16

#womenofwords
🔏NOT ALL GLITTERS ARE GOLD💫

(BA DUK KYALLI BANE GWAL)✨

     Be with 👇

*𝐴𝑊𝐸-𝐼𝑁𝑆𝑃𝐼𝑅𝐼𝑁𝐺 𝐼𝑁𝐾🥌*

Tagwayen tafiya Mai sihirtattaciyar Ma'ana ta ban Mamaki daga jerin Tawwada d'aya Al-'kalami biyu first series.

*LOKACI.!*

Halish Sultan.

*BA DUK 'KYALLI BANE GWAL.!*

Chuchu jay

  Chapter 16

YANKEE

A cikin class ɗin da su Akram ke ɗaukar karatu Saffiyya ce zaune tana mai faman karkaɗa ƙafa tana mai jiran Akram ya idar sallar da yake ta kankara masa,tun safiya take san magana dashi yake mata hanya hanya shi yasa bayan kowa ya watse a ajin ta tsaya jiran sa ,yana idar da Sallah ko lazimi bata bari yayi ba ta koma gaban sa tace "Akram we need to talk,abun nan fa ba ni ce zan abun kunya ba wallahi kaine dan kuwa i will disgrace you Babu ruwana da wani flat mate da ka ƙwasowa kan ka dama nasan kayi ne saboda ni to wallahi ka sauraren da kunnen basira ko ba kai ɗaya bane zan shiga gurin ka dole ne wallahi ka cika responsibility dake kan ka i don't give a fuck about how you will do it"..shafa addu'ar sa yayi ya tashi yana mai kallan ta yace"Ni nasan Allah da nayi imani dashi wallahi yafi karfin ki Saffiyya ,duk yarda kike so kici galaba a kaina wallahi Allah yafi ƙarfin ki kuma Flat mate nawa ne ba naki ba saboda i need to feel secure musamman a ɗabi'un da kika koyawa kan ki dole ne nayi nesa da ke so if you'll excuse me ni zanje na tari sabon maƙoci na.

Kuka ta fashe dashi wanda yasa Akram kasa cigaba da tafiyar da yake,cikin kuka take faɗin"Nima bani na sawa kaina ba Akram da kake wulaƙanta ni a duk wani chance da ka samu,shin laifi ne dan na kamu da sanka"?.juyawa yayi yace "ba laifi bane Saffiyya amma ina so ki sani Abunda kike mun ba dai dai bane,kina shiga hakkina,na faɗa miki babu soyayya tsakanin na dake ballantana har a kai ga Ni dake mun aikata zina,waiyazubillah dan Allah Saffiyya ki daina saka ni a cikin tsaka mai wahala,kada ki bari shaiɗan yayi tasiri wajen ruguza Abunda ke tsakani na dake,kin san cewa zuciya ta is no where near you,I don't love you romantically Dan Allah spare me".."zuciyar ka na gurin Nafisa ko?wai mene jikin yarinyar nan da kake san lalata rayuwar ka saboda ita?ni banga komai tattare da Nafisa ba bayan balai da jidali,a rayuwa kuma babu abinda Nafisa zata iya tsinana maka illa ma ta zamar maka liability,beside babu wanda yasan inda ma take wanda abune mai kyau,amma ni fa Akram?zan baka gudunmawa ta duk inda baka zato,bangaren Abinda Ya shafi aikin ka i will be there saboda field ɗaya muke , bangaren komai ma ni nasan nafi wannan ƙwailar yarinyar nesa ba kusa ba ". kallan ta yayi na wasu ɗakikun lokaci kafun ya kaɗa kansa yace "Allah ya shirye ki"ya juya ya fita .

Kai tsaye bayan fitar sa Airport ya nufa dan taho da sabon room mate ɗin sa,Sunansa ne ɗauke jikin board ya ɗaga yana hoping Ya gane sa cikin Sauri ,yana wannan tsayuwar matashin Saurayin da ba zai wuce sa ba ya ƙarasa da Murmushin sa yace"Akram"?.kaɗa masa kai Akram yayi yace"barka da zuwa Ohio Salman Bukar Mamman sabon House mate ɗina,naji daɗin haɗuwa da kai.

******************************************

    Kamar wasa haka Sultan ya fara koyawa Nafisa turanci kamar yarda Salman ya buƙata gare sa,farkon haɗuwarsu kuwa ba ƙaramin gwagwagwa aka sha ba musamman da yaga duk abinda yake bata ɗauka da uwar wahala ya samu ta fara riƙewa kaɗan kaɗan shima sai da ya karance ta tukunna ya fara neman strategies na koya mata English ɗin maganar lesson kuwa tuni an aje ta gefe dan kamar yarda take faɗa masa ɗin babu wani abu da yake shiga,a tare har sun cinye wata guda wanda take ɗan ɗiba kaɗan, bangaren Ummu kuwa tunda Nafisa ta fara shiga sashen ta cin abinci a boye taji tana mutuƙar ƙaunar ta ɗan haka take jinta jikin ta sosai duba da nutsuwa da take samu da ita.

Kamar kullum yau ma suna ɓoye ita da Sultan a backyard ɗin Hajiya Hadiza suna karatun da Kafun a gama sai anyi faɗa,kallan bakin sa tayi tace "wai Ni kai ya Sultan wane irin iyayi kake wa turancin nan ne?sai na ce na kasa ka fara faɗa mun magana bayan baki ɗaya wani irin turanci kake kamar bana ƙasar nan ba ".dariya yayi yace"Yo ni ai bakina bai jiƙu da miyar kuka ba kamar na naki".wane haɗe rai tayi tace"kaji to ni Wani yace maka bakina ya jiƙu da miyar kuka?to wallahi a gidan mu babu ƴar gata iri na sai Abunda nake so nake ci kana Wasa and ƙwanan nan idan na fara turanci wallahi Sai yafi naka kuma..".fincikota da Akayi shine ya ƙatse ta daga faɗin Abunda take niyar ƙarawa,wani irin gigitaccen mari Hajiya saddiqa ta ɗauke ta dashi tana mai cewa"munafuka annamimiya dama ai Muna na faɗa mun kin ƙulla alaƙa dasu ban yarda ba sai yau Allah ya saka na gani da idona,.tasowa Sultan yayi yace"Aunty bafa yarda kike tunani bane",nuna sa tayi da yatsa tace"Rufe mun baki munafuki,idan ba haka bane yaya ne?wato kana jawo ta bayan gida dan ka hure mata kunne ko?ko kayi lalata da ita ko tunda gaba ɗaya ƴan ɗakin ku babu na Allah ,to ka tsaya inda Allah ya aje ka, Nafisa kaya na ce kuma nice nake da ikon yin duk yarda naga dama da ita,dukan Nafisa ta fara ,ihu Nafisa take kan yarda Hajiya Saddiqa ke yi mata dukan tashin Hankali,hayaniya da ihun Nafisa yasa Alhaji Bukar da Hajiya Hadiza zagayowa gurin,da sauri Hajiya Hadiza ta isa inda suke ta fincike Nafisa tana mai cewa "shin Saddiqa kashe ta zakiyi ne?"hannun Nafisa Hajiya Saddiqa ta kama tana mai nuna Hajiya Hadiza da hannu tace"ki kama kanki kada kisa zuciya ta ɗebe ni na wanka miki mari Wallahi, kece kika haife ta ko kuwa kina da alaƙa da ita?.da mamaki Hajiya Hadiza tace "ni Zaki mara Saddiqa?lallai wuyan ki ya isa yanka,bani na haife ta ba amma ki sani ita ma haihuwar ta akayi kuma ita karma bata taɓa barin ki lokacin daya zata miki mugun juyi,ga Nafisa nan ki kashe ta Saddiqa dan Allah shine zaki burge tunda dai ke muguwa ce, azzaluma wallahi lokacin da zaki wulakanta dana saninki ta makara".tana ƙare zance ta tabar gurin dan haka nan taji wani irin hawaye da zafi zuciyar ta nayi mata musamman da tasan babu wani abu da zata iyawa Nafisa.

Fincikar Nafisa ta fara kamar jaka tana mai zaginta uwa ta uba,Bin bayan su Alhaji Bukar yayi yana mai cewa"Hajiya kiyi haƙuri mana lesson ne fa kawai suke yi mene laifi".a fusace ta juyo tace"kaima wallahi idan baka mun shiru ba da marin zan iya ɗauke ka babu abinda ya dame ni ,kasan kuma zan iya fiye da haka ma,Kallan Nanny Muna tayi tace"maza shiga ji haɗo mata kayan ta ki ɗauki mun gyale na da mulkin mota na,jiki na Rawa Nanny Muna ta shiga tana mai jin wani irin daɗi za'a mayar da Nafisa inda aka ɗauko ta a nata ganin..ita dai Nafisa babu Abinda take banda kuka gashi Hajiya Saddiqa tayi mata wani irin mugun riƙo ɗin da take ji mata ciwo da farcen ta.bayan Nanny muna ta kawo kayan babu jira ta watsa su cikin bayan motar Hajiya saddiqa wadda ita ma ta cilla Nafisa ciki tana mai cewa"naga aje ki da nayi gidan nan kamar na baki yanci mai yawa ,yanzu zaki je kiyi Abunda ya kamata ace kina yi tun farkon zuwan ki dan uwarki da baki sani ba".tana kai karshen zancenta ta buɗe motar ta shiga ta mata key ta fita a gidan kamar zata tashi sama, dama tun da Khalid yaji maganar a ɗauko key ya wangale gate ,bayan tafiya mai yawa wadda ita kanta Nafisa baza tace ga adadin tafiyar ba amma tasan sun ɗan tafiyu dan tun tana kuka har ta daina ,wani guri suka nufa wanda yake kamar daji dan babu gida gurin sai manyan gine gine da ba'a gama ba, bakin wani ƙaton gate Hajiya saddiqa taje tayi horn,mai gadin na ganin itace yayi saurin buɗe mata gate, cikin maƙeƙen harabar gurin dake ɗauke da ƙasar birji ta shiga ta faka motar,tana ƙokarin buɗewa wani yazo da gudunsa ya buɗe mata yana na cewa hajjaju makkatun da kanta,fitowa tayi tana mai buɗe bayan motar tace "fito dan uban ki,"babu musu Nafisa ta fito tana aikin zazzare ido,kallan Mutumin Hajiya Saddiqa tayi tace "ina da abinyi yanzu Saleh amma ga ƙarin ƴar aiki nan,ina san a koya mata komai dake a akwai,ina san ta zama expert yarda zata zama mai Amfani "da mamaki Saleh yace"Hajiya ma'aikatan gidan nan hala kin manta duk maza ne,kuma baki ɗayan mu BQ muke"wani irin kallo ta basa tace"ina ce nice na aje ku kuma ni na mallaki gurin?to nasan mene nake ba sai ka tuna mun ba,aje a bata ɗaki a BQ ɗin sannan kusa a ranku kamar kaza aka kawo muku saman Abinci ku cinye ku gwagwiya yarda kuke so amma kada ku tauna ƙashi"dariya sosai Saleh yasa yace "sai hajjaju wanda yace baya yinki uban sa"kallan Nafisa dake aikin zare ido yayi yace"wuce muje ko,maza ɗauko kayan ki,wani irin kallon Nafisa ta bawa Hajiya Saddiqa kafin tayi Murmushi wanda ita kanta Hajiya Saddiqa ɗin bata San na mene ba amma tabbas murmushi Nafisa tayi mata,kaɗa kai tayi tana mai kallan Saleh tace"ina dawowa Saleh a cigaba da kula mun da komai ,ke kuma ki zauna anan ki gyara halayyar ki tukunna tunda naga alamun ke baki da mutunci,da haka ta shiga motar ta ta figa ta fita a gurin.

Tbc

Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top