11


CHUCHU JAY✍️
Be with 👇
𝐴𝑊𝐸-𝐼𝑁𝑆𝑃𝐼𝑅𝐼𝑁𝐺 𝐼𝑁𝐾📔
Tagwayen tafiya mai shirtacciyar ma'ana ta ban mamaki daga jerin tawada ɗaya Al-ƙalami biyu.First Series.

LOKACI!
Halish Sultan

BA DUK ƘYALLI BANE GWAL!
Chuchujay

    Tsahin Hankali a ranar shine abokin kowa dake cikin gidan nan musamman a lokacin da aka kasa samun gawawwakin Big Mummy da Mummy Nadiya sakamakon ƙonewa da sukayi suna masu ƙoƙarin ceton ransu ,a yarda aka gan su shine kowa da ƙasusuwan sa da kuma abunda baza a rasa ba kan gadon sa ,yarda abun ya faru kuwa Allah kaɗai ya barwa kansa sani,duk inda ka ratsa kuka kawai kake ji musamman na yaran gidan da basu taɓa shiga tashin hankali ba makamancin na Ranar,bacci kuwa ya yanke wa kowa babu idanun ma da zaka koma kayi dasu domin suna kan Aikin ganiya ne na kuka,duk da cewa ba sune kaɗai iyayen gidan ba amma sune manya waɗan da suke tun farƙon ƙirƙirar gidan ,sune mutane biyu da Alhaji Muhammad Tukur ya amincewa ya basu dukkan wata yarda da Amanar yaran sakamakon sanin cewa sun san zafin abinda yaran ke ji tunda shi dasu tare suka girma gidan Marayu.
    Tunda Nafisa ta farfaɗo kalmar BIg Mummy kawai ta iya furta wa sau ɗaya bata sake faɗin wani abu ba illa zama da tayi ba tare da ta sake cewa komai ba sai bin guri ɗaya da ido da tayi wanda hakan yasa yan ɗakin su sake shiga tashin hankali,jijjigata Khadijah ta fara cike da karayar zuciya idanun ta ɗauke da hawaye tace"dan Allah Nafisa idan baza kiyi magana ba kiyi kuka ko da zaka ji sassauci wani abu a zuciyar ki,wannan shiru da rashin Kuka babu abinda zai haifa miki sai ciwo,dukkan mu musulmai ne kuma tun farkon rayuwa dama mun san da cewa zamu koma ,sanin hanyar komawar mu kuma Allah kaɗai ya sani kamar yarda babu wanda yasan wannan Ƙaddarar zata faɗawa su Big Mummy,mune muke rashin su amma su kuwa Shahada sukayi, kuma insha Allahu Aljanna zasu shiga".shiru Still babu wani response daga Nafisa ,shirun nan dai shine Abunda tayi idanun ta kuma tsaye suna Kallan waje guda,kuka Hamamatu da Suwaiba suka sake rushewa dashi yayin da Khadijah ta rungume Nafisa ita ma tana kukan tace "komai zai dai dai ta Nafisa,zamu tsallake wannan jarabawar tare,everything is going to be okay insha Allah". Abu kamar wasa haka ya tabbata an rasa Big Mummy da Mummy Nadiya,Bayan ƙwana uku da yi masu sutura Mummy Zaina ta ƙarɓi jagoranci cigaba da riƙon gidan wanda dama ta dade tana ƙwaɗayi ,duk da ba a bata muƙamin shugaba ba amma tana matsayin wadda ta cigaba da kulawa da komai da ya danganci yaran a cewar Alhaji Muhammad Tukur wanda da kansa yazo aka musu Sallah,sosai yaji mutuƙar zafin rashin su duba da yarda suka tashi tare sun zama kamar yan uwa,yaso basu arziƙin da zasu yi duk irin rayuwar da suka so amma suka zaɓi zama tare da marayun yaran a cewarsu sune gidan su,tunda Al'amarin ya wakana Kwana uku kenan har ranar Nafisa babu Um babu Um,hatta abinci bata kai bakin ta ba illa Ruwa kawai da Khadijah ke aikin ɗura mata da Spoon,koda khadija ta samu Mummy Zaina da batun faɗa mata tayi kada ta dameta tunda dai bata san ƙaddara ba abarta ta bisu ita baza ta iya da fitina ba,a ranar kuwa da ta ƙarba tasa sunan Nafisa a cikin yaran da za'ayi Adopting domin dama kuwa ta saka a ranta duk ranar da aka bata babban matsayi a gidan sai ta bada Adopting ɗin Nafisa taje chan ta ƙarata.haka nan Khadijah ta dawo tana kallan yanayin da Nafisa ke ciki kawai sai ta rushe da Kuka tana mai jin mutuƙar tausayin ta .
    Bayan Sati da rasuwar Su Big Mummy Hajiya Saddiqa wadda ke da ƙwanaki Bakwai a garin ta kawo ziyara gidan Alheri tare da ƙanwarta Hajiya Sakina Matar Alhaji Muhammad Tukur Mamallakin gidan,koda suka zo Babu wani ɓata lokaci Aka jero yaran da ke da Appointment na visiting ciki kuwa har da Nafisa Wadda har lokacin gata nan ne dai duk da kuwa an samu tana karɓan Abinci idan wani a ɗakin na bata,idan kuma tana san Abu takan faɗi sunan sa sau ɗaya bata ƙarawa.haka yaran suka fara gaida Hajiya Saddiqa da Sakina cikin su har da Sa'adatu da Suwaiba tunda a yarda Hajiya Sakina ta zayyanawa Mummy Zaina musu shekaru sha uku su ke so,a haka yaran suka gaida su ɗaya bayan ɗaya,lokacin da aka zo kan Nafisa wani irin faɗuwa Gaban Hajiya Saddiqa yayi ,nuna ta tayi tace"ke ya sunan ki?"Kallan ta kawai Nafisa tayi ta ɗauke kai ba tare da tace mata komai ba,ganin haka yasa Mummy Zaina talaɓe ƙeyarta tace"Ana miki magana kina ji kina faman bin mutane da ido kamar wata mayya,zaki je ki gaida su ne ko sai ran ki ya ɓaci?".
"Mummy Zaina Bata da lafiya fa"Suwaiba dake gefe ta faɗa idanun ta na ƙoƙarin kawo ruwa dan tunda Nafisa ta koma haka kuka ya daina wa Suwaiba Wahala duk da kuwa da ikirarin ƙiyayyar da take aikin faɗan tana mata a baya..wani irin Kallo Mummy Zaina tayi mata kafin tace"General hospital ne Akan ta". Murmushi Hajiya Sakina tayi kafin ta kalli Hajiya Saddiqa tace"yaya nasan ba za ki so ɓata lokacin ki ba idan nace miki munzo gurin da ya kamata,and kina Kallan ta she's just traumatized nasan ba sai na faɗa miki yarda zata warke ba "ƴar Dariya Hajiya Saddiqa tayi tana mai tashi tsaye ta kalli Mummy Zaina tace "ta haɗo kayan ta and zan filling forms ɗin da ya kamata na cike and nasan bana buƙatar ƙwakƙwaran Bincike tunda dai na tabbata kinsan Hajiya Sakina Ni kuma yar ta ce uwa ɗaya uba ɗaya,komai nawa zan Saka a File ɗin Adopting ɗin ta".washe baki Mummy Zaina tayi tana Mai cewa Suwaiba "ku tafi tare ta haɗo kayan ta,Hajiya muje ki cike Documents ɗin", Babu Musu Suwaiba ta  kama hannun Nafisa tana kuka Sa'adatu ma na gefen ta tana yi ,suna zuwa ɗaki suka shaidawa Hamamatu da Khadijah dake faman Addu'ar Allah yasa kada a zaɓi Nafisa,Suma dai Kukan suka fara ,Asiya da ke jin wani irin tausayin Nafisan ne tace da Khadijah"Dije mai zai hana mu gudu tare da Nafisa?cos ni banga amfanin kuma cigaba da zama a gidan nan ba,duk tsaurin Big Mummy wallahi itace gidan Nan amma kinga Mummy Zaina muguwar munafuka ce wallahi".Goge hawaye khadija tayi tace"Asiya idan mun gudu muje ina?ko kin manta Bama da kowa bamu da komai idan ba nan gidan ba?ƙilan Adopting da za'ayi na Nafisa ya zamar mata Alheri,Who knows Abunda ke ɗauke da tafiyan nata,duk Abinda Allah ya rubuta mu baza mu iya gogewa ba,sai ya faru"Sudden kukan da Nafisa tasa shine ya basu mamaki ganin sati guda kukan ma bata iya ba, rungume ta Khadija tayi wanda lokaci guda ta ƙara jiniyar kukan nata har da shesheƙa,Cikin Kukan ta ke kiran Big Mummy kamar ranta zai fita wanda hakan yasa kowa ɗakin tayata kukan dan dukkanin su ta matuƙar basu tausayi yarda rayuwarta tayi wani irin mugun Juyi da babu wanda yayi zato balle tsammani.
   Bayan gama dukkan wai Necessary abun da ya kamata ayi Hajiya Saddiqa da Sakina suka ɗauki Nafisa Wadda wasu ke murnar taffiyarta hannu guda kuma wasu ke jin rashin daɗin tafiyar tata,tunda suka ɗauki titi Babu abinda Nafisa tace illa kallan window da take tana mai jin baki ɗaya rayuwar ma ta ishe ta Amma yarda zata yi ta Fassara shine bata sani ba,daga gefe Guda tana mai jin Hajiya Saddiqa na cewa"wai Ni Sakina kina ganin Yarinyar nan lafiyarta ƙalau kuwa babu wata matsala ta hauka tattare da ita?kada fa cikin rashin sani na ɗauki mahaukaciya na haɗa da yara na".Ƴar Dariya Hajiya Sakina tayi tana mai cewa"yaya wallahi kina da abun dariya,Na faɗa Maki yarinyar nan is traumatise,kada ki manta Ni likita ce a kallo ɗaya kuma zan banbance Mai trauma da kuma mahaukaci,and beside Bata buƙatar wani asibi balle kije kina wani asarar kuɗin ki,wahala ma kan ciro mutum daga Trauma dan uban sa".dariya Hajiya Saddiqa tasa tana mai cewa"haba ƴar ƙanwata daga Adopting kuma sai azaba?na faɗa miki mai maye gurbin Halisa nake nema,wadda zata zamarwa Khafilat komai,ba sai na Maki ƙarin bayani ba nasan kin fahimta,yanzu dai Muje Allah yasa Mutumin na Nan da Bazan bar garin nan ba tare da naga Karkarazu ba ". yankar wata ƙwana Hajiya Sakina tayi tace"duk abunda kika ce Aunty ai haka za'ayi"..Bayan dogon ride a hanyar da take kamar za'a bar gari Hajiya Sakina tayi parking motarta a gefe guda tana mai Kallan Wata hanya da mota baza ta shiga ba tace"Yaya ke kaɗai fa zaki shiga dajin nan dan Ni babu abinda ke sosa mun kamar nazo gurin nan na shiga dajin nan"Kallan ta Hajiya Saddiqa tayi kafin tace"Amma ai buƙatar ki ida ta taso baki ganin dajin nan kike ratsawa ki shiga,kada ki damu bari na shiga tunda nima tawa buƙatar ta kawo Ni kuma bazan fito ba sai an biya mun."tana kai Aya ta buɗe motar ta fita da doshi hanyar tana mai ɗage Rigarta saboda ciyayin dake gurin ,ita dai Nafisa har lokacin tayi shiru tana mai kallan waje tana mai jin kamar ta buɗe motar ta fita ta hau titi,ille kuwa tana mai tunanin yin hakan zuciyarta ta amince mata da ta buɗe motar ta fita ta hau titi ko ta samu mota ya bigeta itama ta mutu ta je inda Big Mummy take, a Hankali tasa hannunta gurin buɗe motar ta danna,yana buɗe wa ta tura ƙofar ta fita ta  doshi Titi da gudu,da sauri Hajiya Sakina ta buɗe kofa jin Alamun buɗe kofar,tana ɗaga
Ido ta hango Nafisa na gudu zata doshi titi,a sittin itama ta fito ta mara mata baya aikuwa tayi sa'ar cin mata,hannu ta saka bayan Rigarta ta kamota da ƙarfi, ba tayi wata wata ba ta ɗauke ta da wani Marin da sai da ta tuntsura kafin tace"dan ubanki kashe kanki zaki yi,baki da hankali zaki hau titi dan ki jamana bala'i,to wallahi da mota tazo ta kashe ki haka zamu wuce mu barki ki ƙarata tunda ke dai yar iskar yarinya ce".janta tayi kamar kaya suna zuwa bakin mota ta tura ta tana mai cewa"matsiyaciya"kafin ta koma driver seat itama ta zauna tana  saka wa ƙofar lock.shiru babu wani abu da Nafisa ta sake yunkurin yi baya ga kukan zuci,.suna nan zaune cikin motar suna jiran Hajiya Saddiqa wadda baya kimanin Awa Guda sai gata,Aunty Sakina na Hango ta tayi unlocking ƙofar,buɗewa tayi ta shigo tana mai faɗin"Wallahi bokan nan shima wani matsiyaci ne guda ,baya da aiki idan kazo ya nemi yayi Iskanci da kai gashi da shegen wari kamar baya wanka,Ai kuwa idan aikin nan baiyyi ba sai na masa rashin mutunci".key Aunty Sakina Ta yiwa motar tana cewa"Ke dai ba buƙatar ki zata biya ba ai na mita bai tashi ba,wannan shegiyar yarinyar Kuma da sai dai ki fito ki ji ta mutu yar iska,kawai na sakankance ta buɗe kofa ta nufi titi da gudu,dan bata san Halina bane, wallahi ni muguwa ce ba dan ke ba barin ta zanyi ta mutu tunda bani na haife ta ba".da Mamaki Aunty Saddiqa ta juya tana mai kalla ta kafin tace"idan mutuwa kike so ki bari zaki mutu amma ba yanzu ba".
  A Ranar suka wuce Lafiya dan tun kafin su ɗauko Nafisa sunyi booking jirgi ,Alhaji da kansa yaje ya ɗauko su a Airport a hanyar su ta komawa sai satar Kallan Nafisa yake wadda window kawai take kalla dan ko gaidasa ba tayi ba,Kallan sa ya maida kan matar sa yace"wai ni kam Hajiya ita yarinyar nan bata magana ne? Naga ko gaishe ni ba tayi ba".juyawa Hajiya Saddiqa tayi tana mai Kallan Nafisa kafun tace"za tayi ne ,Ni dai ba tambayoyi ba kayi sauri muje gida dan ina da abubuwan yi masu amfani"bai sake cewa uffan ba ya mayar da hankalin sa wajen tuƙin da yake gudun kada ya ɓata mata rai dan ba ƙaramin aikin ta bane ta ce ya sauka ta ja motar indai rashin mutuncin Saddiqa ne yafi gaban nan ma.
TBC
08130229878.

Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top