chapter 34

Noorurrahman✔

Ganin umma'ah cikin dakinsa bakaramun
fadar masa gaba yayi ba dan shi har ga Allah yana tsoran fitinarta gashi daddy yace muddin yana san noor to yazama dole yaja bakinsa yayi shiru har a daura masa aure,
Baiso hakan ba amma babu yarda zaiyyi dan har ga Allah yana san noor baya tunanin zai iya rabuwa da ita gashi kuma on the other hand umma'ahn sace wadda baya kaunar fushinta ko daidai da kwayar zarra"

KO kar na shigo ne naga kana mun wani irin kallo fayyaz,
Rufe system dinsa da yake aiki yayi yace a'a umma'ah haba kema kinsan babu yarda zaayi nayi refusing dinki kawai nayi mamakine sabida naga kin kwana biyu baki shigo dakina ba,

Shigowa tayi ta zauna kan cushion tace to yaya za'ayi na shiga dakin wanda bayajin maganata.

Tasowa yayi daga gadon dayake ya dawo kan cushion din datake ya rike hannunta tareda shagwabe fuska yace umma'ah bafa kin maganan ki nake ba kawai dai umma'ah nane yanzu bata sona bata san abunda nakeso and it hurts alot .

Uhm ni fayyaz bantaba kin abunda kake so ba sai wannan karan kuma shima kasan ai da dalili haba baka taba aure bafa sannan kasan yarda nake da burin aurenka sannan ace rana tsaka kace zaka auri wadda ta taba aure"

Kasa yayi da kansa dan bayajin dadin kiyayar umma'ah din ga noor dan kawai ta taba yin aure ta fito ,
Amma umma'ah idan nace miki noor ce rayuwa ta fa"
Wallahi inasan ta sosai irin sanda ban masan da shi ba dan Allah umma'ah ki rufa mun asiri ki bani blessings dinki"

Tashi tayi cikin fushi tace sai kuma kayi tayi ai yaro,sannan inajin wani kishin kishin na cewa daddynka sunje gidan su noor ,
Fayyaz don't outsmart with me dan dukanku bazakuso fushina ba nafada muku"

Umma'ah aikam bakiji daga bakin source din gaskiya ba "
Yaso fada mata amma ganin cewa zata masa danja yasa dole yaji maganar daddy yaja bakinsa yayi gum.

Fita tayi tana kada kai"
Allah yasa"

Ajiyan zuciya ya sauke ,
Huh umma'ah I don't wanna do this but I will have to ,
Forgive me"

***************************************
A cike masallacin umar bin katab yake ,kowane musulmi kagani yabada dukkan nutsuwarsa ne wajen karbar sallar juma'a.
Bayan idar da sallah ne mutum uku suka bada sanarwar daurin aurensu cikinsu kuwa harda Abba"
Bayan anyi guda biyun da suka rigane aka daura auren NOORURRAHMAN MUKTHAR DALA
DA
FAYYAZ UMAR SARAKI"
Inda aka daura aka shaida da ya biya sadakinsa na naira dubu dari da hamsin"

Bayan an gama daura wane aka rarraba alawa da goro ,kowa da ya hallarci gurin nata sanya Alheri da yima mauratan fatan zaman lapia da zuria dayyiba"

Kallo daya zakayiwa ango fayyaz wanda yake cikin farar getzner wadda taci dinkin babbar riga kasan yana cikin dumbin farin ciki dan bakinsa gaba daya yaki rufewa,
Zungurarsa imran yayi yace ango kadan ringa rufe bakin dan Allah kar kowa yasan cewa saban shigane easy mana"

Bai kulasaba dan yau duk iskancinsu bazai kulasu ba"

Bangaren amarya kuwa tunda su baba suka dawo aka shaida mata andaura taji gaba daya bazama ta iya fasalta irin halin datake cikiba,

Kiran ta baba Alhaji yayi,
Hijab dinta tasaka ta tafi falon baban"
Tare ta tarar da baba da Abba,zama tayi tagaishesu cikin ladabi ,
Baba ne ya fara magana ta hanyar cewa ,
Noor Allah yayi maki Albarka ,
Bani da wani abu a rayuwarnan da zan miki fiyeda saka miki albarka"
Ke yarinyace ta gari sannan mai bin maganar iyayenta ,munyi miki ba dai dai ba amma insha Allahu ni inaji a jikina cewa karshen matsalarki kenan sannan biyayar da kikayi abaya wadda bata biyaba amma karki damu ba dole sai a abunda kayi biyayya bane zakaga ribar ,a wani guri daban zakaga ribar abun sannan insha Allahu a wannan auren zakiga ribar biyyar da kikayi abaya ,
Hajiya kaka ta kira dazun kafarta ce tamotsa
Shiyasa bata samu damar zuwa ba amma duba da abun bana farko bane yasana sanar da ita bama sai ta turo ba tunda bawani taro da za'ayi a gidannan insha Allahu Abbanki da kanshi anjima zai kaiki har dakin mijinki,
Kiyi hakuri kiyi biyayya wadda nasan kina daita amma ki kara akanta ,
Kiyi hakuri a zaman da zakiyi na aure sabida shi aure da kika gani Dan biyayyane ,kizauna da mijinki da yanuwansa lapia,
Ki girmamma yan uwansa ,
Kizamanto mai yi masa addua da shi da iyayensa da naki baki daya,
Ki rike addua dan itace makamin mumini,
Ki rike azkar karda kiyi wasa dashi ,
Wannan ba auren ki ne na farko ba duk abunda zan fada miki tishi ne,
Allah yayi ma auren ki albarka ga abbanki nan nasan shima zai miki dan jan kunne"

Ni ai yaya duk wani abu da zan fada ka rigada ka fada,
Ina cikin farin ciki mara misaltuwa wanda banma san tayaya zan fara kwatanceba ,Allah ya baki farinci mai karko noor,
Ke ta daban ce ,Allah yayi miki albarka'
Ta shi kije,
Boye hawayen da yake saukar mata afuska tayi ta fita a falon tana jin kaunar iyayen nata,

Dakin mami tashiga direct ,
Zaune ta tarar da muhammadu auwal a dakin wanda daga gani wata muhimmiyar magana sukeyi ,

Kallansa ya mayar kan noor yace um su o '_o anyi dodar kamar ba itaba ,
Dan dariya mami tayi tace kaidai baka rabo da tsirku,
Ita kadai tasan gyaran da tayima noor din duk da kuwa a sati dayane, dama chan bata sake da bama yaranta dan abunda bazai cutar dasu ba "

*******
Cikeda balai ta kalli sweet din da goro da dabinon da daddy ya aje kan gadonta tace "
Daddyn fayyaz nifa kamar banji abunda kace ba kace ga kayan daurin auren fayyaz ,wanne fayyaz din,
Kuna da wani dan uwane fayyaz a cikin garinnan"
Murmushi yayi yana cire babbar rigar dake jikinsa yace fayyaz dai naki yau aka daura auransa da bazawarar nan da bakiso,Alhamdulilah bakiga yarda daurin auren yayi jama'a ba dadin daurin aure ranar juma'a kenan"

Katainnan ".
Wata dariya tasaka tace niko nidai akayi wa haka ko ,
Ni kalthume ,.akayiwa wannan cin kashin to wallahi da fayyaz din da ita kanta yarinyar sai sunci uwarsu "
Habawa umar mantani kai,.
Sai an gane anmun ba daidai ba,.udaysah kuma kamar ya aureta ya gama ne zakace nafada maka kuma duk wanda yaci tuwo dani ai miya yasha kuma mata dai bai isa ya kawota gidannan ba"

Dan murmushi dadi yayi yace eh bazai kawota nan ba dama kinsan yaran naki akwai kokari ai ya siya gida a nan
Evans estate ,
Bakiga gidan ba gwanin sha'awa,
Ga estate din abun kyau sai ma kinje,
da yayi niyyar kaimune amma kikace baki yarda da aurenba to dama bai gama biyan kudin ba sai na dauke masa lefe dayake iyayen ta ba masu san bidia bane sunce ya bar lefen ma amma bazasu hanashi yimata kayaba amma yayi mata idan taje gidansa bakiga yarda aka cika mata akwatuna da kaya masu kyau da tsaba wane wata budurwar kedai abun ba'a magana sai kin gani "
In ta kaice miki ma anjima kadan za akai mai ita gida, bazawara da saurayi abun gwanin dadi ,shima zuwa goben yazama bazawari dan ya tashi a saurayi,Allah dai ya dauke musu idanun makiya amiin"

Bata kulashiba dan idan tayi magana zata ita sako ashar kuma last abunda zata ma maigidan nata kuwa shine zagi ,
Kamar guguwa haka ta tashi ta fita a falon ranta kamar gawayi indai itace to wallahi aje zuwa zata rera masa irin wakar da ya rera mata lokacin da ta raba fayyaz da noor.
Kuma shima fayyaz din zaizo ya sameta"

A falo ta tarar da udaysah tana shan chocolate,.wani tsaki tasaka mai karfi,
Juyowa udaysah tayi tace A'a honorable umma'ah waya tabaki"

Uwarkice dijen sudan dan ubanki"

Fuuu ta shige daki inda udaysah tasa dariya dan tasan akan auren da ta tsinci Labari yanzu umma'ah din ke fushi"

..
DA yamma guraren karfe hudu da rabi abba  ya dauki noor a motarsa dan kaita dakin mijinta ,tasha kukan rabuwa da gida ga kuma rashin jin dadin cewa auren da ta fada ma iyayenta dan soyayyane ba haka bane sannan idan ta tuna nan da wata 5 ko 6 zata dawo musu gida sai wani rashin dadin yasake kamata musamman idan tana tunanon irin farin cikin dake tattare da su akan wannan auren .
Amma komai ya yafaru yana da dalilinsa sannan tasan solution zai zo mata kamar yarda solution din auren yazo mata "

Abba ya shigar da ita har cikin falan ta bayan ya umarceta kan ta shiga da bisimillah"
Nasiha ya kumayi mata sosai kafun ya tafi"
Bayan tafiyarsa ne udaysah tazo wadda fayyaz ya sa tazo a boye ba tareda sanin umma'ah ba dan tunda muhammadu auwal ya sanar masa noor fa ita kadai aka kai ba kawaye dan haka yasa ya tura udaysah".

...............

Wayyo nasiru ,
Teamnas kozo mu koka "😪😪
Duk da nasan nas jarumine zai kwato mana noor dinmu😪😪

Chu chu jay✍️

Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top