chapter 21

Noorrurrahman✔

Kallan ummi yayi yarda ta wani hade rai,
Lallai aikuwa bazata sabuba "
Ummi kiyi hakuri dan Allah nace miki wannan abun ya wuce mai yasa kike kuma jansa ,idan na saketa ai an bata abunda take so kenan"

Sakin baki ummi tayi ,
Shikenan sun shanye mun kai ,nace idan na isa da kai kaki sakinta sabida sun maka tofi kalashe,
Wallahi bazai iyu ba,
Matsar kwalla ta fara tana sumumin bala'i.
Wallahi tallahi bazan yarda ba bama zata taba iyuwaba ,
Wallahi Allah,.

Tashi yayi ya karass gurinta,
Ummi muje na kaiki gida dan Allah ,buge hannunsa tayi,
DA kai ka kawoni sakaran banza talasolan namiji wanda aka gama shanyewa ,
Duban noor tayi,wallahi sai kinci uwarki.

Janta yayi suka fita yana rarrashinta ,
Tsaye tayi tana kallansa"
Nas anya ba saina nema maka taimako ba,

Yar dariya yayi sanin tsiyar shi ya shukata ,
Haba ummi baki yarda daniba kenan,
Ai tunda ta fito ta nuna sakin takeso gwara a nuna mata bata isaba ta hanyar hanata abun da takeso kinga idan taga dama sai ta kashe kanta ,
Ummi nas dinki nefa kinsan mai zanyi da abunda bazan yiba ,

Dan sassautawa tayi,
To yanzu naji batu,babu komai ka tabbatar ka bata kashin tsiya yarda shegen bakin da yake neman saki zai kumbura yayi tsini"

Haka ya lallabata ta tafi cikeda jin haushin noor".

Dawowa yayi cikin gidan babu kunya,
Inda ya tafi ya barta nan ya sameta tana sharar kwalla"
Wuceta yayi yana wani daure fuska shi a lallai isasshe"

Amma ya nas bantaba tunanin zaka iya min karya har haka ba ,
Ni ba jahila bace kuma bazan taba ma wani ikirarin zan kasheshiba koda wasa..

Wannan maganar banasan ana tayar da ita kingane ,"
Cikin fadi ya cigaba da tafiya shi kwaro,

Da kallo ta bishi har ya bacewa ganinta *
Nasiru kenan .

*****************************************
Yau monday kamar kullum yauma haka tatashi babu wata walwala,tafara manta menene walwala gaba daya,
Idan tayi dariya to tana tareda udaysah ne amma muddin ta dawo gida duk wata sakewarta ta kare,

Mutane da dama zakaji suna fadar dadin zaman gidan aurensu ,zataji suna cewa gidan miji da dadi amma fa ita akasin hakkanne dan jitake gidan nas kamar kurkuku,.
Bata sake bari hanya ta hadata da fayyaz ba gudun kar ma ya taso mata maganar ranar,
Yayi duk yarda zaiyyi su hadu amma ta ki batasan abunda zai kuma zuwa ya zaman mata matsala,

Fitowa tayi da shirinta na zuwa makaranta,
Coffee machine tanufa ta hada coffee duk yana zaune baice mata komaiba itama bata ce masa komai ba ,
A kujeran dining ta zauna tana sipping coffee din a hankali"

Ke yanzu kin daina gaisheni ko"

Eh banga kamala a tattare da kaiba wadda zatasaka na gaisheka ,
Tariga ta kare tuni..
Kitchen ta kai cup din ta fito zata wuce.

A bakin kofar da zata sadata da waje sukayi kicibis,
Hannunshi yasa ya tokare inda zata wuce "

Matsa zan wuce "

BaBu inda zak yau sai munyi settling differences dinmu"

Dariya tayi tace "
Yaya nas wanne differences ne ke tsakanin mu kuma i thought mun riga mungama clearing komai ,ina tunanin kace nace zan kasheka ,shiyasa nake zaman jiran sakina sabida bazani gida batareda takardar saki ba so kawai ka hutama kanka ka sakeni sabida ni ina tantamar ingancin aurenmu.

"Amma noor ke bansan yaushe zakisan wasa ba ,kin manta a april fa muke shine nayi miki keda ummi april fool"

Wani kallan banza tamishi "
Yaya nas kenan tsakanina da ummi sai ka dubo fool din april amma ni im not a one fool of april.
Matsa na wuce.

Kara gyara tsayuwarsa yayi yace"
To noor naji na janye kiyi hakuri nasan ban kyautaba kwana biyunnan a matse nake kuma ke kadai ke gamsar dani dan Allah ina wani hali in yaso daga baya sai ki cigaba da fushin nasan zaki sauko,

Tsaki tayi dan bata da lokacin cigaba sauraransa ,hannunsa ta fincike agurin ta wuce "

Cikin daga murya yake cewa"
Zan hada miki surprise idan kin dawo nasan you'll forgive me'

Bata kulashi ba ta fice a gidan .

Dan murmushi yayi yasan tabbas noor zata yafe masa sabida she's naive .

*****************************************
Kasancewar yau din lecture din shabiyu ne da ita yasa ta tafi inda suka saba zama ita da udaysah ,bata fada mata zatazo da wuri ba hakazalika bata kira tace mata tazo ba, tana bukatar space tana san tayi clearing kan ta for a while"
Alamun mutum taji tsaye kanta,bude idanu tayi dan tunaninta yafi karkata kan udaysah ce "

Fayyaz ne tsaye kanta ,
Maida idanunta tayi ta kulle dan batasan yi masa magana dan idan zaiyyi wata magana tasan akan yaya nas zaiyyi"
.zama yayi dan nesa da ita ,
Ajiyar zuciya yayi yace"
Noorurrahman kin gama guje gujen"

Ina wuni" shine kawai abunda tace masa tayi shiru"

Lapia lau noorrurrahman"
Idan gaisuwar har zuciya kika mun,
Akan abunda ya faru a gidanki,
Kiyi tunani mana hakan dai dai ne ,baki tunanin its not okay "

Kallanta ta maida gareshi tace"
Wai na tambayeka"

Ehem inajinki"

Mai yasa kakeson jefakanka cikin rayuwata"

Good question"
Kinga nima yin hakan ba halina bane ba rayuwana bane kuma duk wanda yasanni zai fada miki haka,
I mean just look at me "
Bansan mai yasa nake da raayi akan rayuwar kiba ,wallahi kullum sai nasa a raina cewa ba abunda ya shafeni bane rayuwarki amma sai nakasa cire kaina a ciki".
Its getting on my nerves seriously.
Hannunsa yasa yayi brushing cikin gashinsa in frustration.
Kawai inasan ganinki cikin farin ciki that's all, nasa irin haduwar da mukai bai kamata ace ita mukai ba amma mu barshi a destiny".
So yanzu mai kikace"
How about my offer",

Ajiyar zuciya tayi tace.".
Sir fayyaz"

Fayyaz nace miki kidaina kirana sir fayyaz"

Okay fayyaz dan Allah ka tashi ka tafi ,duk wanda ya ganmu zayyi tunanin wani abu ,sannan ni ba muharramarka bace haramunne kana kebewa da ni a matsayina na matar aure dan Allah ka rabu dani,i really do appreciate kulawarka gareni nagode wallahi sosai,
Hannayenta biyu ta hada alamar roko.

Bai ce mata komai ba illa tashin da yayi dan komawa inda yafito,
Binsa tayi da idanu har ya bace mata,wani iri takeji azuciyarta bataso ta yaudari kanta ,duk da aurenta gashinan ne dai amma ba a suna bane bazata aikata ba daidai ba abayanshi ,zatayi duk yarda zatayi ta gudu daga zugin shaitan dan yafara mata aiki ta hanyar kawata mata fayyaz"
Fayyaz mai kyaune ,namiji mai aji ,kyau da gayu ,bazaka kallesa a kalo daya ba kace bazaka karaba ,
Da wuya ka kalleshi kaga bai burgeka ba to gudun wannan abun dole ta nesanta kanta dashi dan zuciyarta tana jimata wani abu game dashi idan yana zuwa inda take musamman da yake nuna kulawarsa kuma yake daukar damuwarta tashi.

****************************************
Kai tsaye motarsa yaje ya dauka ya tafi gida, abunda noorrurahman tafada babu kuskure haka yake,amma mey yakasa cireta da damuwarta a lissafinsa ,abun yana damunsa har gaban sosai amma ya rasa yarda zaiyyi, wai yau shi fayyaz ne mace ke kuransa macen ma matar wani shin menene yake damun shine "

Yana shiga gida part din umma'ah ya tafi kai tsaye,
Ita kadai ya samu a falonta tana danna waya ,
Sallama yayi mata ya shiga ya zauna ,
Kallansa tayi a tsanake bayan ta amsa sallamar ,
Thought yau sai yamma zaka dawo gida"

Shafa kansa yayi wanda sabonsa ne yace
"Wallahi Umma'ah kainane yayi zafi shiyasa nazo na huta inyaso idan zaki shiga makarantar ma shiga tare"

Okay yayi dama yau munada bakin turawa dake babban branch dinmu na turkiya"
Kasansu da fitina da kale kale yanzu zasu nemo wallen mutum
Badan su bama bazaniba sabida yau banida lecture amma prof alex yace na daure na zo"

Gutsiran apple din da ke hannunsa yayi yace "
To nan din ma mene banbanci duk su suka cika staffs bakaken ai kirgaggune"
Allah dai ya kyauta"

Umma'ah na tambayeki mana"

Uhum inajinka menene ya faru auta"

Dan kasa yayi da kansa yana tunanin taya zai tambayeta amma sai ya maze sabida karta gano akanshine zai mata tambayar"
Nace umma'ah menene yakesawa kaji lokaci daya ka damu da mutum kaji kawai kai kanaso ka fitar dashi a adamuwa duk yarda kuwa kaso ka hani kanka sai kaji damuwarsa na kara damunka,.sai kanajin kai babban burinka shine kaga wannan mutumin cikin farin ciki and kinsa umma'ah the funny thing is that farkon haduwarku da bad impression ya Fara ,
As in you can't stand mutumin sabida yayi maka abunda bakaso sai kaji gaba daya ka tsaneshi then suddenly kuma da kaganshi cikin wani hali kakejin zafin abunda ke damunsa sosai a cikin zuciya maine yake kawo hakkan umma'ah..

Aje wayanta tayi ta kalleshi da kyau sai kuma ta fara murmushi"
Wanene haka kake ma wannan damuwa"
Dan sauri dage gira yayi,
Umma'ah nikuma ,
Haba dai you know me best ba dai ni ba dama wani abokinane yake jin irin haka,
Haba ni kuma ,fayyaz ,"an tambayeni ne nikuma bani da amsa sabida duk irin wannan abun bansan suba shiyasa nace zan tambaya mishi ke"

Nunawa tayi kamar bata dago shi ba tace "
To acikin abokan naka ,salim ne ko imran nidai su nasani shakikan abokanka wanene daga ciki na tayashi murna ya kamu da soyayya"

Kwarewa yayi daga hadiye grape din dayake kokarin yi ,
DA sauri ya dauki ruwa ya kora kafun ya kalli umma'ah da idanunsa da suka dan kada sabida kwarewar ,
soyayya kuma umma'ah ana zaman lapia,

A'a mene abun tashin hankali kuma ko shi abokin naka an fada maka yana gudun fadawa soyayyar ne kamar kai,
Ai duk wanda yake jin irin wadancan abunda ka lissafo muddin akan mace ne to akwai soyayayarta da tausayinta masu tarijn yawa a zuciyarsa ,sai dai kawai mutayashi da addua da fatan Allah ya cire masoyiyar tashi cikin damuwar da take sannan Allah yasa soyayyarsa tazama mutual kuma mai Alheri"
Daukar wayarsa yayi daga kan center table din da umma'ah ta ja gabanta  tareda mikewa,
"Bari naje na dan watsa ruwa umma'ah nadanyi baccin hour then mu wuce"

Ha an ya kuma bamu gama maganar ba zaka tashi ina salim ya samu yarinya haka"

Da shagwabe fuska yayi
"Umma'ah nifa bance miki salim ko wani imran ba kawai tunaninkine, wani abokinane da muka hadu a Jamaica kwanaki dont get it twisted nidai saina fito.

Dariya tayi kasa kasa bayan ya tafi
"Yaro kenan yamanta shaf ni na haifesa,
Wani farin ciki ke ratsa ta zataso taga wacece wannan da tayi mata charaf da zuciyar yaro dan ko bai fada mata shine ba to tasan shi dinni Allah yasa yar gidan mutuncice ,tasan dai bazai cigaba da boye taba har abada.

Chu chu jay✍️

Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top