chapter 40

Noorurrahman✔
Sakan baki riyya tayi da mamaki tace kai nas wallahi shegene kai ,
Yanzu dan balai yarinyannan tana gidan aurenta saida kasan yarda kayi ka daukota to how safe is this place ,
Very safe "
Yabata amsa,
Daukan car key dinsa yayi yace i will wire you the money,
Har ya fita ya dawo yace and yes riyya please no lesbian shit she's my wife and mine alone dan na dade da sanin kina da idanunki akan noor ,
Dariya tayi bayan ya fita tana wani kanne idanu tana cewa naji i won't force my self on her"
Tashi tayi dan zuwa gurin noor din bayan fitarsa,
Zaune ta tarar da ita ta juya ma kofar baya,
Tanajin alamun shigowan mutum ba dai ta juyo ba tace kayi duk yarda kaga dama yaya nas just know that evil will never win"
Jin an dafata ne kuma ba da hannun namijiba yasa ta kalli hannun taga yasha nails da jan farce ba wani kyau bare tsari ,
Juyowa tayi ,batayi mamakin ganin riyya ba ture hannunnata tayi ,ta tashi tana kokarin mikewane taji ta koma sakamakon jin hannunta a rike ,tsaki tayi ta juya batareda ta tanka ta ba.kujerar da nas ya ke zama idan ya shigo dakin ta jawo ta zauna ,
Kallan noor take batace dai  komai ba,
Tsaki noor tayi tace wai lapia zakizo kisakani a gaba kina kalla kamar kin
ga tv"

Murmushi riyya tayi tace ai kinfi tv baby"
Karki sake kirana baby noor tafada cikin takaicin riyya dan ba tun yau tagane cewa riyya nada shedanin neman mata yan uwanta ba ajikinta"
Hannu riyya ta kawo zata tabata ,
Kwade hannun nata tayi da free hand dinta tace karki kuskura ki tabani da kazamin hannunki da yaji wadannan farcen zakwazakwa,i wonder how you wash up shit"
Dariya irinta wadanda suka dade a iskanci riyya tayi tace mai zai hana na nuna miki,
Tasowa tayi tana matsowa inda noor take, matsawa noor tafarayi tana ja da baya tana cewa"
Bana san iskanci ,idan kina fama da dabbancine to ni nafiki hauka wallahi zan maki illa"
Batadaina matsowa inda take ba itama bata daina matsawaba har saida ta kasa saboda hannunta dayake kulle,
Dariya riyya tayi tasa key ta bude lock din handcuffs din dan dama shi take san ta bude mata din amma tayi teasing dinta in the process ,
Nas yayi tafiya mai muhammanci so yabani ajiyarki na sati so i can't handle seeing you a daure and yes tun ranar dana fara ganinki zuciyata take saka mun abubuwa da dama akanki dan kin hadu amma ni da kikaganni inayin abune da tunani bana forcing kaina a mutum sai da yardarsa so babe chill im not a nasty lesbian"

All lesbians are nasty bitch"
Noor tafada cikeda kyamar riyya "
dariya riyya tayi tace but I might not be that nasty you think ,
Zaki iya fita falo ko kallone kyayi,
FIta riyyan tayi tana cewa idan kina bukatan wani abu  you're free "
Zama noor tayi tana sake taba hannunta da yayi ja.
Alwala tashiga tayi ta dawo tayi sallah,

Bangaren nas kuwa kai tsaye gurin baba yaje ,
Har falonsa ya shiga ya zauna ,gaishesa yayi baban ya amsashi batare da nuna masa wani abuba dan har ga Allah shi bai rike nas din da komai ba,
Kasa yayi da kai yace baba kuma sai naji magana mara dadi farhana take sanar dani wai ba'a ga noor ba "
Kabari kawai nasiru abune yanzu mutum baida shaidar wanda zaiyyi masa amma insha Allahu za'a ganota nan ba da wani dade waba mudai fatan mu da adduar mu Allah yasa karsu cutar da ita kafun a cimmusu and insha Allahu this will be the last mutum dazasuyi kidnapping dan i will make sure an basu punishment daidai laipinsu"
Kada kai nas yayi cikin yar fargaba yace to baba Allah dai ya bayyana noor dukda ni mai laipine kuma mai san zuciya gareta amma tabbas banasan wani abu da zaizo ya cutar da ita sabida ai duk inda akaje aka dawo noor din jininace"

Hakane malam nasir adai ta tayamu da addua Allah ya bayyana mana ita cikin aminci".
Sallama yayiwa baba sannan yaje gurin mami yayi mata jaje ,
Tareda nuna alhininsa sosai ,
Yana kokarin fitane sukaci karo da muhammadu auwal kokarin wucewa muhammadu auwal din yake dan baya tunanin akwai sauran magana tsakaninsa da nas ,
Kamosa nas yayi yace haba dan uwa mai yayi zafi Allah mafa muna masa laipi ya yafe mana to mu mutane suwanene,
Nasan na tafka kuskure da yawa amma ai dan adam ajizine kuma ni na tuba ,yanzu haka bakaji yarda nake jiba da ace zanga wadanda suka dauke noor ni zan yarda su daukeni ita su saketa koba komai ada noor matatace amma kuma a yanzu ai yaruwatace kuma babu abunda zai iya sake wannan alakar"
Dan kallansa muhammadu auwal yayi na yan mintuna kafun yace Allah ya yafe mana baki daya nas,yana fadan haka ya shige gida yana duba wayarsa da aka tura masa sako,
Bayan gama karanta sakon da aka tura masa ne yaga kamar message daga noor,
Kwatakwata shiba ma'abocin shiga inbox bane shiyasama bai gani ba ,
Da sauri ya shiga ya ga sakon dayake dauke da "i need help"
Gidan ya shiga inda nas ya bar Mami nan ya tarar da ita fada mata abunda noor din ta tura masa a ranar da aka dauketa yayi fada ta fara tana cewa da tuntuni mai ya hanaka dubawa da ba tuni anyi locating dinta ba ,
Zama yayi kan kujera yace wallahi mami ban gani ba kinsan bazan taba ganin sako irin wannan daga gurin noor ba nayi ignoring yanzu haka daga gurin da ake tracing layin nake anfara tracing kuma ya katse amma hanyar getse ya nuna"
Juyowa mami tayi ta kallesa tace getse kuma ,
Eh Mami amma munyi waya da fayyaz na fadawa mishi za'a kara tsaro a guraren"
Cike da rashin karyewa mami tace insha Allahu zata bayyana babu abunda zai sameta inshaAllahu...

..
Duk wasu jami'ai da suka chanchanta ansaka domin samo noor amma abu ya gagara dan har anshiga sati na uku babu noor babu duriyarta ,to abinka da na gida duk wani cigaba da za'a samu sai komai ya ruguje sakamakon wadanda suka dauketa din na gidane kuma sunsan duk wani shige da fice ,
Abba yayi baba,daddy, muhammdu auwal sannan uban gayyan fayyaz,
Kallo daya zakama fayyaz kasan cewa yana cikin matsananciyan damuwa sabida gaba dayansa cikin sati uku kawai ya kare ,
Bashida abu sai neman inda zaiji labarin noor ,
Shikadai zai zauna a daki yana hawaye masu zafi dan bai san halin da noor ke cikiba shin tana ma da rai"
Duk wani abu da zaiyyi dan ganin ya saka ta a ido yayi amman abu ya ci tura,
Bamashi da lokacin da zaici abincin da zai koshi zai dai cine kawai dan yasamu karfi nemanta wanda haka daddy ke yawan fada masa "idan bakaci ka koshiba taya zaka samu strength din neman noor "
Zaman gidansu ma ya gagaresa dan gani yake zama gidan shi kadai bashi da amfani,
Yauma kamar kullum ya shigo gidansu kansa na masa ciwo,
Udaysah ya tarar a falo tana zaune tayi jugum,

Kiran sunanta yayi yace dan Allah taimaka mun da sudrex a dakin daddy mana ,
To tace ta tashi ta tafi dakin daddy dan dauko masa maganin,yana bata tausayi sosai dan ita kanta ta shiga wani hali na rashin sanin halinda noor take ciki,
Kwance taje ta tarar dashi idanunsa arufe ,
Aje masa maganin tayi da glass cup din ruwa tace brother ga maganin ka tashi kasha,
Alamu yayi mata da hannu kan taje kawai,bata masa musu ba ta aje maganin ta fita cikeda tausayinsa ,
Baisan lokacin da bacci ya daukesa ba bayan ya sha maganin.

***************************************
Tunda nas yasa riyya tazo ta zauna agidan sau biyu kawai yazo saboda yarda umma'ah ke gargadinshi a kullum akan ya kiyaye ,
Zaune take kamar kullum a cikin dakin da aka ajeta duk da cewa riyya ta bata dama ta ringa fitowa falo amma bata jin iyuwar hakan,
Har yunkurin guduwa tayi amma murtukaken shegen maigadin nas ya kamata,
Sosai riyya tayi ta mata fada akan abunda tayi,
Kallan riyya tayi tace to menene dalilin da zaisa na zauna ba tareda yin yun kurin cetan kainaba ,ke ya zakiji idan aka miki irin haka,
Ina da aurena and nothing can change that ke mace ne duk da nasan ba lallai kiji ciwan ya mace kamar yarda kowace ya mace zatajiba amma kisani wallahi bazan yafe muku ba saboda a cikin wannan abun an cutar dani kuma Allah baya barin mai cutarwa ,
Bayan ta kai ayane tace mai ma yasa nake miki wannan dogan sharhin after all keda yaya nas dukkanku babu na kirki"

Knocking taji an mata a kofar dakin da take ,
A fili tace ko wane irin saban salan ne wannan kuma oho"
Yar dariya riyya tayi ta shigo dakin da sallama ta zauna ,
Dauke kai noor tayi dan tana kyamar mai halayya irin ta riyya sosai,
Dafa hannunta taji riyya tayi kamar wuta ta tabata haka tayi saurin ture hunnunta,
Murmushi ta kuma yi tace""noor kenan bazan fushi ba duk abunda zakimun after all nasan duk wanda yasan mai yake zai kyamaceni din kamar yarda kikeyi,
A dan zamana dake na koya wasu abubuwa da yawa wadanda ke bakisani ba,
Baki wasa da sallah duk da halin da kike ciki amma ni fa tana daya daga cikin abunda bana maida hankali akai,
Sunana riyadah sannan iyayena mutanen adamawa ne ,narasa iyayena sakamakon wani hari da aka kai mana muma da kyar muka sha,
To a haka wata hajia ta taimakemu  babbar macece a cikin harkannan ta neman mata,
To komai namu itace dan munkai mu 20 to a haka ne tafara shigar damu cikin harkar tayyada zamu karbeta hannu biyu sabida duk wani tallafin da take bamu ta janye ,dan dole muka yarda da kudirinta tana kaimu gun manyan mata tana samun makudan kudi,
So sai tsautsayi ya fada mata aka kamata da cocaine dan haka dole taje prison,
Daga baya duk sai kowacce cikin mu ta kama gabanta dan na abinci ma nema yake ya gagaremu saboda babu hanya dan duk matan da take hada mu dasu anayin komai ne ita kadai zatasan inda suke ,tsakaninmu dasu sai dai su kama hotel sugama abunda zasuyi su saukewa hajiya kudi a account,
To ayawona na bariki ne na hadu da su nas da kawata mama wadda ta bani guri nake zaune,
Kince dukkan mu ba na kirki,to yau zan nuna miki dan muna bariki bashine yake nuna bamu da kirki ba nima da kike kallona rayuwar da nake bata mun dadi,
Zan fitar dake daga gidannan ki koma gida ,
Kallanta noor tayi batace komai ba tana juya maganarta a cikin kwakwalwarta kafun tace ,
Allah baya daurawa bawansa irin wannan jarabtar ta lesbianism saidai idan shi zai biyewa shaidan ya dorawa kansa ya kuma kawatar dashi,
Akwai hanyoyi da bawa zai rufawa kansa asiri basai yabi hanyar sabon Allah ba ,idan kinaso ki gyara zaki iya saboda shi Allah gafurur rahim ne kaji tsoransa ki tsarkake zuciyarki kuma kiyi tuba bana muzuru ba ki gujewa duk wani abu da zaina jawo maki jin san kusantar yaruwarki mace ,misali chatting din batsa da yar uwarki mace ko zancen banza duk lokacin da kuka hadu ko kiringa kawata wa kanki jikinta kiji kina sha'awarta ,ki gujema kallan finafinan batsa wanda yanzu anyi normalizing hakan ,waiyazubillah"
Kiga babu wanda zai kyamaceki saboda dama ai halayyarki ake gudu bakeba,
Ki yawaita lazumtar"
"Allahummahgfir zambi wa tahhir kalbi wa has-sin farji(oh Allah forgive my sins,cleanse my heart and guard my chastity )
Ki lazunceta duk bayan sallah kigani,
Allah zai tsareki daga aikata zina da duk wani porn addiction da kike fama dashi.
Sannan ki tsaida ibadarki dan itace ginshikin komai.

Chu chu jay✍️.

Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top