chapter 27


Chapter 27
Noorurrahman✔

Kara karanta sakon tayi har sau biyu da mamaki,
Wakuma ya bawa fayyaz number dinta "
Tasan dai bazai wuce udaysah ba and she will have to answer her saita fada mata abunda ya saka tabashi number dinta itafa he's getting on her nerves and zataje har gidansu ta mayar masa da kudinsa bazata karba ba"

*******
Tunda ya koma gida yake santin girkin noor lallai Allah ya azurtata da iya sarrafa abinci babu laipi"

Yakarbi wayar udaysah ne da nashi motives din wato daukar numbern ta ,baisan mainene damuwarsa ba amma hakanan yaji yana bukatar samun number ta,
Lokacin da Muhammad ya gayyacesa gidan ba karamun dadi yaji ba atleast zai sakata cikin idanunsa dan tunda akayi hutu yake jin rashin dadin ganin nata ,

Tunani yake ya tura mata text ko kar yayi gudun kar ta rainashi,sai yayi typing sai ya goge a haka har garin rashin sani ya tura send,
rimtse idanu yayi yasan yanzu zatayi masa wani fassaran oh no"

Komawa yayi ya kwanta yana kara tunano labarin da udaysah ke bama umma'ah na irin sakin da nas yayi mata ,
Yaji dadi sannan yaji zafi sosai"

Jan blanket yayi ya rufe fuskarsa God, why"
Da tunaninta bacci barawo ya daukeshi "

Washe gari da ya fito breakfast gani yayi umma'ah nata kallansa ,cigaba yayi da karinsa batareda ya nuna damuwa da kallan da take mashi ba".

Ganin bai kula tabane ya satayi magana dan taga bamashi da alamun kula ta din
"Autan umma'ah nayi deciding hadaku aure kaida yar uwarka udaysah tunda naga dukkanku you're not serious idan na cigaba da zuba muku idanu haka zaku cigaba da mayar dani wadda bansan mai nake ba gwanda ayi tuwona maina "

Ba shiri ya kware a abincin da yake ci ,
Tari yafara ba kakkautawa ,da sauri mahaifinsa ya miko masa ruwa tareda cewa"
Kema dai madam ya zaki masa maganar nan yana cin abincin kinsan halin dan nakifa fiye da kowa"
Cigaba tayi da cin abincinta batareda nuna damuwar kwarewar dayayi ba tace amma daddy kasan dai he's old enough and abun nasa yafara wuce gona da iri idan yana da wadda yake so ba sai ya fada ba aje anema masa aurenta"

Udaysah ce tace nima dai ba aurensa zanba umma'ah kinsani ni yanzu tsoran auren gida ma nake tundaga kan noor gashi daga gani brother zayyi muzurai ya bigeka yazo yana maka warwar da idanu ni banaso "

Batareda ya kalleta ba yace nima ai ba aurenkin zanyi ba safiyar farko mutum yatashi ya ganki dau kamar walkiya ni inada wadda nake so"

Atare dukkansu suka ce wacece"

Goge bakinsa yayi da tissue ya mike yana fadin bad habit ne kana cin abinci kana magana umma'ah taught us that"

Dariya daddy yasa yana cewa ja'iri idan tayi tsami zamuji "

Zakuji da lunch tunda gun cin abincin yazama na discussing auren auntan umma'ah ko sweet mom"

Bata rai tayi batareda ta kulasa ba dan taso yafada mata wacece dan dama tayi masa hakan ne ko zai fadi wadda yake so din amma yaki zakuwa tayi ta bibiya har sai ta gano wacece"

Sama ya haura yana murmushi tabbas yana mutukar kaunar family dinsa"

"
Gym ya Shiga wanda yake saman gidan domin motsa jiki,
Da daya numbersa yayi dialling numberta sannan ya fara push up,
Yana jin muryarta alamun daga bacci take tanatacewa hello ,hello,wanene ke magana"
Jin shirune yasaka ta kashe wayar,

Kara kiranta yayi dan hakan na masa dadi ,
Cikeda masifa ta daga wayar tace ,dan Allah idan baza ayi magana ba abarni na yi baccina for God sake this is my phone and I need some peace"
Dif ta kashe wayar"

Dariya yasaka dan wannan yana daya daga cikin halayyarta da take burgesa she's a rebel at times .

Cigaba yayi da work out dinsa yana murmshi akai akai idan yana tunano encounter din su "

Ba sallama udaysah ta shigo gym din tana bin wakan dake kunneta a airpods "
Kan keken motsa jiki ta haye tana cigaba da bin wakar loudly "
Tsaki yayi yace namiki warning like a thousand times udaysah kidai na shigomin idan ina gym dinnan amma bakiji and da acema zaki shigo kiyi shirune da sauki amma kullum da noisy wakokinki ke gashi murya ba dadi ba"

Murguda baki tayi tace aikuwa kasan duk wadda zaka auro bazata kaini komai ba ,Allah dai ya nuna mana wannan budurwa da ake ta wani boyewa .

Murmushi yayi wanda shikadai yasan ma'anarsa"
Yarinya kenan'
Fita yayi yabar mata gun dan baimasan suja magana.

***
Tunda ta kashe wayanta bayan ta gama mishi masifa ta kashe wayar baki daya dan tana tunanin mai kiran natama yanayine just to pissed her up"

Bata tashi ba sai wajen 10 lokacin ta samu isashen baccin da takeso ta samu"

Wanka tayi ta fita domin karyawa tasan dai iyanzu kowa yaci nasa ita din dai ta rage,
Dama tarbiyan gidansu shine gaida iyayensu bayan sallar asuba"
Kitchen ta fada dan hada Sandwich,
Yayane ya shigo kitchen din wanda shima bai tashi da wurinba"

Sis Mai kikeyi ne ,sandwich omo hada dani bari na hada mana coffee"

Okay yaya,kara adadin slice din tayi "

Around 11 tace mami zataje gidansu udaysah "

Lapia dai mami ta tambayeta"

fadan mata abunda ya faru tayi and mami ta nuna sam taje ta mayar masa da kudinsa,

Kiran driver dinsu tayi yazo ya kaita ,wayar udaysah ts kira ta tambayeta tana gida cikeda murna udaysah tace mata tana gida dan tasan babu wai zuwa noor din zatayi ,yana jinsu lokacin da suke wayan da yayi niyar fitane amma jin noor zata zone yasaka ya dauko magazine din kan center table yana dubawa kamar gaske "

Bata wuce minti talatin ba da wayansu ta isa gidan ,
DA wani tsalle udaysah ta dane noor lokacin da tayi sallama ,dariya umma'ah tasa ta girgiza kai udaysah bazata taba girma ba "

Tagefen idanu yake kallan su yana mita a zuciyarsa cewa udaysah zata karyata"

Jawo hannunta udaysah tayi suka shigo falon tana cewa aikam yau dole ki wuni a gidannan Allah ma yasa kinzo da wuri bazakicemun baki tambaya ba im very sure mami ta barki kizo"

Ita dai murmushi kawai take dan bataso ta tarar da umma'ah a falo ba da kawai ta bashi kudinsa amma yanzu dole sai gashi gata ,
Zama tayi ta gaisar da umma'ah ,
Fuskarya dauke da fara'ar nan ta amsata tana tambayanta ya mutan gidan,
Tana ganin kirkin umma'ah sosai,
Mutum ce wadda bata daukan zafi sannan kasancewarta malama ba shine yake saka ta wulakanta dalibai ba ,tana da mutukar girmama mutane "

Kallanta udaysah tayi tace noor tashi muje dakina yau kar kiyimin irin ta ranarnan yau hira zamu sha "

Ita dai umma'ah murmushi kawai take musu ba tareda tace komai ba shi kuwa fayyaz wani haushin udaysah ne ya kamasa shida yake san yayi ta kallanta har ta tafi menene na cewa tatashi suje daki"

Tashi noor tayi dan bin udaysah wadda take janta kamar jela"

Umma'ah ba kince kinasan sanin yarinyar da zan aura ba "

A wani sukwane udaysah ta saki hannun noor ta koma da gudu tana cewa "eh ta fada"

Nunata yayi ya kalli umma yace"
A haka wai akeso na auri wannan,
And beside ni umma'ah nace i don't remember calling your name.

Kallansa umma'ah tayi tana washe baki ,
Autan umma'ah manta da ita fada mun wacece sirikar tawa"

Licking lips dinsa yayi da ya dan yi dry sannan yayi murmushi yace kai umma'ah kalli yarda duk kuka wani nutsu kuna kallona what's the big deal about gf Dina"

Akwaifa big deal autan umma'ah karka manta kai daya ne namijin da na mallaka so komai naka zanso yazama special now tell me who's the lucky girl dan itane zata zama lucky ba kaiba.

Murmushi yayi wanda saida ya nuna dimples dinsa yace gatachan a tsaye ita nakeso and im serious aurenta nake so nayi'.

Atare umma'ah da udaysah suka juya dan ganin wa yake nunawa "

A tare sukace noor"

Batareda bacewar murmushin fuskarsa ba yace eh ita umma'ah i don't know when it started amma yarda nakejina yanzu i cant live without her seriously"

Dariya umma'ah tasaka tace "
Baka isa ba idan ma wasa kake ka bari,
Karya kake wallahi "

Ina BAZAWARAR
.
Chu chu jay✍️

Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top