chapter 33

Noorurrahman✔
Juyowa tayi hannunta akan kuncinta inda marin ya sauka so take taga ubanda ya mareta a cikin gidan ubanta"

da mamaki ta kalleta baki bude tace menene dalilinki"

Sorry shine abunda tace kawai tare da kasa da kanta "

Sorry for what?
Ta tambayeta cikeda mamaki "

Ta bude baki zatayi magana ta hango fayyaz yana takowa tabayan fayyaz"
Sharar kwalla tafara tace"
I just hate you no or,na tsaneki a rayuwarki baki taba san cigabana,
Kullum bakida buri da ya wuce ki rabani da abinda nakeso tun muna yara ,
Har yanzu wannan halin naki bai chanza ba sannan fayyaz dinma da kikaga and da kiksan yarda kikai kika rabani dashi nayi hakuri amma yanzu bazan jureba kinsan cewa ai yaya nas nada HIV and kuma ke matarsa ce babu yarda Za'ayi kice bakidashi nan bakina da naki kikace sai kisama maza ishirin"

Baki ta rike hawaye ba bin kuncinta wanda batasan zuwansuba ,
Ba marin ko kazafinne yayi mata zafi ba a'a wanda yayi "

Jawo noor baya fayyaz yayi ta dawo kusa dashi sosai kafun ya kalleta yace bany wacece wannan din".

Jan hancinta tayi tace FARHANA idan wannan wani wasane kikeyi ki bari sabida its not funny at all ,

Babu wasa AI a zancenta munafuka ,
Atare suka maida kallansu kan yaya nas da ya shigo yana wani irin makirin murmushi"

Eh kinsan ai inda HIv din nasani kinsani amma kika kife ciki sabida kedai muguwa ce"

Chukumo ta farhana taje zatayi aa fayyaz ya turata bayansa ya dauketa da mari"
DA wani huci nas ya yo kansa amma sai yaji anrikosa ta baya"

Muhammadu auwal ne wanda duk abunda ya faru a idanunsa dan ya biyo noor ne yaga tashiga gun fayyaz din ko bataje ba jira yake yaga gudun ruwansu.

Cikani muh kanagani ai marin farhana yayi how dare he ,

Da bacin rai muhammadu auwal yace ka godewa Allah shi ya mareta bani ba dan dani na mareta zata iya daina gani wallahi,
Shasha mahaukaci sakarayi wadda batasan inda yake mata ciwo ba ,
Fada ba sai ya dawo tsakanin nas da muhammad ba "
Fayyaz na kokarin rabasu baba da Abba da suka dawo gidan dan cin abinci tare kasancewar ranar jumaace,
Da mamaki suka tarar da yarannasu suna dukan juna kamar yara fayyaz yana kokarin raba su inda noor babu abunda take sai kuka farhana ma kukan take amma nata yafi karkata ga zagin da muhammadu auwal yayi mata"

**************************************
Zazzaune suke a falon baki ran kowa a bace karma ace muhammad su yayi a barshi ya karya nas dan dama acike yake dashi"

Zaku iya mana bayanin abunda ya saku fada cikin gida gaban kannen ku kamar yara kai ko yara da masu nutsuwa bazasuyi and abunda kukayiba"

Fayyaz ya zayyane musu abunda ya faru, cikeda mamaki abba yace yaya akai bamusan kana da sida ma nasiru sai da auren noor ya taso,

Eh Abba ai shiyasa naso ta dawo gidanta mucigaba da rufa ma juna asiri tunda tasan ina da ita kuma itama tana da ita

Kuka noor wadda tunda suka shigo dama take sharar kwalla ta fashe da tace wallahi Abba karya yakeyi kawai baya sona da Alheri ne wallahi karya yake ni bani da Hiv"

Fayyaz da tunda aka fara abun yasan da burbushin karyane ya katse noor ta hanyar cewa ai baba bana ganin akwai matsala sai ayi gwaji tunda abun yazo da haka shi malam nasir yace yana da ita sannan koda noor tana da ita ni zan aureta na dora ta kan magani har ta warke dan yanzu zamani ya cigaba idan kanashan magani kan ka'ida kana warkewa.

Kana nufin zata shafa makane kaima ka hau kan magani nas yafada  cikeda jin haushin fayyaz"

A'a ba haka nake nufiba malam nasiru zamu kiyayene ni zan iya jira har ta warke sannan idan ma na diba ai ba komai zamufi shan maganin a kan kaida".

Baba ne yayi gyran murya yace kamar yarda fayyaz yayi suggesting aje ayi gwaji haka zaayi dama dole zasuje suyi na genotype da hIv din duka sai a aje ayi ran monday,

Cikin ladabi fayyaz yace ai baba ko gobema zaaiya yi akwai abokina yana da asibitin kudi sai muje tunda abun yazo cikin gaggawa in yaso ran monday sai ka tura mu gurin likitan da ka yarda dashi tunda wannan dai abokinane"

Cikin yaba hankalinsa Baba yace idan da inda za'ayi din goben ai sai ayi and na yarda da kai wanda zakuyi ma ai zai wadatar
Kushirya goben sai kuje da muhammad auwal.

Banda ni zaa nas ya tambaya yana faman zare idanu,

Eh banda kai ,idan mukasamu ita lapiayarta kalau kai chan kaje ciwan ya kashe ka,Abba ya bashi amsa sannan ya maida kallansa kan farhana wadda tayi tsamo tsamo tana dana sanin shiga wannan abun yace ke kuma zakiyi bayanin inda noor tafada miki tanada sida muddin akaje akayi gwajinan bata dashi "

Kutshi kuje"

Duk yarda fayyaz yaso su gana da noor amma yaci tura dan taki yarda babu abunda take a dakin mami sai ruzar kuka tana cewa mami ni farhana zatayima haka i can understand when it comes to yaya nas amma mami farhanaa mai natabayi mata,
Rarashinta mami take akan Allah na tareda mai gaskiya ,

Tsaki muhammadu auwal yayi yace a haka zan aureta,
Allah ya kiyaye wallahi koda mata zasu kare bazan auri wannan yarinyarba ballagaza.
.

Koda farhana ta koma gida kuka ta saka wa ummi wadda ke cewa ke meye hakan an dace ko ba'a dace ba ai wallahi noor bazata sake aure ba idan ina duniya ke ko na fari bakiyi ba,

Kukan tacigaba tace ummi nidai keda yaya nas kun cuceni dan sauran mutuncin nawa ma da yaya muh din yake gani ya bare bakiji zagin da yayi mun ba ni wallahi da nasan cewa haka zai faru tun farko bazan shigaba ke kanki kinsan dan kince zakisan yarda zakiya yaya muh ya aurenine yasa na muku abinda kukeso amma aikinsa noor bata chanchanci na mata hakaba and addition to this Abba yace sai na gane korena idan aka gane karya nake"

Wani kukan ta sake rushe wa dashi,

Tsaki ummi tayi ke ar koda ace sun dau mataki at least ansawa mai auren nata shakku kedai kawai ki zuba mun idanu"

.........

Washegari da wuri fayyaz ya shirya cikin black kaftan wanda suka dada fito da haskensa sosai kansa kuma dauke da bakar hula
,saukowa yake daga kan steps yana daura agogon sa a tsintsiyar hannunsa ,
Ciki early morning masifa ya jiyo muryar umma'ah a bayansa tana cewa gidan uwarwa zakaje"

Juyowa yayi yace umma'ah kinsan fa ni yawo ba abuna vane zamuje daurin auren cousin din imran ne fa ,

Um kada kai tayi
Kaje ka dawo Allah yasa abunda nake jin kishin kishin ba gaskiya bane dan idan gaskiya ne wallahi daga kar daddyn ka gidannan sai yayi muku zafi ,

Rabesa tayi ta wuce tana kwalama udaysah kira,

Koda yaje gidan su noor already sun riga sun shirya shi kawai suke jira ,

Dan satar kallan noor yake wadda tasa nikaf sannan tasaka bakin shade wanda yana gani ya tabbatar masa tasha kukane"

Fakar idanun muhammad yayi ya riko hannunta ya murza a hankali in a way of comforting someone ,

Wani hawayen taji ya sake zubo mata da sauri ta janye hannunta lokacin da sukajiyo muryar muhammad yana cewa tsintsaye inada abunyi yau dinan fa kuzo mu wuce kunyane ta kama noor amma fayyaz kuwa ko ajikinsa sai cewa yayi kabarni na lallashi matana please,

Shigewa motan tayi da sauri tana jinjina rashin kunyansa,

Lokacin da suka ida asibitin kai tsaye office din dr saleem suka shiga da jagorarsa ,
Salim da yake kallan katafaren window dinsa da yake basa view din garden yana sipping black tea ne a hannunsa yace na dai fada maka kadaina shigo mun office bakayi knocking ba kar dai kayi mugun gamu wataran,
Batareda ya juyoba dan yasan fayyaz dinne basai an fada masaba,

To dan iskan likita tareda sirikina da matata nake sai ka kame bakinka ,
Kwarewa yayi jin yace sirikinsa dan har ga Allah ya dau mahaifin noor ne
DA sauri ya juyo yana aje cup din yana ina kwana,

Dariya sukasa harda noor da take cikin nikaf,
Tsaki salim yayi yace baka hadu ba,

Mikama muhammad hannu yayi suka gaisa sannan ya kalli noor wadda fuskarta ke rufe ,
Amaryar mu hala ana mana rowar fuskarne to babu komai zamu zo har gidanne,

Kaga kamana abunda ya kawomu ina daya dan isakan gynecologist din ,
Wai imran ai yau bai shigo ba kasan dai dole muke zuwa weekend din yanzu dai muje lab ,

Awa daya da rabi suka dauka aka kammala komai aka basu result ,

Bawanda ya bude daga nata har na fayyaz dan yace zaifi kyau akaima su abba su bude ,
Hakan kuwa akai ,
Hankalin kowa atashe karma ace abba Addua yake Allah yasa karyane dan idan yazama gaskiyane bazai taba yafewa kansa ba .

Bude result din fayyaz baba ya fara yi yace
,babu HIV,
Blood group O
Genotype AA
Na noor ya bude wadda sai da gabanta ya fadi duk da kuwa tasan komai karyane ,

Blood group,
b+
Genotype
AA
Babu HIV"

Hamdala Abba yayi wadda sai da yafito fili sanann ya kalli nas da yayi tsuro tsuro yace dan ubanka kai kadai kake da kuma kai kadai zata kashe,

Nima dai to zancen gasakiya banda ita din Abba
Kawai dai dan siddabarune da dabaru "
Dama dan amayarmun da matanane kuma wallahi sai an bani matata"
,salati Abba yasa yayi kansa har yana kokari faduwa,
DA sauri baba ya tarosa yana cewa kar ka illata kanka umaru akan yaro,

Kasa yayi da kanshi yace yaya wallahi kunyarka nakeji nakasa baaa yarana tarbiyyar da ta kamata ,
Kallansa ya mayarkan farhana yace saura ke ,
Kuka tasa tayi bayan kujerar Baba Alhaji tana cewa Wallahi Abba ummi ce ta sani tace wai zatasa na auri yaya muh nikuma sabida ina sanshi yasa nayi"

Aikuwa zaki mutu bakiyi aurba muhammad ya tsinci kansa da fada"

Rike hannun Abba baba yayi yace umaru kwantar da hankalinka ni ban rike komai a raina yaran yanzu ka haifesune baka haifi halinsu ba ,
Babu Komai kuma banso kaje kaci zarafin matarka akan wannan abun nasan halinka ya wuce auren fayyaz da noor ne kamar anyi angama insha Allah ,sannan malam nasiru a kiyaye bansan asake makamancin haka damace an baka kayi watse da...

Chu chu jay✍️

Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top