chapter 41
Noorurrahman✔
Share hawaye riyya tayi ta kalli noor tace nagode ,
Babu wanda ya taba fadamun gaskiya mai daci irin wannan sai ke ayau kuma Allah shi kadai yasan irin ladan da zakisamu sabida yarda kikayi moving zuciyata rana daya, yau naji ina kyama da kunyar hallaya irintawa wadda a baya banajin kunyar kowa yasani amma yau kin nuna mun wata hanya wadda babu wanda ya taba nuna mun ita ko a cikin abokai na dan abokaina ma babu wadanda acikinsu zasuga kana abu mara kyau su hanaka tunda dukansu neman shiriya suke ,
Nayi wa kaina Alkawarin chanzawa kuma nasan Allah zai taimaka mun tunda har cikin zuciyata nakejin san chanzawan ,
Tashi tayi tace zan fitar dake a nan yanzu baki chanchanci abunda yake faruwa dake ba bari na san yarda zanyi da Daniel"
Tana kokarin fita noor tace"
Baki gudun ke kifada cikin matsala ni idan kika fitar dani"
Licking lips dinta na kasa tayi dan tabbas bawai batajin tsoro bane tanaji dan tasan nas sai ya kusa kasheta ta fitar da noor a gidan amma dole koma menene zai faru ta fitar da ita ,
Kar ki damu indai nice im okay babu abunda zai sameni,
Kada kai noor tayi tace okay"
Bayan minti uku da fitarta sai gata ta dawo tace yauwa taso na aikesa waje mika mata jakarta tayi tace gashi na daukone a dakin da nas ke zama,
Karba tayi ta rataya ta bi bayan riyya suka fita a dakin zuciyarta na mata wani irin dadi yau muddin tabar gidannan to kashin yaya nas ya bushe murus ,
Motar riyya suka shiga tare ta fige motan daga gidan da gudu kar Daniel ya dawo da wuri"
Sunyi tafiya mai nisa kafun noor tafara ganin alamun kwalta ,bata taba shigowa irin nan ba tunda take a rayuwarta saboda gurin irin shiru dinanne sannan babu yawaitar gidaje ,tasani tabbas da ace riyya bata taimaketaba to da Allah ne kawai zai fitar da ita ba dai mutum ba saboda babu wanda zai iya kawo nan gurin aka kawota ,
Saida suka hau titi sosai sannan riyya ta tambayeta ina zata kaina "
Gidansu yaya nas ta bata amsa ba tareda ta kalleta ba,
Maida hankali riyya tayi kan tukin da take tace gidansu kuma baki tsoro ma ,
Bani yi ta bata amsa cikin gajarcewa"
Bata sake cewa komaiba illa maida hankali da tayi akan tukinta,
Saida suka zo daf da shiga kan layinsu noor tace"
Riyya tsaya ,
Ba musu riyya ta tsaya da tambaya a fuskanta ,
Scrunching hancinta tayi tace idan yaya nas ya tuhumeki a tayarda na gudu kice na buga miki wani abune a akai lokacin da kika aiki Daniel na gudu ,idan akace ya akai Daniel ya dawo bai sameki gidaba tunda nasan yanzu zai iya komawa sai kice kinbi sahunane kiga ko zaki ganni ni zan sauka anan.
Tana kokarin fita taji riyya ta dafa mata kafada,
Juyowa tayi ta kalleta dan san taji lapia kuma,
Bata dauke idanunta akantaba tace noor be careful, ki kula and thank you,
Smiling noor tayi mata kawai kafun tace kema ki kula nagode
Make sure kin fadi abunda nace and yayi sounding real zaki iya hurting kanki kadan dan kara sakashi gasgata abun and karki damu bazan taba cewa ke kika taimakeniba,
Bayan rabuwarta da riyya kai tsaye gidansu nas ta nufa ,
Da mamaki baba maigadi yake kallonta ,
Noor kece nake gani haka"
Bata tsaya kulasaba illa wucewa ciki da tayi dan yau muddin ta tarar da shi gidansu akwai balai dan riyya ta shaida mata sunyi waya yace yana gida dan yanzu Abba ya dan sassauta masa"
Batayi sallama ba ta fara kwalla masa kira lokacin da tashiga falon tana fadin nasiru"
Ummi ce dake kitchen ta fito hannunta dauke da spatula
"
Da mamaki take kallon noor kafun tace 'a'a gudadda kinga barikin baci kindawo ko'
Sniffing tayii tace "
Eh ummi babuci shine na dawo amma inasan nasiru ya fito sai ya kara miki karin bayani a irin barikin da mukaje mukayi ,
Wallahi ummi gwanda kice masa ya fito dan wallahi bazai ci a banza ba akan abunda yayi ko su baba basu dauka mataki ba ni dakaina zan kaishi kara koto kuma mijina zai tsayamun wallahi sai na dauresa"
Sakin baki ummi tayi da mamaki tace ni kike gayawa magana haka noor ,
Sharrin uwartaki yau kuma kan nas ya koma to wallahi a hir dinku baku isa ba"
Batareda tsoro ko kunya ba noor tace eh nikaina ba dadi nakeji ba idan ina fada miki magana haka saboda a da ke din uwar mijinace sannan kuma bayan hakanke matar kawu nane da nafiso amma babu yarda zanyi saboda irin tarbiyyar da kika dora yayanki akai irin takice sannan kinsan ance idan babba bai ji nauyin hawa jaki ba jaki bazaiji kunyar kayar dashiba
And nasan ina fita zaki kira nasiru kice ya gudu to abunda nafiso kenan yazama criminal on the run yazama gurin zamama sai ya gagareshi baya gidan mahaifinshiba baya gidansa ba dan trust me when I say this duk inda nas yashiga a fadin kasarnan sai na sa an nemoshi sai gurin dazai zaunama a ko inane ya gagaresa dan bana tunanin kinada dukiyar da zai ta rayuwa da ita har ya mutu nikuma ina nan ina jiransa daga nan har inda numfashina zai katse yanzu kuma gurin aikinsa sai nasa an koreshi dan daga nan ko gida bazan jeba sai nafara zuwa nashigar da kidnapping complain,and nan da 24 hours kujira sakon korarsa and i will post it on media yarda reputation dinsa zai zama tarnish nangaba kinga babu mai basa aiki bare mata so the choice is yours KO kisa yazo yayi confessing ko kuma kisa ya gudu baidameni ba yanzu ni fitana zanje office dinsu and no one can stop me KO baba ne kuma ,
Juyawa tayi ummi nata faman kwala mata kira amma taki sauraranta sabida ta tsorata dan muddin noor tafara watsama duniya zancennan tayi ruining mata da"
Har baki gate ta bita tana mata magiya amma noor taki sauraranta sai ma cewa tayi da wannan magiyan gwanda ki koma kusamawa kanku mafita"
Tana fita ta tsari dan sahu Allah ya taimaketa da kudi a jakarta bai kwasheba ,
Baban branch dinsu taje, tadade kafin akayi approving taga babbansu Saboda irin kukan da ta ringayi musu rashe rashe"
Umarni ya bayar da abarta tashiga,
Babban mutumne kamili da yayi mata kwarjini,
Umarni yabatada ta zauna,
Zamatayi tace ina wuni"
Kallanta yayi na dan tsawon lokuta yana karantarta kafun yace lapia"
Tayaya zan taimakeki dan bansanki ba bantaba ganinki ba sannan bakida appointment dani ina fatan hakan da kikayi kinyisane akan babban dalili dan idan ba babba bane zansane akamaki saboda batamun lokaci da kikayi"
Ganin mutumin baisan nonsense ne yasata fara kuka tace kayi hakuri rankan ya dade ni macece mai rauni wadda tazo kwatar yancinta,
A bankin ,ya katseta,
Kasa tayi da kaita sake fashewa da kuka mai ratsa zuciya dan tanasone ya tausaya mata sosai,
Kada kai tayi tace a banki ranka ya dade
Banida inda ya wuce nan din da zaa kwatar mun yancina,
Nakawo karar staff dinkune wanda yayi kidnapping dina wajen sati uku kenan,
A da mijinane kuma dan uwana wanda aka kaini gidansu riko tun ina karama amma azabar yau daban ta gobe daban then bayan girmana ya nuna yana sona mahaifiyarsa ta goya masa baya ya aureni basan gaskiya bane ranka ya dade aurene akayishi na sha'awa naci wuya sosai a hannunsa sai Allah ya taimakeni muka rabu shine ranka ya dade har nama koma garinmu amma yaje suka sato ni suka ajeni suna ta ban wahala a gurinda yanzu koda bindiga bazan iya kai kainaba,Allah dai kadai yasa na kubuta to yanzu ranka ya dade ina zankai kara a kwatar mun yancina a Matsayina na takala mara galihu,
Da tausayinta yace to yanzu kinaso na tsaya mikine ki kai kara ,
Kada kai tayi da sauri tace A'a ranka ya dade so nake a koreshi daga kan aikinsa saboda nasan kaima bazakaso kimar bankinan ta zube ba dan daga nan ma gidan radio nayi zanje nakai kararsa sannan inason zanjene na fadi sunansa da aikinsa yarda duniya zatayi wadai dashi"
Saboda mai zan dau zancenki idan karya kikefa ,
Kara kasa tayi da kai tana kara marairaicewa tace saboda mai zan maka karya idan zan tuna a zancena nafada maka dan uwanane duk da shi yasamu rayuwa mai inganci ni ban samu ba haka bazaisa nayi masa bakin cinkin rayuwaba saboda aikinsa shine rayuwarsa amma ka bincika na tsinkayesa yana waya a lokacin da nake hannunsa da wani dan gurin aikinsu yanacewa dan Allah ya cigaba da yi masa cover saboda yanema lib na cuta kuma yana so ya cigaba dayimasa hanya dan yasamu yashiga cikin jaimanku dazaku tura turkiya suyi shekara,ranka ya dade bani da ilimi amma nasan cewa kunnena yajimun daidai kuma yanasan yaje turkiyyane saboda chan yakeso yatafi dani sai maihaifinsa ya gajida nemana tukunna,idan baka yarda daniba ranka ya dade kasa aduba maka idan har yana kan sik lib din da sauke fada kuma yayi sati uku wanda shine adadin satikan danayi a hanunsa ,ranka ya dade ka kalleni da kyau bakaga kayan jikina da dauda ba tunda naje sune a jikina sannan baka ga hannun a yageba daga hijab dinta tayi dan nuna masa amma ya hanata gefen goshinta ta nuna masa wanda yake dauke da bandage tace ranka ya dade kalli goshina sai hannunta da yayi ja dan har yayi alamun ciwo tace wannan hannun hankaf akasakamun a jikin gado gudun karna gudu,
Amma Allah da shike ba azzalimin bawansa bane sai gashi ma kubuta takarashe zancen da kuka,
Tausayinta yaji har ransa yace ya sunansa,
Da sauri tace nasir umar dala,
Kallanta yayi da tausayi yace zan bincike a kai and idan har abunda kika fada gaskiyane zaa koresa daga aiki dan bazamu iya cigaba da zama da shiba,godiya ta mishi ta tashi tana ta karamasa godia kamar yasata a aljanna tana kokarin fita a office dinne taci karo da wani Saurayi yana kokarin shigowa bakinsa dauke da dad,
Gefe ta juyar da fuskarta ta fita a office din while shikuma tana fita ya bita da kallo dan kamar ya santa duk da side view ne.
Chu chu jay✍️
Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top