chapter 31

Noorurrahman✔

Koda ta tashi da sassafe dan hada breakfast tunanine dayawa a cikin kanta ,
Ta zurfafa a tunnanin inda zata samo miji kwatsam sai ga kiran fayyaz a wayarta ,

Bataso tayi amfani dashi ko kadan amma gani take kamar shine last hope dinta ,

Sharp sharp ta hada musu breakfast taci nata ganin ba wanda ya tashi dama jiya ta sanar ma mami zataje makaranta dan yin wani abu mai amfani ,
Bata mata karyaba tunda zataje gurin makarantar sannan abunda zatayi yana da amfani,
Abune da ya shafi rayuwarta da future dinta baki daya"

Dama tayi wanka tunda tayi sallar asuba dan haka bayan ta tabbatar da tayi duk abunda ya zamo sabonta ne na aiki a cikin gidan ne ta sakai ta fita fuskarta dauke da nikaf"
Karfe 8:10 ta isa inda tace masa yaje,
Tana isa tayi dialing numbersa sabida bata ganshi a gurinba ,
Kira daya ya dauka ,

Nazo ban ganka ba shine abunda kawai ta tsinci kanta da fada bayan tayi masa sallama".murmushi yayi daga daya side din yace ni kuma na ganki babu wani abu da zaisa na kasa gane ninja ta a koina"

Batace masa komai ba ta kashe wayar ,tsintar kanta tayi da yin murmushi wanda batasan dalilinsaba"
Daga gefensa motarsa tayi parking"

Fitowa yayi yana tafiyarsa nan ta eligible bachelor "
Ta gefen ido ta ke kallansa har ya karaso inda take"

Good morning beautiful"
Juyowa tayi tana facing dinsa tace good morning '
Shiru tayi dan duk wani hikimarta ta magana yau ta narke agaban fayyaz"

Karantarta da yayine yasa yayi murmushin shi mai kyau yace ko zakizo muyi magana cikin mota ne "

DA Sauri ta kada kai da A'a
Muje restaurant din chan ba na baya"

Bamusu yace muje dama sarauniyar mata ta tasoni ban yi breakfast ba,

Murmushi tayi cikin nikaf dinta ba dai ta ce masa komai ba suka nufi restaurant din da dama usually 7:30 an budeshi .

Zama sukayi bayan sun shiga restaurant din inda babu bata lokaci waiter yazo ya kawo musu menu,
Bata bude ba tace coffee please"
Murmushi fayyaz yayi yace black coffee please"

Karban menu din waiter din yayi ya tafi "
Bayan mintuna kadan sai gashi da ordernsu wanda still zaman basuce ma juna komai ba ita tana tunanin ta ina zata fara shikuma ya zuba mata idanunsa yana tunanin dalilin kiran nasa da tayi"

I bet we ain't here just  to drink coffee '
Sipping coffee dinsa yayi kadan yana jiran tayi magana".

I know I might sound selfish you know"
Wasa take da yatsunta in nervousness"

Ai kya daga nikaf din yarda zan na ganin bakinki ba "
Kamar bazata daga ba amma sai ta daga din"

Ina cikin wani haline ne da nake tunanin i will need your help"
Tafada tana tsoran ta inda zata fara"

Uhum just say the word and zanmiki komenene in a heart heat Indai bai sabawa shariah ba.

Hada lips dinta da babu komai face white balm tayi tace "
Wani abu ya faru wanda bazan iya discussing dinshi da kai ba wanda yasa baba yace nafito da miji in five days of time idan ba haka ba zai sake daura mun aure da yaya nas"
And nasan bai kamata nayi involving dinka a ciki ba so '
Sai kuma tayi shiru ta kasa karasawa anya bata bada kanta ba ,anya ba da kanta take kokarin jefa kanta ramun kuraye ba"
Bazata taba manta karansu da umma'ah ba babu dadi"

So "ya Katse mata hanzari ,
So mene go on mai kikeso ayi"

Cire duk wani tunaninta tayi tace ,
Idan har abunda kafadamun a gidan ku is still valid ,
I'm ready "

Dan smirking yayi yace you're ready for what .

Ganin kamar abun nasa da rainin hankaline yasa ta tashi tareda daukan jakanta ,
She shouldn't have been here first place"
Musamman idan ta tuna abunda tafadawa mahaifiyarsa na bata sanshi and iya gaskiyarta kenan ita ba sanshi take ba"
I'm sorry na bata maka lokaci ,kamanta da namaka maganar nan please ,.

Ta juya zata fara tafiya  yayi saurin cewa na amince ,
Zan tura iyayena gidanku in five days of time .

Jitayi kamar tayi tsalle batayi expecting hakan daga gurinshiba ,
Juyawa tayi ta koma ta zauna tace"
I will be forever greatful to you amma wani hanzari ba gudu ba"
Umma'ah fa can we do this without her knowledge"

Aje mug din coffee dinsa yayi yace "
Sure amma babu yarda za'ayi muyi aure ba saninta after all shes my mother and ina girmamata fiye da komai "

Its okay face na fahimta amma inasan aurenan ne bada wani manufa ba nasan wannan babban decision ne da zamu dauka "
Inaso idan munyi aure ni da kai after some months idan maganan yaya nas ta lafa kasakeni"
saboda our feelings are not mutual nasan kaima kana fada abakine amma ba wannan san nawa kakeyi ba mubarshi a kai anaso kayi aure a gidanku nimana anaso nayi aure a gidanmu after 5 to 6 months haka said muyi divorcing are you okay with it.

Shiru yayi baice mata komai ba yacigaba da shan coffee dinsa idanunsa kuma akanta akai akai kuma yana murmushi"
Ganin bazaice komai din bane yasa tace idan you're not okay with it I won't force you zanyi tunanin wani abun"

Aje mug din yayi yace na amince "
Kisha coffee dinki nasan ma ya huce"

Dan murmushin jin dadi tayi tace ya yi sanyi kuma na rasa appetite din sha bari naje nayi payment nakama is on me "

Bai ce mata komai ba ta tafi gun cashier tana kokarin biya cashier din tace madam ba a charging oga da friends dinsa a nan sabida da gurin shi ne "

Juyawa tayi ta kalleshu taga bama ita yake kalla ba ,
Kallanta ta mayar kan cashier din tace i insist ni a cire kudina "
Banakar ban charity "

Tasowa yayi daga zaunen da yake ya ja hannunta su yafara tafiya,tanata mitan ya
Cikata amma yaki saida sukaje bakin car dinsa.'
Hannunta ta leave tareda sauke nikaf dinta tace kadaina kamamun hannu anyhow nida kai ba muharramai bane"

Shafa gashin kanshi yayi yace amma dai mukusa zama muharramaiba "

Bamuzama ba tukkuna so please ka daina bani so"

Kara kai yayi yace its okay na DA in a yanzu muje na saukeki gida"

Sauri kada kai tayi a'a zan samu keke"

Ganin ya kafene yasa tace to taji amma ba har kofar gida zai sauketa ba ,.

A kan layinsu ya sauketa ,
Godia tayi masa ta fita a motar"
Tana fita ya daki sitiyarin motarsa yace "yes finally ".
Jan motarsa yayi ya bar layin zuciyarsa fara sol dole yaje suyi maganar fahimta da mahaifinshi dan yasan shi kadaine zai mara masa baya"

Koda ya shiga gida yayi mamakin ganin meerah da munnirat a falo suna hira da umma'ah"
Tunda ya shigo yaga muneerat na masa wani kallo yasancewa umma'ah ta fada musu abunda yake faruwa"
Sannuku da zuwa ina yaran shine abunda ya fada bayan ya zauna "

Da yatsina fuska munnirat tayi batareda tace masa komai ba sai meerah ce tace suna school"

Au that's great umma'ah barka da gida bari nashiga na dan rama baccin safenan da banba"

Inakaje cewar munirat tana wani hade rai
Dan murmushi yayi yace sis kenan har yanzu kallan yaro dai kike mun ,sha nasan rashin aurenane ya jawo haka amma soon zan kawo muku kanwa"

Bazawarar" babu mamaki ma babbace"
Maybe kadan kagirme mata ko kuyi sa'ani

wani murmushin ya kuma yi aransa yace anzo gurin amma afili sai cewa yayi eh sis ita dai bazawarar and hala baki samu full details ba amma yarinayane kaddara ta fadawa ta mutuwar aure wadda itace Alkhairin ,
If you'll excuse me "

Kwafa tayi tashiga kwala masa kira kan ya dawo amma yayi mata banza batareda ya juyaba dan idan ya biyeta zasuyi fadane tanata faman hura hanci wai ita babba"

Wallahi umma'ah bazai iyuba kina kallan tun yanzu an fara inaga sunyi auren"

Shiyasa nace ai bai isaba wallahi ko yana yawo da ubansa udaysan dai da baya zo ita zan aura mishi cewar umma'ah'

Meerah da tunda aka fara maganar bata tofa albarkacin bakinta bace tace"
Big sis keda umma'ah kunaso kuce fayyaz dole bazai aura wadda yakeso ba sai udaysah baku tunanin hakan ba dai dai bane,
Nidai banga aibun auren bazawaraba sabida it can happen to each of us,idan ba saki akwai mutuwa to mai yasa dan Allah ya dora masa san wadda tayi aure ta fito sai kuce bazai yiba kamar wanda yake shirin aikata haram,
Ni ganinake its best abarshi yayi abunda yake so fisabililahi_.

Dallah rufe mana baki sakariya aike ba a taba fadan aibun abunsa a gabanki sai kinsan yarda kikayi kika kawowa mutane kabli da ba'adi,
To ni uwarsa nace bazai aureta ba .

Daukar jakarta tayi tace Allah ya baki hakuri umma'ah ni ina da seminar ma bari na tafi amma bari naje naga fayyaz kan na wuce"

Eh kije zuwan kin  bazai chanza hukuncin da umma'ah ta dauka ba bazai auretaba munnirat tafada cikeda masifa"

Dan Dariya meerah tayi tafara tafiya tareda cewa rabo dai yana kisa kuma wannan ba asan zafin rabontaba ,

Tanaji munnirat na zazaga balai amma bata kulata ba ta haura gun fayyaz,
Xaune ta sameshi yana komarin cire takalmi,
Xama tayi kusa dashi tace brother kana tunanin daidai ne abunda kake i mean kana tunanin babu matsala"

Murmushi yayi dan yasan she will always support him"
Look sis wallahi ina santa and bakiga abunda umma'ah tayi mata ranannan ba banji dadi ba and yarinyarnan fa tsautsayine yafada kanta da har tashiga sahon zawarawa,
Briefly yabata labarin noor kana yace shin menene laipinta .

Shiru tayi tana nazari kafun tace ina bayanka fayyaz kayi duk abunda zuciyarka ta saka listen to your heart nasan with time umma'ah zata fahimta and zai zama kamar baayiba All the best ,hope zaa sa time a kawon ita mugaisa".

Shafa kansa yayi yana murmushi yace kar ki wani damu sis insha Allahu ma nasan soon zata zama tawa inaji a jikina ki tayai addua kawai.

Chu chu jay✍️

Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top