chapter 24

Chapter 24
Noorurrahman✔

Wani fayau noor take jin kanta ,tabbas igiyoyin yaya nas dake kanta bakarami nauyine dasu ba ,yau da aka saukesu jitake kamar an dauke mata wani abu mai nauyi akafada,
Taji dadi sosai tunda baba Alhaji yau ya goya mata baya bai mata dole akan saita komaba wanda a lokacin ta kudiri niyyar bijire masa muddin yace sai ta koma gidan yaya nas".

Kallan yarda take ta murmushi muhammadu auwal yayi yace duk murnar freedom dinne haka sis"

Murmushi kawai tayi dan ita kadai tasan ya takeji a lokacin finallly Allah ya yaye mata damuwarta .
Tunda dai ya rabata da yaya nas"

Gyaran mirya mami tayi ta saka dukkan serious face dinta tace "
To noor bawai dan kinga abunan ya faruba kuma kice zakisamu damar raina nasiru ,a'a bazan lamunta ba koda babu aure tsakaninku to girmamawar da kike ma yayanki ita zaki masa ".

Dan shagwabe fuska tayi tace "
Mami kinsanni kuma kinsan irin tarbiyyar da kika mun insha Allahu bazan taba raina yaya nas ba sabida abunda ya faru"

Tabe baki muhammdu auwal yayi yace "
Bare ma ni banga abun girmamawa a gunsa ba "

Bugu mami ta kaimasa da mificin dake hannunta '
Tashi ka bamu guri"

DA dariya ya tashi ya bar falon yana cewa mami maine na duka duk da irin cuda miki ya da yayi amma kina zabansa sama dani ko its okay ba komai"

Murmushi mami tayi ,tabbas bata kin nasiru halayyarsa ce bataso amma dukda abunnan da ya faru, ko daya bataji matsayinsa a zuciyarta ya sauya ba ,amma abu daya ta yarda dashi shine bazata yarda da cigaban auransa da yarta ba kowa Allah ya bashi dai dai dashi "

Noor bata koma makarantaba sai da akayi sati da rabuwarta da nas "
Yau monday ta shirya dan zuwa makaranta ,
Fushi take da udaysah wadda tunda satin chan ya kama bata kirataba taji mai nene ya hanata zuwa makaranta ba"

Tunda ya shiga cikin harabar makarantar taga kamar ana kallanta ,
Cigaba tayi da tafiya dan isa department dinsu"

Kiyi sauri kin tsaya kamar wadda kwai ya fashewa a ciki and kin tare hanyan kamar nakine ke kadai,
Juyawa tayi dan jin muryar fayyaz datayi akanta "

Matsa masa gefe tayi alamun ya wuce "
Kin wucewa yayi ya tsaya yana kalanta cikin ido wanda ya fara having effect akanta"
Sir fayyaz na matsa ka wuce "

Bakiji ke kam nace kidaina kirana sir amma bakiji"

Sir Mai yasa bazan ce maka sir ba ,
Kaifa malaminane to wanne alaka ne ke tsaninmu da zata saka na ringa kiranka da fayyaz kawai"..

Side smirk yayi yace amma ai baki kiran muhamamdu auwal sir ko"

Sir please I'm getting late ko na wuce din"
Tafada tana kara tsuke fuska"
.
dan jan hancinsa yayi yace "
Its okay idan kikayi late tare kukayi keda malamin da zai dauke ku lecture"

Tana kokarin magana muryar nas ta hanata"
Lallai noor kin bani mamaki ashe sabida wanann kika ki yarda ki koma ma auremu"
Kisani noor wanda kasani yafi wanda zaka sani nan gaba gwanda wanda kikasan halayyarsa akan wanda baki sani bama kwatakwata"
Are you blind kallo daya zakiyi masa kisan cewa fuck boy ne"

Bata tankasaba tayi gaba dan tana ganin kulashin ma bashida amfani".

Kallonsa fayyaz yayi kafun yayi yar dariya "
Ashe kun Rabu"
Been week already nasha ganinka cikin makarantar nan ashe biko kake zuwa ,
Wannan ne best news da na tsinta cikin safiyyar yau ,
Gaskiya ka chanchanci kyauta "
Mai zan baka naji dadi"

Wani tsaki nas ya saka yace"
Ban Sani ba dama nasan kaine kake hure mata kunne dama nasani jikina ya dade yana bani cewa kaida noor kuna cin amanata ashe ba kuskure nayi ba da aurena kake nemanta,
To kasani ,noor tawace ni kadai ,yarda na fara saninta ni zan kare a saninta amma ba wani banza ba ka rubuta ka aje sai na mayar da noor dakin ta kuma kana kallo da kai da duk wani wanda baya so zata koma dakina"
Fuuu ya wuce ya bar fayyaz da farin cikin da baisan dalilin saukarsa ba ,
Zaiyyi mata farin ciki idan ta rabu da nas for sure amma wannan da yake ya wuce misali ya dade bai ji shi a farin ciki irin wannan ba "

Lecture din da ya karbar wa umma'ah ya tafi domin yayi cikin farin ciki"

Cikin nutsuwa yake basu lecture din kamar bashi da wani abu a gabansa face ilimin da yake basu,
Fayyaz kenan mutum ne shi da yake bawa kowanne abu muhimmacin sa idan yana bawa dalibai karatu baya dauko wani tunani yasaka aransa face wannan karatun da yake gabansa .

Kamar ance masa ya daga kansa ya hango udaysah da noor suna surutu kasa kasa,
Yi yayi kamar bai gansu ba amma ganin sunki bari yasa yace "
Hey ninja ke da friend dinki ku tashi ku fita "
Lokaci guda ajin ya dauke da dariyar dalibai  saboda sunan da yakira noor dashi na ninja"

Ranta ya baci dan haka ta tashi cikin fushi tabar ajin,mara mata baya udaysah tayi itama tana turirin fushi brother yanada wulakanci,

Zama sukayi a wajen ajin kasan cewar yana fita wani lecture din zaayi"
dafata udaysah tayi"
Look sweety forget about fayyaz,
Mai yahana ki zuwa school through out last week and anyi test fa har guda biyu Allah dai yasa naje na miki reporting "

Hmm bazaki gane ba nagode zanje nayi and ai nayi fushi dake ko ki kira kiji lapia na kalau"

Dan tsaki udaysah tayi bari kar ki tuno mun da abun bakin ciki brother fayyaz nefa ya kwace wayana daga kawai nayi wani bako wai sai akafara cewa dan iskane and umma'ah ta biye masa shine fa ya karbe wayana and beb bakiga guy din ba very hot .

Smiling noor tayi"
Kema kina da fitina ga mijin aure a gida amma kike ganin na waje"

Dan shiru udaysah tayi alamun tunani kafun tace wait wai kina nufin brother fayyaz ,
Wata dariya tasaka "
You're not okay ,I wont even give it a second thought aka aura mun fayyaz dambe zamunayi kamar mu kashe kanmu ,kibarni dai na samu dan chawaswas a waje ya fimun,
Yanzu mazannan da ba amana su tubirbidaka ma "
I'm sorry badan na fama miki wani guri na fada ba"

Dan dariya tayi tace "
Its okay fa nima Allah ya yaye mun"
Labarin abunda ya faru ta fara bata har karshe "

Rike baki udaysah tayi tace"
Just the guts,
Guy dinan yana da liver da yawa wato shi ba sakin ki yayi ba it was just a game "

Dariya tasaka kafun kuma ta ce im sorry ba wai abunne yake ban dariya ba kawai ina ma kokarinsa dariya amma trust ma naji maki dadi sosai wallah im very happy for you da Allah ya rabaki da nas dinan wallahi kwata kwata ba mijin aure bane ba "
Allah dai ya kara tsarewa "

Hmm Ameen to ni yanzu ma babu aure ko dating or what so ever a rayuwana karatuna ne main goal dina yanzun"

Ina bayanki "

Basuga fitarsa ba bayan ankare lecture din sai hayaniyar dalibai wanda shi ya tabbatar musu cewa ya fita din"

suna tashi sir Garrick  yana shiga dan haka kai tsaye suka koma ajin dan daukar next lecture tunda basu samu jin ta fayyaz ba.

Sai 4 suka gama lecture"

Udaysah ce ta tafi rakata gurin malaman da tayi missing test dinsu,
Aciki kuwa harda umma'ah,

Yauwa mufara zuwa gun umma'ah tukunna "
Aikuwa ba umma'ah tayi test dinan ba fayyaz ne kuma shi zai miki makeup"

Fayyaz kuma ".bata rai noor tayi na hakura".

Kallanta udaysah tayi tace you're not okay "
30 marks bansan ya zaki hadasu ba mainene damuwarki da shi just yayi miki test din da bakiyi ba shine damuwa come on my frnd"

Kamar jela haka tabi udaysah office din nasa ,
Knocking sukayi yace su shigo zaune sukaga wata yarinya yar final year mai suna shona ,
Yar kwalliyya ,kowa yasanta indai shona ne "
Sai wani kwaynane take masa shikuma gaba daya hankalinsa ma baya kanta complain din da ta kawo masa na bataga test dinta ba kawai yake dubawa"

Kallanta yayi fuska ba wasa yace "
Baki rubuta test dinnan ba amma sabida kince kinyi submitting kuma harda class captain dinki yace kinyi din shiyasa zan miki wani "
Kizo gobe around 9 kiyi wani"

Da wani iyayi ta amsa da to wanda saida yasa noor da udaysah suka kalli juna suna boye dariyarsu"

Kallanshi ya maida kansu bayan shona ta fita yace yes whats the complain and wane yake dashi"

Its me sir noor ta bashi amsa tana mamakin mood swings dinsa"

Okay daya fa mene nata complain din"

da takaici udaysah tace brother kasan fa rakota nayi"

Bai dago ba yace okay get out tunda ba wani abu mai muhimmanci ne ya kawoki ba.

Bata kuma cemasa komai ba ta fice a office din tana mai jin haushin sa idan wulakancine to nan yafi kauri and wallahi sai yabata wayarta aikin banza .

Chu chu jay✍️

Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top