chapter 8
Noorurrahman ✔
Autan umma'ah mai yasa wai bazaka saki fuskanka bane i thought mungama maganar nan already idan kacigaba da bacin rannan zanyi tunanin har yanzu ba da zuciya daya zakayi mun alfarman nan ba"
Dan yamutsa baki yayi "
No umma'ah you know me best tunda nace zanyi to zanyi it's just that na tsani cudanyya irinna dalibai, kinsani banisan hayaniya da yawa and daliban jamia sun fi kowa sanin takan hayani but for you Zanyi koma menene dan dai intro lecture na kwana daya its okay
I just hope kar na kara samo mayya irinta last year data Hanani sakat and umma'ah kika ringa biyeta ,
Yanwancin student dinki are weird ,Allah ya ciremun that husna of a girl out of my life Allah yasa kar wata ta kara mannemun cos bazasu samu me suke so ba i just don't have time for all these love rubbish stuffs .
Yar dariya umma'ah tayi
"To yanzu autan umma'ah idan banda abunka idan bakayi soyayyaba ta tayaya zakayi aure har ka haifamun jika nima naga jininka ,you're not getting any younger fa,you're turning 29 this year fa"
Come on mother don't start that,I thought big sis tabaki jikoki har uku sannan ga sis meerah itama ta baki guda biyu what's next?
Beside nifa bance bazanyi auren nan ba zanyi ne kawai lokacine bayyi ba".
To Allah ya kawoshi yanzu dai kayi sauri kar ka yi late.
Gyara zaman necktie dinsa yayi kafun ya fita yana mata sallaman sai ya dawo sannan ta gaishe masa da yan kungiyan da zasuyi taron duk da yasan excuse ne ta bashi domin kawai yaje mata lecture .
Umma'ah kenan"
*******************
FAYYAZ UMAR SARAKI"
Fayyaz dane tilo daya a gurin Alhaji umar saraki "
Alhaji umar saraki mutumin gashuwane wanda sanaar audiga ta kawo shi kano wasa da wasa kuma zaman ya daure inda kasuwancinsa ya bunkasa daga kan audiga zuwa sanaar kayyayyaki"
Dan babu abunda zakanema karasa a cikin babban boutique dinsa"
SARAKI collections,
Kayyayaki masu inganci wanda direct daga company dinsa ake hadasu "
SARAKI Corporation .
A lokacin da yayi shekara ta uku a garin kano iyayensa suka hadashi da yaruwarsa kalthume shuwa wadda suke zaune a kasar sudan"
Bayan aurensu ta zurafafa da karatu wanda tasamun goyan bayan maigidanta dari bisa dari wanda a yanzu haka babbar professor ce a skyline university dake cikin garin kano
"
Yaransu uku ,munnirat wadda itace babba sai samira wadda suke kira da meerah sai autansu wato fayyaz,
Munnirat da meerah sunyi aure suna zaune cikin garin sai fayyaz wanda shi a yanzu lecturer ne a makarantar da mahaifiyarsa ke koyarwa saidai shi yana under special course da aka turashi so zaibar makarantanne da zarar ya gama abunda ya kaishi "
***************************************
Dan sahu ta tara lokacin da ita isa babban titi,duba lokaci take akai akai saboda gudun kar tayi late zuwanta makaranta na farko tunda an gama mata komai hatta registration number dinta yana hannunta abunda zatafara shine lectures kawai ,
Lokacin da ta isa makarantan haka tayi ta waiwaye tana rarraba idanu dan bama tasan ta ina zata fara ba "
Da tambaya aka sadata da department dinsu na banking and finance ..
Koda ta isa hall din cike yake da dalibai jitayi kamar ta zura da gudu ,
Wani dogon kyakyawan malami tagani well dressed cikin grey suit tsaye a gaban board projector,
Hankalinsa yafi karkata kan macbook din dake gabansa inda board projector din take haska ma daliban abunda yake ciki,
Ta daya kofar ta koma sadaf sadaf zata shige"
GET OUT"
Shine abunda ta tsinta lokacin datake kokarin zama a empty seat ,
Dago kai tayi ta kalli inda yake amma ga mamakinta idanunsa suna nan kan system din dake gaban sa dan haka sai tayi tunanin get out din yana cikin abinda yake kalla ,
Zama takara kokarinyi ,
Hey ninja I said get out"
Sai a lokacin ne ta gane da ita yake sabida nikaf din dake daure kanta ,duk da cewa bata rufasa ba amma kana kalla kasan nikaf ne ga kuma uwar katon hijab da taci dole ya kirata ninja"
Amma ba laipi taji haushin ninjan da yafada mata musamman yarda kowa dake ajin yasa dariya ,
Bunbula hijab dinta tayi tafice daga ajin aranta tana jin zafin wannan dogon banzan malamin"
Kan kujerun dake gaban ajin tasamu ta zauna ,
Wayarta ta dauko ta shiga candy crush at least ta rage lokaci"
Hayaniyar daliban ne ya tabbatar mata da an gama ,
Tunda daliban suka fara fitowa bata koda dago ta kalli kowa ba ,
Ninja "
Taji muryar namiji a kanta ,
Dago kai tayi taga wanne mai isasshen guts dinne yake kiranta ninja "
Kai kuwa menene hakan "
Muryar budurwar da ta nufo inda suke ta katse mata balain dake shirin fito mata a baki"
Karema saurayin da yakirata da ninja kallo tayi shikuma sai wata dariyar shakiyanci yakeyi,
Abokinsa ne ya karaso gurin ya dafasa "
Haba abdulbasit wai kai mai yasa kake da neman balai ne menene na kiranta ninja.
Kanada wawanci"
Baiwar Allah dan Allah kiyi hakuri,
Jan Hannun abdulbasit yayi wanda yake ta masifar mai yasa zai ce masa wawa"
Dan siririn tsaki tayi kafun ta maida kallonta kan budurwar data dafata tana aikama Abdulbasit harara dan murmushi tayi mata ".
Nagode"
Zama kyakywar budurwar tayi a gefenta "
Ki daina mun godia na tsani naga namiji na cima mace fuska wallahi shima wancan malamin da ya kiraki ninja kar ki damu zan miki maganinsa "
Sunana udaysah muhammad "
Inasan zama friend dinki idan babu damu ,ive been checking our mates through amma banga wadda hankalina ya kwanta daita kamarkiba"
Kallonta noor ta kuma yi tana mamakin yadda wannan tsaleliyar yarinyar kesan abota da ita dan ta koina ta hadune gata da kyau wanda daga gani ta sirkice ba sai an fada ba
Sannan duk da dai bawani sanin kaya tayi sosai ba amma tabbas kayan jikinta masu tsada ne gata yar gayu ajin farko dan a kallo daya zaka gane hakan"
Kana ganin fatar ta ma kasan hutu ya zauna amma mene abun mamaki ma tunda duk wanda zaka gani cikin makarantar ba dan talaka ,da wuya ,
Bazata raina kanta ba tunda itama ba yar matsiyata bane kawai Allah ne dai yahadata da dan iskan miji".
Hannu udaysah tayi mata waving "
Hello kodai bakisan abota dani ne"
Cikin sauri noor tace aa im sorry dan Allah bahaka bane "
Hannun da tuntuni udaysah ta miko mata takama sukayi mubayaah ,
Noor.
Noorurrahman muktar dala,
And why not zamu iya zama abokai mana ,
Washe white well arranged hokoranta tayi kafun tayi hugging noor wadda abun yazo mata weird haka "
You're pretty "
Kallanta tayi tace thank you ,kema kina da kyau sosai "
Dan Dariya udaysah tayi tace oh please bawani nan fa insan irin color din skin dinki nawa yayi wani dau i use to thought da a albino zan zo duniya Allah ya dubeni"
Wata dariyace ta kwace ma noor wadda bata san ma ya akai tazoba daga gani udaysah bata da matsala "
Amma dai ke fulanine ko ,
Kada mata kai noor tayi"
Hausa Fulani"
Dan clapping hands udaysah tayi wanda daga dan zamansu noor ta fahimci sabontane "
Ai daga ganinki ma basai an tambayaba your color is rich caramel "
Dan Dariya noor tayi kafun ta tambayeta wane yarene ita"
baggara from sudan (shuwa arab )karatu ya kawoni nigeria since ina one three ,(13)fa
Amma im fond of this country shiyasa ban wani damuwa.
Kada kai noor tayi
"Aikuwa basai mutum ma ya tambayaba daga gani its obvious hope zaki koyamun yaranku"
Sosai har sai ya isheki ,
Zokirakani admin kafun next lec zan karbo sako"
Babu musu tabita"
Office din malamai suka nufa ita dai noor batace komaiba amma acikin ranta tana addua Allah kar yakara hadata da wannan mara mutuncin malamin.
Dai dai bakin wani office udaysah tafara knocking ,
Daga kai noor tayi tana karanta allon sunan dake saman ofishin kowane malami'
DA babban harafi taga anrubuta FAYAZ .U SARAKI"
daga daya bangaren aka basu daman shigowa
,turus tayi ganin malamin da ya kirata da ninja
DA Sauri ta dauke idanunta dan jitayi kamar ta ruga da gudu ta tsani wulakanci sannan da tasan nan udaysah zata jawota to da bazata zo ba amma in the first place mai ma ya kawosu office dinsa*
Bata gama tunaniba taji udaysah ta buga teburin dake gabansa tareda dora kafa daya kan kujerar dake gaban tebur din"
Malam how dare you, I mean wanene yabaka ikon kiran kawata ninja ,
Dama iri iren malaman nan munsan irinku bakuda aiki sai takurawa yayan jamaa "
Nannade hannun rigarta tafarayi "
To Bari kaji yau zan koya maka lesson din da bazaka mantaba muddin baka bama kawana hakuri ba oya"
Wani iriin mugun kululuwa cikin noor yayi"
Take wata zufa ta fara keto mata
"Nashiga uku ni noor what have I gotten my self into "
Da in ina tafara magana sir dan Allah kayi hakuri tana da matsalan aljanune dan Allah kar kasa a koremu ,
Hannun udaysah ta fara ja dan su gudu domin itakam ji take dama kasa ta bude ta shige yau idan aka koreta mai zata fadama abba"
Let go of me "udaysah tafada tana kwace hannunta i thought nafada miki yau sai na koya masa hankali ai"
Zai gane ya taboma kansa rigima
Sir da kai muke ka kuremu da na mujiya zaka bada hakurinne ko kuwa"
Wata gudawar tsoro ke neman kwacewa noor dan tunda uwarta ta haifeta bata taba shiga kidima da tsoro irin na yau ba ,dama udaysah bata da hankali bata sani ba.
Dagudu ta juya zata bar office din Allah ma yasa haduwarsu kenan ....
***************************************"
Noor ina zakije🤣🤣🤣😂ni kaina na tsorata da karfin halin udaysah wannan ai sai ta cuci rayuwar karatun ka🤣🤣🤣🤣😂😂😂
Muje dai zuwa kunsha ruwa lapia?
Chu chu jay✍️
Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top