Rumtse idano yayi ya buɗe yace"Yes ba sai an ɗauka ba" .
A tare suka je wurin biyan kuɗi ya biya aka saka a leda,kallan ta yayi yana mai murmushi yace "your bill on me and naga Baki ɗauka komai ba ,i can wait for you".ɗaga hannu tayi tana murmushi tace"oh come on it's okay kada ka damu You don't have to buy me anything ,a gaida mun da madam an ace mata she's very lucky,maybe wata rana mu haɗu, sunana Hindu"
"Jamal "ya bata amsa yana murmushi,ganin tana binsa da ido still yasa yace "something on my face?"dariya tayi tace"sunan Madam nake jira" ƴar dariya yayi yace"Nafisa,and insha Allahu zan faɗa mata contribution ɗin ki.da haka sukayi sallama ba tare da ya damu da yayi creating wani alaƙa da Hindu ba after all tace taimako tayi and he's grateful,bayan fitar sa ya nufi pharmacy ɗin cikin Mall ɗin ya siya mata magani sannan ya wuce...koda ya koma da saurin sa ya nufi daƙin sa kai tsaye,ta daina kukan amma tana ta faman Shesheƙa ta haɗa kai da gwiwa,cike da damuwa ya duƙa gaban ta ganin ko amsa sallamar sa bata yi ba ,hannun sa yasa ya ɗago kanta ,da sauri ta ƙwace tana mai sake rushewa da kuka tace "Nephew wani cikin kake sake mun bayan wanda kamu?"da mamaki yace "ciki kuma?wanne irin ciki ".cike da Shesheƙar kuka tace",har alƙawari kayi babu abinda zaka mun a ɗakin nan amma daga fara jini na sai da kasan yarda kayi kamun ciki"shiru yayi yana kallan ta ganin yarda take maganar haiƙan da gaskiyar ta,clearing throat ɗin sa yayi yace"to ni yanzu Nafisa kin saka ni duhu,ki faɗa mun wane irin ciki nayi Miki".Cikin muryar Kuka tace"kai dai kawai ka cuce ni,ban san abinda zan fara faɗawa Boda Akram ba ,ai nasan cewa idan mace na jini namiji ya taɓata shikenan tayi ciki kuma kana shigowa ɗazu ka taɓa mun hannuna,yanzu ma kazo ka sake taɓa Ni dan na sake wani cikin,wallahi bazan haihu ba sai dai a cire, wallahi kuma bazan yafe ba".Dariya, tausayi, takaici shine yanayi uku da suka saukarwa Jamal,zama yayi yace"naji yanzu je ki wanke jikin ki ga pad nan na siyo Miki sai kisa ga kuma magani duk da naga kamar marar ta daina.
Karɓar ledar tayi ta buɗe tace"to shi wannan ɗin yaya zan saka shi ,ni ban san ya ake yin ba".shima ɗin ba sanin yarda ake yi ɗin yayi ba dan haka yace "bari in duba naga ya ake a Google sai ki gani kisa". searching how to fix a pad yayi Wanda results da yawa suka watso masa,guda ɗaya ya shiga inda yake nuna yarda ake saka pad a pant step by step,miƙamata wayar yayi yace"ki kalla ki gani"kalla tayi kafin tace"Ni wallahi ban gane ba, kawai wayarka ce take kallo na nima nake kallanta kamar yarda muke da littafi idan kai ka gane na ɗauko maka pant ɗin ba sai ka saka min ba".
"Ni ɗin?"ya faɗa da saurin sa yana mai kallan ta,kallan sa itama take tace"kai mana".
"A'a bari na nemo Miki video a YouTube sai ki gani ki koya "wayar sa ya kar ba ya shiga YouTube yayi searching ya kunna ya bata yace gashi,.karɓa tayi ta kalla sannan ta aje masa wayar ta tashi tana mai kakkare jikin ta tace"sai kuma idan na fito asan yaya za'ayi da cikin nan wallahi".bai ce mata komai ba ta shiga bayin shi kuma ya fara gyara inda ta ɓata ɗin yana mai jin tausayin Nafisa,ace a shekarun ta a karatun idan namiji ya taɓa ka lokacin haila ka samu ciki take,gaskiya ita ɗin abun tausayi ce , tunanin yarda zai fara fahimtar da ita ya fara,koda ta fito all dressed guri ta samu ta zauna tana mai haɗe rai, ya ma rasa ta inda zai fara dan literally tana buƙatar sex Education,he can't Blv he's doing this dan ko wani yace masa zai samu kansa cikin situation ɗin nan sai ya ƙaryata,kamar yana tsoro yace"Nafisa ki saurareni nan,babu wanda ya taɓa baki sex education ko yaya ne?"ba tare da ta kalle sa ba tace "kai ka san sa". Murmushi yayi yace "nasan baza ki wuce thirteen ,fourteen ba and Normal ne idan kika fara period a wannan lokacin,amma a yanzu yarda ilimi ya yawaita ɗaiɗaikun teenagers ne zaka zauna kana bawa sex Education personally Dan duk sun sani ,ni ban Miki ciki ba sannan ina so ki sani idan namiji ya taɓa hannun mace ba shine yake nufin yayi mata ciki ba,Yes yanzu da kika fara jini alaƙa mara kyau na shiga tsakanin ki da namiji zaki iya samun ciki ,Alaƙa kuwa mara kyau tana nufin illegal sex ".Wani irin kallo take masa Kafun tace"shi wannan ɗin mene?
Rasa yarda zai mata bayani yayi cos bazai karya ba wannan Shine embarrassing conversation da ya taɓa yi da wani,gyara zaman sa yayi yace"kamar mace da namiji su haɗu jiki da jiki,gado ɗaya suna suna Abu mara kyau". buɗe baki tayi tace"kace mun kawai iskanci,ai nasan yana saka ciki tunda Naji wasu sister's ɗin mu na hirar,and na taɓa kama sister Asiya da hudu mai gadin mu kafin ta tuba suna iskancin su har nake faɗi wata rana sai tayi cikin shege,to kuma sai ake faɗa mana idan ka fara jini namiji ya taɓa ka shima kana samun ciki,nayi zatan duka hanya biyun ai ana samun ciki amma daban".
Dariya yayi yace"to hanya ɗaya ce Wadda idan namiji da mace sun haɗu,Kinga musamman idan babu Aure addini ma ya haramta,amma Kinga idan da Aure halal ne babu zunubi sai ma lada,a yanzu kuwa da kike mace ,kada ki bari koda da wasa wani namiji yayi ƙoƙarin Miki wayau,and yanzu tunda kika fara period yana nufin littafin ki na zunubi da lada ya buɗe,idan ya zaman kinyi missing sallah ɗaya ko sallar ki bata inganta ba to hukunci ki yana daidai dana baligi, baligi kuwa shine wanda hukunci ya hau kansa kuma dole ya kiyaye dokokin ubangiji,Kinga a yanzu ni dake mun zama dai dai ,kamar yarda za'a rubuta mun zunubi idan nayi aikin da ba dai dai ba kema haka nan za'a rubuta Miki kin fahimta ko?,sannan dole ki zamana mai suturta kanki duk yarda kuwa zaki sake Dani ina san ki san muba muharramai bane,zaman mu haka ni da ke ma bai halatta ba amma saboda yanayi na fin ƙarfi yasa muke nan a yanzu,kuma na miki alƙawarin kiyaye mutuncin ki da Sanin geji na".
ɗaga kai tayi tace to naji ance sai kayi wanka idan ka gama haila?.yaya ake yi?..cike da ilimi ya fara nuna mata yarda za tayi da kuma abubuwa da dama da ya kamata ta sani,sai daga baya ne taga abubuwan da ya siya mata tayi ta murna tana masa godiya.
A iya fahimtar da yayi wa Nafisa a ƴan kwanakin ta bangaren Abinda Ya shafi karatu ya fahimci tana fama da dyslexia ,shi dyslexia kuma yanayi ne wanda ya zamana mai ɗauke dashi baya fahimtar karatu,ma'ana learning disability musamman ga abinda baka da ra'ayi,yawancin celebrities na da shi ba tare da sun sani ba domin kuwa galibi sun aje karatun ne saboda rashin fahimta,a bangare guda kuma da ya duba yayi nazari ya fahimci cewa zata iya koyan skills musamman abunda take sha'awa dan haka yayi making up mind ɗin sa waje ganin ya koya mata abunda ya iya.
Authors Note
Assalamu alaikum fatan kuna jin daɗin Littafin nan,and hey not all men are scum,Jamal zai maku proving,and yes gare ku iyaye,ya kamata ace Sex education daga bakin ku yaran ku ya kamata su fara ji,Babu rashin ɗa'a ko rashin kunya dan kin zauna matsayinki na Uwa kin nunawa yaran ki both maza da mata muhimmanci sex education da kuma abinda ya kunsa,tsakanin ka da abinda ka haita babu kunya,kada kuma muce har a wannan zamanin zamu zauna akan faɗawa yaran mu "idan namiji ya taɓa hannun ki zaki samu ciki"zamanin yanzu dana da ba ɗaya bane sai taje ta kiyaye kada a taɓa hannun nata babban al'amari ya faru tunda baki faɗa mata illar sa ba da kuma abinda yake nufi, Allah ya bamu ikon kulawa da zuri'ar mu ,ya saka mana hannu a ciki.
Chuchujay ✍️
Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top