chapter two
NOOR-UR-RAHMAN.
Tunda mahaifinnata yamata maganar aurenta da nasir bata sake shiga gidansuba haka zalika bata sake sakashi cikin ido ba dan dama chan shi ba ma'abocin zaman gida bane bugu da kari kuma bawata shakuwa ce mai tsanani tsakaninta dashiba. zadaita gaisheshi kuma zai amsata da faraar sa da sakin fuska .
Tayi nisa cikin duba wayarta taji muryar muhammadu auwal akanta yana cewa baby sis dan Allah na aikeki gidan Abba mana "
Dago kai tayi ta kallesa tace "yaya please kasan fa ni yanzu basan shiga gidan Abba nake ba wallahi ko kadan "
Zama yayi kusaa da ita yace i know sis" wallahi important drive zaki karbo mun gun nas and ina aikine yanzu kuma idan na shiga gun nas kinsan bazan fito da wuri ba.
Murmushin yake tayi tace okay tom '
I'm sorry"
Murmushi tasake yi tace yaya kenan what are you sorry for"?
Dan Ka Aikeni sai kana bani hakuri kuma it doesn't matter nasan yanzu kana zuwa for sure yaya nas bai barinka kafito and nima dama inasan ganin farhana kwana biyu bamu gaisaba"
Hijab dinta ta dauka wanda ta idar da sallah dashi, fita tayi a dakin tana dari dari domin ba yaya nas ba hatta mamansu hajiya talle bawani sakar musu takeyi ba har gwanda gwanda sister dinsa farhana tunda tare suka tashi takan ignoring halin mahaifiyar tasu taja yan uwanta jiki.
DA sallama abakinta tashiga baban falon gidan ,
Azaune ta tarar da hajiya talle tana danne danne a wayarta ,
A dan dakile ta amsa mata wanda hakan ya tabbatarwa da noor cewa akwai kura idan har ita zata zama sirikarta "
Cikeda faraarta ta karasa cikin falon tareda zama kasan kujerar datake cikin biyayya tace ummi ina wuni"
Batareda ta dago daga kan wayarba tace lapia"
Batayi kasa a gwiwa ba takuma cewa "ummi yaya nas fa yaya ne ya aikoni gurinsa,.
Sai a wannan karonne ta dago da idanunta ta zubasu kan noor cikeda fitina tace "nikam noor gidan nan bakonkine ko yau kika fara shigar sane?
KO kuma wata sabuwar gulmarce ke cinki da zaki zauna kina cikani da surutu eye?
Sim sim ta mike dan bata cika san masifar hajiya talle ba domin idan tafarata bata tsagaitawa yarda kasan jiranka take ,
Hanyar dakin farhana ta nufa tareda yin knocking "
Daga daya bangaren aka bata izini akan ta shigo "
Budurwace mai matsakaicin kyau zaune a bakin miror tana kwalliya hankalinta kwance "
Kallo daya zaka mata kasan sun hada iri ita da noor saidai ita din tafi noor hasken fata sosai wanda harda taimakon mai a ciki,
Kule kofar da ke bayanta tayi ta zauna agefen gadonta tace "
Hajiyan yan gayu sai ina "
Fadadden murmushi farhana tayi tace "ki share hajiyata wallahi wani zafaffan party yan department dinmu suka hada shine nake kankaro mutunchi sabida kar a rainani"
Goga jambaki tayi a labbanta ta kara dacewa badai kinki jamia ba to wallahi kinbar ongan rayuwa sannan inanan ina zuba idanu naga gudun ruwanki na abunda kika tanadama rayuwarki "
Dan tabe baki noor tayi domin idan da sabo tasaba da hallayar farhana ta soshalawa indai party ne to zaka hangota gurin ,tun tana kwabarta har ta hakura domin babu ranar da bazata mata magana kan dabiuntaba basuyi fadaba amma bayan wannan babu wani aibu a tattareda ita ta hanyar zamantakewa dasu ,
...rakani gurin yaya nas mana idan yana gida "
A sukwane farhana ta juyo tace yaya nas ?
Nizan rakaki gurin yaya nas ?
Chap Ashe wanda ya mutu zai dawo,
Kinga idan zaki tashi kije da kanki kitashi domin intakaice miki zancema nida yaya nas bamu magana dan jiya yamun shegen bugu dan kawai yaganni da sameer din gidan Alhaji habib na karshen layi wai tsayuwar da mukai batayi masaba dan haka nida yaya nas wallahi hayhata hayhata kuma wallahi sai yaga abunda zanyi masa..
Mikewa noor tayi dan idan ta cigaba da zama a dakin farhana zata bata lokacintane sannan ta batama yayanta nashi lokacin ,
Kwata kwata batasan yaushe farhana zata yi hankali ba tasan samarin nan babu abunda ke kawosu gareta sai iskanci ,inma banda lalace ina ita ina sameer yaron da kowa yasan kwarewarsa gurin iskanci da biye biyen mata a anguwa,
Bata sake cemata komaiba ta fita a dakin domin zuwa dakin yaya nas"
Sau biyu tana knocking amma bataji alamun muryar mutum ba saida tayi na uku sannan tafara kokarin juyawa dan tayi tunanin koba kowa a dakin"
Deep muryarsace ta tsayar da ita inda yace "ke lapia"
Juyowa tayi cikeda fargaba then kuma ta juya da sauri sakamakon ganinsa da tayi dagashi sai boxers sannan fuskarsa dauke da alamun bacci wanda yake nuna knocking dinta ya tasheshi "
DA inda inda tace dama yaya ne yace nazo gurinka na karbar masa drive "
Karar kulle kofar da tajine yasaka ta juyo ,ajiyar zuciya tayi aranta tace kai dai kasani "
Fitowa yayi a karo na biyu jikinsa sanye da bakar jallabiya hannunsa kuma dauke da drive din "
Mika hannu tayi zata karba ya kada matakai wannan karen fuskar sa dauke da wata shuumar faraar da zata iya cewa bai tabayi mataba yace" nope ba baki zanyiba muje nima gidan zanje dama and im sorry da kika tarar dani a haka i thought farhanace ".
Kada kai kawai tayi dan wani ban barakwai taji abun ,yaya nas din da kullum cikin shan kunu da wani zazzare idanu wai shi yake cemata sorry !
Gaba tayi yana binta a baya, wannan karon basu tarar da ummi a falo ba wanda hakan yayi mata dadi domin tasan babu wai sai ta yaba mata magana musamman idan tagansu tare "
Kadan kadan yake jifantada hira har suka shiga gida itadai nata "eh "umum"
Direct bangarensu tayi inda shikum ya nufa gurin muhammad auwal"
****
Naseer baban dane kuma namiji tilo agurin alhaji umar dan uwan mahaifin su noor ,
Alhaji umar da Alhaji muktar yan uwane da suka samu jituwa da shakuwa da junansu ,sosai suka tashi da kaunar juna wanda hakan yasaka suka hada hannun kasuwancinsu tare inda Allah ya bunkasa musu dai dai gwargwado "
Lokaci daya suka siya gida a tare jikin juna ,Alhaji muktar shiyafara aure inda bayan shekara shima Alhaji umar ya aura matarsa hajiya talle wadda Allah ya azurtasu da yara biyu ,naseer da farhana .
Naseer matashin saurayine mai jini a jika ,yakasance irin samarinnan ne masu zakin baki waenda dawuya su tare mace basu shawo kantaba inda shikuma muhammadu Auwal kwata kwata tara yan matan wofi baya gabansa dukda kuwa irin matan dake kawo masa hari,
Halayyar su tasha bambam ta gurare da dama inda sautari naseer din kan tsokaneshi da bagidajen gidanmu shikuma sai yayi dariya yace "babu komai naji"
Ganin cewa dagaskefa muhammad auwal bashida raayi irin nashi yasaka yakan boye masa abubuwa da suka shafeshi da dama .
Muhammadu auwal ya karanci aikin jarida ne inda shikuma nas yakaranci aikin banki wanda hakan ma ya taka Babbar gudun mawa wajen rashin gane wane hali kowanensu yake ciki dan sau tari sai weekend sukan hadu.
************
Wasa wasa Alhaji mukthar ya maida maganar auran nas da noor babba wanda Alhaji umar yabada goyan bayansa dari bisa dari amma hajiya talle kuwa tunda taji wannan magana mara dadi a cewarta gaba daya ta tashi hankalinta ,
Koda tasamu mijinta da maganar cewa itafa bata yarda ba ,fafur yanuna mata bama yasan ta sake tasar maganar ko kuma ta nuna kyamar hadin nasu ,
Tana shakar sa duk iskancin ta dan haka cikin fushi ta tashi tabar masa dakin tareda kudirar niyyar idan har ita ta haifi naseer bazai taba auran noor ba.
Kaman guguwa haka tafito babban falon gidan inda ta tarar da nas da farhana suna kallo ,
Guri ta samu ta zauna tareda kiran sunansa cikin kakkausar mirya ,
DA Sauri ya amsata dan yasan akwai danja .
Cikeda iko tace inasan kace bazaka auri noor ba sabida bakasanta sannan kanada wadda zaka aura .
......Ashe igiyar auranki zata fara lilo kuwa babu tantama "kakkausar muryan Alhj umar ta daki kunnuwansu baki daya "_
Cikeda inda inda tace "maikuma yayi zafi haka abban nas daga nace bazai auri noor ba sai kuma igiyar aurena tafara rawa?
Dama na nacene sabida kar azo daga baya zuminci yabaci kasan yanayin wani auren zumincin"_
Batareda ya karaso inda sukeba yace "sai dai inke zaki batashi amma muddin nasake jin bakiki akan maganar aurennan talle wallahi baza'a jimu da dadi ba ki kiyaye .
Hanyar fita ya nufa yana fadin"kai naseeru taso karakani ,
Wata tsuka hajia talle tasaka bayan fitarsu tareda yin kwafa "
Tashi farhana tayi dan barin gurin "
Cikeda masifa hajiya talle tace "shegiya antaba kannen uwarki ba dole ki tashi kitafi ai sakariya wadda batada kishin uwarta maryam tagama baku kun lashe duk zakuci ubanku.
Dan murmushi farhana tayi tareda fadin "yo ummi inbanda abunki menene aibun noor yarinya mai nutsuwa da hankali menene laipinta ?
Wallahi ummi abun farin cikine ace yau noor tazama matar danki domin noor one in a million Ce samun kamarta sai antona hatta ni nakanyi kishi da hallayarta masu kyau wanda bani dashi instead kiyita fadan nan ummi har abba ya harzuka gwanda kawai kiyi hakuri ayi abunnan cikin kwanciyar hankali tunda hatta shi kanshi yaya nas nasan yana farin ciki da wannan hadin,muyita aduaa kawai in ranar tazo musha chasu .
Ai batasan lokacin da ta dauki flower din center table ta kaimata jifa ba ,da gudu farhana ta bargurin inda daga nesa take jiyo muryan ummin nata tanata banbami tareda kiranta mara tarbiyya'
Idan da sabo sun saba.
Chuchujay✍️
Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top