chapter 22

Noorurrahman✔

Kai tsaye bathroom ya shiga bayan ya wuce dakinsa ya sakarma kansa ruwan sanyi,
No ,No this cant be happening ,
No ,no way babu yarda zaayi duk matan duniyarnan ya fada san matar aure ,no he was only trying to help her sabida Allah amma badan selfish reason ba har ga Zuciyarsa amma mai yasa wanann abun kuma zai bijiro ,
Kada kansa yayi "
A'a umma'ah bata fahimci mai yake nufi sosaiba ,
To in ma hakane dole ya nisanta kansa nadan wani lokaci dan yaga mai kuma zai faru ,

***************************************
Tafe suke ita da udaysah suna hira amma gaba daya hankalinta baga hirar yake ba wani tunanin chan tatafi,
Dafata udaysah tayi "
Wai tunanin me kikeyi haka ina ta surutu amma gaba daya ma ke hankalinki yaje wani guri daban"

Murmushi tayi"
Kibari kawai dan adam ai baya rabuwa da tunanin duniya "

Allah yasa na duniyar kawai kike ,zo ki rakani gurin sir fayyaz na karbi abu "

DA sauri tace baza ni ba wallahi ,
Dan kallanta udaysah tayi da alamun tambaya "
And why ?

Haka nan bazani bane kedai kije sai gobe ma hadu "

Inane bazaaje ba
Muryarsa ta katse su "
A tare suka juya ,suna hada idanu ya dauke idansa ya maidasu kan udaysah".
Ganin ya yi hakkan ne yasa ta juya batareda tayi ma udaysah sallamaba ta tafi "

Kallonsa udaysah tayi"
Brother mene kana ganin noor kawani bata rai gashi kasa tatafi"

wuce muje na baki wayanki dan Allah ki wuce ki tafi banasan surutu .

Bataja ba tabi bayansa batareda tasa abun a cikin kanta ba"

........
Tundaga bakin gate take jin karar kida ,
Kasan Cewar ba bakon abu bane a gurinta yasa tashiga gidan hankalinta a kwance ,

Ta backyard ta shiga dan tasan babu mamaki shida jamaarsane "
Daki tashiga batareda ta shiga falon ba ,
Kai tsaye wanka ta shiga dan gaba daya jikinta a gajiye yake ,
Tana bayi taji alamun mutum ya bude mata wardrobe,tasan shine dan haka ta karasa alwalarta a tsanake.

Farin towel dinta ta jawo ta daura sannan ta fita daga bathroom din"

Da mamaki cike a fuskarta take kallon mama a bakin wardrobe dinta tana firfito mata da kaya"

Karasawa tayi da mamakindai da yakasa barinta"
Hannun mama dake kokarin jawo set din kayanta na sama tayi"
"Baiwar Allah lapia,kin mun ajiya ne.

A wani chake mama ta juyo tana kallan noor
"DA murya irin ta wadanda suke lintsum cikin maye tace"
Ke ,ke ,ke bakki da hankali zaki da-dameeni ni a dakina"
Zan zan abunda naga da-dama da kayanki babu yarda zakiyi dan gemun tsohhoo"

Batasan lokacin da ta dauketa da mari ba,katon hijabin da yake kaimata harkasa tasaka "
Hannunta ta kama ta jawota har falon da yake cike da yan iskan abokanan nas.

DA Sauri nas dake rike da pipe ya karaso garesu"
Wani irin kallan kyama noor ta bishi dashi
Yana kokarin magana ta daga mishi hannu "
Kaga malam dakata "
Dama ni nasan za'ayi haka ai babu yarda zaayi ace dan mai tulo yaki deban ruwa"
Wallahi tallahi tir da halayyarka "_
Allah wadaran naka ya lalace ,

Da karfi mama ta fisge hannunta ta fada jikin nas wanda kana kallansa kasan shima a bugen yake "
Kukan munafurci tasaka tace "
Baby bakaga marinn da da ta mun ba .

Dan tureta ya fara yana cewa mama na fada miki yau ranan noor ne ,
And Mai zaisa ta mareki"

Jin muryarsa dauke da mayene yasaka taji wani bakin ciki a wuyanta wai yau wannan ne mijin aurenka da zakayi alfahari da
,juyawa tayi zata tafi taji muryar daya daga cikin abokansa yana cewa ,nas bafa haka mukayi da kai ba game dinnan na truth or dare kasan rules dinsa and ka zaba dare kuma harisco dare you to divorce noor 2 times in ka isa, ai game ne ba wani abu ba sakin doesn't count"
Gabanta ne yayi mumunar faduwa "

Dariya nas ya saka  au na manta wallahi ,
Ni nas na saki noor saki daya, biyu under dare,
Wata irin shewa suka saka baki dayan su inda itakuma noor taji kamar an watsa mata garwashi a cikin kirji,
Tabbas tana san nas ya saketa amma ba ta wannan hanyar ba amma ko ma yaya ne saki sakine kuma ta riga ta saku babu yarda zaiyyi.

Tafiyya ta farayi ya rikota ,juyowa tayi tamasa wani irin banzan kallo,
Zaka cikanine ko sai na falla maka mari akan fuskar kanan and trust me idan na kwada maka mari saika fita daga mayen da kake yanzunnan babu bata lokaci ,.cikani.

dan lankwashe wuya yayi yace "don't telll me noor har yanzu kina fushi dani ,nahada party dinan ne fa saboda ke i even ordered cake for you ,
And nasan you'll like everything about today ,
Hannunta biyar ta sauke masa a fuska kafin yasake magana ta kara kwasheshi da wani marin ,idanunta sunyi ja sabida takaici.
"Idan dukkanku nan taran jahilai ne ni ba jahila bace nayi mamaki yarda kazama jahili lokaci guda to inaso kasani aurena dakai ya kare a nan gurin kuma inaso kasa aranka cewa daganan aurenmu ya kare har abada .

Daki ta shige ta jawo akwatinta guda biyu ta fara loda kaya tana sharar kwalla"
Da gudunsa ya shigo dakin ya rike hannunta daga saka takalmin da zatayi cikin akwati "
Zaman dirshan yayi a kasa"
Noor look dan Allah ki rufa mun asiri dan Allah dan annabi ,wallahi tallahi ni ba sakinki nayi ba game ne kawai fa and kinaji sukafada game ne trust me haka nan bazan sakeki ba and har cikin zuciyata ma Allah yasani dana fada a matsayi dare yake "

Hannunsa ta bige ,
Ka fita daga mayen kenan"
DA sauri yace dama fa ba maye nake ba noor hankalina daya fa "

Dariya tayi ta takaici dama ai dan maye akwai musu ,kar ka sake rikeni wallahi idan ka kuma zan illataka na ranste da Allah "

Rufe akwatinan tayi ta jasu ta fita ta kofar baya,tanajan akwatinan biyu cikin karfin hali yana binta abaya yana mata magiya "
Maigadi ta kwalama kira ,da saurinsa ya zo yana cewa hajjaju gani"

Kai min akwatinan nan titi,
Lapia dai baba maigadi ya tambaya"

Lapia ta bashi amsa kaidai kaimun titi kawai"
Yana kokarin ja nas ya buga masa tsawa amma maimakon ya bari sai yayi gaba yana murnar abun dan shi yasani noor tachanci mijin da yafi nas yana tausayin yarinyar sosai "

rufa masa baya tayi nas kuma na bayanta yana ta mata magiya"
Noor dan girma Allah kar ki tona mana asiri kizo muyi zamanmu babu wanda ya sani fa daga ni sai ke dan Allah noor Abba zai bani kashin tsiya dan girman Allah kar kije kice na sakeki wallahi ni ban sake kiba "
Bata kulashiba ta haye keken da baba mai gadi ya tsarar mata wanda already an loda kayanta a ciki,

Yana magiyarsa tace me keken su tafi"

Wani banzan kallo yabawa baba maigadi "
Daga nan kaje ka kwashe kayanka na koreka".

Ba komai matarka ma ta bar gidan ballanta na ni dama sabida ita nake zaune amma yanzu bazan iya gadin mashayi ba.

Bai bi ta kanshi ba ya koma gidan dan dauko motarsa yabi noor"

Kai tsaye gida mai keken ya aje noor ,
Tana kokarin jawo akwatinan nata muhammadu auwal ya iso gurin cikin motarsa "
A kofar gidan yayi parking motar ya fito yana kallonta da mamaki".
Lapia ke kuma da akwatina rigim rigim"
Fadawa jikinsa tayi tasaka kuka mai cin rai"

Okay yi shiru haka mushiga ciki tukunna"

Akwatin ya ja da taimakon mai gadin gidansu aka shigar mata dasu ".

Mami dake zaune falo mahnaz na yanke mata farce ta mike tana tambayar lapia "
Shigowa noor tayi still tana kuka ,
Jikin mami ta fada ta cigaba da kukan ,
Zaunar da ita mami tayi tace mahnaz kawo mata ruwa ,
Jiki a sabule mahnaz ta tashi dan kawowa noor ruwa"

Saida ta sha ruwan tayi kukanta mai isarta kafun mami tace idan kingama kukan sai ki fada mana mai ya faru ,mai nasirun yayi miki"

Mami sakina yayi saki biyu"

wani dogon tsaki muhammadu auwal yayi
"Shine kike wannan kukan kamar ranki zai fita menene dan nas ya sakeki"

Cikin shashshekar kuka tace nifa yaya ba sakinne yake sani kuka ba yarda ya sakeni ne yake kara bakantan rai yaya cikin abokansa fa ,kuma wai a matsayin dare ,kuma yaya acikin maye "

Maye ,"
Tare mami da muhammadu auwal suka hada baki wajen tambaya"
Dama nas na shaye shaye mami tasake tamabaya cikin rudu"

Eh ta kada kai tafara bawa mami labarin abinda ya yafaru a  yau din ta kara dacewa mami dan Allah kar ki bari baba Alhaji ya mayar dani gidan yaya nas wallahi bazan iya kara zama dashi ba wallahi mami na cutu"

Rungume ta mami tayi cike da tausayi ,
Insha Allahu noor bazaki kara komawa gidan sa ba bari baban naki yadawo duk yarda zaayi sai dai ayi amma bazan yarda ki koma gidan dan maye ba yanzu je daki kinhuta ,
Mahnaz kai mata maganin ciwan kannan da na baki dazu dan naji kanta yayi zafi"

Bayan sun tafi ne muhammad ya kalli mami"
To yanzu mami mai auran nan ya haifar shi yasa nace ni bazan auri farhanaba dan bana santa ,ita yanzu noor kalli da yarintarta ya maidata karamar bazawara maine amfanin haka dan Allah,dama ni tun a police station dinnan nake zargin da kyar idan baya shaye shaye ,kwata kwata abun da yayi bana dauka bane bari baban ya dawo kuma wallahi sai ya gane ya wulakanta noor"

Ajiyar zuciya mami tayi tace baruwanka dashi su Alhajin nasan ai bazasu juyawa maganar bayaba zasu zo sai dai ayita ta kare amma muddin sukace zasu maidata gidan nasiru sai inda karfina ya kare wallahi nayi na Allah banni kuma wani hakurin babu nasiru babu noor Allah ya hada kowa da rabonsa.

Chuchujay✍️

Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top