Chapter 53

Chapter 53
Noorurrahman✔
Dariya likitan tasa tace aa gama dai murnar yaran da aka haifa maka sai muyi maganan mata,
Kunya ne ta kamasa yace i was overjoy i mean kyautan yara uku fa,
Mami haska mun noor please,
Mami na kokarin haskota ta karba wayan ta kashe gaba daya,
A'a da sauran karfinki cewan mami,
Murmushi doctor din tayi tace karfun hali dai tear biyu ta samu in and out so yanzu zaayi mata dinki and if not for drip din da aka sama da bazata zauna hayyacinta ba cos ta zubar da jini ,.

Kwanansu biyu a asibitin aka sallamesu ,washe garin dawowansu daga asibiti tana zaune tana bama maccen nono dan mazan sun fita kamawa taji sallamansa ,
Tanajin yana gaisawa da mami tana masa barka da hanya ,.
A hankali ya murda kofar dakin nata ya shiga bakinsa da sallama,mahnaz ce tayi saurin juyawa tace la brother ashe kazo ina wuni ,sannu da zuwa ya hanya,
Alhamdulilah yar kanwana,
Babban da take bawa madara ta mika masa karamun kuma na kan cradle bed yana bacci"fita tayi tana dariyan yarda noor ta wani hade rai ita ala dole tayi fushi,
Babban ya farawa huduba sannan ya dauko mai baccin yayi masa then ya kwantar dasu duka dan yaga bacci shima yake ji,
Komawa yayi kusa da ita ya zauna ya jawota jikinsa yace haba noor dita hasken idaniyata wannan fushin naki kinsan yana azabtar dani da yawa ba ,
Kinsan ba laipina bane yasa banzo ba ,aikine yasa and ina samun chance na taho come on amma ai i witnessed everything and yarda kika kawo mun yaran nan da ikon Allah i can't love you less Allah yayi miki albarka ,and karki damu gift dinki yana sharjah waiting for you tho nasan ba gift din da zan baki na biyaki amma i promise you zuciyata takice ke kadai dagake sai yaranmu ,namiki alkwarin baki farin ciki mai dumbin yawa, bazance bazan taba saba miki ba ko nayi miki ba daidai ba dominn dan adam ajizine amma na miki alkawarin kulawa da ke da yaranmu har karshen rayuwata, smile for me mana ko hankalina zai kwanta, tsintar kanta tayi dayi masa murmushin jikinsa ta fada tana share hawayen farin cikin da suke zubar mata ,bata taba tunanin cewa zata samu maisanta duniya kamar yarda fayyaz yake santa ba ,
Karban mace yayi ya mata huduba sannan ya daga mata gira yace zabi sunan da kikeso asama yarinyan ki cos sunan maza na kwace miki ,
Fara'a tayi tace dan wayau without even discussing it with me ,naji fara fadamun sunan da kasa musu sai na fada maka nawa"
Okay naji, babban nasa masa HAMMAD(praising Allah) shikuma karamun nasamasa MUHAMMAD..

Murmushi tayi cikeda san sunan tace ka iya zaban suna hubby i love it inasan both sunan dan koda kace nazaba dama dole akwai muhammad a ciki hammad ne dai ban kawo ba so nazaba macen UMMEROOMAN(first wife of abubakar (RA) mother of nana Aysha(Ra) ,
Kissing goshinta yayi yayiwa ummerooman huduba da sunan da ta zaba.
Bajinta yayi sosai ranar sunan yan uku wanda ya samu hallarcin yanuwa da dama daga na dangin fayyaz dake gashuwa da na sudan ,
Itama noor haka nata dangin sukayi dandazo hajia kakane bata samu damar zuwaba still kafanta, bataji dadi ba amma fayyaz ya tabbatar mata zasuje kafun su wuce har gashuwa zai kaita da gun danginsa na sudan.
Har yanzu dai ummi ba wani san noor take ba dan tagama sawa aranta itace ta jawo ma danta zaman gidan kaso wanda suke irga ranankun dawowarsa yanzun ,amma dai ta barwa zuciyarta ita kadai dan duk iskancin ta bataso aurenta ya mutu wanda tagama karantar Abba akan noor zaiiya yin komai,

Tsakanin noor da farhana kuwa kamar basu taba samun sabani ba dan sau da yawa ma gidan takan yini da muhammad a hannunta wanda shine mara rigima amma hammad kuwa rigimansa yawa gareta, to ummerooman ce ita ma da dan sauki"
Ganin sa bikin farhana kusa da arbain dinta yasa tace masa yayi gaba ita sai angama biki zata taho ,
Baiso ba amma ganin ranakun da ya diba basu da yawa yasa yace shikenan amma ni da kaina zanzo na dauke ku sai mu tafi da udaysah tunda zata sudan tayi kwanaki and kinga ma zamu gashuwa da bauchi duk sai ki bari sai nazo,

Ranar da yace mata yanasan tafiya ya zo gidan mami dan ganawa da ita kwana 20 kenan da haihuwanta,
Ganin da gaske tafiyan zaiyyi yasa tace amma hubby ni a tunanina bai kamata katafi ba kasan kuma yau zaman su umma'ah zai kare a prison we should welcome her as her relatives and nasan zatayi farin ciki mutuka na ganin yan jikokinta,
Dan bata rai yayi yace as if,
Ke wai mene damuwanki da ita,
Riko hannunsa tayi tace nikuwa nakeda damuwa da ita bandan ita ba ina zan samu tsulelen gaye kamarka kuma ina zan samu wadannan yayan da nagama haihuwa akansu,
Dariya karshen maganar tata tabashi yace karya kuma kike yarinya ni yara uku basu isheni ba idan ba so kike naje na kara aure ba,
DA dariyarta tace to kaje kayi mana ga fili ga mai doki,
Shi da udaysah ne kawai sukaje dauko umma'ah dan daddy yace bazai jeba dan bakaramun fushi yake da ita ba dole suka rabu dashi suka tafi su biyun,
DA Sauri udyasah ta fada jikin umma'ah tana kukan ,
Itama umma'ah kwalla take tana kallan fayyaz wanda yaki yarda ya hada idanu da ita,
Har sukaje gida baice mata uffan ba ,ganin bazai mata magana bane yasa tasa kuka tace fayyaz nasan na maka ba dai dai ba amma tunda na tuba na gane laipina ai na chanchanci  yafiyanka ba ,
Munnirat ce wadda sukazo suka tarar ita da meerah tace umma'ah kibarsa mana yaje ya kari fushinsa tunda shi ba'a masa abu shi wai mai mata"
DA Sauri umma'ah ta tareta dan tasan halin zafin kan munnirat kuma tasan na fayyaz musamman idan aka masa ba daidai ba"
Look munnirat kema kinsani nice banida gaskiya i was wrong so fayyaz yana da duk wani right nayin fushi dani bazan hanasa ba idan bazaku tayani neman yafiyansa ba kar ku bata masa rai,
Rike hannunsa meerah data fahimci ya karaya tayi ta kada masa kai,
Babu musu ya zauna kasan kujeran da take ya dora kansa kan gwiwarta yace umma'ah kidaina sakawa ina zama kamar yaro mara tausayi da tarbiyya a gabanki ,
Nasan kinyi ba daidai ba kuma Allah ma bai hanamu nunama iyayenmu idan suna kan ba daidaiba ,nina yafe miki kuma noor ma na tabbata har zuciyarta ta yafe miki so please umma'ah ki cire komai a ranki game da noor sabida yanzu itace rayuwata saboda itace uwar yayana"
Shafa kansa tayi tana kara ganin wautarta na yi ma Allah shishshigi a al'amarinsa Allah mayasa rabon yara ukunnan ba kasheta sukayi ba prison suka kaita,
Cikeda kaunar fayyaz tace insha Allahu baza'a sake samuna da kuskure makamancin wannan ba shima din na biyewa kidan shaidan ne amma daga rana mai kaman ta yau noor yatace kuma matar dana daya tilo mafi soyuwa a cikin raina.
Tabe baki munnirat tayi tace au umma'ah a gaban mu.
Dariya suka saka wanda harda daddy da basu san shigowarsa ba,
Shima yaji dadin nadamar umma'ah sannan ya karbi tubanta.

Babu yarda fayyaz bayyiba kan umma'ha tahuta tukunna da zuwa gurin noor washegari udaysah ta kaitaba amma tace fafur ita sai taje ta nema yafiyar noor kuma taga jikokinta,
Dole yasa suka tafi baki daya harda su munnirat wadda taki zuwa suna ita ala dole tana fushi,
Babu yarda meerah batayi da itaba amma taki zuwa,

Sunyi mamakin yarda iyalan gidansu noor suka nuna kamar ma babu abunda umma'ah din tayi suka karbeta hannu biyu wanda hakan yayi wa fayyaz dadi kuma ya kara tabbatar masa cewa baiyyi zaban tumin dare ba ,
Kamar umma'ah zata maida noor da su hammad ciki dan murna ,ta dauki wannan ta dauki wannan har saida udaysah tadinga tsokanarta ".

Bangaren haji nasir kuwa baba da muhammadu auwal suka daukosa kuka ya ringa yi musu wiwi dan yafa jijiki gidan maza musamman dayaje yahadu da bullies na prison suka dinga bashi kashi,
Bangaren muhammaduauwal baba yace suje yayi wanka ya hutu ya zauna ya danyi jinyan jikinsa kafun ya shawo kan Abba dan yana bukatar kulawa, ba musu muhammadu ya kaisa gurinsa yabashi kaya yayi wanka sannan yaje ya karbo masa abinci ya fita dan yanada gun zuwa,
Ummi yafara zuwa yasanarwa nas dinna gida kafun ya wuce,
Bata yiwa mami sallamaba tayi bangaren muhammad din dayake sai kashiga babu wanda yaganka cikin gida,
Matsar kwalla tafara da taganshi,
Shima kukan yasa yana ganinta rugumarsa tayi tana shafa kansa tana cewa its okay nas komai zai daidaita tunda dai gashi ka fito its personal sai mun dau fansa,
Dan tureta yayi kadan yace wazai dau fansa,
cikin rashin fahimta tace mu mana,.
Dan dariya yayi yace ah haba hajiya ummi aininan da kike ganina bawata fansa a gabana,
Akanwa zan dau fansa ,
Kinga ummi na baki shawara kifita ,kifita da fitarki kije ki tambayi hajiya kalthume ya zaman yari yake ,kinga duk kibarkinnan wallahi sai kin kare ,karma azo ga abinci bama abincinba uwar wahalar, kai bazaki fahimta ba duk yarda zan fada miki amma idan kinaso ki fahimta sosai to kidau fansa inada tabbacin zaki shigo hannu sai kije gidan yari kiji ya ake ji,
Kara gyara zamansa yayi yace ni fansa ,.haba ummi barni na karasa rayuwata a hankali ni gurin hajiya kaka ma zani ta hadani da mata adambam dinan nayi aurena na zama irin yaran da Abba yake buri nagari insha Allahu nidai Abba ya gama kuka dani so kema ummi indai danni kikeyi to ni nayafe wallahi,ki bari ki aurar da yarki cikin limana"

Jin karfun gwiwar tata ta kare yasa batace komai ba dan tabbas kamar yarda nas din yace ta fita ba ruwanta  ta fita din.

Harda noor a yan taya nas rokan Abba and ya yarda ya yafe masa amma da sharadin zai basa wata 3 yaga gudun ruwansa.

Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top