chapter 16

Noorrurrahman✔

Ehem muna sauraranka mutumin banza sai kayi mana bayanin dalilin da yasaka ka daki matar ka har da kuma bakuwarta dan tsabagen rashin mutunci da iskanci"

A'a Abban nasir ba a haka,
Sai ka tambayi abunda tayi mishi ni na tabbata nas bazai dake ta babu daliliba sai kace wani dan kwaya"
Ummi ta tsomo baki"

keep quiet woman ,
Danki da kika kasa bawa tarbiyya mai kyau dashi nake magana,sannan kwayarma ai bazai rasa sha ba ,ki kallesa da kyau yarda duk ya hargitse mana idan ba kwayarba yataba gani mu iyayensa munsawa matan mu hannu"
Kai nake saurara sakarai.

Kallan mutanen dake babban falon nas yayi ,
Mami,baba Alhaji,ummi,noor ,muhammadu auwal ,sunkuyar da kai nas yayi"

Abba ni banida bakin magana nasan nayi laifi amma ayafe mun abani dama na gyara abunda na bata insha Allahu bazaa kara samuna da wata matsalaba ,
Ayi mun afuwa dan Allah"

Afuwar ubanka zaamaka ,lokacin da ka sa hannu ka daketa kayi tunanin afuwa ina kyautata zatan bawannan ne karo na farko ba"
Noor karkiji tsoransa kifada duk abunda yake miki wallahi sai na daukar miki mataki tunda ba gata kika rasaba"

Kasa noor tayi da kanta tanasan magana tana tsoran shirun baba Alhaji,
Wannan ce damarta idan tayi shiru maybe next time bazata samu dama ba irin ta yau"

Kallon nas tayi wanda duka ya chanza ma kammanni ,marairaice mata yayi da fuska irin ta rufa masa asiri dan yasan tabbas ta bude bakinta to ba mamaki abba zai iya ciresa cikin yayansa .
Tana shirin magana Baba alhaji yasa baki"

Umaru tunda ya ce ya tuba abashi chance ,Allah ma muna masa laipi murokesa kuma ya dawo ya yafe mana so mu su wanene da zaayi mana laipi a roke mu mu gaza yafiya ,da mu iyayayenka da noorrurahman mun baka wani chance din"

Take ya washe hakora yafara zubo uwar godia"
Wani kululun bakin cikine ya cika cikin mami,
Badan karta bada kanta gaban kanin mijinta ba da tashi zatayi ta bar gurin.
Bakaramin bacin rai muhammadu auwal ya shigaba da hukuncin mahaifin nasa ,wai shin baba Alhaji wane irin mutum ne.

Kuka noor takeso tayi amma ta kasa ta nemi hawayen sama da kasa ta rasasu ,wanne irin mahaifi ne da ita da baidamu da halin da take ciki ba sabida kawai zumuntakarsa "
Wannan wanne irin kaddarace "
Ya Allah kaida ka dora mun kaddarar nan ka bani ikon cinyewa"..

Wani kallan banza ummi ke bawa nas jin irin godiyar da yake kamar an bashi aljanna
Ta so ace auran nan ya mutu amma wannan baba Alhajin yawani bankanbankan a alamarin"

Allah ya muku albarka ke tashi ki bi mijinki ku tafi yana bukatar kulawarki yanzu".

Tashi tayi kamar bata da laka ta fita a dakin ,
A baya nas ya tashi zai bita muryar baba Alhaji ta tsayar dashi"

Nasiru bana baka matar ka bane kasake dukan ta ,
Bazan yarda da duka ba ,
Kul banasan nasakejin ka daki noor .

Insha Allahu baba baza akuma ba ._

Allah yayi muku albarka..

Bayan kowa ya watse ne ya zamana saura Abba da baba"
Kallan baba Abba yayi"
Yaya banida bakin da zan maka godia ,
Nagode sosai Allah ya saka da Alheri Allah ya kara mana dankon zuminci,
Bansan mai yake damun nasir ba kuma nasani nasiru bazai taba samun mata wadda takai noor ba ,
Amma yaya ina neman alfarmarka dukda baa fatan wata baraka tasake tasowa tsakaninsu amma yaya idan irin haka ta kara faruwa ka yarje mun na yanke hukunci saboda bashi iyuwa ace yaron nan ya cigaba da cutar da noor a cigaba da sasantasu abin zai zama da cutar wa.

Nayarda da nasir kuma nasan bazai bani kunya ba "
Shine kawai amsar da baba alhaji ya bawa Abba ya tashi ya fita ..

****************************************
Lokacin da suka isa gida ji tayi kamar tafita da gudu tashiga duniya kowa ya huta"

Ya kikaja kika tsaya kamar wata soja
Kallansa tayi taga bakinsa kamar wani kara zototo yayi "
Ciki tashiga,
Kai tsaye bathroom ta shiga ta hada masa ruwan zafi wanda idan yayi wanka zaiji dadin sa "

Fitowa tayi dan sanar dashi ta hada masa ruwa "
Hugging dinta taji anyita baya"
Nayi missing komai naki noor kibani second chance and trust me I will mend my ways ,nayi kuskure dayawa da dama abaya amma yanzu na tuba bazan sake ba insha Allah"
Dan zamewa tayi daga rikon da yayi mata"
"Ya nas kaje kagasa jikinka ko zaka ji dadi sanan ga maganin malaria chan yaya yabani na kawo mika"

Dan iska "ya furta chan kasan makoshi"

Mai kace"

Aa. Bakomai nace nagode ne bari na fito and zan nuna miki na tuba sosai and hope zaki yafe mun kinsan shi dan adam ajizine sannan nasanki da hakuri noor ke din maratus salaha ce"

Ita dai batace masa komai ba har ya shiga bandakin,.
Allah yasa gaske kake katuba din ba tuban muzuru kayi ba"

*
Bayan ya fito ne tafara gasa masa bakinsa "
Yaya nas ya maganar udaysah fa ta tsinci kanta da fada"

Banasan sake jin sunan ta noor please yanzu maganarmu akeyi and ba ta wasu ba yau zan nuna miki irin adadin kewarki da nayi "
Tasowa yayi ya matso gareta".
Hannunta biyu tasa  ta taresa"
I'm on my period"

Shit yace tareda dukan cushion din da yake kai ,sai kuma ya rike hannun yanafadin asshh

Kamawa tayi tana masa sannu "

Na tsani fayyaz dinan and i will make sure munyi settling scores "

Aw yaya nazata komai ai ya wuce idan ba so kake ka kara kuma jawo mana matsala ba .
Dan kallanta yayi tareda bata rai saikuma kamar an mintsileshi ya saki fuska "

Komai ya wuce AI kinga ashe babansa ma abokin kasuwancin su abba ne "

Allah sarki shine abunda kawai ta iya cewa"

Ranar gaba daya ta noor ce dan sai da yayi duk abunda zayyi ta sake yarda dashi a karo na biyu"

***************************************
Washe gari weekend da wani irin zazzabi nas ya tashi"
Babu abunda take masa sai sannu"
Asibiti ta kaishi ya ga likita inda ya tabbatar musu zazzabin cizan sauro ne ,
Ya kiyaye kwana cikin sauro "

Dan makale dariyar da ta kusa kwace mata tayi"
Lallai da gaske cell ta kunshi vampires masu zuba cuta"

Bayan yasha magungunan da likita ya bashine abun ya dan masa sauki"

Suna zaune a falo tana matsa masa kafarsa wayarsa tayi kara ,
Kallan wayar da ke gefenta tayi
"Mama tagani rubuce jikin screen din"

Wake kirana ".

Mama ke kiranka hala akwai wani party din  ta amsa masa tana bashi wayar"

Ke dadina dake abu baya wucewa a gurinki,
Ni ba dauka zan ba bani ma na kashe wayar ina fama da kaina wacce mama ke gabana dan Allah .

Murmushi kawai tayi"
Allah yasa da gaske yaya nas ya tuba ,dukda bata jin tana masa san mata da miji amma zata hora kanta tafara sansa a hankali ko yayane.

Chu chu jay✍️

Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top