chapter 42

Norrurrahman✔

Juyowa yayi yace daddy wannan fa,
Dan tsaki daddyn nasa yayi yace kabari kawai imran wallahi wani maaikacin mu ne fayake tsohon mijinta shine dan rashin imani yasace ta har garinsu bayan sun rabu yaje yanata gana mata azaba shinefa Allah da taimakonsa ya kubutar da ita danma tana da fasaha shine ta garzayo ta kawo kararasa nan dan a koresa inaga shi kadaine zai wanke mata raunin da yayi mata a zuciya ,this kidnapping stuffs is getting out of hand wallahi "ehem anga matar fayyaz kuwa,

shafa gefan sajensa yayi yace ,A'a wallahi daddy bakaga yarda duk ya fita hayyacinsa ba saboda yarda ya saka abun a ransa anadai ta kan bincike ,wannan din yasunan mijin nata daddy yasake dawo da maganar noor "
Eh wai sunansa nasir umar dala ni sunan ma yayi mun sounding familiar amma muddin nayi bincike nagane gaskiya take fada zaa koreshine gaba daya saboda aje irinsu ba karamun anoba bane"

Shiru imran yayi kafun yace to Allah ya kyauta ya kara tsaremu daddy bari naje dama hanya ya biyo dani"
sallama yayi ma mahaifinsa ya fita a office din,yana fita yakira fayyaz yace kai yama sunan mijin matarka na baya,
Nasir yabashi amsa ,
In full fa".
Nasir umar dala wani abune "
DA Sauri imran yafita a bankin ko zaici karo da noor ,
Lapia fayyaz ya sake tambayarsa"

Yanzu haka ina office din daddy and tabbas naga noor dan side view dinta dai nagani amma da nashiga nake tambayan daddy yace karar mijinta da yayi kidnapping dinta ta kawo amma yarda ta bawa dad labarin ba haka yake ba shiyasa nake tambayarka,
Zumbur fayyaz ya tashi daga kwancen da yake yace imran duba mun kar ta bace maka dan Allah itace wallahi nama san itace"

Ai abokina ban ganta ba tunda na fito nake dubata ga dukkan alamu ta tafi,
Shit fayyaz ya fada yace to kaga bari naje gidansu nasan dole gida tayi amma idan kaga wani abun ka kirani dan Allah ,dif ya kashe wayar ya saka kayan sa ya fita ko sallama baiya kowa ba ya nufa gidansu noor,

Bangaren noor kuwa tana fitowa ta samu keke a wajen ta tsara saida ta hauma tace ga inda zai kaita,
Cire fake plaster din dake goshinta tayi sannan tayi murmushi tace nas nas ,bakai kadaine dan iskaba,
Na'am "mai keken ya tambaya jin ko dashi take ,
Bada kai nake ba "
Maida hankalinsa yayi kan tukinsa,
Tana sane lokacin da riyya tace zata fitar da ita tasaka kayan da sukafi kowanne datti wato kayan da aka kaita dasu duk da cewa kuwa riyya ta kawo mata kaya,
Farka hannun tayi lokacin da ta siya plaster dan karyar tata ta tafi da kyau,
Bata damu da karyar da tayi ba ita dai idan har bukatarta zata biya to kowa ma na duniya ya kirata makaryaciya,
Kai tsaye gida tayi,
DA sauri mai gadinsu ya bude kofar jin tace itace,
Hajiya noor kace ashe dai maigadin gidan alhaji ba karya yayiba ,
Gaishe shi tayi da dan murmushi a fuskarta, gidan ta shiga, bakinta dauke da sallama takarasa falon datagani a bude,
Jitayi an rugumeta gam gam kokarin kwacewa take taji muryarsa yana cewa "nayi kewanki sosai im sorry i couldn't be the one to save you I'm sorry ,nayi duk yarda zanyi amma ban taba cire hope ba,
Cikata yayi yana dubata yana cewa tell me nuna mun babu abinda ya sakemi ko,
Ganin yarda yake a rudene yasa tace masa calm down babu abunda ya sameni,kissing dinta yayi a goshi sannan ya kara mannata jikinsa kamar zai maidata ciki,
Gyaran murya muhammdu auwal yayi yace to ai dai akan bar halak dan kunya idan ni ka rainani bakajin kunyana amma ai kanajin kunyar sirikarka ko,
Sai a lokacinne yayi Realizing abunda yayi he couldn't help it,
Cikata yayi yana sunkuyar da kai yar dariya mami tayi wadda tunda taga abunda yayi tayi kasa da kanta,
Hawayene da suka taronmaa noor a ido suka zubo dagudu tafada jikin mami tana kuka,
Rungumeta mami tayi ajikinta tanajin wani irin dadi yana ratsata da kuka mahnaz tazo tayi joining dinsu tanace wa didi"
Dan gyaran murya muhammadu auwal yayi yace saura ni"
Janyosa fayyaz yayi yarda shi kadai zaijishi yace wallahi kar ka kuskura ka rungumar mun mata,
Dariya muhammadu auwal yayi shima cikin rada yace sannu masu mata ina tunanin kamanta kanwatace ko.
Haka Dai akai ta murnar dawowar noor wanka tace zatayi mami tace taje dakinta yananan babu abunda aka taba mata kuma yana datti mahnaz ke gyarawa.

Saida tayi wanka tayi sallolin da ake binta sannan taci abinci ,
Fayyaz nagama waya da imran ya kira muhammadu auwal dan jin ko noor ta zo gida amma yace masa a'a nanne yake fada masa abunda imran ya sanar dashi,
Shikuma ba bata lokaci ya kira baba ya fada masa,
Babu wanda ya tambayi noor abunda ya faru itama babu wanda tayima maganar a ciki ,jiran baba da Abba kawai take wadanda suke gaf da shigowa gidan duba da magreeb da akayi,
Haji fayyaz kuwa yaki tafiya kunyar mami yakeji shiyasa baibi noor dakinta ba amma ji yake kamar yatashi yabita wanda mami ta fahimci hakan
Bayan idar da sallah Abba da baba suka shigo gidan da zumidin ganin noor kar ma ace Abba wanda nashi ya fi fitowa fili ,lokacin da yake jin labarin cewa noor ta dawo gida yaso tafiya amma baba ya hanasa yace yabari suje a tsanake,
Hannu Abba ya budewa noor lokacin da ya shiga falon yace zo yarinyar abba ,babu musu taje dan haka take masa tunda kuruciya,
Kallonsu fayyaz yake kamar yace a sakar masa mata amma shi a wa yayi kadan,.
Zaki iya gane wanda suka kamaki ko suna ko gurinda aka kaiki,
Eh Abba bazan gane inda aka kaini ba amma abba wanda ya sace ni ba kowa bane face yaya nas da taimakon wata.
" nasiru ,
Abba da baba suka hada baki wajen fada ,mami kuwa batayi mamaki ba,amma yaron nan anyi dan iska wato duk zuwa jajen da yake kina hannunsa a kulle sannan wacece ke taimaka masa din,
Shiru tayi tana kallan fayyaz wanda yacee look noor ki fadi wacece kar kiji tsoro dukan mu nan mun tsaya miki your family are with you ,
Bansan waceceba amma dai nasan a family take ta tsinci kanta da fada saboda yarda idanun fayyaz suka mata nauyi,
Kallan Abba tayi tace Abba amma nasan idan aka kamashi zai fadi wacece,

Cikeda bacin rai abba yace yo zai wuce uwarsa aikuwa muddin nagane da sa hannunta a al'amarin nan wallahi bazataji da dadi ba ko kadan dan zataga abunda bata taba ganiba tattare dani tunda mukai aure ,
Fuu ya tashi ya tafi gida domin tarfa ummi da nas dan bai san noor taje gidansa ba ,
Falo ya tarar da ummi da uban tissue a gabanta tana ta kuka tana share majina,
Yana shiga ta taso tace kaji ko kaji abunda nas ya jawo mana ko,
Batanba sanin gatan da nake nuna masa matsala bane sai yau yanzu ga abunda ya faru noor takai kidnapping complain gurin aikinsa sannan gashi tace ya zaba ko yayi confessing ko ta yada a media bakaga rokan danake mata ba yarinyar nan ko kallona batayi ba sannan namasa nasihar akan yazo ya fadi gaskiya ko zai samu sassauci tunda abunan na gida ne amma ya zabi da yazama criminal on the run kamar yarda noor din ke fata bakaga yarda idanunta suka kekyashe ba dazu,

Ture hannunta yayi daga rikon da tayi masa yace look here woman bana san wata drama ai nasan komai kuma muddin na kamasa naji yace da sa hannunki ko sai kin bar gidanan sannan kici prison shikuma ko baije prison ba dakaina zansa akamashi a kaishi sannan noor kuma da ace bata kaishi kara gun aikinsa ba da kaina zan kaisa a koreshi,waya yafara kira a gabanta tayi mamakin jin yanacewa eh acp maganar kidnapping yarinyana da akekai an ganta sannan an gano wadanda sukayi kidnapping nata yaron gurinane nasiru dsn Allah inaso yanzu a kara securities duk junction yarda zakamashi gudun kar yabar gari,
Wani irin ihu tasa bayan Abba ya fita agidan  yana waya,binsa tayi tana cewa amma dai Alhaji baka kyautawa da nasir da noor waka haifa yanzu dan cikinka dan cikinka zakayiwa haka dan girman Allah alhaji kasake dubawa ,
Baikulata ba yafita a gidan yana maijin zafinta dan ita ta gaza a gurare da dama takasa bawa yaransu tarbiyya idan ba haka ba mainene zai bawa nas kwarin gwiwa har yakai ga dauke noor,
Koda ya koma ya shaidawa baba ya gudu baice komaiba sai shiru da yayi amma tabbas abun yayi masa zafi ,yaso ace sun zauna anyi abunan a gidaa amma yana ganin abun ya wuce nan,
Nan noor take fadan abunda ya faru da taje gun aikin nas shima dan taji muhammdu auwal yana tambayane mai yakaita gurin,
Da fada Baba yace wanene ya aikeki yin hakan yazaki masa wasa da career ,

Katsesa abba yayi ta hanyar cewa amma yaya naga yarinyar nan ita wasa yayi mata da rayuwa koda batayi hakanba ni zanyi sannan yanzu zankira babban nasu ai ina da numbersa na kara tabbatar masa da babu karya a azancentan,
Baba na kiransa amma ya fita dan kiran daddyn imran,
Shikansa yayi mamaki da ya shaida masa cewa shi mahaifin nas ne kuma ya samu number dinsa ne da dadewa gurin nasirun sannan maganar da matarsa ta fada dazun gaskiyane dan haka bai wani ja ba ya kira yace gobe 7 ayi issuing takardar korar nas.
Baima koma gidan ba dan ya kudiri niyyar wannan karan bazai saurari baba ba sai ya gurfanar da nas an hukuntashi.

Taso ta kwana gida amma da fayyaz ya nuna yanasan yatafi da ita baba ya bashi dama akace ya tafi da matarsa  yaji dadi dan yana da magana mai tarin yawa abakinsa,
Bata kulashiba koda suka dau hanyar tafiya gidan dan itama ta fahimci yanada maganar ne ita kuma abunda yasa taki fadar cewa mahaifiyarsa ce saboda idan sa ,taji nauyinsa sosai dan haka tafiso idan aka kama yaya nas yafada da bakinsa,.

Chuchujay✍️

Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top