chapter 23

Noorurrahman✔

Kowa ya hallara a cikin babban falon da ake zama dan tattauna damuwar familyn amma banda nas wanda anfi mintuna talatin ana jiransa "
Ran Abba idan yayi dubu ya baci saboda babu wanda ke tsallake lokacin da baba Alhaji yasaka musamman idan yayi irin wannan kiran wanda kowa yasan kira ne mai muhimmanci duk da kuwa bai fada musu dalili ba "

Kallan ummi Abba yayi a karo na babu iyaka yace "
Waini kam yaron nan naki mai ya mayar da mutane ne ki sake kiransa bamu taru anan gurin bafa domin mujirasa ba"

Dan murguda baki tayi ta juyarda kai dan kara kiran nas din"

Kamar an jefosa haka ya shigo falon bakinsa dauke da Sallama"
Afuwan wallah holdup ne ya rikeni "
Zama yayi ya gaisar da iyayensa inda kanennasa suka gaisheshi ,noor kuwa dauke kai tayi dan bata san ma tayi masa magana"
Kula da hakan da Abba yayi ne ya tabbatar masa da cewa matsalar daga su ne "

Kallan kowa na dakin nas yayi ganin kowa da kowa ya hallarta ciki kuwa harda farhana da mahnaz hakan ya tabbatar masa yau ranar tonan asirice "

Umartar muhammadu auwal baba yayi ya bude taro da adduaa "..
Bayan yayi adduan ne baba yafara magana kamar haka"
Godia ta tabbata ga Allah da ya bamu damar tashi cikin koshin lapia."
A taron da ya taramu na baya munyi shine a kan nasiru da matarsa noor to yau ma dai su dinne suka tara mu "
Wato jiya na dawo nake samun labari a bakin ita mahaifuyar noor kan cewa nasiru ya saki noorrurahman har saki biyu"

Saki "
Abba ya fada cike da mamaki "
Kallansa ya maida kan nas ".a'a ashe da abunda ka shuka dole ka barmu muna jira dan uwarka sai kamana bayanin abunda yasa ka saketa "

Kasa yayi da kansa gabansa na dukan uku uku,"Abba wallahi ni ba sakinta nayi da gaske ba sakin gan gan ne"

Dauke masa fuska da mari Abba yayi"
Kaci ubanka ,nace kaci ubanka dama ana sakin gan gan ne ,nizaka fadawa sakin gan gan"
Noor yanzu fada mun abunda ya faru"

Babu musu ta zayyano duk abunda ya faru da yarda ya mata sakin karkashin game kuma cikin maye "

Maye Abba da baba suka fada a tare"
Dama nasiru na shaye shaye baki taba fada ba "
Abba ya Kara ,
Yanzu inaso kifadamun duk abunda yayi miki da kuna tare kar ki boyemun wallahi sai  na saba masa yarda baya tsammani "
Yaya kabarni yau na yanken hukuncin nan da kaina kasan kamun al kawari last time"

Kada kai baba yayi yace nabaka amma inaso abawa nasiru dama shima yafadi ta bakinsa karkayi mamaki jairar ita take tunzura shi kai nasiru abunda ta fada gaskiya ne"

Baya so yayi karya a hanashi matarshi dan haka yasa yace eh baba komai ta fada gaskiya ne amma ayi min afuwa wallahi inasan matata sharrin shaidan ne da kuma bad friends influence amma baba a cikin zuciyata under dare na saketa ba akan sakin addini ba"

Yar dariya Abba yasa kafun yace Allah wadai da hallayya irin taka ,ina takaici ace yau ni ne nan wanda ya haifeka kuma ya baka tarbiyya a matsayin uba "
To Saki Saki ne idan ka manta ilimin addinin da muka baka bari na tuna maka ,idan ka saki matarka a cikin maye ko a hankalinka to dukkansu saki ne,kuma noor daga yau ba matar ka bace kuma bazata kuma zama matar ka ba, kuma daga nan kar na sake ganin kafarka cikin gidana "

Katsesa baba yayi ' a'a umaru ba ayi haka ba,shifa sha'anin aure kasan yarda yake '

Addua noor take kar baba ya kwafsa mata bata san lokacin da tace "
Baba dan Allah kar kuce na koma gidan yaya nas "
Dukkan abunda yayi mun a lokacin auren mu na yafe masa kuma kun hane mu da tonawa mazajen mu asiri dan haka zan bar komai a matsayin sirrin mijina amma dan Allah Abba kasa baki kar baba yace na koma gidan yaya nas dan Allah"

DA mamaki nas yace noor yanzu duk soyayyar da nake miki kinfi so a rabamu ,kina tunanin da wanda zai kare mutuncin ki sama dani dan uwanki da muka hada jini daya ,haba noor nasan ki da hakuri da yafiya dan Allah kar ki bari a rabamu"
Da sauri ummi tace kaidai anyi talasolon namiji akan matar dake ikirarin zata kasheka idan baka saketaba ita kake so kamayar gidanka ,matar da ke zaginka uwa uba ita kake ma wannann abun ,ko baayi hakaba inace har gidan naje "

Keep quiet woman "
Baki taba kashe abu sai dai ki assasashi"
Inace a cikin rashin tarbiyyarki yake koyan wani abun"

A'a umaru abun dubawane ,yaran yanzu baka shaidarsu kai nasiru da gaskene abunda umminkan ta fada kan noor tana ikirarin zata kasheka idan baka saketaba"

Girgiza kai yayi dan yasa a ransa zai fadi gaskiya ko gaskiyarsa zata saka a mayar masa da matarsa"
Aa baba bata taba ikirarin zata kasheni ba nafadane ranar sabida sabanin da muka samu amma baba noor matace ta kirki wadda samun irinta yana da wuya"

Aikuwa ka rasata Abba ya fada a fusace "
Babu yarda za'ayi ace mu baka yarinya kana cutar da ita dan bakar mugunta ,ankare"

Rokansa ya mayar ga baba ,dan Allah baba a tausayamun wallahi zan shiryu nayi alkawarin barin duk wani hallayya mara kyau, dan Allah baba kaji kaina kar ka bari a rabani da noor"

Bangaren noor kuwa jitake kamar ta saka masa duka ganin yarda yake ta magiyar kar a rabashi da ita kamar gaske,
Addua kawai take aranta Allah ya taimaketa ,ta wani bangaren kuma idan ta tuna da abba a gurin sai taji sanyi aranta ".

Gyaran murya baba yayi kafun ya fara magana"
To mun hada auren ku ne dama sabida cikar zumuncin mu wanda munso ya tafi yarda ya kamata amma aka samu akasin haka "
Ni bazance noor dole sai ta koma gidanka ba amma idan har kuka sasanta kanku kaida ita to falillahil hamdu mu haka muke so amma idan har baku daidai ta ba to babu yarda zamuyi sai hakuri sannan maganar muhammadu da farhana da mukai an janye tunda naga abun idan muka muku mu muna ganin gatane sai kuma ku bamu kunya ,duk wanda a cikinku ya samu wanda yakeso sai ya kawo maganar gida ayi kunga duk abunda ya tashi ba fata ba kai dai ka kawo bamu muka zaba maka ba "
Addua yayi taro ya watse ".wani dadi abba yaji dan yasan halin yayan nasa yanzu sai yayi ma noor dole wanda shikuma bazai lamunta ba abun ai da cutarwa "

Kowa ya watse dakin aka bar daga ummi sai farhana sai kuma nas da yake sharar kuka na ba gaira ba dalili"

Tsaki ummi tasaka "
amma dai wallahi kai ko anyi sakarai,
Akan mace kake kuka macen ma wai noor"
Ka bude makogaro yana mai kiran sallah kake ta kuka wai kai an raba ka da noor,
To wallahi kaji da kyau idan har ina raye baka isa ka maida noor ba ,kai babu ma yarda zaayi kusake zaman aure tare badai ni ka karyata ka goyi bayantaba "

cikin kukan yace ummi bakisan mai nake jiba ni bansan ina san noor ba sai da ta subucemun kuma har ga Allah na cutar da ita sosai, bazaki gane mai nake nufiba sabida shi sirrin dake cikin aure sai ma'aurata biyu ,kuma ranar danace miki zata kasheni ai yaci ace kinsan karya nake "
Ummi yau da'ace  noor ta fallasa asirin auren mu inajin abba tsine mun zaiyyi"

Tsaki tayi akaro na ba iyaka tace
"Shashasha,zan karya asirin dake dawainiyya da kai ne sannan shima Abban naku dake rawar kai akansu zan maganinsa "

Sai a wannan lokacinne farhana tayi magana "
Ummi kenan ,kinfa fi kowa sanin cewa danki bashi da gaskiya zancen Allah fa "
Kamar kece Abba ya kawo miki yan iska yan shaye shaye sannan ya sakeki karkashin daregame  ya zakiji"

Kutumar uwarki"
Ummi ta sirfo mata ashar"ni kike ma fata  asaka karkashin dare dan kanwar uwarki"
Ni kike jawowa mugun al kabai"

Ashe dai kema ummi kinsan babu dadi"
Mikewa tayi ta kara da cewa nidai yaya nas ya riga ya jawomun tsiya ,ke kanki ummi kinsan ai inasan yaya moha gashi sabida ku aurenmu ya baci dama kuma nasan shi yaya mohan ba sona yake ba "kowa yaji da kanshi amma fa ku sani a cikin rabuwar nan yaya nas shike da asara ba noor ba dan wallahi samun iri ta sai an ton kai ko an tona din ma da wuyaa, ku gwada kugani"
Barin gun tayi tana jiyo sautin ashar din da ummi ke sarfafo mata ,
Sudai basuyi sa'ar uwa ba gashinan sanadin hakan yasa suma basu da wata isashiyar tarbiyya amma insha allahu sai ta auri yaya muhammad Allah dai ya taimaketa dan wallahi sanshi ya mata da bai bayi kuma idan bata sameshi ba akwai damuwa mai tsanani"

Ganin nas bazai daina kukan banzan da take kira bane yasa ta tashi ta bar mishi gun tana ta ruwan balai"

Shima bayan tafiyar ummin ya mike dan komawa gida yasa aransa duk wuya duk runtsi sai ya maida noor matarsa kuma yayi ma kansa Alkwarin bata soyayya mai inganci indai shine nasir".

Chu chu jay✍️

Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top