chapter 17
Noorurrahman✔..
Iya yarda nas zai nunama noor ya shiryu yayi kuma ta gamsu "
Kamar sauran ranaku biyar da suka shude yauma shi ya shirya tsaf zai kaita makaranta "
Cikin peach riga da skirt na lace ta shirya "
Gyale ta yafo ta fito dan ta kusa late"
Da idanu ya kafeta harta karaso inda yake "
Hura masa iska tayi a fuska"
Ya namaka kyaune har haka "
Murmushi mai kyau yayi ,
Ke mai kyauce ai noor"
Itama murmushin tayi ta shafa gefen sajensa da yasha gyara "
Kaima ai mai kyaune yaya nas ,mutafi nakusa late"
Kamo hannuta yayi ya hada ta da kirjinsa "
Kamshinta yake shaka a hankali a wuyanta "
Habibty yakamata a sake mun suna sanan banasan wannan turaren da kike shafawa idan zaki fita ,
Kinsan ai ko a musulunci haramune,
Kallonsa tayi tayi yar dariya tana mamakin wai nas yasan abu haramun ne"
Mene kike mun dariya "
Aa ba dariya nake maka ba,
Nadaina sakawa daga yau and kamun afuwa kasan yaya nas ya saba da bakina sosai maybe sai a hankali na saba maka da wani sunan"
Maybe"ya tambaya yana sake hadata da jikinsa "
Yaya nas please zanyi latti fa.
Okay muje tunda makarantar ki ta fini amfani"
Fita yayi yabarta tsaye ,kada kai tayi ta bi bayansa ,
Yaya nas kenan"
rai hade ta tarar dashi cikin motar ,
Ita har ga Allah har yanzu tana tsoran sakin jikinta sosai dashi,
Ta gamsu da ya tuba amma har ga Allah tana tsoran yaya nas ,
Tana tsoran kar ace tafara sanshi ya juya mata baya"
Shiga tayi ta zauna ,batareda ya ce mata kala ba ya ja motar ,
Sunyi tafiya mai nisa baice komai ba ganin haka yasa tace "
Yaya nas kayi hakuri idan kacigaba da fushin nan zakasa Allah yayi fushi dani .
Dan sakin fuska yayi kadan ,
Naji ni ba fushi nake ba ,karfe nawa zan dawo na daukeki,
Kallansa tayi sannan tayi murmushi"
Karfe biyu zan tashi "
Mai zan siya miki idan zan dawo"
Komai kagani yayi maka inaso"
Gatchu karki damu zan kawo miki abun dadi ki kula a maida hankali a karatu.
Saida ya fita a makarantar kafun ta fara tafiya dan zuwa aji ,
Allah yasa yaya nas ba tuban muzuru yayi ba Atleast duk da bata sanshi amma zuciya a hankali take san mai kyautata mata amma yazama dole tayi kaffa kaffa dan wannan mutuncin yaya nas din abun tsoro ne.
I can see har kun shirya"
Juyawa tayi dan ganin da ita ake dan maganar a kusa da ita sosai akayi"
Tayi mamakin ganin sir fayyaz .
Bata masa maganaba tacigaba da tafiya dan ga dukkanin alamu ba da ita yake ba and ita kam ta hani kanta dako gaisheshi gudun wulakanci,
Tunda akai case din yaya nas bata sake ganinsa ba sai yau din"
Kina tunanin bakuyi kuskure ba"
Ya kara tsintar kanshi da fada ganin bata kulashi ba"
Lokacin da suka shigo makarantar yana bayansu ,kwana biyar kenan yana kula nas ke kawo noor sannan yazo ya dauke ta ,baisan mai yasa yake jin abun ba daidai ba amma sai ya barwa zuciyarsa cewa tausayinta yake kuma yana guje mata rayuwar gidan yaya nas again dan a yarda ya karancesa mutumin banzane,
Ya dade a mota yana kallan su ta tint window dinsa and tabbas murmushin da noor kema nas babu kiyayya a cikinsa ,
Shin wai menene damuwarsa,
Mai yake damunsa ,
Kamar ya wuce amma sai ya tsinci kansa da cewa noorurrahman dake nake"
Juyowa tayi a dan tsorace "
Ni sir fayyaz"
Eh ke "
Mai kace"
Nace idan kin gama abunda kikeyi ki sameni a office ,yana gama fadan haka ya wani bata rai ya wuce "
tabe baki tayi "ko wanne sabon balain ne kuma wannan oho,
Na dauki yar'uwarsa in masifar ce idan ya ganta ya sassauta masifaffe"
Gaba daya ta ma manta da fayyaz yace ta sameshi office idan tagama duk da cewa ba laipinta bane idan ta manta dan suna gama lecture lecturern da zata tayi musu darasi nagaba ta shigo"
Bata tashi tunaawa ba saida yaya nas ya kirata a waya kan tafito idan ta gama"
So kawai tayi tafiyarta tunda idanma taje tasan masifa ce zai mata "
..
Ya dade yana zaune jiranta amma shiru,
Duk da baisan mai yasa yace tazo dinba "
Amma a matsayinsa na brother in deen dinta yana ganin bai kamata ace tana zaune da mugun miji kamar nasir ba kuma yayi shiru .
Tunda ma ai iyayensu abokai ne kenan ai shi ya zama yayanta,
Yes sure yazama yayanta bugu da kari jiya da sukayi waya da muhamamdu auwal ya basa amanarta cikin makarantar ,
Wayarsa ya ciro ya kira udaysah"
Kun gama lectures ne "
Shine abunda ya tambayeta "
Eh brother har na tafi gida ma"
Ke kadai"
Eh brother was I suppose to go with someone"
Kashe wayan yayi karta fada mishi maganar banza ".
Mai yake damunsa ne ,
A da bai taba tunanin damuwar wani zata dameshi ba amma yarasa mai yasa damuwar yarinyar da bai sani ba take damun sa ,
Ya Allah".
***************************************
Zama taga yayi lokacin da suka je gida ".
Yaya nas bazaka koma gun aiki bane "
Kice kawai kina korana sabida kar nace inajin yunwa ,
To bazan fadaba yanzu ki kintsa muje muci abinci na gano mana wani restaurant and inasan cin abincin gurin danhaka sonake ace gani ga sarauniyata a gefena dukda nasan cewa abincin bazai kai naki ba amma consider fitan as our first date after marriage ,
Daga mata gira daya yayi "
Wani kunyansa kuma taji ta shigeta so dama yaya nas yanada wannan side din nashi amma yake ta wulakantata, da ace haka yake mata ai da tuni tafara sanshi a ranta.
Wanka ta sake tayi simple makeup ,atampa ta dauko dinkin pencil straight gown"
Gyale mai dan girma ta yafo ,
A hankali take takowa cikin flat dinta mai kyau ,hannunta kuma rike da jakarta ta kelvin ".
Idanu ya zuba mata har ta karaso inda yake cikin takunta mai jan hankali"
Kinyi kyau inasan naga matana tayi kyau idan zamu fita sabida kowa idan ya ganmu yasan na auri mata mai kyau kuma yar gayu"
Wani iri taji maganar tashi amma sai bata sa komai a ranta ba ,
Kayi kyau kaima mijina "
Cikin sweatpants grey yake da black polo shirt ,
Dole kice nayi kyau mana tunda kikaki jirana muyi wankan tare daga zuwa daki na fito kika gudu"
Dan yake tayi cos batasan mai yasaba take ji jikinta bazata iya shiga wanka da ya nas ba abun ma abaki sai tajishi wani iri"
Muje ko "
A sannu ta taka cikin kwarewa a tafiya mai nutsuwa ,ta isa har bakin mota inda ya bude mata ta shiga suka fita a gidan"
A gurin adana motocin masu kaima restaurant din ziyara ya aje motarsa tana kokarin budewa ya fito da saurinsa dan bude mata "
Ita dai mamaki take dan itafa har yanzu ta kasa gasgata tuban nas abun nasa gani take is way too much ga mutumin da yagama shuka rashin mutuncinsa kala kala,
Tare suka shiga cikin al'ena'bella restaurant ,
Gurin ya kayatu iya kayatu ,
Kallan fuskanta yayi "
"Babe daga gani gurin ya burgeki ko "
Kada kai tayi"
Gun yayi kyau i just hope abincin nasu ma zai kayatar"
Naji dadi da gurin yayi miki if you like zamuna zuwa idan mun samu time"
Murmushi tayi"
Ya nas ko abincin gun bamu cibafa amma kake kiran zamuna zuwa ,
Let's taste what they have first .
Suna tsaka da cin abinci ne wata budurwa wadda kallo daya zaka mata kasan bata da kamun kai tazo guri "
Wanake gani kamar nas baby"
Kallanta noor tayi sannan ta kalleshi "
Ture hannun budurwar da ta dora akan kafadarsa yayi ya wani bata rai"
Ke meye haka"
Dariya irinta yan duniya tayi"
Haba baby kodan kayi new catch ne zaka nuna baka sanni ba katunafa last time dakaje abuja muna tare duk lokacin and kamun alkwarin zamu kasance tare duk lokacin da muka hadu hala ka manta har kake bani labarin kuchakar matar ka hope kun rabu dai"
Ke wacce irin mahaukaciya ce daga ganin mutum zakizo kina masa wani zancen banza ina na sanki dan Allah ki kara gaba nan gurin babu kasuwa"
Haba nas bari na fayyace maka na sanka ,
Kallon noor tayi wadda take binsu da idanu kawai"
"Baiwar Allah ina tunanin ke da shi were intimate ,
Ina nufin s*x sabida nasansa da jaraba and bazai iya dauke idanunsa kan mai kyau irinki ba"
Kin taba kula da birthmark din dake ci yarsa,
I told him inason birthmark din and yace its all mine nayi ta shafawa "
Batai aune ba ya dauke ta da mari yanata wani muzurai.
Chu chu jay✍️
Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top