14
🔏NOT ALL GLITTERS ARE GOLD💫
(BA DUK KYALLI BANE GWAL)✨
Be with 👇
*𝐴𝑊𝐸-𝐼𝑁𝑆𝑃𝐼𝑅𝐼𝑁𝐺 𝐼𝑁𝐾🥌*
Tagwayen tafiya Mai sihirtattaciyar Ma'ana ta ban Mamaki daga jerin Tawwada d'aya Al-'kalami biyu first series.
*LOKACI.!*
Halish Sultan.
*BA DUK 'KYALLI BANE GWAL.!*
Chuchu jay
https://whatsapp.com/channel/0029VaRpQeUHwXb52H0abb05
Ga masu nema daga farko👆
Chapter 14
2 weeks later
A hankali cikin yardar Allah Nafisa ta cinye sati Biyu Gidan Alhaji Bukar ,kamar yarda Hajiya Saddiqa ta gargaɗeta tayi ƙokari wajen ganin bata fita ba ballantana wani abu ya haɗa ta da mutanen gidan wanda tasan da wahala ta fita ɗin wani abu bai haɗa su ba dan ita baza ta boye ba har ga Allah Salman yayi mata kyau kuma tasan indai yana da kyau to yan uwan sa ma na da kyau gashi ita kuma Allah yasa masu kyau na burge ta,jin alamun sashen Hajiya Saddiqa shiru yasa ta sake tabbatarwa baki ɗayan su sun fita, Murmushi tayi ta tashi dan fita waje, ta gaji da zaman ɗakin nan na kullum dan masifa, tana ƙokarin fita daga main door Muryar Nanny Muna ya tare ta inda take cewa"sai ina kuma kinibabba?juyowa tayi tana mai kallan ta sannan ta juya tana mai kallan bayan ta ko ba da ita Nanny Muna take ba,ganin babu kowa yasa ta nuna kanta da yatsa tace"Ni?.
"A'a Ni dan uwar ki,Shegiya kin zo duk zaki kanainayewa mutane guri,to bari kiji na faɗa miki lokacinki ƙidiyayye ne a cikin gidan nan sannan baki isa ki maye gurbin da kike tunanin an baki ba"da mamaki Nafisa tace"kema kenan?,to kinsan mene za'ayi a gidan nan?kija girman ki naja nawa dan na tabbata kowa da matsayin sa a yarda aka aje mu,Ni sunan ƴar gida ake san mayar Dani ko nace an mayar Dani ma,Yayar Khaffy ƙanwar Khalid,ke kuwa a ƙiyasin da nayi matsayin mai dafa abinci ce,dan Allah kada ki bari na ƙi ganin girman ki ,Ni wallahi nayi zaton ke ɗin gwana ce ta daban ashe kalar duk ja ce"tana kai aya ta fita ta bar Nanny Muna tana mai san blending cewa wai da ita Nafisa take,ƙwafa tayi a fili tace"da kin san inda Allah ya jefo ki baza ma ki samu bakin buɗewa kimun rashin kunya ba sai dai ki fara tunanin hanyar ceton kan ki,amma muje zuwa zamu ga wanda zai dara daga ƙarshe.
Koda Nafisa ta fito bin gidan ta fara da kallo,taɓe baki tayi tace"mu a faɗa mana girman gida"takawa ta fara tana mai bin ko ina da ido, idanun ta ne suka sauka akan wani lilo mai biyu wanda ke ƙalla madaidaicin filin wasan gida,da gudun ta ta nufi lilon ta hau ta fara shillawa ,dariya tasa tunawa da Safiyya da tayi a fili sai cewa tayi"ko ya ta ƙare da ɓalallan haƙori?ko ya Boda Akram ɗina yake?Allah sarki Big Mummy na da mummy Nadiya,take kuma sai ta fara kuka,sosai take kukan mai sauti kamar wadda aka yiwa shegen duka,Salman da shigowar sa gidan kenan ya jiyo sautin kukan ta,da mamakin ya zaga gurin dan tabbatar wa da ita ce ɗin dan tun Abunda ya faru bai sake ganin ta ba cikin satukan ,jin alamun mutum yasa tayi saurin juyawa tana mai share hawayen dake kuncin ta kafin tace"lafiya?".ƴar dariya yayi yace "lafiya?,ke zanwa wannan tambayar da kika zauna mana a compound ɗin gida kina aikin kuka",Sniffing tayi tace"muma dai muna da gidan nan kuma wallahi ya tattaka wannan,ka tambayi Auntyn ka da taje ta ɗauko ni idan baka yarda ba,a gidan mu kowa tsoro na ake Sannan muna da yawan gaske",
"Kuma duka baban ku ɗaya?"ya tambaye ta yana mai samun guri ya zauna a ɗaya swing ɗin,Dariya tasa tana mai kallan sa tace"ina fa babu wanda yasan ina ma nasa iyayen suke,yawancin mu ko an tsince mu ko an kawo mu,galibi ma dai yan tsintuwa ne,kaga kamar ni dan wulaƙanci nesa da gate aka aje ni ga ruwa ana yi, ga dare,shi yasa duk wanda yayi ƙoƙarin dawo mun da ainayi na muke chakuwa babu abinda ya dameni ai ba kaina aka faraba ba kaina kuma za'a gama ba,abu ɗaya na sani wata rana duk da bana fatan ranar tazo kawai misali ace wai wata mace tace itace mama na zan goga mata,dan ni bana da uwa da ta wuce Big Mummy na itace uwa ta ita ce ubana Kuma sai gashi yanzu ta rasu a wuta,ai shine yasa kaji ina kuka, kawai ranar suka ƙone cikin gobara shine Auntyn ka taje ta ɗauko ni tana san na zama ƴar uwar Khafilat da Khalid sannan tace mun babu ruwa na da duk wani ɗan sashen ku saboda ku Mayu ne,Ni bana munafurci ne shi yasa na faɗa maka kada wata rana kaji kace nayi munafurci,to ni Kuma Ina da wani lurura idan abu ya shafi ƙyawawa wallahi sai dai ku cinye ni,amma Kafun nan dan Allah ku bari na fara ganin mijin da zai Aure Ni,Boda na abun ƙauna ta yana chan ƙasar waje yana karatu,in da Hali ma ku bari sai na Aure sa dan Allah,Kaji?"idanun ta ta ɗora kan Salman wanda tunda ta fara magana babu tsayawa yake kallon ta inda a yarda ya fahimta gidan marayu Hajiya Saddiqa ta ɗauko ta sannan take faɗa mata su Mayu ne, definitely yasan akwai dalilin da yasa ta ɗauko ta dan babu ma yarda za'ayi wai ace Hajiya Saddiqa ta ɗauko ta ne dan kawai ta taimake ta,tho yaji Ummu na maganar cewa zatayi adopting gidan marayu amma baiyyi zaton cewa har tayi ɗin ba,"Yaya sunan ki?"
"Nafisa"ta bashi amsa tana Murmushi kafin ta ƙara da cewa,"bafa kowa nake kulawa ba kawai dai kamun ƙyau ne"dariya yayi kafin yace , sunana Salman,ina da ƙani wanda ya bawa Khalid shekara ɗaya ,sai ƙanwa Saima sa'ar Khafilat ce then Samrat Autar mu ita she's just five".ajiyar zuciya tayi kafin tace"kaga tunda na baka labari na bari na faɗa maka wani sirri na amanatul Amana,kaga sau uku ana mun repeating js 1 har yanzu a chan nake da shekara sha uku,sannan ban bari kowa ya sani ba ,bana jin turanci ko su wancan Khalid ɗin ban faɗawa ba kada su raina ni ,amma kai na faɗa maka ne saboda na yarda da kai sirri ne,amma dan Allah zaka na koya mun turanci dan na iya ko zan sani idan su Khafilat na zagina da turanci".ɗan Murmushi yayi yace"shi kaɗai kike so ki iya?ita sabuwar mum ɗin ki baza ta saki makaranta ba".
Lila kanta ta cigaba tana mai cewa"ina fa zata sani tasan na maimaita aji sau uku,har jaka ta kira ni ko a jiki na dan naji wanda ya fi nata , ni bokon ma kaga bata gaba na dan da zan iya da nayi ƙoƙari wajen cikawa Mummy burin ta duk da bata Duniya,amma wallahi bazan iya ba duk yarda na daure,ni ɗan turancin kawai nake so,dan Allah zaka koya mun?"kaɗa kai yayi yace"well Kinga inda akayi rashin sa'a gobe da safe jirgina zai tashi zan wuce kasar waje karatu amma zan wa Sultan magana zai na koya miki har da lesson ma".hannunta tasa kan kuncin ta tana kallan sa tace"dan Allah ya kaika kyau?"dariya yayi yace"har ya fini ma ke dai ki bari zaku haɗu sannan ina san ki sani mu ba Mayu bane ,Ummun mu kuma tana da kirki sosai nasan kuma idan ta ganki zata soki ,sabuwar maman ki kuma da duk ta tsara miki wannan ina ga da ita ya kamata kibi a hankali kiyi ta addu'a and nasan baki iya munafurci ba amma kada kije ki faɗa mata abunda na faɗa miki fa dan tsaf zata yanka ki ba ruwana wlh".Dariya tasa sosai har da ƙyaƙyatawa kafin tace"wlh ka bani dariya,nifa da kaganni nan wayau gare ni har da na siyarwa,dan Allah Ni dai idan kaje ƙasar wajen nan ka faɗawa boda Akram ina gidan ku ina jiran sa nasan zaka gan shi,wani mai kyau haka ga kirki"
"To ke kam idan banda abun ki ina zan gan shi yarda ƙasar waje keda girma,ta iya iyuwa ma ba ƙasa ɗaya zamu zauna ba,idan ma ƙasa ɗaya ne ni ina nasan shi tunda ban taɓa ganin sa ba ke Kuma baƙya da hoton sa"kaɗa kai tayi tace"kuma haka ne amma dai yana da mutuƙar kyau sosai dan wallahi duk kyan ka ya fika"...tashi yayi yana dariya yace "naji Nafisa,dama ai ke kika ce ina da kyau bani na faɗa ba,Ni bari naje ɗauko su Ummu a makaranta lokacin tashi ya kusa mene zan siyo miki?"cike da Murnar ta har da dirowa kan lilon tace"dan Allah da gaske kake ko mene nake so?.
Kaɗa mata kai yayi,cike da zumuɗi tace wallahi dafaffen gyaɗa nake so da kuma aya mai gishiri ko mai sigar".haɗe girar sa yayi yace"kawai?"da saurinta ta gyaɗa kai tana mai cewa"kawai,Nagode kafin ka siyo mun sai ka dawo,ina jin motar ku zan fito kazo ka ɓoye mun a nan zan zo na ɗauka amma kada ka aje yarda za'a sace".yana tafiya ya ɗaga mata hannu yace"Allah yasa na samu.
Da dare Hajiya Saddiqa ta tsinci tafiyar Salman ohio Yankee ,cike da tashin hankali tasa Alhaji Bukar kiran meeting na gaggawa a cikin gidan bayan ta gama sille masa akan ya munafurce ta kuma bai isa ba,duk yarda yaran Hajiya Hadiza suka bijirewa zuwa zaman bai iyu ba saboda dole da mahaifiyar su ta musu musamman da ya kasance kiran daga Alhaji Bukar ne,abu na ƙarshe kuma da take buƙata shine yau ace wani ɗan ta ya bijirewa mahaifin sa duk da kuwa tasan idan aka cigaba da tafiya a haka wata rana hakan zai faru ,tare dukkan su suka halarci kiran ,abinda Hajiya Saddiqa ke so kenan dan tana jin daɗi taga ta cima Hajiya Hadiza mutunci gaban Yaran ta da nata yaran ita ma dan bata fatan yaran ta su ki Hajiya Hadiza ko kaɗan a wannan kira kuwa har da Nafisa dan tana so Itama ta saba ta koya domin kuwa duk ranar da ta kamata tana ragawa Hajiya Hadiza sai taci mata mutunci sosai,ita dai Nafisa tunda ta shigo ɗakin babu abinda take sai bin Hajiya Hadiza da yaran ta da take da ido dan sun mata kyau ba kamar su Khafilat ba mara sa kyau ga rashin kyan Hali.
Nuna Alhaji Bukar Hajiya Saddiqa tayi tace"ne ba tun yau nasan cewa Wallahi ka raina ni ba Alhaji,yo idan ba raini ba wace bura ubar zata saka ka ɗauki kuɗinka ka biya wa Salman tafiya America ba da sunan yayi karatu,to wallahi ba zai je ba,dama mana dole ka ɓoye mun munafiki,to wallahi bazai tafi ba,idan ka manta sai na tuna maka ,da kamfanin ka zai tsiyace haka na ɗauki Madarar kuɗi har miliyan dubu ɗari biyar na baka ka ƙara hannun jari ciki dan haka nice silar duk wani abu da kake dashi duk da kuwa ka biya rabi,ba zan taɓa gani wallahi ka zuba su jikin yaran Hadiza ba Salman ba zai je Yankee ba period idan kuma uwar sa ta haɗa kuɗi daga koyarwar da take sai ta biya masa"..dariya Salman yasa lokacin da ta gama maganar sannan ya ɗauko wayar sa yana mai shiga hotuna ya kawo wayar saitin fuskar Hajiya Saddiqa yana mai nuna mata passport ɗin sa yace"wallahi Aunty sai dai Allah,and ke da kike maganar kin bawa Baba miliyan ɗari biyar waye ya baki?me kike kika samu wannan kuɗin? Alhamdulillah Ummu teaching take Kuma mun san duk ƙankantar Abunda take samu halal ne ke fa?Allah kaɗai yasan inda kike samun kuɗi , although kuɗin da kika bawa Baba tsakanin ki ne dashi ba ruwa na amma tafiya ta kuwa wallahi ba dai mutum ba ko malamin ki yayi ƙarya wallahi Aunty"ƙansa tayo tana mai cewa"wallahi sai naci Uwar ka Ni kake faɗawa magana haka?to ko uban ka albarka "saurin matsawa yayi wanda hakan yasa ta tuntsirawa,ɗan tsuke baki yayi yace"watch out Aunt kada ki ji rauni"dariya ƙannen sa suka saka wanda hakan ya sake tunzira Hajiya Saddiqa da yaran ta kar ma ace Khalid dake zaune yana tafarfasa.
Tasowa tayi tana mai kallan Hajiya Hadiza wadda tayi kamar bata gurin,mayar da kallan ta tayi kan Alhaji Bukar wanda nan take ya tashi ya ɗauke Salman da mari yana mai cewa"Babu inda zaka je mara ɗa'a wanda uwar sa ta gagara basa tarbiyya"dafe kuncin sa yayi yana mai kallan mahaifin nasa cikin ido yace"Baba watch me"daga haka ya fita a falon, ganin haka yasa Hajiya Saddiqa ta koma ga Alhaji Bukar tace"kaji ba,watch him,Hadiza yaran ki ke faɗawa uban sa "watch me"to wallahi cikin duniyar nan ko Ni Ko Salman ,duk wanda ya fasa yaci Uban baban sa,idan kika ga Salman ya salwanta kada kiyi tunani na biyu dan nice "
Murmushi Hajiya Hadiza tayi tana mai tashi daga zaune da take tace"Bismillah Saddiqa gaki ga Salman,Ni ai Allahn da nake Bautawa yafi wanda kika yarda dashi dan bana tunanin Allah ɗaya ne zuciyoyin mu,Alhaji dai gaki gashi ku ƙarata amma yarana Wallahi Kinyi ƙarya Allah yana biye dasu a duk inda suke ,Ni bana bacci kullum ina gaban Ubangiji kinga kuwa Ni da ke sai dai Ido Salman kuma insha Allahu gobe kamar ya wuce".da haka ta fice inda su Sultan na ganin haka suka mara mata baya,ganin sun fita duka yasa Khalid dake faman tiriri ya tashi ya bi bayan su,yana fita kuwa sai cewa yayi"Hajiya Hadiza,Abunda kike wa Amah ya isa haka dan wallahi tura ta fara kaiwa bango tun da naga cewa gidan nan yanzu kowa ya raina kowa"da mamaki Sultan yace"da wa kake?"
"Da uwar ka nake"ya basa amsa a fusace.ƙokarin kame kai Sultan yayi ganin Ummu na kallon sa, hannayen sa ya dunƙulle yana mai Jin wani irin zafi a zuciyar sa,Murmushi Ummu tayi tace"Sultan ka bashi Amsa"tana faɗin haka ta juya ta bar gurin aikuwa kamar Mene Sultan ya fara kai masa naushi,sosai suka fara faɗa tsakanin su wanda Khalid ke dakuwa domin kuwa ƙarfin su ba ɗaya bane,ihun sa ya fito da Hajiya Saddiqa wadda tana ganin Sultan na jibgar Khalid ta yi kansu tana zagin Sultan tana kokarin ƙwace Khalid wanda da ƙar ta kwacesa ɗin,ba tare da Sultan ya jira faɗa ko dukan da zai sha gurin Baban su ba ya bar gurin At least ya fasa bakin Khalid, juyawa Hajiya Saddiqa tayi tana mai Kallan Alhaji Bukar kafin tace"Allah wadaran mutuwar zuciyar ka Alhaji,wallahi nayi sanyi"duban Nafisa tayi tace"ke kuma dan kutumar ubanki muje ciki kina da bayanan da zaki mun.
Tbc
Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top