chapter five

NOORURRAHMAN✍️

Ranar bai kwana a gidan ba,hakan yayi mata dadi dan tasan gamansu bazai kyauba kwatakwata, although koma me zai mata" it worth it at least ta sauke dutsen da ya danne mata kirji .

Saida taci ta koshi sannan tafara gyaran gidan ,
Bayan ta kammala ta shiga ta dado wankanta ,
Kallon agogo tayi taga har 9 na safiya yayi ,jitake gidan yayi wani free sakamakon rashin gilmawarsa ,wata iska ta daban take ji tana ratsa ta jitake kamar duk inda yaje kar ya dawo sai ya dauki lokaci mai tsayi .

Kwanciya tayi kan kujera ,wani numfashi ta sauke a hankali kafun ta dauko wayarta ta kunna turkish series dinda tayi downloading "full moon"tafara kalla cikin nishadi ".

Kamar an jefosa haka ya shigo falon,a hankali ta cire earpiece dinda ke kunneta ta kallesa yanata wani faman zazzare idanu ,
Bai ce mata komaiba illa wucewa ta bayan kujerar da take kwance da yayi ya shige daki,
Wata ajiyar zuciyatayi dan ta tsorata sosai tayi mamaki sosai yarda bai daketaba kamar ba nas din da tasaniba dan tabbas nas din da tasani a yarda ya shigo to duka zai rufeta dashi ,

Tabe baki tayi ta cigaba da kallonta ,
Bayan minti 30 yafito jikinsa sanye da black kaftan kansa kuma dauke da hula black "
Karemasa kallo tayi a hankali lokacin da ya zauna dan daura agogo a hannunsa "
Wahalalan kyansa ta zuba ma idanu yarda duk yabi ya lalata kansa da shaye shaye "
Yaya nas namijine amma gaba daya ya daurama kansa masifa da balai na zamaninnan da yazama anoba "
DA sauri ta dauke kanta da ta lura da zai dago da kansa ,

Ki tashi kishirya zamu fita *

Sama taka ta tsinci maganar ,
Uhm?
Tafada irin batajishinnan ba'
Bai kasa a gwiwaba yakara maimaita abunda ya fada "

Batayi masa musuba ta shiga daki ta dauko mayafinta da jaka tana ta saka da warwara na ina zai kaita ,
Gaba yayi tana biye dashi a abaya '
Bata kara shan jinin jikin taba sai da taga ya bude mata gaban mota bai daice komaiba hakazalika itama batace komaiba tashiga gabanta na dukan uku uku dan tasan duk inda takai ta dawo there is something behind this goodness .

Tunda ya tada motar baice mata komaiba ya hau kan titi ,
Bai tsaya ko inaba sai cikin asibitin standard,
Dum gabanta yafadi tana fargabar shin mai suka zo yi asibiti,
A hankali ta bude bakinta tace yaya nas wane bashida lapia ?
Kallanta yayi kana ya maida hankalinsa kan tukin da yake yace "inkin jira zakigani ai"

Already dama yayi booking ganin likita ,bata sake sikewa ba sai da taga likitan ya umarceta da ta shiga dakin scanning ,
Bayan ta fito shima ya shiga then aka basu testes sukaje sukayi ,itadai batace komai ba illa zubama sarautar Allah idanu.
After 1 hour suka kara shiga gurin likitan ,
A tare suka zauna inda likitan ya kalli nas yace "
Malam naseer duk wani gwaje gwaje da ake bukata anyi sannan result din da yafito ya nuna mana cewa daga kai har matar ka lapiyar ku kalau babu wanda yake da matsala wadda ta shafi rashin haihuwa kawai dai abun daga Allah ne wanda at any time Idan yayi niyar baku haihuwa zaibaku"

Caraf nas ya kwace ta hanyar cewa "doctor babu wani artificial method da zamubi ta samu ciki within month ?

Yar dariya likitan yayi yace "nas kenan"
Artificial method kuma?
Duka duka yaushe akai aurennaku da zaka na neman artificial method dan samun haihuwa?
Ai ka kawantar da hankalinka lokacine baiyyiba domin akwai waenda sai suyi shekara sha wani abuma kafun suke samun haihuwar ,kawai ku barwa Allah komai idan lokacin yazo zaayi"

Sosai yayi kokari wajen danne harshensa gudun kar ya fada masa magana mai zafi a matsayinsa na likitan gidansu ,
Godiya kawai yayi masa sannan ya umarceta da ta tashi su tafi "
Batace masa komaiba illa tunani barkatai da yake ta yawo a ranta ,lallai ta tabbatar ya nas bashida hankali da ishashen ilimin addini
Tayima kanta alkawari bazata daina adduar neman tsarin tara zuria dashiba ,biizinillahi sai dai wata ta haifa masa badai itaba "
Wani sudden farin cikine ya lullubeta lokacin dataga ya dauki hanyar gidansu,

Take farin cikin da ke dawainiyya da ita ya gushe lokacin da taga yana horn a gate din gidansu , yasaba mata haka sai suzo unguwar tanaji tana gani zai hanata zuwa gurin iyayenta sai dai ta tsaya gidansu wanda babu abunda take kwasa sai bakaken magana daga bakin ummi ,
Kamar daga sama ta tsinci kanta da cewa yaya nas dan Allah yau kar ka hanani zuwa gaidasu mami dan Allah "

Wani kallon shekeke yabata kafun yace "
Yanzuma kitafi basai kinje kin gaida tawa uwarba tunda ai taki tafi tawa "
Bata kara cewa uffan ba taja bakinta tayi shiru wanda yayi dai dai da tsayar da motar da yayi a cikin harabar gidansu "
A hankali ta bude murfin motar ta fito tana jin faduwar gaba dan muddin suka hadu da ummi to basu wanyewa lapia bata fada mata maganar da zata sata zubar da hawayeba.
Basu tarar da kowa a falon ba dan haka tasamu guri ta rabe daga gefen kujera inda shikuma nas ya wuce yana kwalama umminsa kira "

Shiru shiru babu wanda ya fito falon har tsawan kimamin mintuna 30 wanda hakan yasaka noor fara sikewa ,
Zuciyartace tafara bata shawara akan ta tashi ta tafi gidansu ,batayi yunkurin bawa zuciyar tata kunyaba ta mike sadaf kamar barauniyar tabar gidan "

A verandan da zai sada ka da cikin gidan taci karo da muhammadu auwal yana duba jarida ,
Cikin sarsarfa ta karasa garesa tareda furta yaya "
Kai ya dago sakamakon jin miryar tata dayayi kaman a mafarki ,cikin hanzari yamike yana kiran sunanta
"Baby sis kece yau agari "
Dan bata rai tayi tace eh nice" i don't even know why namaka magana bayan baka zuwa inda nake"
Karasowa yayi gareta tare da janta jikinsa yace come on noor nafada miki banida raayin zuwa gidan kanwata duk da wanda take aure ba bare bane ba amma i just don't feel okay with it amma tunda kinaso zan ringa kokartawa ina zuwa "

Tana kokarin magana muryarta ta sarke sakamakon muryar nas da taji yana cewa ,bamu bukatarka "
Wani fincikota yayi tareda kwasheta da mari "
Dan kin rainani shine kika zo nan din ko bayan ban baki umarni ba"
Zo ki wuce "

da mamaki muhammadu auwal ya kallesa kafun ya iya magana*
Nas!!a gabana kake marin kanwata?
A gabana ?

An mareta din ko zaka rama matane ?
Beside wannan ba huruminka bane hurumin maaurata biyu ne dan haka ke zo ki wuce "
Cikin matsanancin kuka tace "
Wallahi bazan wuceba ,Allah banni komawa gidan dan tasha "

AI baisan lokacin da yayi wani kukan kura zai kamotaba ,
Dagudu tayi bayan muhammadu auwal wanda yakara maidata bayansa zuciyarsa na masa zafi ,

Ni take fadawa dan tasha kake boyeta a baya"

Tafada din "
Ba dan tashan bane ,
Idan ba tashanciba menene zai saka ka daga hannu ka mari matar ka"

To aikuwa za kuga tashanci ,.tattare hannun riga yafara zai fada da muhammadu auwal wanda ya zuba masa ido yana mamakin sabuwar halayyar nas din ,dan sabuwace agurinsa,
Although basu haduwa yanzu kuma basu cika magana ba wanda ya sa a kan cewa sabida aikine amma bai taba tunanin nas ya koma haka ba"

Yana kokarin chakumar sa mami na fitowa wadda mahnaz ta kira a lokacin da ta leko taga ana hayaniyar.
Lapia malam nasiru?

Lapia "
Nas ba nasiru ba "
Ya kara tareda dauke kai "_

Duk yarda muhammadu auwal yasu danne zuciyarsa kasawa yayi ,baisan lokacin da ya dauke nas din da mariba yana fada masa yasan agaban wayake kuma noor bazata koma gidansaba tunda yazama dan iska "

wata dariyar rainin hankali yasaka kafun yace "
Idan kaine kakeda biro a hannunka ai sai ka saketa mugani"
Ke nafara rasa hakurina zo ki wuce "
Cikin kuka tace Allah wallahi bazan bikaba *
Kicin kicin ta tubure yayinda kowa na gidan ya goyi bayanta ,
dan dolen sa ya tafi yana kwafa dan tabbas yau da ace noor ta biyosa to sai ya chanza mata kamanni"

Jimamin sabon Alamarin suka hau yi kar ma ace muhammad.
***
Mai ya kawoki ?
Shine tambayan da Alhaji baba yafara mata lokacin da ta gaishe shi bayan dawowansa da dare,
Gaba dayan su babu wanda tambayan tayi ma dadi kar ma ace mami dan tafita da nas a yau dinnan "

Kamar ya mai yakawota Alhaji ?
Hakanan kuma yarinya batada ikon zuwa gidan mahaifanta sai da dalili?
To a bar ma zancen mai ya kawota dan noor kuwa ta dawo kenan bazata kuma komawa gidan naseeru ba bayan cin kashin da yazo yayi a gidan nan,haba ka kalli yarinyan nan mana ai a ido ma kasan ba dadi takeji ba dan dai kawai yarinyace mai nutsuwa wadda bata fadan laipin mijinta amma nan nan cikin gidan nan nas yazo ya daga hannu a gaban yayanta ya mareta sannan har yake mun gyaran suna da nas dan nakirasa da naseeru,
Gaskiya ba zai iyuba,lokacin da ka aura mata shi gabadayan mu mun maka biyayya kar ma ace yarinyar nan wadda gaba daya bata san yarannan amma haka ta aureshidin ,inaji inagani sai dai na bata kwarin gwiwa amma yanzu gaskiya nazo geji


Chu chu✔

Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top