13

🔏NOT ALL GLITTERS ARE GOLD💫

(BA DUK KYALLI BANE GWAL)✨

     Be with 👇

*𝐴𝑊𝐸-𝐼𝑁𝑆𝑃𝐼𝑅𝐼𝑁𝐺 𝐼𝑁𝐾🥌*

Tagwayen tafiya Mai sihirtattaciyar Ma'ana ta ban Mamaki daga jerin Tawwada d'aya Al-'kalami biyu first series.

*LOKACI.!*

Halish Sultan.

*BA DUK 'KYALLI BANE GWAL.!*

Chuchu jay

https://whatsapp.com/channel/0029VaRpQeUHwXb52H0abb05

Ga masu nema daga farko👆

Chapter 13

    Baya ga abinci da ake kawowa Nafisa dan mitsil babu ƙarin wani abu ga kulle ta da akayi a ɗaki kamar yar prison,kwana uku kenan  abu guda ne sannan bata saka Hajiya Saddiqa a idanun ta ba sai wannan mata dake kawo mata abinci wadda tana kawowa zata juya ba tare da tace wani abu ba,a rana ta ukun tana kwance tana bacci da sassafe taji ana murɗa key ɗin ɗakin kamar a mafarki,buɗe idanun ta tayi tunanin ta yau wannan zaman kulle ɗin ya ƙare,saukar ruwan sanyin da taji jikin ta shine ya tada ta zaune da sauri tana mai faɗin"innalillahi waina ilaihir rajiun"dariya Khafilat dake ɗauke da karamin bowl tayi tace"ashe kina magana,stupid silly girl kin Wani zo gidan mu ke wai kin samu family,to bari kiji kin kawo kan ki mutu dan kuma muddin ina gidan nan wallahi baza ki samu zaman lafiya ba ,You won't snatch my mom from me,Amah nace daga Ni sai ya Khalid babu ƙari dan haka ki koma chan Hoodlum da kika fito cos nan ne yafi dace wa dake",juyawa tayi zata fita Nafisa tayi saurin kamo hannunta ,kafin ta juyo ta farga ta jawo ta ƙasa sannan ta sa hannunta guda ɗaya ta rufe mata baki ɗayan kuma ta Murɗe mata Hannu ,a hankali tace"Sunana Nafisa and gidan ku nazo na zauna ne kamar yarda Amah ɗin mu tafa faɗa zan zama yayar ki zama yayar ki kuma yana tafe ne da abubuwa da dama,idan kika sake kwatan ta mun abu makamancin wannan sai naci kutumar ubanki wallahi,idan kika je gidan Alheri kika tambaya wace Nafisa tun daga gate har garun ƙarshen dunga zakiji sunana yana tashi, wallahi idan ba kiyi wasa ba sai na shaƙeki dan uwarki,Shegiya mumuna"hankaɗa ta tayi,tashi Khafilat tayi tana mai nuna ta da ɗan yatsa tace"Amah must hear this"da haka ta juya ta fita tana matsar ƙwalla,duk da Cewa Nafisa bata San Abunda ta faɗa ba amma tasan ƙarar ta zata kai dan haka ta fara lalube a ɗakin,chan idanunta ya sauka kan wani clip ɗin karfe ɗaukowa tayi ta saka a kumatun ta da ƙarfi ta matsa,take idanun ta ya kawo ruwa ,aje clip ɗin tayi ta fara matsar ƙwalla tana jiran zuwan Hajiya Saddiqa da shegiyar yarinyar ta,koda Khafilat ta fita kai tsaye ɗakin Amah ɗinta ta nufa tana kuka kamar ranta zai fita,da sauri Hajiya Saddiqa da fitowar ta kenan a bayi ta iso gare ta tana mai cewa"baby na what happened  da safen nan kika tashi da kuka,mene ya faru talk to me"cikin kuka Khafilat tace"Amah ba kece kika je kika ɗauko waccan mayyar ba ,baki ji Abunda take faɗa mu ba har da murɗe mu hannu kamar zata karya Ni Allah sai ta bar gidan nan yau,har da zagina tayi fa".da mamaki Hajiya Saddiqa tace"Nafisa ɗin?".cikin kuka Khafilat tace"ita mana"kamo hannun ta Hajiya Saddiqa tayi tace muje,suna isa kukan Nafisa Shine abunda ya fara dukan kunnuwan Hajiya Saddiqa wanda take yin sa kaɗan kaɗan ,da sauri ta kalli Khafilat wadda ta fara girgiza kai ,suna shiga ɗakin Nafisa tayi saurin ɗagowa tana mai goge hawayen ta tace"kiyi haƙuri Khafilat dan Allah,Hajiya kice tayi hakuri idan na bar gidan nan ban san inda zanje ba ,wallahi zan ɗauka ko kullum zatayi ta matsa mun clip ne a fuska amma kada tace na bar gidan nan,bani da wani gun da yafi nan kuma insha Allahu bazan baku wani dalilin da zakuyi dana sani na aje Ni ba.

Kallan Khafilat da ta zaro ido Hajiya Saddiqa tayi tace"so Khaffy tell me something ,ni nasan kina san ta bar gidan nan amma ba shine zai saka ki je ki zuga mun karya ba,yaushe kika koyi ƙarya?cike da in ina tace"wal-lllahi Amah itace ke ƙarya ,har cewa tayi mun mumuna kuma sai ta shaƙeni"kuka sosai Nafisa ta fashe dashi tace"Ni ɗin,na shiga uku Ni Nafisa". kallan Khafilat Amah tayi tace"this should not repeat it self Khaffy,Maza ki wuce kije ki shirya school.tana faɗin haka ta juya ta fita,kallan Khafilat Nafisa tayi ta mata Gwalo wanda ya saka Khafilat bin Amah ɗin ta da shagwaɓa tana cewa"Allah Amah I'm not lying" don't get late kije ki shirya wa school"shine abinda Hajiya Saddiqa ta faɗa tana mai komawa ɗakin ta ,suna fita Nafisa ta share hawayen ta tana mai cewa ,zaku ci uban ku duka babu wanda zai takani gidan nan wallahi na ƙyale sa ko Hajiyar ce sai nasan inda nabi na rama,ganin an bar mata ƙofar a buɗe ya saka ta fito tana mai kallan falon a hankali,tana nan tsaye Khalid ya fito,wani sheƙeƙen kallo ya bata kafin yace "ke kuma daga ina?"Murmushi tayi tace "ya Khalid ba zaka ce ka manta da wuri haka ba,wannan yarinyar ce mai wari ,ƙanwar ka"tsaki yayi ya nufi kitchen yana mai faɗin"Nanny Muna where is my breakfast"taɓe baki Nafisa tayi tace"ai tunda mamanku ta ɗauko ni kun shiga uku gidan nan ,babu mai yaga ni ban cinye sa ba,amma yanzu bari na fara karantar ku baki ɗayan ku,tana yan kalle kallen ta Hajiya Saddiqa ta fito,da mamaki tace"a'a Nafisa wa ya buɗe ki?" Binta Nafisa tayi da kallo a ranta tana mai faɗin lallai ma matar nan kafin a zahiri tace"ɗazu Hajiya ai baki kulle ƙofar ba shi yasa nayi tunanin an gama mun kullen ne".bin ta Hajiya Saddiqa tayi na wani lokaci jin Abunda tace kafun ta yi ɗan Murmushi tace "ba kulle na miki ba Feenah,i thought kina buƙatar space ne ki gama kewar gida ". "Na gama"Nafisa ta faɗa da saurin ta domin abu na ƙarshe da take so shine a sake kulle ta ,zama Hajiya Saddiqa tayi kan kujera kafin tace "zo nan muyi Magana".Babu musu Nafisa ta je daga gefen kujerar da take zaune ta zauna ƙasa,Murmushi Hajiya Saddiqa tayi dan tana ganin biyar da Nafisa ba zai mata wahala ba,cike da makirci tace "Hope baki ɗauki kulle ki da nayi a zuciya ba",da ƙaramin Murmushi Nafisa tace"ko kaɗan Hajiya,kamar yarda kika ce nayi kewar gida na gama sannan na amince da cewa nan gidan shine sabuwar rayuwa ta kuma na ɗauke ta hannu biyu biyu,in Allah ya yarda bazan taɓa baki kunya ba.

"Good yanzu abun farko dake damu na da na ke samun labarin cewa ke daƙikiya ce babu komai a kan ki,to dama Bana planning saka ki makaranta dan labarin jakantar ki na maimaita aji guda Sau uku yazo kunne na ,so akwai space dana tanada domin ke,ina running wani Babban Kasuwanci wanda ake haɗe takalma da jaka da kuma kaya na kanti, duk wani kaya da zaki gani masu ɗauke da tag na LGs to nawa ne and komai nawa designer ne ,ko da yake nasan baki san designers ba amma zaki sani,a babban secret warehouse ɗina da komai ke wakana ina san aje ki dan ina san ki koyi skills na sarrafa komai,ina fatan jakin kanki kuma ya ɗauka,shine gatan farko da zan miki,ina san ki zama mai riƙe sirri na dan zaki san da yawa,abu da ya danganci gidan nan kuma,kinga mai sashen dake gefen nawa,kada ki kuskura ki je inda take dan mayya ce idan kuma ta cinye ki ni ban san me zan miki ba,dan Mayu ne daga ita har yaran ta,ke idan naga kina wata alaƙa ma dasu wallahi zaki sha mamaki domin kuwa idan ma baki tsane su ba Ni zan koya miki,babu ke babu su,tunanin ki da komai naki kan Khafilat da Khalid zai tsaya,ina fatan kin fahimta"?..... kallan Hajiya Saddiqa Nafisa tayi lokacin da takai karshen maganar ta tana mai watsa mata tambayar ko ta fahimta,ya za'ayi ta kasa fahimtar cin mutunci?duk da karancin shekarun ta tana san fahimtar dalilin alherin da Hajiya Saddiqa ke san mata ,amma duk yarda tayi ta nemo ta kasa,a zahiri sai cewa tayi"Nagode sosai Amah,ke ɗin mutum ce ta gari kuma ni ko sani kika yi na zagi mutum ai na zagai har uwa tai,Nagode sosai Allah ya saka miki da Alheri,insha Allahu kuma bana da ƴan uwa baya ga Khafilat da Ya Khalid,idan wuta kika izza mun kika ce na shiga zan shiga ba tare da nayi wani tunani ba,Dariya Hajiya Saddiqa tayi tace"naji daɗi sosai,duk da cewa kina da ɗakikiyar ƙwaƙwalwa amma kina da wayau,yanzu dai ki tashi muje na miki shopping,Babu musu Nafisa ta shiga ɗaki ta ɗauko hijab ɗin ta dan bin Hajiya Saddiqa shopping,koda suka isa shopping mall ba ƙaramin siyayyah Hajiya Saddiqa tayi mata ba,bayan dawowar su gida chan wuraren yamma dan ta je da ita Warehouse ɗin ta wanda yake dukkan maza ne ma'aikatan,suna shigowa idanun Khafilat suka sauka kan jakar shopping ɗin Nafisa ,ai tana gani tayi gurin ta ta fizge tana mai cewa"Allah Amah nawa ne cos bazan tuna last da kika Kaini Shopping ba, Murmushi Hajiya Saddiqa tayi tana mai satar kallan reaction ɗin Nafisa wadda ta kasa karantar Abunda ke fuskanta ,cike da munafurci ta kwace jakan daga hannun Khafilat tace"bana san Rigima Khaffy kayan yayar ki ne ,ke ina ce kaya kamar zasu kashe ki"miƙawa Nafisa jakar tayi tana jiran taga mene zatayi,cike da hikima kamar Nafisa tasan abinda ke ran Hajiya Saddiqa ta kalli Shopping bag ɗin sannan ta taka gurin Khafilat ta kama hannunta ta saka mata tana mai cewa"abuna ai naki ne Khaffy,ki ɗauka babu komai "jin haka yasa Khafilat ɗaga jakar ta zazzage kayan duka a ƙasa kafin ta saka ƙafa ta taka sannan ta kalli Nafisa tace"babu abinda zanyi da low class kayan ki, after All ba daga kayan Amah bane , designers na LGs sai dai kiga ina sawa"yawu ta tofa a kayan ta juya wanda hakan yayin mutuƙar yiwa Hajiya Saddiqa daɗi amma a fili sai cewa tayi"Khaffy zo nan,wane irin rashin ɗa'a ne haka ,zo nan "ko juyowa Khafilat ba tayi ba yayin da Hajiya Saddiqa ta bita tana mai cigaba da kiran sunan ta,tana shiga ɗakin ta Abunda tayi ita kanta Khafilat sai da ya bata mamaki, domin kuwa rungume ta tayi tana mai shafa mata kai tace"kinyi abu mai kyau Khaffy na,so nake a duk wani chance da zaki samu kiyi frustrating Nafisa,make sure kin kai mata wuya,ina so naga ƙarshen endurance ɗin ta".wani irin daɗi Khafilat taji da ta fahimci cewa Amah ba wani damuwa da Nafisa tayi ba kamar yarda tayi zato.

    Bayan kwashe kayan wucewa ɗaki Nafisa tayi tana tunanin hanyoyin da zata bi wajen bawa Khafilat kashin ta a hannu ,abu guda ne bai tsalakewa ganin ta ba wanda shine Murmushin da Hajiya Saddiqa tayi lokacin da Khafilat ta watsar da kayan tana takawa ,ɗaurewa kan ta ya sake sanann ta sake gasgatawa cewa Hajiya Saddiqa ba mutuniyar kirki bace amma ko ma mene zata bar wa gaba Wanda tasan a lokacin fahimtar ta zata fi haka.

Kuyi manage da short chapter,

Yanzu aka fara oo🥱

Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top