chapter three
NOOR-UR-RAHMAN✍️
Ganga ganga maganar aureta tashi inda kowane bangare yafara shiri wanda aciki kuwa harda hajia talle wadda ba domin Allah take komaiba tanayine gudu kar duniya tayi mata dariya ace bikin danta guda bata shiryaba .
Bangaren ango nas kuwa tunda aka fara maganar bikin bai ce komaiba illa deep down zuciyarsa na tattare da wani irin farin ciki mara misaltuwa ,yadade yana ganin kyan noor tareda yabawa irin surar da Allah yabata ,sau da dama yakan ayyana aransa cewa duk wanda ya auri noor ya more dumin komai yajice ita dan haka koda abbansa yayi masa maganar auren bai musa ba illa amsawa da yayi cikeda amincewa nan take ,
Bashida wani aiki illa tunanin gashi ga noor a gida daya kuma a matsayin matar sa ta sunna sosai yake godema Allah da baisa ya zubar da girmansa ba har akazo gurin da dattijon nan biyu suka basa ita a matsayin mata dan yasani cewa muddin mai auri noor ba zaiyyi yarda zaiyyi ya dandani zumarta koda sau dayane kafun wani ya aureta amma luckily komai yazo masa yarda ya kamata .
Kamar kullum yarda suke haduwa duk weekend shi da muhammad a gidan Alhaji mukhtar yauma hakance ta faru kasancewar babu mai zuwa aiki,
Zaune suke a balcony inda muhammad auwal ya jefi nas da tambayar da tunda aka fara maganar auransa da noor yakesan yayi masa ,
"Nas da gaske kana san noor tsakani da Allah?
Kallonsa nas yayi tareda yin side smirk yace "cousin kenan ,kana tunanin zan yarda Abba da baba Alhaji su aura mun noor idan bana santa ?
Its high time daya kamata ace kasan wanene ni sannan menene zan iya ,
Kara gyara zamansa yayi yace ka kwantar da hankalin ka namaka alkawarin zan bawa noor rayuwa mai kyau sannan zan sota da dukkanin zuciyata ,
Kuka inhar kaji noor tayi to banawa bane barema zan mata katangar karfe da duk wanda zai sakata kuka a fadin duniyar nan kowanene shi.
Take wani dadi ya ziyarci zuciyar muhammdu auwal domin aduniya babu abunda yake so kamar noor da mahnaz,
Dafa kafadar nas yayi tareda yi masa godia .
Bayan sunyi sallah asr ya kira mahnaz yace ta fada ma noor yanasan magana da ita guest room dan yana ganin its high time daya kamata suyi facing juna.
.........zaune take kan abun sallah tana duba qur'an dinta cikin nutsuwa ,
Kamar an jefo mahnaz haka ta fado dakin tana kwala mata kira ,bata kula ta ba saida takai aya sannan ta rufe quran din ta kalleta cikeda kulawa tace "mahnaz wai yaushe zaki san kingirmane for Godsake?
And idan ban mantaba nasan na hanaki shigo mun daki batareda knocking ba sannan tukkunama menene yafaru kike mun kiran mabarata "
.yar dariya mahnaz tayi tace didi kenan bazaki gane ba ,yaya nas ne yace nafada miki ki sameshi a guest room and I couldn't resist farin cikin da nake ciki sabida a duniyar Allahn nan ina kaunarki da yaya nas sabida wallahi yaya nas one in a billion ne Allah didi kar kiyi sake irinsune mata ke rubibin su yanzu zakiji an kwace miki ,
Wani banzan kallo noor tabata a lokaci daya kuma ta dauke prayer mat din datayi sallah tana ninkewa kana tace "mai zai hana ayi swapping ke a hadashi dake kinga abu yayi dai dai kenan "
Wata irin dariya mahnaz tasaka tace didi kinji mai kike fada kuwa ni ai yaya nas ya mun tsufa just wait kiga time dina yarda zan kawo muku hot guy dan mazan dangin baba shakikai sun kare dan haka inada tabbacin baza'a mun irin nakiba "
Tana karasa maganar tafita a guje daga dakin tana fadin kiyi sauri didi kar ki batamasa time sannan dan Allah ko jan bakine kisaka ".
Kada kai tayi tareda yin dariya,
Batareda ta tsaya wani shafe shafe ba ko sake kaya tanufa guest room din cikin zumbulelen hijabin da tayi sallah da ,
Aduaa kawai take a ranta na Allah yasa yaya nas ya karbi bukatarta na fadama su baba bayasan wannan auren dan a ganinta zasufi daukarsa da muhimmanci.
Da sallama abakinta tashiga dakin inda ta tarar dashi zaune idanunsa kan wayarsa as usual ,
Lokaci daya taga yayi mata kyau da wani kwarjini ,kawar da wannan tunanin tayi domin she's not ready for all this"
Idanunsa ya sauke akanta tareda amsa sallamar cikeda faraa wadda ta tsinta weird domin tsakaninta da yaya nas wannan din sabon abune .
Zama tayi a kujera nesa dashi inda ga mamakinta sai ya taso ya dawo kusa da ita ,wani irin bakon yanayi ta tsinci kanta aciki,
Muryarta dauke da tsoro da fargaba tace "yaya nas mahnaz tace kana kirana Allah yasa lapia"
Shafa gefen fuskarsa yayi yace "yup lapia amaryata i guess inada every right na kiranki domin na ganki cos very soon ma idannaganki naji dadi zaki samu ladane yakarasa zance tareda kashe mata ido ".
Kwat taji ta hadiyi wani yawo ,dukkanin nutsuwarta ta tattaro domin magana akeyi ta rayuwarta cikeda fargaba tace "yaya nas babu wanda ya tambayeni shin inason wannan auren ko banaso and sincerely ko kadan banisan wannan auren sabida bana maka soyayyar aure wanda nasan ita mutual so instead mu cuci kanmu baki daya mai zai hana ka kwato mu daga wannan hadin ,nasan muddin idan kaine kafadawa su abba cewa baka san auren sabida kanada wadda kake so zasu fasa ,
Wani makirin murmushi yasaka lokacin data kai aya tareda cewa "and wane yafada miki inada wadda nake so bayanke ,beside kina tunanin cewa bana san auren ne?
To inasan na aureki and bana tunanin da wanda zai hana wannan auren idan ba Allah ba wanda shine idan ya hana babu yarda zanyi dole ya hanu amma muddin ina shan iskar duniya to ni naseer banida matar da ta wuce noorurrahman haka zalika noor bata da mijin da ya wuce nass dan haka ki kwantar da hankalinki kawai sannan maganar bakiyi min soyayyar aure kuma ki kwantar da hankalinki ni nas namiki assuring cewa zaki soni bayan aurenmu zan koya miki duk wata hanya da zaki bi ki soni"
Mikewa yayi tareda kashe mata idanu yace "yanzu amaryata ki koma gida kicigaba da shirye-shirye make sure kin gyaramin kanki sosai da sosai da haka ya fita a dakin yana murmushi "
A take wani gululun bakin ciki ya tokare mata wuya a hankali ta furta "kanubancan"
Kai tsaye dakin mahaifiyarta tashiga inda ta tarar da ita tana shan fura ,zama tayi kusa da ita ta rusa wani irin kuka mai cin rai "
DA Sauri ta aje furar tareda jawota jikinta tana tambaya lapia"
Cikin kuka tace mami wallahi idan na auri yaya nas zan mutu ,Allah mami banasansa ko kadan ki taimakamun kice ma baba wallahi banasan wannan auren.
A hankali tafara shafa kanta har saida tayi shiru kafun tafara magana tace "noor komenene kikaga ya faru da bawa to kadararsa ce wadda babu yarda zaiyyi ya tsallake ta sannan dukan musulmi anaso ya yarda da kaddara mai kyau da mara kyau wanda nasan kinsan hakan tunda dai dai gwargwado mun baki illimin addini,
Abunda nakeso dake shine noor kiyi hakuri,kiyi biyayya insha Allahu bazaki taba tabewa ba.
Share hawayenta tayi tareda kada kai alamun gamsuwa kafun ta kara rungume mahaifiyartata domin ji take kaman bata da wata mafaka a lokacin data wuce jikin mahaifiyarta .......
*********
Noor bata sake opposing aurenta da nas ba tun ranar da mami tabata baki ,sosai ta nunawa kowa cewa komai ya dai daita hakazalika nas ya dage da zuwa gurinta tareda janta ajiki inda a hankali tafara sakin jiki dashi tareda jin wani abu nadaban atattare dashi wanda bazata kirashi so ba amma dai yana da wani gurbi na daban a cikin zuciyarta "
Akawana atashi babu wuya a haka kwanakin da iyayensu suka dauka na bikinsu suka cika inda a ranar jumaa bayan an idar da sallah aka daura auren naseer da noorurrahman "
Farin cikin da iyayen maza suka shiga bashshi misaltuwa haka zalika mahaifiyarsu dake bauchi da zama takanas ta zo tareda tata tawagar,sunyi sunyi ta zauna dasu a kano bayan rasuwar mahaifinsu amma fafur taki a cewarta gwanda ta koma garinsu da zama tunda su din yanzu ba yara bane kuma bugu da kari batasan tashiga rayuwar matansu.
Lokacin da noor taga hajia kaka jitayi kamar ta shaida mata itafa bawani san auren take ba amma ganin yarda hajia kaka keta wani zumudi yasaka taja bakinta tayi shiru ,
Ba'ayi wasu bidioi ba a bikin bayaga walima da kuma taron yini ,bakaramun shakama farhana abun yayiba wai ace bikin yayanta gudu amma babu wani chasu ko guda daya ,lallai babu wanda ya isa ya hanata party idan nata bikin yazo dan Kan party zata iya hakura da mijin ma baki daya idan ya nuna kyamarsa.
A Daren jumaar baba Alhaji ya dauki noor da kansa a motarsa ya kaita gidan naseer da ke state road wanda kafun ya taho saida yayi mata nasiha sosai mai ratsa jiki inda ya kara da cewa muddin tayi abunda nas zayyi Allah wadai da ita to baiyyafe mata domin dai dai gwargwadon tarbiyya sun bata sannan basu tauyetaba wajen sanin menene auren shikansa ba da shikashikan zamansa ...
Tun a daren da abokanan nas suka kawosa suka tafi tafara fuskantar kalubale ganin irin jarabar da nas ke tattare da ita domin ko da ya nuna mata bakatuwar s*x da ita abokansa na fita bakaramun mamaki tasha ba dan tun kan su tafi yake wani jajjanta jikinsa dadinta daya babu yayanta wanda tasan dama babu yarda zaayi ya rako nas"
Koda ta nuna masa bai kamata ace daga shigowansa ya nemi sex ba batareda sun yi sallah koda rakaa biyu bane sunnuna godiyarsu ga mahalicinsu bakaramin fusata yayi ba wanda gudun fushin Allah yasaka ta bashi hakuri ,hakanan tanaji tana gani ya hayke mata batareda yaduba ita din sabon shiga bace sannan ga wata uwar yunwa da ke cinta haka zalika bata tunanin ma yayi wata aduar saduwa da iyali domin korar shaidanu.
Tunda aka kaita gidansa a kullum idan taji sallamarsa sai gabanta ya fadi domin baya wani sassauta mata dan taga kamar ma ya maida abun tuwon cinsa da fari abun ya fara damunta amma datayi tunani sai ta fawalawa Allah dan abun godia ne ma ace akan matarsa ta sunna take sauke duk wata jarabarsa "
Bata fara sirewa da auren nas ba sai ranar da yashigo mata gida a buge wanda hakan ba karamin tsoratata yayi ba ta tsorata ainun amma sai bata zargesa ba illa tunani daya tayi wanda ko abokansa sukayi spiking drinks dinsa bai saniba .
Koda washe gari ta taresa da maganan babu tsamani taji ya dauketa da mari wanda hakan shine mafarin daga hannunsa gareta ,
Mugun kashedi yayi mata na idan ya sake yaji maganar bakin wani to na lahira sai ya fita jin dadi koda kuwa muhammadu auwal ne dan haka taja bakinta tayi shiru dan yaci saa wajen tsoratata.
Tundaga wannan rana noor ta daina gane kan nas ,shayeshaye batasan kalar da bayayi ba ga kule kulen matan tsiya wanda abun har mamaki yake ba ,daga yayi salary daga sun kare ,ta rasa gidan uban dayake kaisu ,
"Koda yake ina mai shaye shaye da kule kulen mata zai aje kudi"
Zai aje kayan abinci dai dai gwargwado ammafa babu ruwansa da wani kudin gyran jikinta ko wata hidimar gabanta ,
Tarasa wama zata fadama halin datake ciki ,gudun karta fadama mami ta tayar mata da hankali yasaka ta zuba ma sarautar Allah idanu tana Adduar Allah ya kawo mai cireta cikin ukubar dake gidan yaya nas.
Chu✍️
Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top