chapter 25
Chapter 25
Noorurrahman✔
Ehen ina sauraranki,
Sir dama test ne da akayi ban samu nayi ba sabida banzo makaranta ba amma udaysah tayi mun reporting"
Wai"
Na'am tafada tana kallanshi dan bata gane mai wai din take nufi ba"
Jin tayi Shiru ne yasaka ya aje rubutun da yake ya dago yana kallan ta cikin ido hannusa kuma yana twirling biron da yake rubutun"
Hala baki da aikin yi ne as you can see ni ina dashi idan bazaki bude baki kiyi magana ba zaki iya bani guri"
Wani haushinsa taji ya cikata fal badan kar tayi asarar marks ba to da ta hakura da rubuta test di gaba daya"
Cije lebe tayi tace "
Udaysah tayi min reporting bansamu zuwaba wanchan week din sabida wani uziri mai karfi da ya hanani zuwa"
Shi uzirin bashi da suna yasake tambayarta idanunsa a kanta shi babbata ran ma datakeyi dadi yake masa "
Eh sir personal abune ya hanani zuwa amma ,
Please sir "
Kataimaka kayi mun test dinchan"
Menene personal abunda ya hanaki zuwa ko sabida kin rabu da mijinkine kika kwanta cuta ".
Shiru ta mishi bata ce masa komai ba dan batasan mai zatace masa ba idan tayi magana dan ta kosa ma tabar office din sabida irin kallan da yake mata bakaramin tasiri yake akanta ba "
Zauna ki yaga paper da pen"
Ba musu ta zauna a kan cushion ta dauko abunda ya umarceta da ta dauko din"
Questions masu wuya yabata dan ya gwada karfin kwakwalwarta sanin da gayya yayi mata hakan yasa tayi dariya kasa kasa ,abu daya da bai sani ba shine ba zaman banza tayi a gidan ba tayi karatu dai dai gwargwado "
Bata dauka minti goma ba ta gama amsa questions din daya bata ,mayarda pen dinata tayi ta saka wayarta a jaka sannan tatashi ta mika masa takardar "
Kallanta yayi ganin ta saki nikaf din dake fuskanta ,
Dan murmushi yayi da yayi realizing ashefa a iddah take ,
Hijab dinta babba har kasa ga fuskarta fayau babu koda kwalli ,
Ya kula basan wani dogon surutu take so dashiba dan haka yakamata ace yayi respecting hakan ".
Bata sake ce masa komai ba haka shima bai ce mata komai dinba ta fice a office din,
Bayan an mata daya test dinne udaysah ta ajeta gida "
Bayan ta cire kayanta ne tayi wanka tayi sallah sannan ta zauna cin favorite shinkafa da waken da mami ta aje mata ,
Da gudu mahnaz ta shigo dakin tana kwala mata kira lokacin tana kokarin kai spoon din abinci baki"
Da sauri ta tashi tana tambayar lapia dan ta tsoratata"
Dariya tayi tace kai didi you're such a scary cat ,
Daga shigowa zaki wani tsorata to baba Alhaji ne da Abba suke kiranki"
Tsaki tayi tace "wallahi bazaki taba nutsuwa ba, inbanda shirme da girmanki amma bazaki daina shigowa guri da gudu ba "
Tsaki tayi ta dauki hijab dinta dan zuwa amsa kiran iyayen nata"
A zaune ta tarar dasu suna maganar da ta shafi kasuwancinsu amma shigarta ta katsesu, zama tayi cikin nutsuwa ta gaishe su sanan tace dama mahnaz tace kuna kirana "
Eh cewan Abba akan maganar iddan kine "
Sati daya kenan sannan inda tazo da sauki babu shigar ciki ,
"
To shi hukuncin idda kinsan yarda yake amma inasan nasake tunatar dake"
Mace Mai iddah anaso tazamto a suturce har tagama iddanta immaga wadda mijinta ya mutu ko kuma wadda mijinta ya sake ta kuma anaso ta yi iddantane a cikin gidan mijinta "
Amma zata iya barin gidan mijinnata idan akwai abubuwa kamar haka "
Idan har gidan na hayane kuma bata da kudin cikewa "
"KO rayuwarka tana cikin wani hadari ko dukiyar ka ko mutuncinka,
"Idan darajatta zata tabo ko tana zaune da wanda zai cutar da ita .
"KO idan tana tsoran gidan da take yin iddar aciki da sauransu to ya hallarta ta fita daga gidan tayi iddarta a wani gurin.
Sannan baa yarda da mai idda ta saka kwalliyaba ko turare,
Idan larura ta kama ko ta ciwan kai kota wani abu da zata saka wani oil akanta to zata iya sawa amma yazama ba mai kamshiba "
Idan akwai damuwar eyes balm zata iya sawa da dare ta goge da safe "
"Sai wajen kaya shes allowed to wear silken..
Sai ban
garenki wato zuwa makaranta,
Idan uziri ya kama mai idda wanda yake uzirine babba zata iya fita amma fa babu uzirin biki,ko wani function dai ko wani meeting amma an yarje mata zuwa neman ilimi amma fa ta sani dole sai ta kiyaye sharidan iddah ".
akwai hadith ingantacce
Anrawaito daga jabir ,
Auntinsa aurenta ya mutu sai ta fita tsinkar dabino ,sai wani yayi mata magana akan ta fito lokacin iddar ta wanda hakan ba dai dai bane"
Sai taje gurin annabi muhammad sallalahu alaihi wasalam,
Sai yace mata zata iya zuwa tsinkan dabinonta sabida maybe zatayi sadaqa ne,ko wani abun kirkin amma sai dai tafita a bisa cika sarriah ta musulunci wanda shine saka hijab,
Guje sa turare da kwaliyya da sauransu ,
Allah knows best.
So kiyi iddanki cikin gidanku sannan zakije makaranta sabida ta kama amma kiji tsoran Allah"
.
Nagode Abba sannan insha Allahu zan kiyaye duk abunda ka fada mun na kiyaye.
Yauwa Allah yayi miki Albarka ,Allah ya inganta rayuwarki insha Allahu bazaki taba tabewa ba.
Kallan baba Alhaji tayi ko zai ce mata wani abu amma sai yace tashi kije komai da nake san fada miki Abbanki ya riga ya fada miki sai a kiyaye .
Tashi tayi tafita daga falon baba Alhaji tana jin dadin zata iya zuwa makaranta dan dama tunanin da take tayi kenan kar ace ta daina zuwa sai ta gama iddah da kuwa ta tsinewa yaya nas da ya jawo mata wannan abu duk da cewa it worth it *.
Daki ta koma dan cigaba da cin abincinta amma ga mamakinta sai ganin yaya nas tayi zaune gaban abincin data fara ci yama kusa cinyewa ,
Wani bakin takaici ne ya kamata dan last abincin kenan,amma bama wannan ba ta ina ya shigo mata daki"
Juyawa tayi zata fice a dakin da zafin nama ya kamota ya tura kofar dakin"
Bata rai tayi sosai dan taga alamun idan batayi da gaske ba zai cigaba da bibiyarta ne"
Menene hakan da kawani rike ni ka tura daki"
Yaya nas please kabarni mu karasa da sauran mutuncinka na yan uwantaka da nake da sauransa,.
Kar kasake shigarmun daki sabida yanzu ni ba muharramar ka bace"
Dariya yayi irinta ta kaici ,
Lallaima noor ni kike kallan kwayar idanuna kike fadan cewa ni ba muharraminki bane "
Noor kar ki manta nifa mijinki ne "
Da sauri ta gyara masa "
A da ,kai mijinane amma a da,amma yanzu yan uwantaka ce kawai ke tsakanina dai kai dan Allah kasa hakan acikin ranka zaifi mana sauki baki daya"
dariya ya kuma yi wadda tafi ta farko yace "
Noor noor"
Kar ki manta ni nafara saninki a ya mace ,ni na budeki a leda sabuwa fes sannan babu wanda zai fada mun zumarki so its best mu koma aurenmu asirin mu a rufe kar aje nayi abunda bai kamata ba"
Fincike hannunta tayi daga rikon da yayi mata tace "
Idan ka fasa yaya nas baka tsoran Allah idan kafasa abunda bai kamata ba "
Menene zakayi yanzu kaban mamaki,
Sannan magana da kake cewa kai ka fara sanina sai akayi mene wannan ai ba a kaina farau ba ba kuma kaina karauba ,Alhamdulilah ba zina naje nayi ba ko a lokacin da aurenka a kaina so do your worst".
Amma warning daya nake so namaka shine ka fita hanya na sannan kazo kayi saurin barin dakin nan wallahi idan kuma ba haka ba ,Abba yana cikin gidanan sannan idan yasan kana cikin dakina kafi kowa sanin mai ne zai faru so get out"
Bango ya kaita yayi mata rumfa ,
Shafe gefen gashinta yayi sannan yayi smirking "
Yace "
Baby zan tafi amma keep this in mind ,zan dawo sannan wannan gayen da yake manne miki kamar chewgum yayi ya gama ni nas ban taba faduwa ba its either nayi winning ko kowa ya rasa ,
Kisa wannan a ranki ke noor baki da miji a duniya da ya wuce ni nasir umar dala "
Yawun bakinta ta hado ta watsa masa a fuska"
Dukan ginin bayanta yayi wanda sai da ta firgita kafun yasa hannunsa ya goge miyan ya mayar bakinsa sannan ya juya ya fita a dakin yana dariya "
Yuck ,
Kazamin banza "
Allah yasa mami ta kamasa ko yaci karo da Abba a hanya yacimasa kaniya,
Nonsense yazo ya cinye mata abincinta and ga yunwa na damunta"
Mahnaz ta fara kwalawa kira
Wanna Karan bada gudun da ta saba ba ta shigo dakin wanda yasa noor cewa "
Yau ba'ashigo da gudun haukan ba "
Dan Allah dafa mun noodles biyu ,ki sa mun sardine daya a ciki amma kar ki soya mun kwai "
Then ki dan sa mun soy sauce in zaki dafa "
And Kar"..
DA sauri mahnaz ta karasa "
Kar ta dafe sosai taste dinki har yanzu dai bai sake ba "
Amma didi na tambayeki ,
Yanzu fa kika gama cin shinkafar nan fa and nasan a yanayin cinki ta isheki "
Banzan kallo ta watsa mata cikeda masifar cinye mata shinkafar da yayi tace idan zaki wuce ki wuce banasan munafurci "
Bata kuma ce mata komaiba ta fice tana tunanin maybe baba Alhaji da Abba ne suka fada mata wani abu da bai mata dadi ba dan haka ta maida hankalinta kan abunda ta sata"
Tana tsaka da cin noodles din da mahnaz ta kawo mata farhana ta shigo daki da sallama dauke a bakinta amma ganin noodles din yasa tama kasa karasa sallamar ta taho da gudunta tana fadin tamu ta samu dama dai inasan dahuwan ki"
Janye plate din gafe tayi tace to bama ni na dafa ba mahnaz ce narasa mai yasa keda yayanki bazaku barni nayi kiba ba"
Zama farhana tayi tace "
Nida yayana kina nufin nas, yazo nan ne "
A'a tace mata dan dama subutar baki yasa tace ita da yayanta "
Zamatayi kusa da ita tace"
Noor nasan yaya nas bai kyauta ba sannan ko nice zanyi hauka sosai na tashi hankalin kowa amma noor sati kawai amma yaya nas ya gane kurensa baki ganin baikamata ki bashi second chance ba, i mean you're young baki tunanin yayi kusa ki zama bazawara ,
Nasani cewa im sounding selfish amma ni gani nake idan kika bashi chance zai gyara yana sanki sosai and saida abunan ya faru yayi realizing"
Dariya noor ta saka"
Kinsa mai kike fada kuwa,ni na koma gidan yaya nas"
Amma akan me "
Look farhana im sorry nasan magana na zai iya miki zafi amma ni nan da kika ganni bana san yaya nas ,
Bazan kuma iya kara zaman aure dashiba koda kadanne trust me it wasn't funny "
Yaya nas is a drunkard sannan yan iska yake kawo min gida ciki harda girlfriend,
Yaya nas bana laipi kadan sai yayi mun mugun duka ,duka mai sunan duka kamar ya samu jaka amma babu wanda nake fadawa sannan yanzu na samu enci sai ace na koma ,a'a bazai iyu ba .
Shiru farhana tayi tana jin jina abun tabbas taso kanta amma ya zatayi babu abinda ya kai jini"
Tura mata plate din noodles din noor tayi tace nasan idan bakici ba zaki iya hadiyar zuciya ki made and nasan bakisan mutuwa yanzu sai kin auri yayana cos i smell rat "
Atare suka saka dariya"
Chu chu jay❤
Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top