chapter 19

Noorurrahman✔

Shi yafara fita kafun su.
Ki shiga gaba tunda ni zaa fara saukewa sai.....

Bata tsaya jin karshen zancen nataba ta bude kofar baya ta shige"
sanin halin fayyaz na bata isa ya tuka mota tana bayaba yasa udaysah yin dariya ta shiga gaba "badai zaa sauke taba zataga ya zasu kare.

Ribado road suka fara zuwa suka sauke udaysah,
Sallama tayi ma noor kan sai sun hadu a makaranta ,

Bayan wucewar udaysah taji shiru yaki tada mota itakuma jira take taga sun tafi dan hankalinta ba a kwance yake ba musamman da umma'ah ta kara tunatar da ita tsinuwar malaiku akan matar da ta je guri bada umarnin mijinta ba.

Kallanta yake ta cikin mirror itama sai ta kalleshi din then ta dauke idanunta ta maidasu titi,
Kallan agogon hannunta tayi taga 5:30,

"Sir fayyaz hala motar ta samu matsalane "
Ta tsinci kanta da fada"

Gyara zamansa yayi"
Bawata matsala amma bana tunanin nazama driver dinki ai,
Shiru tayi tana nazarin zama agaban,tasan ba daidai bane ace tana zaune gaban motar malaminta a matsayinta kuma na matar aure"

Dan rumtse idanu tayi "
Sir fayyaz bari na sauka nan sai kawai na hau keke tunda na kusa gida ma Allah ya saka da Alheri"
Tana kokarin bude motar ya saka lock'
"
Idan baki dawo gabannan kinzauna ba to ki tabbatar wannan useless mijin naki zai dumamaki sabida kinyi dare"

Batasan jan maganar yaya nas dashi dan haka tace "
Bude mun na fito na koma gaban"

Yar dariya yayi"
Ashe taurin kanki kadanne"
Bude mata lock din yayi tafito daga bayan ta shiga gaban gabadaya a dari dari'.
Ina muka nufa '

"Badawa"

Tada motar yayi yana smirking ".

Shiru suna tafiya babu wanda yace ma kowa komai".
Ita tana jinta a takure shikuma a takuren daya fahimci take yayi masa dadi"

Ke yanzu kin zabi zama da mijin da zai na dukanki ko"
Ya tsinci kansa da fada".
Kisani namiji idan ya zama mai duka da wuya ya chanza halayyarsa,
Kodayake bansan mai kika gani a taredashi ba da kika nace duk da irin cin kashin dayake miki,
Sai a lokacin ne ta dago idanunta ta kalleshi"
Sir fayyaz"

Fayyaz "
Kar ki sake kirana sir ,call me fayyaz please"

Okay fayyaz bansan mai yasa suddenly kakesan shiga hurumin aurena ba amma ni anawa sanin bamuyi wannan kusancin da zaisaka na raba damuwar aurena da kai ba and ni ban taba ce maka ina da damuwar aure ba,
So please with all due respect mu tsaya a matsayin malami da dalibarsa.

Dan murmushi yayi amma tabbas maganarta tayi masa zafi wanda baisan dalili ba ,
"Kar Ki damu, zan samu kusanci dake nasani and you'll share your problems with me nan kusa,
I'm willing to pest you,har sai kin saki jiki dani and trust me I mean no harm,
Kawai inada sudden urge ne na protecting dinki and trust me Nima bana san haka,

Zan sauka a nan shine kawai abunda ta iya fadamasa dan bata tunanin komai is okay"

Har kofar gida umma'ah tace na kaiki and bana mata rashin biyayya,ko kina tsoran kar mijinki ya ganmu yayi zargin wani abu,
Gaskiya mijin nan naki have a cheap mindset "

Kokarin bude kofar take amma ta kasa sabida yasakata a lock,
Fayyaz dan Allah open the door inace munzo badawa,

Eh munzo badawa amma muna bakin kofa so tell me wanne layi zamu shiga na kaiki na aje nima naje nayi abunda yake gabana ,
Gudun batawa kanta lokaci yasa ta masa kwatance ,
Saida sukaje daidai saitin gate din gidan kuma ya tabbatar ba karya take masa ba sannan ya bude mata lock din motar ,

Godia kawai ta masa ta bude motar zata fita ,
"Consider abunda nafada miki dazu , i am your well wisher sannan inasan fighting
Miki right dinki"
Bata ce masa komai ba ta bude motar ta fice ,
Tana fitowa a motar yana fitowa daga gidan ,
Kallan kallo suka fara bawa juna,haka kawai taji gabanta ya fadi dukda tasan ba wani abu mara kyau ta aikataba amma wani mumunan faduwan gaba taji ya ziyarceta,
Dakewa tayi ta rabe zata wuce ,
Hannunsa yasa ya fincikota waje "

Ashe gurin kwartan ki kika tafi shiyasa kika tafi daga restaurant din kamar guguwa"
To yau Allah ya tona miki asiri ashe bani kadaine dan iskan ba "
Kokarin kara rabesa tayi zata wuce gudun kar ya bar mata abun magama duk da unguwarsu ba mai yawan karikicen jamaa bace "
Kara finciko ta yayi ,
Ya daga hannu zai sauke mata a fuska ya ji an rike masa hannun tamaumau"

Dagowa yayi idanunsa cike da fitina ,
Au ka fito ka...
Bai karasaba ganin wanda ya rike masa hannun.
Ran Fayyaz yayi mumunan baci kallan nas yayi da kyau"
Amma kaji kunya kai ba namiji bane ,kai yanzu iskancinka har ya kai ka mari matarka a kofar gida sabida kawai mota ta sauke ta,wato yanzu na fahimta hala kana da biyebiyen mata shine kake tunanin duk motsin matarka na biye biyene,
Shame on you ,
Kaji kunya and you're not worth to be call a man,.
Kallansa ya maida kan noor wadda babu abunda ke zuba idanunta said hawaye ,kallo daya zaka mata kasan baccin rai na nan kwance kan fuskarta',
"Wuce muje na kaiki gida yau i will explain everything to your dad,zanyima Mahaifinki bayanin irin mijin da ya aura miki ,ni eye witnesses ne and zan fada ma mahaifinki yarda shameless mijinki yadaga hannu zai mareki a kofar gida,
Muje"

Fayyaz bai gajiya da bata mamaki ,
Wani lokacin ka gaza gane shi wani lokacin kuma idan yayi wani abu kamar bashiba ,
Jinjina karfin halinsa tayi amma for the first time taji dadin wani yau ya tsaya mata amma bazata bi fayyaz ba abu yazo ya tabarbare mata.
Tasan halin baba Alhaji tsaf ,yanzu reshe zai juye da mujiya musamman idan nas yace taje gidansu udaysah batareda saninsa ba ,baba bazai taba duba duk wani abu da zata fada ba akan nas din".

Cikin gidan ta shige tabar fayyaz da bude baki,
Dariya nas ya saka ganin noor ta gwasile fayyaz,
Wani mugun bacin raine tattare dashi, tabbas idan ya biye nas zai iya kashe banza sabida bakin cikin da ya shiga bazai misaltu ba ,

Wani haushinta da tausayinta ne suka dabaibayeshi,
Kallan nas da yake mai dariyar shakawa yayi,
Baiyyi wata wata ba ya kai masa naushi a fuska,
Shake masa kwalar riga yayi tareda nunasa da dan yatsa ,
Ka rubuta ka aje i will turn noor against you, sai na rabaka da ita na maka alkawari,
Noor ba kalar matar ka bace ,sai na rabata da wannan kazamin abun da kake kira gida,
Juyawa yayi a fusace ya nufi motarsa.

Hala kalar matar kace,
Nas ya jefesa da tambayar,
Idan ka isa ka rabani da ita mugani,
Ni da noor da kake gani sai ta Allah,
Kar ka manta babanta yayan mahaifi nane sannan duk duniya kowa zai fada masa laipi na bazai gani ba ,kana tunanin idan ka kai noor gida zata fada ne ,zan hada karyar da zata kwashi kashin tsiyane gun mahaifinta ka gwada kuma kagani,
Nida kai shege kafasa.

Wani yawon takaici fayyaz ya hadiya ,
Bai juyaba dan tabbas idan ya koma za'a iya daukar gawar nas a gurin dan sai ya shake masa wuya dan uwatar.
Motarsa ya shiga ya tasheta da mugun gudu ya bar unguwar".

Kai tsaye nas ya shiga gidan yana kwala kiran sunan noor .

Chu chu jay✍️

Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top