chapter 45
Chapter 45
Noorurrahman✔
Lokacin da sakon noor ya iskesa bai wata wata ba ya tashi yanacewa yes umma'ah you can do the needful inada important abu amma idan na gama zan zo,
Yana tafiya yafara tsinkayo muryarta tana fadin kawai na fara shiri ko,
Eh kawai yace mata ya fita dan yasan definitely yau sai sun kama nas ,
Text ya turama babban jami'in tsaron da suke aikin tare yace gashi suyi tracking dinsa down numbern na aiki,
Muhammadu auwal ya kira ya shaida masa abunda yake faruwa so koda ya isa station din har ya riga sa zuwa kasancewar ya fisa kusa da gurin,
Gaisawa sukai yace ya aikai noor ta samu numbern nas,
Kada kai fayyaz yayi yace bro wallahi bansaniba ina gidan umma'ah ta tura mun so I dont know ya ta Samu, koma yayane ai insha Allahu zaa samu biyan bukata wannan karan dai nasir sai ya shigo hannu,
Ajiyan zuciya muhammad yayi yace bansan mai yasa nas yake obsessed akan noor ba ,
I don't know yarda akai yazama this stupid amma da nasir he's not close to this abun yana bani mamaki and yanzu just look at yarda ake nemansa kamar wanda yayi kisa had it been ya Kawo kansa tun wuri im very sure da komai yazo da sauki amma look abunda ya jawo yarda abba yake fushi da cin alwashin sai yasa yaci prison its scary,
Kada kai fayyaz yayi yace Allah dai ya kyauta kawai aransa amma ya kudiri niyyar ko kowa baice a kulle nas ba shi sai yasan yarda zaiyyi yasa a kullesa ko zai mending ways dinsa amma its not safe for noor ace yana kan halayyarsa ta baya,
Muryar mai tracking dinne ta kashe su lokacin da yake kallan red din dayake tafiya a cikin computer yace "sir he's within Sufi mall area kamar ma yana ciki dan under the roof ya nuna ,
Umarni babbansu ya bada na su tafi area din umarni akayima tracker din da ya cigaba da bin location din nasa yana updating dinsu,
Rufar wa inda aka gansan sukayi fayyaz kuma da muhammad auwal kowa yatafi a motarsa ,
A nitse nas yake cikin black hoodie da pcap da sunglasses,
Yagama sakankancewa dan yayi waya da umma'ah ta tabbatar masa har yanzu ba'asan inda yake ba dan haka ya lafe a nan gidan wani abokinsa da yake dubai bai fada masa abunda yake faruwaba amma kasan cewar sun saba irin haka da nas din yace gate man dinsa yabasa key din ko ina nagidan,
Washe gari yake san ya gudu lagos dan Already umma'ah ta tura masa flight ticket da enough kudi abunda ya rage masa kawai dare dan jirgin dare zaibi saboda hakan yazo siyayyar abunda yake bukata,
Wanda yake tracking dinsa ya kara tabbatar musu yana gurin dan haka suka cigaba da bin location din da ya turo musu, muhammadu auwal ne a gaba dan shine a kowane irin yanayi zai iya gane nas din,
Kamar ance ya daga kai ya saukensu akan nas wanda yake dauko turare a bangaren turaruka ,
Juyawa yayi ya taba fayyaz yace bro ga guy nas chan fa yana duba turare,
Da zafi fayyaz ya yunkura zaije gun yanacewa to mai muke jira,
Rikesa muhammadu auwal yayi yace haba mijin noor karkayi mana wasa da damar da mukayi ta nema bamu samu ba mana kana tunanin a banza yansandan da suka shigo taredamu suke sake da kayan gida ba uniforms ba,
Tsaya ka kalle mun bari na duba dpo,
Yajuya zai tafi kenan fayyaz ya hango DPO din a kusa da nas shima yana daga turaren ,
Kallan nas yayi kafun ya kalli turaren dake hannun nas yace turaren hannunka yanada dadin kamshi dashi nake amfani trust me bazakayi dana sanin amfani dashi ba,
Kallan sa nas yayi yace aikuwa kaman kasan inasan sake turarene ,
Oh
Idannun Dpo dinne yasauka akan bangaren dasu fayyaz suke"
Alamu fayyaz yake yiwa dpo din akan nas ne , kasancewar bayan nas a juye yake dan haka baisan wainar da ake toyawa ba,
Nagode shine abunda nas yace "
Nagode da zabin turaren nan bari na wuce ina sauri ne,
Ya juya kenan dan zuwa biyan kudi idanunsa suka dira kansu fayyaz ,wani mugun faduwa gabansa yayi a dubu ya juya amma ganin wanda ya tayashi zabar turare gabansa yasa yayi turus yana waskewa,
Lapia"
Dpo ya tambayeshi,
DA inda inda yace ,eh_eh lapia inasan sake siyan wani abune kaga ashe ma ban gamaba,
Wucesa yayi dan barin gurin,
Dafasa dpo yayi yana juyowa yaci karo da handcuffs dinda dpo ya daga masa yace you're under arrest nasir umar dala"
Juyawa yayi zai gudu amma ga mamakinsa sai ganin yansanda biyu yayi a bayansa cikin kakinsu,
Karasowa fayyaz da muhammadu auwal sukayi gurin,
Tafa hannu fayyaz yayi yace game over malam nas,
Handcuffs aka gaba masa akayi gaba dashi yanata fisge fisge,
Waya mahammadu auwal yayi ma abba yafada masa an kama nas,babu shiri ya bar duk wani abu da yake ya nufa station din da muhammad ya fada masa,
Tsaye fayyaz yake bakin cell din da aka kulle nas "
Kallansa yake sama da kasa kafun yace"
Kai yanzu dan Allah nasir menene amfanin duk wannan abunda ka aikata,
Yanzu dai kalla ,kalli halin da kake ciki
Niyanzu abu daya nakeso shine ka fadi wanda ke taimaka maka cikin sauki dan samarwa kanka sassauci,
Wata dariya yasa yace fayyaz kenan,
Kaci sa'ar kamoni har nake cikin cell a kulle yanzu,babu komai amma inaso kasani ka tafka babban kuskure na hadakar da akayi da kai aka kamoni, kayi kuskure fayyaz dan kana tunanin ka rusa mun rayuwa ko to rayuwarmu tare ka hadu ka rusa ,
Yana cikin magana yaji muryar Abba yana cewa muhammdu ina wannan dan iskan yaron ina fatan ya chanza kamanni yanzu ,
Kallan babban dansandan yayi yace kai dan sanda yana ina inafatan ya daku sosai yarda uwarsa ma zata kasa ganeshi sannan yafadi sunan uwarsadin datake taimaka masako,
Haryanzu bamu samu cikkaken bayani abakinsa ba ranka ya dade muna jirane mubi duk wani method din da zamu bi idan bayyi magana ba sai ayi ta yarda zaiyyi dole,
Dansandan yabawa Abba amsa*
Kai ar ni ubansa na baku dama ku daka minshi har sai ya fadi uwarda take taimaka masa ,
Basu kuma ja da abba ba babban dansanda ya diba kurata biyu suka tafi cell din nas,
To kasan kurata an samu abunda ake nema da suka fara daka nas duka mai ratsa bargo baisan lokacin da yafara ihun zai fada ,zai fada wadda ke taimaka masa,
Uhum muna jinka dan uwarka ,dansanda namasan uwarshice kawai ya fada aje a kamota ta tayashi zama prison,
Wallahi Abba ba ummi bace beside itace ma tace na dawo gida amma mai taimakamun hajia kalthume ce,
Wacce jairar ce kuma kalthume ,Abba ya tambaya yana gyara babbar rigarsa,
Shima dai fayyaz so yake yaji wacce jairar ce ta bakin Abban dan shi yama manta sunan umma'ah kalthume"
Maihaifiyar fayyaz wallahi Abba itace idan baku yarda ba kuma ku duba wayana duk wani sako da muke turawa juna,
A lokacin da tafara kirana akan maganar noor nayi mamaki sannan ban amince da itaba har saida nayiwa abun nisan tunani saboda abba inasan noor shiyasa na amince da bukatarta ,
Lokacin da ta shaidamun batasan danta da noor ne nikuma na hau kan damar shine ta turo noor bayan container dake cikin makarantarsu sannan duk wadanda mukayi aikin dasu wallahi babu wanda nasani hatta Daniel duk ita ta kawosu har wadanda suka kama noor,ni kawai kaini gidan akaiyi ,
Amma daga kudi zuwa komai ita ke bayarwa sannan tace nadan bata lokaci dan har visa tayi mana zamu bar kasar nida noor baki daya,and ita ke sanar dani duk halin da ake ciki.
Mutuwa fayyaz yayi a tsaye ji yake kamar kansa zai tarwatse,
Cikin rudewa yace A'a karya kake ,umma'ah wont do this to me ,baazata taba yin haka ba ,nayarda ada bata san noor amma kuma daga baya ai ta sako dan batan noor dinnan ko udaysah ce ta bata abunda zatayi kenan,
Ai namasan karya yake wato bazaka tuba ba kenan duk dukan da kasha ko,
Abba ya fada yana mamakin irin yarda nas ya shirya wannan uwar karyar a cewarsa,
DA Kuka nas yace haba Abba kalli bakina fa kalli fuskata ,kalli jikina Abba agabanka akamun wannan dukan sakwaran tayaya zanyi karya aduba wayata mana aishi fayyaz din yasan layin mahaifiyarsa ,
DA sauri fayyaz ya karbi wayar nas daga hannun dansanda yafara lalube ,aikuwa layin mahaifiyarsane saboda duk duniya shine layin da yafara har dace wa a duniya,
Sakin wayar yayi ya koma ya zauna ya dafe kansa,
Daga cikin cell din nas yace bana fada maka rusani rusa kanka bane,
Wani kuka mai cin rai fayyaz yasaka tabbas babu tantama umma'ah ce ta taimakawa nas dan sai yanzune ya ke tuno inda ya san gidan da nas ya aje noorr,
Tabbas gidan umma'ah ne dan a lokacin da tasiya gidan bai samu yaje ba da taje ta dauko masa hotunan gidan,
Kara karfin kukansa yayi yana cewa why why,
God please ,
Dafasa muhammad yayi yace fayyaz ka kwantar da hankalinka dan Allah kabar kukan nan haka,
Kallansa yayi yace taya zan kwantar da hankalina muhammad ai babu zancen kwanciyar hankali kuma ,kasan noor ta fada mun cewa umma'ah ke taimakawa nas amma na kasa yarda da ita saboda hakan ma har fushi nake da ita,
Naki yarda da ita,
Karkaga laipina ,
Mahaifiyatace wadda banyi zatan hakan a tattare da itaba
Share hawayen dake bin kuncinsa yayi ya mike tsaye yace Dpo ka sa wadanda zasu kamota na rakasu gidan,
Rikosa Abba wanda bai gama fita daga shock dinba yayi yace A'a fayyaz baza'ayi hakaba ,
Bai kamata ace kai kayi jagorar kama mahaifiyarka ba"
Sniffing yayi yace Abba ko banje ba dolene za'akamota tunda babu yarda za'ayi su tsallake hukunci dole a hukuntasu saboda idan ba hukuncin aka musu ba ko yaya ne bazasu gyara halayyarsu ba ,maihaifiya tace ina jin zafin abun amma jin zafina bashine zaisa a kyaleta ba,
Abba bai kuma cemasa komai ba suka tafi shida yan sanda dan arresting umma'ah.
waya ya kira daddy ya fada masa abunda yake faruwa ,shikanshi abin yadakesa kuma yazo masa a bazata da ace wani yafada masa ba fayyaz ba babu yarda ma za'ayi ya yarda"
Shima gidan ya koma kai tsaye ,koda sukaje gidan kinshiga fayyaz yayi ,
Yan sanda biyu suka shiga gidan cikin mutunci da sallamarsu,
A bakin falon da zai sada ka da cikin gidan suka tsaya sukace mai gadi ya shiga ya musu sallama da ita,
Bata kawo komaiba koda mai gadi yafada mata yansanda ne,
Gyalenta ta yafo ta fito tana tambayarsu lapia ko,
Ba lapia ba mai zafin ciki tabata amsa munzo arresting dinkine for being the master behind noorurrahman's kidnapping zaki iya kin magana dan komene kikace zaiyi amfani ne akanki idan mukaje station,
Inji uwarki nazama master ,
Umma'ah tafada cikeda fitina,to wallahi babu inda zanije sai lawyer na yazo,
Tana kokarin komawa taji muryar daddy dayake shigowa yace ai baki isaba sai kin bisu wallahi,
Duk yarda taso tirjewa haka aka buga mata ankwa aka tafi da ita,
Ai fayyaz baikuma shiga tashin hankaliba saida ya ga an Riko umma'ah an turata cikin motar yansanda,
Yana ganin daddy yana tahowa inda motarsa take ya tasheta ya bar gurin dan baisan mai zaice masa ba,
Yana tuki amma hankalinsa yana kan noorrurahman.
Tayama xai fara da ita.
Chu chu jay✍️
Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top