chapter 18

Noorurrahman✔

Dafe kuncinta tayi"
Ni kamara"
Ni xixoo ka mara,
Zakasan ka mareni ,ke kuma gwanda ki kama kanki dan wannan da kike gani SHEGENE,
Kuma daga ganinki sabon yanka ce"

Har ta juya zata tafi noor ta riko mata hannu"
Jiyowa xixoo tayi tana mata kallan lapia"

Dan murmushi noor tayi"
Kin gama zaki tafi baki jira ta bakin wannan sabon yankanba"
Listen idan kikaje guri kafun ki fadi wani abun akan mutum ki fara bude idanunki sosai ki kallesu kiga irinkine karuwai ko kuma akasin haka"

Listen nida kika ganni ba karuwa bace da namiji zai wulakanta anyhow,
Kuchakar da aka fada miki ita ke zaune and nasan kallo daya kinsan batayi kama da kuchakar ba,and abu daya danake san kisani duk na mijin da zai zagi matarsa a gaban ki to yanayi ne saboda samun wani abu a gareki ,ina nufin he was only trying to get through your pants , ke ai shaidace da yasamu biyan bukata yanzunnan ya nuna bai sanki ba saboda baki da daraja ,
Zaki iya tafiya amma kibi a hankali da rayuwa batada tabbas"

Ni kike fadawa magana san ranki?

"Anfada miki zaki dakenine "

Kada kai xixoo tayi tareda yin kwafa tabar gurin.

Maida kallanta tayi ga nas wanda ya zazzaro idanu kamar an kada bera a buta "

Noor I can explain"

Jakarta ta dauka batare da tace masa komai ba ta fice a restaurant din.

Dukan table din yayi da kafa ,
Mai yasa haka zai faru dashi ,uban mai ma ya kawo xixoo gurinnan da har ta bata masa komai nasa ,
Yafara samun yardar noor lokaci guda tazo ta dawo masa da komai sabo"
Binta yayi dan ya cimmata amma ko inuwarta bai gani ba yayi mamaki"

Wayar udaysah ta kira akan ta mata kwatancen gidansu zatazo in tana gida "

Location ta kunna mata ,
Tana fitowa kuwa cikin saa ta samu mai keke ya aje wasu"

A bakin gate din gidan a ka ajeta ,
Kallon tsantsareren gidan take tana tunanin shiga ,
Kiran udaysah tayi awaya akan tana bakin gate,jiranta tace tayi kan tana zuwa.
Tsaye tayi tana karema yanayin unguwar kallo ,komai shiru babu wata hayaniya .

Tunda ya shigo gate din layin yaga kamar ita a tsaye,
Kauda tunanin itace din yayi,sai da yazo bakin gate din ya tabbatar itace ,
Amma mai takeyi a kofar gidansu,
Ya na kokarin fitowa a motar udaysah na bude kofar gate tana fitowa"
Lokaci guda kuma mai gadi yana wangale masa katan gate din"
Kai tsaye ya danna kan motar sa ciki kar ma ya tsaya su rainashi.

"Inbanda abunki ai da kin shigo"

Kawai sai na shigo haka nan kedai tunda kin fito muje "
Kallanta udaysah ta kuma da kyau"

Aa irin kyau haka amma dai badaga gida kike ba"

Daga gida nake mana shikenan idan zan fito kuma kar na kintsa kedai wallahi baki rabo da zolaya"

Jan hannunta udaysah tayi suka shiga gidan tana cewa "
Naga kin chanza munne bantaba ganinki da makeup ba koda kuwa simple ne .

Falon hajia kalthume suka je dan noor ta gaisheta ,
A hankimce suka sameta tana daga atamfofin da tayi order "
Sallama sukayi mata ta amsa"
Yauwa udaysah zo kiga ga atamfofin danayi order sunzo zo ki zaba wadanda kikeso'

Yeeh umma'ah ashe sunzo bari nazo na duba
Amma kafunnan ga bakuwa na kawo miki ku gaisa"

Gaishe da umma'ah noor tayi cikin girmamawa".
Da faraarta ta amsa ,
Noor ko"

Eh itace udaysah ta bata amsa tana daga atampar da ta dauki hankalinta"

Allah sarki ya gida da mutanen gida"
Lapia lau tabata amsa "

Umma'ah nazaba guda hudunnan ni sukadai suka mun kyau"

Dama ai ke bakisan kyauba
Noor kema zo ki zaba wadanda suka miki kyau"

Da sauri noor ta kada kai '
A'a ma'am nagode"

Ma'am a school amma a gida umma'ah ce and come on my friend zoki zaba kar raina ya baci"

Kema dai umma'ah bakuwa daga zuwanta kice tazo ta zabi kayan da takeso .
Atare duk suka juya jin muryar fayyaz"

Auntan umma'ah yaushe ka dawo banma jika ba gaba daya"

Umma'ah ina zakijini kin baje hajja"

Kaniyarka"

Gaisheshi noor tayi kanta a kasa dan ita haushinshi takeji ita kwatakwata ma ta manta cewa gidansu daya da udaysah da bazatazo ba gudun haduwa da shi ga bugu da kari yace yana nemanta bataje ba"

Jin Kiran sallar laasar yasata tashi "

A'a sai ina cewar umma'ah"

Gida umma'ah naga yamma tayi"

Aw hakane cewar umma'ah kar mai gida ya dawo baa masa abincin dare ba "

Mai gida indeed "cewar fayyaz bayan ya aje glass cup din da yasha ruwa dashi kan dining  .
Baisake cewa komai ba ya nemi guri ya zauna a kusa da umma'ah"

Karki kulashi noor ,wannan dakika ganshi ya iya neman magana"
Usaysah je dauko mun gift bag babba guda daya .

Kallon noor udaysah tayi"
Amma noor ko minti talatin fa bakiyiba kuma zaki tafi gida ko hira bamuyi ba amma kince wani yamma yayi nidai banji dadi ba.

Oh udaysah Allah zan sake zuwa yanzu kinga ai zuwan yamman nayi gidan naji shiru so nace bari na dan fita"

Ai ba komai yanzun ma kin kyauta next time dai dawuri zakizo ki wuni mana amma fa idan mijinki ya barki"
Kinsan shi miji anasan a girmamashi fitarki ma idan bai saniba malaikun Allah zasuyita tsine miki har kidawo daga inda kikaje"

Wani dum gaba noor ya fadi ,koda kowa yaya nas ya bata mata bai kamata tazo gidansu udaysah ba batareda saninshi ba kamata yayi daga restaurant din tayi gida amma she couldn't help it ,
Gaba daya zuciyarta ce a cunkushe .

Gift bag din udaysah taje ta kawowa umma'ah "
Atampa uku ,takalmi ,gyale sai amber perfume na oriflame "
Umma'ah tasa aciki ta mikawa noor "
Gashi yata naji dadin ziyarar nan taki"

Kin karba noor tayi dan abubuwa nemasu tsada so mai yasa zata karba dan kawai tazo gidansu "_
Aikuwa baki isa na baki abu ba ki kikarba .

Amma umma'ah..

Daga mata hannu tayi ta bata rai
"Idan Baki karba ba zanga kamar kin rainane"

Bata kuma musuba ta sa hannu ta karba tareda mata godia,
Tana da kirki.
Kodayake kana ganinta macece wadda ta gaji arziki so yima mutum kyauta batajinsa a komai"

Yar kauye "

Kallansa duka sukayi suga da wa yake amma ga mamakinsu hankalinsa na kan tv dawuya ma idana yanajin mai suke .

Da gefen ido yake kallansu ,
Kome sukeyi hankalinsa na kansu amma bazaka taba tunanin hankalin nashi na kansu ba sabida idanunsa nakan tv".

Kai Hakimi tashi ka ajesu gida ,
Kafara aje udaysah gidan hajiya usaina zata kaimun sako and tana jiranta yanzunnan so tunda yafi kusa kuma hanyane ka aje ta .

Dan chuno baki udaysah tayi"
Amma umma'ah i can also drive,
Muje sai nafara kai mata sakon then sai mu wuce na kai noor gida tunda nasan gidan nata"

A'a kin manta kenan sabida rough driving dinki nace sai kinyi wata baki hau mota ba oya fayyaz ya kaiki ya aje idan ya kai noor ya dawo zai dauke ki cos da inda zaku keda hajiya usaina zaki karbon sako in return and inace bakifi fayyaz sanin gariba shima da kwatancen noor zai kaita gida safely.

Udaysah zata sake magana muryar fayyaz ta katse ta"
Ke kin cika musu banasan bata lokaci
Anfada miki nima san kaiku din nakeyi .
Kawai biyayyace nafiki da rashin musu.

Murguda masa baki tayi ta tafi dauko gyale"

Gaba daya noor ji take kamar tana cikin ruwane ,
Ita dama zasu barta taje ta hau keke ta wuce gida dan harga Allah basan hawa motar fayyaz take ba
Amma ba dama tayiwa umma'ah musu .

Chuchujay✍️

Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top