10
Be with 👇
𝐴𝑊𝐸-𝐼𝑁𝑆𝑃𝐼𝑅𝐼𝑁𝐺 𝐼𝑁𝐾𝑆📔
Domin samun litattafai masu zafi daga tawada ɗaya alƙalami biyu.
HALISH SULTAN ɗauke da littafin
Lokaci✏️
CHUCHU JAY ɗauke da littafin,
Ba duk ƙyalli bane Gwal✏️
Zaune dukkan yaran gidan Suke a falon Alhaji Bukar inda Khafilat ke kwance da kanta bisa kafaɗar sa tana aikin zumɓure zumɓure ,sauran yaran Hajiya Hadiza kuwa baki ɗayan su suna gefe guda saboda tun tashi basu da wannan sabon ko shaƙuwa da mahaifin nasu bugu da ƙari kuma indai abun irin wannan ya tashi to dama kowa yasan bayan wa zai bi,cike da Yamutsa Fuska Hajiya Saddiqa tace"kaga Alhaji Ni ba wai nace ka tara mu anan kana faman irgamu da ido bane,hukunci zaka yanke kuma ni na riga na taimaka wajen yanke wa bine kawai kowa zaiyyi,bazan ɗauka ba gaskiya zaman Salman da Khafilat guri ɗaya dole ne ya bar gidan nan ,kana Kallan cikin idanun sa dama ai kasan Abunda ka haifa,jaraba ce tsagwaranta ciki shine yake neman sauke wa kan ƴar ta shin nace ɗakin su ba mata Biyu bane?yaje chan ya cigaba da lalacewar da su mana tunda nasan Anayi,to wallahi muddin Salman bai bar gidan nan ba daga nan gidan yari yayi".da mutuƙar mamaki Hajiya Hadiza tace"Sadiqqa to idan Salman ya bar gidan Mahaifin sa ina kike so yaje?".hayayyaƙowa Hajiya Saddiqa tayi tana mai nuna ta da yatsa tana faɗin"kada ki raina mun wayau Hadiza ,wallahi ba yaran ki ba hatta ke rayuwar ki a ɗan yatsa na take ina kaɗawa zata ƙare ki kiyaye ni kuma Salman ne sai ya bar gidan nan wallahi ina yaso idan ya fita sai yayi ma na waje ciki ki raina amma ba gida na ba".ƴar Dariya Hajiya Hadiza tayi tana mai duban ta da kyau kafin tace"daɗi na dake Saddiqa jahilci,idan ba jahilci ba ta ina kike riƙe da Rayuwata da ta yara na,ai abunda kika lissafa Allah ne kawai zai iya yin haka ga bawan sa amma ba abinda ya halitta ba,Salman Kuma duk abunda kike yawo dashi a zani babu inda zashi dan Baya da gidan uban da yafi wannan ,duk ɗacin ki kuma baza ki sake hakan ba".wata irin Shewa Hajiya Saddiqa tayi tana mai faɗin"a haye wato Hadiza har kin yi bakin da zaki faɗa mun magana kai kuma Alhaji kana ji kana kallo,to wallahi ko ka nuna wa Hadiza matsayi na yanzun nan ko na bar maka gidan nan".Marin da Alhaji Bukar ya taso ya ɗauke Hajiya Hadiza dashi ne ya saka ilahirin ɗakin yayi shiru bayan ƙarar marin da ya sauka, dariyar Hajiya Sadiqqa itace abu na farko da ya katse shirin wucin gadin,tasowa tayi tana mai ɗora kanta bisa kafaɗar sa tace"Alhaji na saura Barin Salman gidan nan,ni ai nasan a rayuwar nan baza ka taɓa bani kunya ba"cikin wani irin yanayi yace"to yanzu Hajiya Saddiqa ina kike so Salman yaje?". hannunta ta ɗaga tana mai cewa"ban sani ba kuma bai dame Ni ba,Ni dai ya bar gidan nan"tashi Hajiya Hadiza tayi ta bar falon idanun ta na neman kawo ruwa wanda hakan a akan idanun yaran ta,Tashi Sultan yayi dan mara mata baya amma tsawar Hajiya Saddiqa ya dakatar dashi lokacin da take faɗin"gidan uwarka zaka ,ai da kai da Saima yau sai Baban ku ya zane mun ku ita ladan faɗa da Khafilat kai kuma na takalar Khalid".Samrat ce ta tashi tana kuka ta ruga tabi Ummun su dan duk da ƙarancin shekarun ta tasan cewa ba'a san su musamman mahaifin ta da ko kallan inda take bayayi,wani abu wai shi daɗin uba ko ɗaya bata sani ba.taɓe baki Hajiya Saddiqa tayi tace "taron munafukai ,Alhaji kai nake jira""kada ki damu"shine kawai abunda Alhajin yace wanda ya saka Salma ɗago kai ya kalleshi da wani irin takaici da bazai iya misaltawa ba,tashi yayi daga duƙen da yake yana mai yin murmushin takaici yace"dama ba wai dan ban san mene zaka faɗa ba Baba Amma na jira ne naga ko wannan karan baza kayi rawa da bazar da wannan matar ke kaɗawa ba,amma kash tun marin Ummu nasan inda abun zaije,kana tunanin Baba zamu zauna kana wulaƙanta mahaifiyar mu gaban mu kayi tsammanin nan gaba muji ƙanka? wallahi baza muji ba kuma wallahi nata ma baza suji ƙanka ba ,gidan nan kuma idan kana san na barshi so nake kazo muje muyi DNA muddin naga kai ba ubana bane zan barshi har abada kuma bazan juyo ba,amma muddin ya zamana na kasance matsayin ɗanka babu wata ƙaramar macen da ta isa ta Koreni wallahi duk da kuwa gidan ka ne,idan kuma ba haka ba za a je lokacin da ɗa zai kai uban sa kotu tun da Rayuwar sa ya basa hakkin haihuwarsa da yayi,ke kuma Ni dake wanda ya fasa baya tsoran Allah".a wani hargitse Khalid ya taso yana mai cewa kada ka ma Amah rashin kunya Wallahi zan manta wane kai"tasowa Sultan yayi shima ya shiga tsakiya yana mai cewa bismillah Khalid".matsar da Sultan Salman yayi yana mai ɗauke Khalid da marin da sai da ya ga wuta kafin yace "dan uwar ka na karya ka in karya banza wallahi".bai kuma cewa komai ba ya juya yana mai cewa Saima "ke tashi muje".Babu musu Saima ta tashi ta bisa yayin da Sultan ma ya mara musu baya yana mai mutuƙar jin daɗi yau Salman ya faɗi abunda ke cikin sa,maganar da ya faɗa gaskiya ce ,babu wani daga cikin su da yake jin san taimakon Baban su nan gaba ko kuma wai suji Soyayyar sa ,wannan gurbin tuntuni suka rufe musamman ganin yarda yake kaima Ummun su Hannu gaban su,kada Kuma aje da magana mara daɗi.
Suna fita Alhaji ya kalli Hajiya Saddiqa wadda ta mutu a tsaye dan ko a mafarki bata taɓa tunanin wai Salman zai iya tsayawa gaban ta dana Alhaji Bukar ba ya faɗi abunda ya faɗa yanzu,dole ne ma ta koma gurin bokan ta,duk yarda zaiyyi yayi ya damƙa mata su Salman baza ta ɗauki maganar wai kada tayi ƙoƙarin ma Hadiza da yaranta Asiri ba idan ba haka ba zai koma kan ta, dole ne yayi mata wani abu tunda Salman ya fara tsayawa kansa akwai muguwar damuwa,ɗan yatsanta guda ɗaya ta ɗaga tace"Alhaji yanzu kamun booking jirgi zuwa Yobe ba wai sai gobe ba"da sauri da murna Khafilat ta tashi tana mai faɗin "yeah zamu gidan Anty"kallan ta Hajiya Sadiqqa tayi ganin yarda take faman mura kafin tace"zaku zauna a gida nima ƙwana biyu zanyi, Baban ku zai na muku Abinci ban yarda kuma wani ya baku abinci gidan nan ba ku karɓa,kai Kuma maganar Salman tana nan ,Allah sai ya bar gidan nan".mayar da maganar ta tayi kan Alhaji wanda bai iya faɗin komai ba zuciyar sa baki ɗaya ta karkata ne kan maganganun da Salman yayi,Nauyi yaji ƙirjin sa nayi masa a wannan lokacin ji yake kamar ba shi ba...Lokacin da su Salman suka shiga sashen Mahaifiyar su falo Suka tarar da ita idanun ta na zubar hawaye,tana ganin su tayi saurin goge wa tana mai cewa"maza Salman kazo ka haɗa kayan ka na yi magana da Atika zaka je gurin ta,kada ma kace mun makaranta,kaje chan ka cigaba,zan nema maka BUK ka fara ,zai fi maka kwanciyar hankali".kusa da ita yazo ya zauna yana mai cewa"Ummu kada kice dole sai naje gurin Aunty Atika na zauna ,abinda Aunty Saddiqa ke so kenan na bar gidan nan idan kuma muka mata mubaya'a tayi nasara,Ni na riga na faɗa wa Baba babu inda zani sai dai in idan ba shine ya haife ni ba kinga dole na bar masa gidan sa".cike da mutuƙar damuwa Hajiya Hadiza tace"wani ya faɗa maka gasa ce ake da wani zai Nasara akan wani?"
"aikuwa Ummu gidan nan zaman gasa ne wanda yayi Nasara ya ƙwaci kansa ,idan ma Ya Salman ya bar gidan nan wallahi ni ina nan anyi ta bala'i karshe a kai wani maƙabarta tunda naga abunda ake so kenan,ai Ya Salman ma mai haƙuri ne dan ni wallahi idan nafi haka girma a irin zuciyata ma zan iya sawa sashen Aunty Saddiqa wuta kowa ya mutu in yaso nima a kashe ni, wallahi ko ba Ya Salman gidan nan akwai ni"Sultan ya faɗa wanda kai karshen maganar sa yayi dai dai da tasowar Hajiya Hadiza da kuma Marin da ta kai masa bisa Fuska,Nuna sa tayi da ɗan yatsa kafin tace"Wannan ya zaman na ƙarshe da zan sake jin mummunar magana bakin ka Sultan har kana maganar kashe mutum, wallahi zanyi mutuƙar saɓa maka fiye da yarda baka tunani". gyaran Muryar mahaifinsu ita tasa baki ɗaya suka mayar da hankalin su kan ƙofar shigowa,ganin suna Kallan sa ya saka shi yin sallama wadda cikin su babu wanda ya amsa shi illa tashi da suka fara ɗaya bayan ɗaya dan bar masa falon,guri ya samu ya zauna yana mai Kallan yaran da already sun bar masa gurin yayi kafin ya mayar da hankalin sa kan Hajiya Hadiza yace"wato Ummun Sultan yau Salman ya bani mamaki".ba tare da ta kallesa ba koda sau ɗaya tace"ka kira Ni Hadiza Alhaji ba sai ka tsaya wani kame kame ba,shin kazo ka sake mari nane ko Yaya ?Dan nasan zuwan ka sashe na ba Alheri bane dan Allah ka faɗa ka tashi ka tafi".ɗan shiru yayi kafin yace"Salman zan biyawa ƙudi ya wuce Yankee Karatu kinga idan ya tafi makaranta abun ya ɗan lafa kafin kuma ya sake zuwa".wani irin kallo tayi masa kafin tace"kana so kace mun wato Alhaji ka yarda Salman yayi ƙoƙarin haikewa Khafilat ba".
Saurin mata alamu yayi da hannu yace"a'a fa ,kawai saboda gudun rigima ne ,kin san Hajiyya Saddiqa akwai zafi bana san rigimar ta", yanayi yarda ya faɗa yasa Hajiya Hadiza saurin kaɗa masa hannu tace"naji Please ka tashi kaje,Salman zai je Yankee Allah yasa hakan shine mafi Alheri". tashi yayi kamar yana tsoran mata magana yace"ba wata damuwa dai ko?"banza da tayi masa yasa yayi sum sum ya fita kamar munafiki,binsa tayi da kallo tana mai jin wai irin zazzafan Hawaye a kumatun ta,ta rasa gane lamarin Alhaji ko kaɗan,ya mayar da rayuwar sa baki ɗaya sai Abinda Saddiqa tace, tashi tayi ta wuce ɗakin ta tana masu fatan shiriya..
*************************************
1:30 AM
Alheri orphanage
Yanayin Ihun dake tashi cikin gidan shine Abunda yayi sanadin tashin duk wani mai bacci a gidan, baki ɗaya ƙwansu da ƙwarƙwata suka fito musamman da kowa yaji ana ihun Wuta,.ɗakin Big Mummy da Mummy Nadiya ne ke cin Balbali Na wuta wanda ba sai an faɗa maka tunani na halin da waɗanda ke ciki suke ba domin kuwa idan ba Allah ba babu yar da za'ayi mutum ya rayu cikin Wannan wuta, wani irin ihu Nafisa ta saka lokacin da idanunta suka sauka a inda wutar Keci kamar wutar kara duk da kuwa yarda mazan gidan ke ƙoƙari wajen ganin sun kashe wutar,da wani irin gudu ta nufi gurin gada gadan zata shiga tana mai faɗin"Big Mummy"kamo ta akayi tana mai ƙwacewa akan lallai sai ta shiga ta ciro Big Mummy,kafun masu riƙe tan su farga sai ganin ta sukayi ta zube a ƙasa kamar matacciya, Sister Hajjo ce da su Khadija suka kamanta suka shiga da ita ciki .lokaci mara sa yawa yan fire Service ɗin da aka kira suka bayyana ,babu ɓata lokaci wasu suka shiga wasu kuma suka ƙarasa kashe wutar amma Kash already mai iyuwa ta riga ta faru.
😭😭Typing this chapter was a heartbroken mthd for me.
Tbc
Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top