15

🔏NOT ALL GLITTERS ARE GOLD💫

(BA DUK KYALLI BANE GWAL)✨

     Be with 👇

*𝐴𝑊𝐸-𝐼𝑁𝑆𝑃𝐼𝑅𝐼𝑁𝐺 𝐼𝑁𝐾🥌*

Tagwayen tafiya Mai sihirtattaciyar Ma'ana ta ban Mamaki daga jerin Tawwada d'aya Al-'kalami biyu first series.

*LOKACI.!*

Halish Sultan.

*BA DUK 'KYALLI BANE GWAL.!*

Chuchu jay

Chapter 15

    Kamar jela haka Nafisa tabi bayan Hajiya Saddiqa,ba tasan menene zata mata ba amma ganin yarda ta zageta tasan ba abun kirki yasa tace ta biyo ta ba ,maimakon zuciyarta ta tsaya nan kawai sai ta tafi tunanin ƙasar da taji ana maganar Salman zai je,indai kunnen ta ya ji mata dai dai Yankee taji ance ,duk ɗakiƙancin ta kuma baza ta manta ƙasar da Boda Akram ya je ba,ta riƙe sunan gurin kamar rayuwar ta,cike da rashin tsoro tace "Hajiya naji kamar ana maganar Yankee Ya Salman zai je"sakin Khalid Hajiya Saddiqa tayi ta juyo tana mai kallan ta,bata iya ce mata komai ba Illa juyawa da tayi tana neman abun duka,Usb na chargern Nanny Muna idanun ta suka sauka akai aikuwa ta Ciro ta fara zulawa Nafisa babu ƙakƙautawa,ihu Nafisa take tana neman afuwa amma Hajiya Saddiqa bata daina dukan ta ba sai da ta tabbatar ta sauke dukkan wani frustration dake ranta kan Nafisa da duka,bayan ta daina dukan ne ta kalleta tace"ki haɗiye mun wannan kuka ki fara faɗa mun Abunda na baki kin binne ne ko baki binne ba,wallahi idan naje aka faɗa mun baki binne ba sai na kashe ki".cikin Kuka Nafisa tace"Hajiya na binne ,bazan Maki ƙarya ba idan kuma baki yarda ba bari naje na tono miki,tashi tayi kamar gaske tace bari naje,tsawa hajiya Saddiqa ta buga mata tace"dawo nan dan uwar ki,na farko idan na sake jin kin kira Salman yaya sai na shaƙe ki, sannan kada ki sake kirana Hajiya Amah zaki faɗa dan ubanki ban ɗauko ki dan kina bina kina faɗa mun Hajiya ba, tashi ki wuce ɗakin ki babu fita har ƙwana uku,Nanny Muna zata kawo miki abinci"a zabure tace"kwana uku kuma"wani irin kallo Hajiya Saddiqa ta bata tace"kina da ja ne?"kaɗa kai Nafisa tayi ta juya dan nufa ɗakin nata zuciyarta kuma baki ɗaya tana ga Salman da taji ance zai je Yankee ba za taso kuma ya wuce ba ta tabbatar daga bakin sa ba,indai kullewa ne ai ayi a gama karshe tasan baza ta kashe ta ba.

Bangaren su Hajiya Hadiza kuwa Salman na shiga gidan ya fara haɗa kayan sa,cike da damuwa Hajiya Hadiza tace"Salman ina zaka je?"goge ƙwallar dake idanun sa yayi gudun kada ta gani kafin ya juyo yana kallan ta yace"Ummu gidan Nene zanje daga chan na wuce Airport da safe saboda muddin na zauna a gidan nan ina gani bazan tafi ɗin ba,sannan kin sani Ummu Allah yarda nake jin zuciya ta komai zai iya faruwa ,na gaji wallahi ,na gaji waccan matar zata iya sani Abunda zan zo nayi dama sani gwanda kawai na wuce i can't take it anymore,a cikin gidan nan ta samun ido fiye da kowa kamar na kashe mata wani,and Sadly tana kallo wallahi zan samu nasara a rayuwa and she's going to do nothing About it".Shiru Hajiya Hadiza tayi tana kallan sa domin kuwa har ga Allah bata so situation na gida ya kai wannan gejin ba, everything na gida is a big fat mess ,Kayan nasa ta cigaba da taya sa haɗawa tana mai cewa zan saka maka kuɗin da na faɗa maka zan sa ma anjima yanzu zaku wuce kai da Sultan gidan Nene ɗin and kada ka faɗa mata komai dan bana san hankalin ta ya tashi,yarda bata San Abunda ke faruwa ba a cigaba da tafiya a haka tunda ko ta sani babu abinda zata iya sai dai ma ta sake tada wa kanta hankali ga tsufa ga larura,bana san wani Abu da zai haɗa Nene da Saddiqa,da safe idan Allah ya kaimu Dani da ƙannen ka zamu zo Gidan Nene ɗin zan kaika Airport da kaina and nayi ma frnd ɗina magana already an sama maka apartment amma ba kai ɗaya bane akwai flat mate dan gurin  yayi tsada i can't afford it Amma insha Allah idan na samu isasshen kuɗi sai na kama maka separate,nayi magana da flat mate ɗin naka zai tare ka idan kaje airport,dan Allah Salman be good bana san wannan yawan zuciyar taka ,kasan abunda ya kaika sannan Kayi ƙoƙarin wajen achieving "

Rungume ta yayi yana mai Jin idanun sa yana kawo ruwa kafin yace"insha Allah Ummu bazan baki kunya ba,and insha Allahu my first plan idan nayi kuɗi zan ɗauke ki daga wannan gidan dan zaman ki da Baba bashi da wani amfani"shafa kansa tayi tace Allah yayi maka albarka.

  Tare suka fita shi da Sultan yana mai  taya sa ɗaukar Akwatin sa,Nafisa dake ɗakin ta tana faman leƙe ta window kuwa kamar ta yi tsuntsuwa ta fita gashi babu damar ta ƙwala masa kira,haka tana ji tana gani har suka bar harabar gidan ,komawa tayi ta zauna tana mai breathing in and out Kafun tace"Nafisa ki kwantar da hankalin ki komai zai zama dai dai".Kamar yarda Nafisa ke leƙen Salman haka Hajiya Saddiqa ke leƙensa ta balcony Zuciyar ta nayi mata wani irin zafi,Khalid dake gefen ta ne yace"Amah Wallahi ji nake dama Sultan da Salman su mutu bana san su".shafa masa gefen kunci tayi tace"kada ka damu Khalid ai da su mutu gwara su wulaƙanta tukunna ,wata rana sai su Salman sun dawo bayan ka suna Maula nice na faɗa maka"Murmushi yayi yace"Allah ya nuna min ranar nan Amah zan yaga su kuwa fiye da tunani kada ma Salman da ya ɗauki sarar miki rashin kunya".bin gate ɗin tayi da kallo tace "muje zuwa dai".

*******************************************

    "Haba Salmanu ,ai Ni ba sai ka faɗa mun akwai damuwa gidan Bukar ba jikina yana faɗa mun da akwai amma na saka hannuna akai ne na kasa ,na rasa me ne damuwar amma fa tabbas akwai kama daina mun ɓoye ɓoye,shi wannan gashi nan da rauni a hannu idan ba Rigima kuka yi ba ina ya samo?"ina ce Ni da kai munyi banƙwana?,shekaran jiya kana gidan nan yau ma sai kace bankwana kazo?akwai wata a ƙasa tabbas".kallan ta Salman yayi yace "shin tsohuwa ko na tashi na wuce ne?dan nazo sake ganin ki mene,idan kika bari fa na wuce kina mun irin haka wallahi bazan na kiran ki ba kuma wallahi ina tashi dawowa na taho da mata yar chan mai kyau , gashi har gadon baya ba irin naki ba kamar wayar nepa ba"dariya Sultan ya kece da yayin da Nene ta kaiwa Salman bugu tana mai kiran sa ja'ri,.da haka suka shashantar da maganar gidan su,.da dare suna zaune falon Nene suna cin abincin dare Alhaji Bukar yayi sallama,Nene da Sultan suka amsa banda Salman wanda yake jin wani irin haushin mahaifin sa,zama yayi yana mai gaida Nene yayin da Sultan da Salman suka tashi dan basu guri,da Mamakin Nene tace"kai dan ƙundun uban ku baku ga uban ku ba kuka tashi zaku fita?"ba tare da Salman ya juyo ba yace"Kaji Nene mun Gaisa a gida ai"bai kuma faɗin komai ba ya bar ɗakin Sultan ya mara masa baya,da mamakin Nene tace"tabbas Bukar akwai abinda ke faruwa gidan ka,shin mene shi?Ni nasan yaran Hadiza nada tarbiyya da haƙuri to mene ya kawo wannan ɗacin?hala wannan makirar matar taka ce Saddiqa ,Ni dama Wallahi nasan wannan yarinyar sheɗaniya ce,a kallo ɗaya idan nayi wa Hadiza ni nasan cewa tana cikin damuwa,amma idan babu wanda zai faɗa mun Akwai Allah kuma ku sani kai da mummunar matar ka wallahi hakki bazai bar ku ba".ɗan shiru yayi kafin yace"Nene babu fa wani abu dake faruwa,shima Nan Salman ɗin fushi ne kawai yake dan da nace ya ɗan jira tafiyar sa amma daga baya kuma nace ya tafi to sai da naje Ummun sa ke faɗa mun yazo sallama gurin ki".kallan sa kawai tayi amma a zuciyar ta tasan karya ne,kallan ƙwanan abincin da suke ci yayi yace" Nene alƙubus kika yi kenan a ɗan zuba mun na ɗanci kafin naje na samu Salman ɗin dan wallahi nayi kewar abincin ki".taɓe baki tayi tace"uhum ai da kayi kewar abincin nawa baza ka ɗauke kafar ka daga gida na ba,yau wata uku kenan ban saka ka ido ba sai anyi magana kace aiki,wallahi zan baka abincin nan amma ka sani sadaqa ne "Murmushi kawai yayi yayin da ita kuma ta tashi dan zuba masa abincin.

    Ɗakin da suka saba zama Salman da Sultan suka wuce ,bayan sun zauna ne Sultan yace"Ya Salman Ni wallahi gidan mu ya ishe Ni kamar na gudu,dan Ni wallahi kana tafiya ma gidan Nene zan dawo,kallan sa Salman yayi yana mai aje wayar da yake kallo yace"Babu inda zaka Sultan,nima da na tafi insha Allahu tafiya na zai zamar mana Alheri,ka mayar da hankali kan karatun ka sannan ka kula da Ummu dasu Saimah,a yarda bana nan they need you and bance maka kaje Kayi ta faɗa da su Khalid ba ko kaje kana ma Aunty rashin kunya ba,bana san naji kayi involving kan ka cikin lamarin su,kayi ƙokari wajen ganin ka na danne zuciyar ka kan su ,nasan fushin ka Sultan ,duk da ina da fushi nasan yarda zan sarrafa sa amma kai naka ban ma san mene zan kira sa ba,Baba kuma duk abinda zaiyyi bana san naji wani Abu mara daɗi tsakanin ka dashi ,keep your calm and komai zai zo da sauki,time zai zo da zamu ɗauke Ummu daga wannan gidan and trust me insha Allahu lokacin ba zai daɗe ba dan idan naje makaranta zan ware lokacin neman kuɗi ,idan da addu'ar Ummu da naku nasan da yarda Allah i will make it,and yes Kafun na manta ,wannan yarinyar dake sashen Aunty munyi magana da ita zaka na koya mata English kana haɗa mata da ɗan lesson ma da karatun Kur'ani cos nasan ƙanin nawa hafizi ne".da sauri Sultan ya ɗago ido yana mai cewa"Ya Salman ina mata lesson da koyan English da Qur'an kuma? Gaskiya i will reject you this once Dan bazan iya haɗa guri da duk wani da ya fito daga sashen Aunty ba ,zan iya abinda babu mai so".Ƴar dariya Salman yayi ganin yarda ya haɗe girar sama da ta ƙasa yace"bro take a chill pill,dey calm down dude,ita wannan she's different and idan kaji labarin ta abun tausayi ce,Aunty taje tayi adopting ɗin ta gidan marayu and kaima kasan cewa akwai wata a ƙasa cos Aunty baza ta taɓa abun alheri ba,maybe ta kawo ta ɗan ta maida yar aikin ta ne,but I'm sure idan ka san Nafisa zaka so ta cos tana da shiga rai,ka taimaka mata dan da ace ba tafiya zanyi Bama i won't bother you,help the poor girl please ". Nazarin Maganar Sultan ya ɗan yi Kafun yace"shikenan Ya Salman insha Allahu zan taimaka mata.shirun su ke da Wuya Alhaji Bukar yayi sallama ɗakin ,bai jira amsawar su ba ya shigo,binsa dukkannin su sukayi da kallo Yayin da shima yake kallon nasu kafin yace "zan iya zama?"

    "Zaka iya mana Baba"Salman ya basa amsa a taƙaice yana mai kallan sa,zama yayi kafin shima ya bisu da ido yarda suke binsa ,ganin suna wasan ƴar kallan kallo ne yasa shi katsewa ta hanyar faɗin"Salman ban zo dan hana ka tafiya waje ba ,ina san ka sani duk wani abu dake faruwa is just within my power I can't help it Amma Allah ya sani ina san ku babu yarda zanyi ne da Saddiqa she's so demanding and Annoying Allah ka yafe mu " a tare Salman da Sultan suka jiyo suna kallan juna kafin lokaci guda kuma suka koma kallan Mahaifin nasu wanda ya ma rasa mene zai sake faɗi kuma,gyaran murya yayi yace"kuyi haƙuri da komai dake faruwa nayi imani da Allah komai zai daidai ta,wata rana ne itama Ummun ku bata jin magana,maimakon ta tayani muyiwa Saddiqa biyayya sai tana bijirewa kuma a fili ,wannan matar fa tana bina abubuwa da dama ,tayi playing babban role ga cigaba na kunji dai ai ɗaya daga cikin su ta faɗa gaban ku,bana san kuna bijire mata kar ma kai Salman,amma yanzu ba wannan ba ,zuwan ka gidan Nene kayi dabara ,na saka maka 700k a account ɗin ka kayi amfani da su Kafun na sake waiwwayen ka ,babu kuɗi ne.Allah yayi muku albarka ya kuma sauke ka lafiya,shin kai yanzu zaka wuce mu tafi tare ne ko sai anjima?"ya mayar da maganar sa ga Sultan.kaɗa kai Sultan yayi yace"A'a Baba kaje dai ni sai gobe kaga kada ma Aunty ta gammu tare ran mu ya bacci"tashi yayi yana mai kaɗe babbar rigar sa yace"kuma haka ne kayi magana mai kyau,dan wallahi tana ganin mu tare kowa ya shiga uku,ni bari na wuce".Kallan juna suka yi a tare kafin Sultan yace"Brother this is serious,like damn serious Baba fa yana buƙatar taimako".ƴar dariya Salman yayi kafin yace"Allah ya taimaka masa "dan shi abu guda yasa a ransa da ace Baban su ba je ya yayiɓo Hajiya saddiqa ba da sunan taimako da yanzu family ɗin su abun burgewa ne,idan ma kuma asiri na tayi masa ai shi yaja shi ya riga da ya haɗe zuciyar sa guri ɗaya.

Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top