chapter 32
Noorurrahman✔
Da yamma bayan daddy ya dawone fayyaz ya je falonsa domin suyi magana akan maganar noor"
Zaune ya tarar dashi yana shan black tea din da yasaba duk yamma"
Gaishesa yayi sannan ya samu guri kasan carpet ya zauna yayi shiru"
Nasan dai akwai magana abakin autan umma'ah"
Shafa kainsa yayi yace wallahi daddy akan maganan yarinyan da umma'ah tayi ne shine nake so namaka magana"
Dama daddy mahaifanta ne sukace idan da gaske nake na tura itayena nan da kwana hudu zuwa biyar ayi magana duba da cewa ita noor din ba yanzune aurenta na farko ba"
To cewar daddy ,
Su iyayenta suna so ne a tura nan da kwana biyar hala ka jima kama zuwa gurin yarsu hira babu kwakkwaran magana"
Tsintar kansa yayi da cewa eh dan bayaso wani abu ya kawo masa mishkila a maganar aurennan"
Okay dukda dai kwana biyar yayi kusa amma babu damuwa zaaje ranar juma'a nan da kwana uku kenan zanma su Alhaji magana yar wanne gidace yarinyar"
Da sauri fayyaz yace eh daddy yariyar Alhaji muktar dala ce "
Wadda akayi case dinnan da mijinta "
Ikon Allah kar dai kace mun yarannan nasir ya saketa "
Kai abu bai dadi ba abu na gida kuma"
Gyara glasses din fuskar sa yayi yace ,kenan anjima da abun tunda har ka fara zuaa gunta "
Eh daddy "
To ba damuwa ai gidane zan yi waya da Alhaji muktar din na sanar masa da zuwan mu.
DA murna ya tashi ya fita a falon yana jin wani irin dadi mara misaltuwa a hanya yaci karo da umma'ah ,
Matsa mata yayi inda ita kuma ta bishi da wani banzan kallo"
Kai tsaye dakin daddy ta shiga dan dama bata yarda da dadewar da fayyaz yayi ba adakin"
Zama tayi a kusa dashi tace daddyn fayyaz hala wani bukatan fayyaz yazo maka dashi nasan bai rabo da musamman da Allah ya hadashi da bazawara.
Murmushi kawai yayi yana mamakin rigunar mata"
Maganace data danganci aikinsa "
Dan shiru tayi badan ta yardaba tace dama sabida yarinyan chan dole na nema masa transfer wani gun yaje chan ya kare project dinsa
Maybe idan bai ganinta zai hakura"
Kalthume kenan dafa ke kike tura yarannan yayi miki lecture kodan ya samu yarinyar da yake so sai kuma yanzu ya samu kice ke baki yarda ba"
A'a fa ita ma noor din da bata taba aureba banda matsala amma fa aurefa ta tabayi"
Just imagine yarda kike fada kamar yarinyar nan zina aka kamata tanayi kaddarafa bata wuce kan kowa ba kema kuma kinada yaya matanan"
saurin taresa tayi da tufff tuff ,
Insha Allahu yayana bazasu fito ba kar ma kayi musu baki"
Bai sake cemata komai ba dan baya tunanin zata fahimci duk wani abu da zai fada mata "
Zaune noor take a falo tana tunanin ko fayyaz yama iyayensa magana"
Ringing din wayantane ya fito da ita daga tunanin ta ta zurafafa ,ganun fayyaz ne yasa tayi sauri ta daua tareda barin falon wani kallo mami ta bita da shi dan kwata kwata taki yarda suyi maganar wanene tace ma su baba Tana so ,idan ta tambayeta sai tace mata wani abu take jira zata fada mata "
Saida ta sama kofar ta key sannan ta daga wayan ,shiru tayi tana jira taji yayi magana katse shirun yayi ta hanyar yi mata sallama"
Amsawa tayi still tana jiran taji mai zaice"
Tunda gumbiya bataso tayi mun magana naji muryarta naji dadi ni bari nabata albishir mai dadi saurraro,
Daddy zasuzo su nema mun aurenki ranar friday and yace zai kira baba ma"
Shiru tayi tana tunanin inda daddynsa yasan baba sai kuma realization yazo mata ashe fa sunsan juna.
Okay Allah ya Kai mu shine abunda kawai tace "
Cikesa nishadi yace nakasa nutsuwa musamman idan na tuna cewa kin kusa zama mallakina gaskiya ni babban mai sa'ane"
Ganin yan asan wuce gona da irine acewarta yasa tace fayyaz kamar ka manta ba zaman auren din din din zamuyi ba yakamaata ka sanar da zuciyarka tun yanzu ni da kake ganina nan bana tunanin zuciyata zataso wani da namiji ba dai a wannan rayuwarba "
Tashi yayi daga kwancen da yake yana kara jinjina wautar noor kamar ta maidashi wanda baisan mai yake ba "
Kar ki damu ,ni ai abun alfahari nane ace na aureki koda kuwa na kwana daya ne zan mutu ba mai nadama ba so ki barni na yaba niimar da Allah yayi mun koda kuwa ta one second Ce"
Batasake cemasa komai ba shima ganin bazata sake fadan wani abun bane yasa yace da ita okay babe zamuyi waya anjima i love you,
Muah"
Dauke wayan tayi daga kunnenta jin karar kiss din ya bata wani yar and goosebumps tsaki tayi bayan ya kashe wayan tace bazamu shirya ba fayyaz dan naga kai burbushin naka iskancin yana nema ya bani damuwa"
Tashi tayi ta koma falo still mami na nan inda ta batta,
Tana zama taji mami tace noor yakamata kifadamun wanene kika fadawa mahaifinki kinaso kuma zai turo ,kinsan ni na haifeki sannan banaso ki sake shiga tarkon da namiji kamar yarda kika fada a baya wanenen shi wannan din and ya akayi bansan da shi ba"
Kasa tayi da kanta tana tunanin kalar karyar da zata gilla wa mami"
Mami brother din udaysah ne koma abokin yaya ne yaron gidan Alhaji unar saraki"
Dan shiru tayi cikin nazari tace fayyaz dai da sukai case da nasir".
Eh shi Mami"
Ikon Allah ta dama chan kuna san junane"
Eh mami".
Banasan fada mikine kice nayi gaggawa ".
Charaf muhammadu auwal da yashigo ya tsinkayi maganar tasu yace aikuwa mami fayyaz mutumin kirkine amma shine baku taba fadan kuna soyayyaba sis daga ke harshi aa dole ranar kice mun lecturern kune ne to ya kuka kare"
Dan murmushi tayi tace yace iyayensa zasu zo ranar friday"
Allah ya kaimu shine abunda mami tace amma zuciyarta na mata wani iri dai"
Dafa ta muhammadu auwal yayi yace mami trust me fayyaz mutumin kirkine hes nothing like nas and nasan zai rike noor cikin amana sannan zai share nata hawayenta ya mantar da ita komai da ya faru a rayuwarta sannan idan baki gamsu ba zan sake miki bincike akansa"
To muhammad Allah dai ya tsaba abunda yafi alheri"
******
Ranar friday kamar yarda su daddy sukasaka bayan sallar jumaa sukazo gidan su noor,
Hannu biyu biyu baba da Abba da makocinsu Alhaji ilya suka karbu iyayen fayyaz ,
Baba yayi mutukar farin ciki lokacin da yagane wanda yarshi take soyayya da yayi farinciki sosai musamman daya fadada bincike kan fayyaz ya gano mutumin kirkine dan haka koda suka tsayar da magana a take daddy yace ko a tambayo noor tasa sadakinta ya bada"
Murmushi baba yayi yace haji umar kenan noor yarinyace Allah dai ya kaddawo mata zawarcine da kananun shekaru amma ko me kuka bayar Allah yasa musu albarka amma banasan dukiyar aure mai yawa"
Naira dubu dari da hamsin daddy yabada sadakin noor ,
Ba musu baba ya karba yace basu san wani jan lokacin tunda aurennan bana budurwa baneba"
Nan suka tsayar da magana akan satin daya za'a daura auren juma'a dazata kama bayan an idar da sallar juma'a.'
Da mutunta juna suka tafi bayan anyi duk wani abu da yakamata ".
Tun a waya daddy yakira fayyaz ya shaida masa abunda ya faru ,murna kamar xaiyyi me har saida imran yace kakuwa kai kadai fa kake zumidin nan nasan noor batayi tunda ba aurenta na farko kenan ba"
Tsaki yayi yace kai tsiyata da kai munafurci sai akayi me kuma ,
Insha Allahu aurenane zai zama mata na karshe "
Dariya salim yasa yaafara masa wakar shakiyanci.
Tashi yayi ya bar musu dakin dan zuwa ya gana da sahibarsa"
Maimakon ya kirata awaya sai ya kira muhammad yace masa idan yana gida zai shigo ,yar dariya muhammad yayi yace eh ina gida noor ma kuma tana gida sirikina abokina"
Kai wallahi kana da jan magana nidai sai nazo"
A compound ya Tatar da muhammadu auwal da noor suna hira ,
Shi yana aiki a system dinsa itakuma tana ta masa zuba"
A waje yayi parking motarsa yayi knocking aka bude masa yayi niyar ya tsaya a harabar gidan ya kira muhammad tunda yaba ta kiransa bata shiga"
Muhammad yafara hangosa sannan ita "
Da gudu ta tashi tayi gida sabida skirt din jikinta ya kamata sanna kanta babu dan kwali and fadan da muhammad din yamata kenan tace masa ai mahnaz ce ta jika matashi da lemo shine ta bata ta dauraye then kuma ta hangosa wajen shine tazo,
Dariya muhammad ya yana jin dadi cikin ransa dan yanaji jikinsa soyayyarsu zata wanke mata komai"
Zama yazo yayi kan kujerar da ta tashi"
Kallansa muhammad yayi yace ango ba jira kacika zumudi wallahi daga zuwa tambaya maka aure sai kuma zuwa ganin mata oh ni muhammadu"
Kaifa baka da kirki wallahi kasan fa ba kai nazo gani ba dan Allah ka turan ita,
Aw sirinkin naka kake fada ma haka karfa nasa a dawo ma da kudinka"
A tare sukai dariya fayyaz nacewa da baayi zangazanga ba nama ta fulani"
Falon baki muhammad ya ma fayyaz iso saannan ya tafi turo masa noor din"
Mami da mahnaz kawai ya tarar a falo tace kai kuma waccan mai aka mata ta shigo da gudu"
Dariya yayi yace fayyaz fa ta gani "
Maganin mai yawo ba dan kwali ai"
Gashin taga tana dashi ni mai gashi kamar akushi na fita haka mana ,
Mahnaz ta kara"
Atare suka dara wannan karan harda mami"
Daki yaje ya sameta zaune tayi wani kicin kicin hartaso ta bashi dariya ,
Kanwar lapia dai ko bakiga fayyaz ba gurinki yazo fa.
Baki tayi pouting tace gurinka dai yaya ai bai fadan zaizo ba"
To naji yanzu dai tashi kije ,
Batasan ma yayan nata musu dan haka ta dauka katon hijab zata fita ,
Jawo hijab din muhamamdu auwal yayi yace kee"
A haka zaki kamar mai takaba"
A haba dawonan kayan jikinki are okay amma ki sake hijab dinan idan dole shi zakisa kisa wanda bai kaisa ba jifa har wani ja da kasa yake.
Kai yaya"
Oh come on banso a rainan kanwa ,
Wani nude hijab dinta da ya wuce gwiwa ta dauko tasa ,
Dan kallanta yayi yace to dandai kin nace sakashi"
Saura dan jan baki kinsan maza na kaunar dan jan bakinnan"
Ni yaya bazansa jan baki ba Allah .
Dallah zo "
Wani janbakinta da yagani shigen kalan lips dinta ya dauko yace dan tabe lips dinki,
Dariyatasa tace kai yaya"
Eh mana kinsan nine yayanki mace da kuma namiji ,
Tabewan tayi ya shafa mata sannan yace yauwa hadesu,
Dariya tasa ta duba mirror ta gyara.
KO kefa kidinga yar kwarkwasannan da zata sake sace zuciyar dan banza"
Saura turare fes fes ya fesa mata
DA Dariya suka fita tare tanacewa kai yaya
"
Fita tayi mami nacewa ayi ladabi dai banda magana gatse gatse"
Hakannan gabanta ke faduwa dan batasan wanne ido zatasa ta kalli fayyaz ba duk da cewa komai karyane amma tanajin wani iri"
Tana kokarin shiga dakin taji an jawota an dauketa da mari.
Chu chu jay✍️
Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top