17
#womenofwords/WA
🔏NOT ALL GLITTERS ARE GOLD💫
(BA DUK KYALLI BANE GWAL)✨
Be with 👇
*𝐴𝑊𝐸-𝐼𝑁𝑆𝑃𝐼𝑅𝐼𝑁𝐺 𝐼𝑁𝐾🥌*
Tagwayen tafiya Mai sihirtattaciyar Ma'ana ta ban Mamaki daga jerin Tawwada d'aya Al-'kalami biyu first series.
*LOKACI.!*
Halish Sultan.
*BA DUK 'KYALLI BANE GWAL.!*
Chuchu jay
https://whatsapp.com/channel/0029VaRpQeUHwXb52H0abb05
Ga masu nema daga farko 👆
Chapter 17
Bin Saleh kawai Nafisa take tana mai bin gurin da ido,gurin Babba ne sosai,bin sa take tana mai jin wani iri a zuciyar ta bangare guda kuma tana san sanin mene yasa Hajiya Saddiqa ta kawo ta nan,bakin wasu ɗakuna suka tsaya,murmushi Saleh yayi ya nuna mata wani ɗaki yace "ki shiga nan ki aje kayan ki nan ne ɗakin ku dan babu ɗaki ɗaya da zamu baki dole kiyi Sharing da Jamal shine baya da room mate amma kuma idan zaki zauna Dani ne sai Ibrahim ya dawo ɗakin Jamal ni ki dawo nawa "...hannun sa ya kai kuncin ta yana mai shafa wa ,saurin matsawa tayi tace"kana nufin da Namiji zan zauna?, gaskiya A'a ni bazan zauna da namiji ba dan babu kyau".dariya sosai Saleh yayi yace"to naji kina magana kamar kina da wani zaɓi,to ai nan da kika ganki kin shigo ramin kura ne maza goma sha taƙwas ne a gurin nan ke kaɗai ce mace kuma zuwan ki nan yana nufin zamu sauke damuwar mu ne ai"ƙeyar ta ya talle yace"shiga muje ciki na a fara Dani .
"Ku fara menene? and ita wannan ɗin wace da kake ƙokarin tura mun ita ɗaki uncle Saleh?Jamal mamallakin ɗakin ya tambaya yana mai ƙarasowa inda Nafisa da Saleh suke idanun sa kan Nafisa then kuma ya koma kallan Saleh ".. murmushi Saleh yayi ya kamo hannun sa yana mai cewa"nephew ba wani abu bane , Hajiya ce ta kawo wata ma'akaciyar to ita ma nan zata zauna kuma kaga babu spare ɗaki naka ne kawai baka da mate ,but i can take her with me idan kaga baza ka iya Sharing ba in yaso sai ibi ya dawo ku zauna"...da mamaki Jamal yace"Please take me out of this confusing situation,last I remember we have eighteen ass grown men here and sune kaɗai ma'aikata, menene zai kawo mace har ace kuma wai zatayi Sharing ɗaki da namiji?..murmushi Saleh yayi Sanin halin Jamal da bin diddigi a taƙaice yace"Well kamar yarda na faɗa maka zan ɗauke ta Ibi yazo ya zauna da kai dan dole a bata mahalli,maganar kuma mene take yi anan Aiki ya kawo ta kamar kowa kuma Hajiya ta kawo ta kaga kuwa Vip ce,ke muje"ya maida maganar ga Nafisa yana kallan ta kamar zai cinye ta,a hankali Nafisa ta fara bin bayan Saleh,Muryar Jamal ta tsayar da su inda yake cewa"it's okay Uncle zata iya zama although it's not proper hope ita hajiyan zata sama mata separate guri idan dole ne sai ta mata aiki".Murmushi Saleh yayi ya dawo ya dafa kafaɗar Jamal yace"My little Nephew kamar baka gane Abunda zaman yarinyar nan a gidan nan yake nufi ba ko?well tana ɗaya daga cikin feast ɗin da Hajiya ta tanadar mana,I mean Kaza ce a saman Shinkafa ,kayi imaging irin Digging ɗin da zaka mata"jin Disgusting abinda Saleh ke faɗa yasa Jamal cire hannun sa daga kan kafaɗar sa yana mai cewa"I've heard you uncle Kuma na gode ,tunda ka riga ka kawo ta kayi considering yaran yayan ka da kake kulawa dashi ai abune mai kyau,Nagode da kyautar ka kuma zan tabbata nayi Digging mai kyau ,bazan baka kunya ba insha Allah".washe baki Saleh yayi yace"Now you're talking ,yanzu nasan kana da jini a jika, enjoy Baby boy"Yana faɗin haka ya juya ya bar gurin yana fito.
Kallan Nafisa Jamal yayi fuskar sa cike da damuwa,ganin ya ƙura mata Ido yasa itama ta zuba masa nata idanun,tsaki yayi yace"mene kike wani kallo na kamar mayya"taɓe baki tayi tace"kaima ai naga kallan nawa kake kamar maye shi yasa nima nake kallan ka,duk da ni ban wani fahimci abinda wancan Mutumin ke faɗa maka ba amma nasan shi ba mutumin kirki bane,kuma ni ba kaza bace dan Allah zaka mun hanya na gudu?"shiru yayi na ɗan wani lokaci kafun yace "ina iyayen ki suke ,kuma mene yasa Hajiya ta kawo ki nan kiyi Aiki bayan tasan dukkan mu maza ne ?kin san cewa you're in a great danger ?"hannayen ta ta wara Kafun tace"nima bansan iyaye na ba,big mummy ce dani ita kuma ta rasu to shine Hajiya Saddiqa taje ta ɗauko ni gidan Marayun da nake ,daga Sultan fa yana koya mun turanci shikenan matar nan ta kamani tayi ta duka kamar jaka daga ƙarshe ta ɗauke ni ta kawo nan akan wai nazo na gyara halina,ni idan zaka kashe ni wallahi ban san mene laifin da zan gyara ba ,kawai dai Hajiya ce wani lokacin idan ta maka mugunta wallahi kamar ba musulma ba,kamar bata da zuciyar musulmai,ita dole na daina kula su Sultan akan ai Mayu ne ,kuma baka ga yarda suke min mutunci ba su da Ummun su,ita Hajiya ma nata yaran ne kamar Mayun dan basu da mutunci kar ma Khalid yaji labari ,bai da mutunci ko kaɗan mugun Azzalumi ne,ni wallahi da zata mayar dani gidan mu wallahi da yafi mun tunda ina zaman zama na taje ta ɗauko ni,ko da su Sister Khadijah ta barni wallahi bazan wahala ba,kuma ni turancin da kayi great kawai na iya cikin abinda Sultan ke koya mun amma sauran kuwa ban san mene ba ko za'a yanka ni ".
Hannayen sa yayi folding yana mai kallan ta kafin yace"wanene Sultan and Ina gidan Marayun naku yake?"..washe baki tayi tace"Sultan yaran Ummu ne kishiyar Hajiya Saddiqa data kawo ni,gidan mu kuma yana Gashuwa ne dan Allah zaka mayar Dani?"yana ƙokarin bata amsa Saleh ya bayyana a gurin yana mai cewa"Nephew na manta ban faɗa maka ba ,yarinyar nan is a great deal fa and I'm very sure you don't wanna mess with Hajiya Saddiqa,kasan matar nan is mad as a hornet,yarda take da lose screw ɗin nan she will definitely screw you up idan kayi wani funny move,I've warned you,just have fun a wuce gurin kada kasa kanka inda ba'a saka ba, bazan iya dealing da wannan matar ba"..rumtse Ido kawai Jamal yayi kafin yace"I've Heard you uncle zaka iya tafiya Please.
Juyawa Saleh yayi yabar gurin,.kallan Nafisa Jamal yayi yace "yaya sunan ki?"
"Nafisa,amma zaka iya kirana Feenah,dan Allah dai yanzu zaka bar ni na gudu?wallahi Ni ina da Saurayi Boda Akram yana Ƙasar waje karatu ,idan wani abu ya sameni wallahi zai mutu ne yana so na da yawa ,kuma nasan zama mace da namiji Haramun ne Allah ma baya so musamman idan babu alaƙa ta jini kuma kaga ni da kai ba yan uwa bane bana san Allah ya ƙona ni"Ɗan Murmushi Jamal yayi kafin yace"mu shiga ciki ki aje kayan ki in yaso sai mu zauna muyi planning yarda zaki gudu ɗin amma idan baki so ki mutu kafin saurayin ki dole ki zama mai jin magana".Turjewa tayi bakin ɗakin tana mai saka kayanta a kirjin ta tace"kace ka rantse da Ubangiji idan mun shiga babu abinda zaka mun,ni wallahi tsoro nake ji"rushewa tayi da kuka wanda Jamal ya jisa har ransa yana mai Tunanin Halin da ƙanwar sa Jannah ke ciki,idan da ace yana tare da Jannah a yanzu zata zama exactly shekarun Nafisa,a kullum assurance da Uncle Saleh ke basa shine Jannah zata bayyana as far as ya maida hankali yayi aiki mai kyau a wurin shi zai taimaka masa da connection ɗin Hajiya Saddiqa wanda ita Hajiya saddiqa ɗin take faɗa masa tasan inda take sannan she's safe as far as zai mata aiki na shekaru Huɗu, a yanzu yaci shekara guda saura Uku, shi kan sa yasan komai was a set up amma he was so naive ,young and desperate a lokacin da ya amince musu ,Jamal da Jannah yaran Yayan Saleh ne wanda Allah yayi wa rasu a hatsari da sukayi shi da matar sa da ƙanin su Jamal , Jameel,Mahaifin su na da dukiya sosai wanda bayan rasuwar sa Effcc suka ƙwace komai nasa akan ana zargin sa da dukiyar da ya tara dan haka sai anyi babban bincike a kai, Saleh shine wanda yayi kanai kanai kan abun sannan ya ɗauki Jannah da Jamal akan zai riƙe su, bayan Shekara da rasuwar mahaifin su aka nemi Jannah sama ko ƙasa aka rasa daga zuwa makaranta ,sosai Jamal ya shiga tashin hankali ba kaɗan ba gashi shi ba wai yasan wani abokin mahaifin sa da zai iya komawa domin taimako ba sai Uncle Saleh ɗin nan dai da ke nuna masu duk duniya babu abunda yake so sama dasu, Although Jamal yasan ƙarya ne amma ya danne musamman da ya zamana yana zargin cewa yana da masaniyar inda Jannah take sannan ya ɗauke ta ne dan kawai yayi amfani da baiwar da Allah yayi masa wajen Ƙirƙirar Unique abu, dukkan wani Style dake fita daga Company ɗin Hajiya Saddiqa Jamal ke Bada Sketch nasa sannan ya fitar, yana da basirar da zai fitar da Tremendous and breathtaking designs ,kama daga takalma ne ,Bags, clothes da sauransu,ta wannan bangaren kyauta ce kawai Allah ya basa dan haka uncle Saleh yayi amfani da wannan baiwar shi da Hajiya Saddiqa suka ɗaure Jamal da ita,duk abinda yake so yana samu a gidan domin kuwa idan babu Jamal Ita kanta Hajiya Saddiqa tasan ba karamar asara zata tafka ba.
"Hey,hey Nephew"Nafisa ta faɗa tana mai waving hannunta fuskar Jamal da ya zuba mata ido yana tunani gefen idanun sa kuma ɗauke da ƙwalla,da Mamakin Nafisa tace "kuka fa kake,sunan nawa ne ya saka ka kuka ko kukan da nake ko kuma mene?wallahi nima nasan sunan tsofaffi ne baya da wani daɗi,amma ai Feenah da sauƙi".Jakar hannunta ya karba Yace"kin gama Kukan kenan,note ba sunana Nephew ba sunana jamal".da Mamaki tace"amma ai naji wancan yana faɗa maka Nephew,dariya yayi yace"uncle ɗina na ni yaran yayan sa ne Kinga kuwa ni Nephew ɗin sa ne".kaɗa kai tayi tace"ni da Sultan bamu zo nan ba,amma nasan da ace Hajiya bata kawo ni nan ba da ya cigaba da koya mun turanci da turancin sa kamar na yan America,
"Nima idan kina so zan koya miki, yanzu dai muje ciki and na miki alƙawari babu abinda zan miki,ni ba mutumin banza bane "gaba yayi ya shiga ɗakin,dan turus tayi kafin tabi bayan sa,. kallo ɗakin take a hankali,komai na ɗakin Is manly ,size two bed ne wanda aka lailayesa da white and black beddings , jikin bangon duka gefe da gefe ɗauke suke da paintings masu ɗaukar hankali,gefe guda set ɗin kayan kallon sa ne da mini Speaker gefe guda,sai bangare na wardrobe ɗin sa Mai biyu wadda tasha stickers na ben ten,dariya Nafisa tasa ganin stickers ɗin tace "kai mene kake da wannan yaran jiki durowar ka".murmushi yayi yana mai shafa kansa bayan ya sa jakar kayan ta cikin wardrobe ɗin Cos first time a rayuwar sa yaji kunya wani ya ga stickers na Ben ten jikin wardrobe ɗin sa,for God's sake he's 23 amma har yanzu yana da wannan childhood Male addiction ɗin na Ben ten,kallan yarda yake blushing Nafisa tayi tana mai tsoron faɗin yana da kyau dan ta tsare kanta kada yayi taking advantage ɗin hakan da ita ,amma tasan fa yana da kyau,tho he's Caramel brown amma fa he's a big catch ,duk bala'i san Nafisa da masu kyau tasan inda take Allah kawai zai kare ta and hopely Jamal,shima ɗin bata san shi ba but wani sashe na zuciyar ta yana san yarda dashi,abun na cin ta amma ta danne ,zata faɗa masa yana da kyau amma fa sai ta san shi sosai cos yanzu kawai tayi gambling ne ta biyo sa ɗaki...haɗe hannayen sa biyu yayi yace"well ga ɗaki na nan da zamuyi Sharing na ɗan wani lokaci dan nasan dole Hajiya zata nema Miki guri tunda dai aiki take so kiyi anan,maganar guduwan ki kuma let's not be in a rush,mu jira muga ya komai zai wakana ,and dole Kiyi takatsantsan a gidan nan,idan kina da wata damuwa just talk to me ,for today I will use the couch ke sai Kiyi amfani da gadon kafin na yiwa Uncle Saleh magana yayi Miki fixing,so yanzu dai ni zan koma cikin ma'aikata ga bathroom nan idan zakiyi amfani dashi,and ɗayan ƙofar kitchen ne akwai abinci a kula na aje You can help your self.
Murmushi kawai Nafisa tayi tana mai bin sa da kallo, juyawa yayi ya fita dan dole yayi magana da Uncle Saleh cos man dukkan situation ɗin nan is just insane,Nafisa might be young amma jikin ta says other wise ,ita mace ne komai ƙanƙantar ta bugu da ƙari kuma she don't have a bad body,duk da yanzu komai na jikin ta ke fitowa amma still shi yasan Guys ɗin cikin gidan nan Are just hungry and horny demons,yasan cewa ba Uncle Saleh kawai zai zamar wa Nafisa matsala ba,wuyar ta yaje ya buɗe bakin sa ya faɗa musu cewa Hajiya ta kawo ta ne suyi easing damuwar su sannan kuma su ɗora idanun su akan ta ,dan tana da kyau ba sai an faɗa maka sau biyu ba.
Cikin Office ɗin dake gefen inda suke haɗa abubuwa ya shiga dan Nan Uncle Saleh ke zama kasancewar sa na shugaban gurin,zaune ya tarar dashi yana duba wasu files, sallama yayi ya shiga ya zauna,kallon sa Uncle Saleh yayi yace"Nephew lafiya dai,kai da ya kamata ace kana chan kana jin daɗin ka mene ya fito da kai,kaje ka huta cos you've worked enough for today". Murmushin takaici yayi yace"Uncle seriously?shin da gaske kana goyan baya na akan nayi lalata da minor yarinyar chan?".wani irin kallo Uncle Saleh ya basa yace"aw Kana da second thought kenan,kalli nan Jamal idan baka so ka saki wasu su fara,na faɗa maka amfanin yarinyar nan kenan fa,Hajiya ta tausaya mana ganin yarda muke aiki tuƙuru wani lokacin ma bama da time ɗin fita so ta kawo mana kayan marmari ,a matsayina na kawun ka na fara baka kaci ka rage amma kake tunani?,na fahimta kana tsoro ace kayi raping nata but trust me you're all covered,nasan you're a virgin and she's to shi yasa na baka ka sha roman damokaraɗiya ,I'm sure you have needs,so go and enjoy in kuma baka so ne akwai mabuƙata".
Da mamaki wanda Jamal ya gaji da sha yace"a'a ina so mana Uncle,abu guda nake tsoro naje na san yarinyar chan kuma wani yayi ƙokarin neman ta,matsala zata faru fa,cos the moment I taste her then she's mine,uncle forget about wai kana da abu a kai na I'm sure kasan kayi better than letting Jannah get hurt ,I will create a mad chaos and start a bastard havoc,worst part ɗin kuma shine kasan I'm not bluffing...da mutukar Mamaki Uncle Saleh ya kalli Jamal Kafun yace,"na jika Jamal, forget about situation da muke ciki kai ka sani ina mutuwar san ku,kuma kana abu kamar Ni na sace Jannah,i just told you nasan wasu a inda take kuma ana bata kulawa kuma zata fito, she's beyond safe Kai dai ka mayar da hankali a contract da ka cike kana fita zaka haɗu da Jannah alƙawari na maka".
Tashi Jamal yayi yana mai ƙosawa da rainin hankalin Uncle Saleh, murmushi yayi masa yace"muma muna san ka Uncle,and Ina Fatan zaka tuna duk wani abu da ka faɗa,and Ina San wani bed ɗin a ɗaki na after all I have a partner "Yana kai Aya ya juya,har ya kai bakin kofa ya juyo yace"thank you for the gift uncle "...wata irin Ajiyar Zuciya Uncle Saleh ya sauke Kafun ya Ciro waya dan kiran Hajiya Saddiqa, ringing biyu ta ɗauka,cike da bala'i tace"Saleh lafiya kake kira na da yamman nan,hope ba Nafisa ce ta gudu ba dan idan ita ce to har gwara ace ba kira na kayi ba neman ta ka fita".
"Hajiya wannan ta wuce damuwar Nafisa ita wannan ai karamar alhaki ce amma Jannah kuwa kin san babbar case ce,Hajiya ina fatan kina cika naki bangaren,bana san damuwa fa"ya ƙarasa cike da damuwa kamar yana gaban Hajiya Saddiqa.. murmushi tayi tace"Saleh kenan,duk yarda nake da ƙiyayya mai zafi dangane da Alhaji Haruna Babba bazan banzantar da yaran sa ba after all dukkan su masu amfani ne,kada ka damu Jannah tana hannu mai kyau besides shi kan sa yayan nata zai alfahari dani nan gaba".ajiyar zuciya Saleh yayi yace"na yarda dake Hajiya,kaya kuma sun sauka wannan karan kuma kuɗin da za'a samu ba kaɗan bane sunfi na last set". hannayenta biyu ta tafa tace"yanzu kake magana mai daɗi Saleh,aje ayi ciniki dan na yarda da cinikin ka ɗari bisa ɗari".
Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top