chapter 9
Noorrurahman👑
Charaf taji udaysah ta rike mata hannu "
Ina zakije ,
Ai ba inda zakije idan bai bada hakuri ba idan muka barshi haka gobe zai kiraki da spider woman ne dan haka dole yasan yayi ba dai dai ba "
Hawayen da tun dazu suka fara biyo kuncinta ne suka kara gudu, kwace hannunta tayi ta fice a office din tana matsar hawaye "
Mai yasane ita bata da sa'a a rayuwarta ,mai ma yasaka ta kula udaysah da har ta jawo mata wannan balai haka '
Gaba daya ji tayi jikinta ya mutu ga wani baci da ranta yayi dan haka kawai tayi deciding ta tafi gida .
Dago idanunsa yayi yasauke su kan udaysah hade da kara bata rai sosai sosai"
Wannan wane irin haukane haka ,
Kinsan ba kowane irin rashin hankaline nakeso ba
And uban menene alakarki da waccan yarinyar da har zaki kawo mun ita na bata hakuri,
Wato har kin fara kawaye daga zuwanki makaranta ko,
Its okay zamuyi maganan da kyau a gida get out"
Bata rai tayi ta kuma turo baki"
Amma dai brother fayyaaz kasan abunda kayi bai dace ba ko,
Daga ganin baiwar Allah sai ka fara kiranta ninja yanzu gashi kasaka har wani yana kiranta sunan"
Udaysah bana san na kara maimaita kaina kifice mun daga office idan baso kikeyi na karkaryaki na watsa waje ba yanzun nan ,zakisan ni kika zubarwa da mutunci a idanun wachan stupid yarinyar ,zakisani tunda ni abokin wasan kine"
To da menene kai idan ba abokin wasana ba legally kai abokin wasanane tunda dai umma'ah kanwar abuh ce,
Murguda bakinta tayi sannan ta fice a office din dan karya ballatan da yafada"
Fayyaz mutum ne wanda bayasan rubbish amma hakan baisaka udaysah daina tsokanarsa ba aduk lokacin da ta samu chance ,.yasha fadama umma'ah tayi ma yarinyanta kashedi kan ta fita harkarsa amma kamar ma itaa ke zugata '
Udaysah yarinyar yayan umma'ah ne dake chan gida sudan "
Ta daukota da zumar tayi karatu tun tana shekara goma sha uku amma sabida soyayyar da takeyiwa udaysah yasa mahaifin udaysahn ya ce ta riketa har gama karatunta idan kuma ta samu miji a Nigeria shi ya yarje su aurar da ita "
Umma'ah taji dadin wannan karamci na dan uwanta dan haka yasa take da wani personal motive na hada udaysah da danta tilo daya aure"
Amma ba nan ba, sanin halin dan yau yasaka bata fadawa kowa komaiba ta basu dama ko zasu kawo mata wadanda suke so dan yana daya daga cikin dalilin dayasaka take tura fayyaz yayi mata lectures attimes ko zaiga wadda ta kwanta mishi"
Lokaci bai jiran kowa dan haka ta kudiri niyyar muddin fayyaz bai ga wadda yakesoba a wannan zuwan mata lec din da yayi to zata hadashi da yar uwarsa asirinsu rufe tunda duk ta basu isashen chance amma babu wanda yataba cemata ga wadda yake so...
*******************************
Wanka tafarayi da ruwan sanyi ko zataji sanyi a cikin jikinta da ranta ,
Shikenan murnar da ta kwana tanayi ta tarwatse lokaci daya sakamakon kawancen da bashi taje yi makaranta ba ,
Shikenan burin yaya nas ya cika zata dawo gida ta zauna "
Amma udaysah ta cuceta dan tasan dole yanzu tana chan school authority sun kamata and tasan dole zata fadi sunanta.
Abincin ma kasa cin na kirki tayi ,komai ma bayayyi mata dadi '
Quran dinta ta dauko tafara tilawa a hankali dan yanzu shine abokin da ke yaye mata kewa sosai ,
Kamar kullum yauma haka ya fado uwar dakinta ,
Bata kulashi ba saida ta kai aya "
Zama yayi a gefen gado"
Wato yau daya kin koyo sabuwar halayya kina jina amma dan tsabar rashin mutunci saida kika gama abunda kikeyi"
Kallon shekeke tayi masa"
Yaya nas bafa karatun jarida kashigo kaga inayiba karatun quranine sannan inakai aya na gaisheka"
Batayi auneba yasaka bayan hannunsa ya buge mata baki"
Rufe mun shegen bakinki'
Wato yau daya kin koyo wani sabon salon ko to wallahi kicigaba zakici dan uban duka ne ,sannan yau abokaina zasuzo dinner da dare ki hada musu abinci sannan kiyi kwalliya mai kyau.
Yana gama fadin haka ya fada bathroom".
Ajiyar zuciya tayi ,
At least yin abinda take kauna zai sa ta manta da abunda ya faru a makaranta wato girki"
Tun karfe hudu tashiga kitchen dan nas ya kara jaddada mata yanasan komai yazama dai dai bayasan kuskure ,
Bayan tagama hada musu abinci mai rai da lapia ne tashiga domin yin wanka ,
sallah tayi bayan ta fito a wanka sannan ta jawo riga da zani na atampa tasaka don tasan tabbas tunda ya nas yace ta shirya ma bakinsa abinci to tabbas abokan kirkine da yake jin kunya zasu zo.
Wuraren karfe takwas na dare ta tsinkayi tsayuwar motoci wanda hakan ya tabbatar mata cewa bakinsu sun iso,
Bata fita ba dan batasan abunda zaizo yasa su saida hali a gaban bakin nasa ,tanajin karar bude kofarsu sai sautin muryoyi da taji suna tashi ciki harda na mata wanda ta tsinta familiar.
Banko kofar yayi ba tareda sallama ba "
Mai kike nufi bazaki fita ki gaishesu ba '
Dama ina jirankane "tabashi amsa a takaice "kiyi hanzari ,daga haka ya juya ya bar mata dakin,wardrobe dinta ta bude ta dauko hijab mai dan girma dan kare mutuncinta da na mijinta duk da bawani mutunci ne dashiba"
Cikin nutsuwa take taku har ta isa falon'
Zazzaune ta samesu sun bata baya ,kowannensu ya zubama kansa abinci sunaci suna hayaniya da santi kamar wasu mayun wata"
Cikin sunkuyar da kai ta karasa garesu bakin ta dauke da sallama"
Baki dayansu suka maido da hankalisu gareta sai kuma suka kwashe da dariya ,
Nas wai yaushe matarka zata wayene dan Allah kalli wata shiga datayi kamar zataje islamiyya ,
Daya daga cikin abokansa ya fada cikeda isgilanci inda baki dayansu suka kwashe da wata dariyar ,
Wani gululun bakin cikine ya tsaya mata a makoshi ,abokansa ne na ranan nan tareda yan matan ranar ,datasan su zasuzo wallahi da bazata bata lokacinta wajen musu wahalaba koda kuwa zai kasheta.'
Juyawa tayi zata bar gurin ,hannu yasa ya fincikota "
Ina zakije ".
Marairaice fuska tayi"
Yaya nas please ,just let me go karabu dani .
Kara karfin rike mata hannu yayi ,kicire wannan abun ,yabata umarni ga nuni da hijab dinta '
Gaskiya dai tacire Allah ya azurta ki da sura mai kyau amma kina rufewa ni saboda na ganki nazo gidan nanfa to be frank ,
Riyya ta fada tana kallon noor wadda take daf da fashewa da bakin ciki
"
Baby bana tunanin matarka dinnan zata waye gaba dayanta local ce amma masha Allahu ta iya girki idan mukayi aure na huta zanci abinci mai dadi mama ta kara"
Kuka take sanyi ,amma ta kasa dan gaba daya idanunta a soye suke ,a rayuwar aurenta da yaya nas wannan na daya daga cikin kololuwar rashin mutunci da tozarci da ya taba mata"
Bakijini bane nace ki cire wannan banzan abun kizo ki zauna anan ya nuna mata kujerar kusa da riyya "
Juyawa kawai tayi batareda tace komai ba tabar gurin daki tashege ta dauko karamin akwati tasaka kaya kala biyu da duk wani abu dazata bukata na zuwa makaranta dan ta yanke shawarar zuwa makarantan dan taga menene matsayinta "
Kai tsaye gidansu nas ta wuce gudun kartaje gida Baba alhaji ya saba mata ".
Farhana ta tarar a falo tana kallo ,da gudu farhana ta taso tadane ta tana murnar ganinta "
Dan tureta noor tayi"
Farhana kar ki karyani mana"
Dan kallo farhana ta bata "
Anya "
Tureta noor tayi ,ke bakida aiki sai na ciki dan Allah rabuda ni"
Kallon akwatin tayi"
Wannan akwatinfa yaji kikayi"_
Yake noor tayi"
Yaji kuma shikenan bazanzo gidaba sai in yaji nayi ,
Ya nas na roka ya barni nazo naganki naji dadi ko na kwana biyu ne and na zata ma bazai barni ba amma ga mamakina sai yace nazo kinga nan yama fi kusa da makaranta, shi ya kawoni da kansa ma sabida dare yayi, ummi fa "
Dala mata duka tayi acinya "
Yes talking about makaranta muje ki huta kiban labari and ummi taje dubai sarin kaya yau kwanan ta hudu"
Dan tabe baki noor tayi tana mamakin halayya irinta ummi"
Tashi tayi farhana na binta abaya tanata mata zuba wai tabata labarin hadaddun yaran masu kudi dake makarantarsu "
Kinga babu wani abun bayarwa gameda makarantar mu kedai bari naje na gaishe da abba na baki labarin wata shegiyar yarinya da na hadu da a makarantar.
***************************************
Washe gari da safe ita ta fara tashi ta hada breakfast,
Taji dadin kwanan gidan atleast sunyi hira da farhana damuwarta ta gushe ,
Batasan yan gidansu su san tazo dan dole zasu tsireta da tambayoyi musamman ma baba Alhaji dan haka ta roki farhana kar tafada wa kowa tazo ".
Suna tsaka da breakfast ya shigo gidan cikin kananun kaya"kallo daya tamishi ta dauke idanu dan wata tsanarsa ke shigarta idan tayi arba da idanunsa ,
Zama yayi a kujerar dake nesa da ita ya gaisar da Abba"
Abba ina kwana ,barka da safiya"
Barka dai nasiru,
Jiya ai naga matarka cikin dare nayi tunanin akwai damuwane amma da ta sanar dani kai ka kawota sabida taje makaranta da wuri kwana biyu tunda nan yafi kusa sai hankalina ya kwanta'
Banasan abunda zai kawo wata baraka a cikin zaman takewarku dan haka nake rokan ku kucigaba da hakuri da juna"
Ta gefen ido ya kalleta ranshi yayi balain baci amma dolensa ya danne"
Sunkuyar da kai yayi "
Ai abba babu wata damuwa insha allahu ,dama jiya ta makarane to yau kuma akwai meeting da muke dashi a Abuja na kwana biyu shiyasa nace tazo nan din ,
At least ma yafi kusa da makarantar tasu*
To to Allah ya muku albarka yayi jagora".abba ya karasa yana kokarin tashi dan yagama,da sauri noor ma ta tashi tana jan jakarta dan tagama shirin makaranta dama and last gangancin dazatayi shine ta zauna abba ya tafi ya barta da yaya nas a nan"
Ki bari na kaiki mana"
Muryan nas ya daki kunnenta "
DA sauri ta kada kai tana kwasar abubuwanta "
A'a yaya yanzufa kazo ko breakfast bakayiba bari nabi farhana sai su fara ajeni tunda makarantan mu yafi kusa ,just take care and idan ka isa Abuja ka kirani"
Dan side smirk yayi zai kuma ja Abba ya katse shi"
Kaje abunka driver zai ajesu da haka ya bar gurin inda itama bata wani bata lokaciba tabar gurin.
Kallon farhana yayi wadda take karantar su a tsanake'
Meye kike kallona dan ubanki"
Tea dinta ta karasa sha tareda mikewa "
Ubana yanzu ya fita "
Kafun yakara cewa wani abu ta bar gurin".
Kwafa yayi"
Ba gidannan zaki dawwama ba wallahi sai na miki mugun bugu tukunna zaki dawo hankalinki .
Chu chu jay✍️
Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top