chapter 15

Noorurrahman✔

Tuna yarda tazo tana masa kuka yayi da kuma yau yarda take kuka dan an kama mijinta ,
Amma menene labarinta ,
Menene yasa take damuwa da mijin nata ,

Ayarda udaysah ta fada masa basanshi take ba amma idan gaskiya ne mai yake sata kuka ,mai yasa ta jure duk wani humiliation akansa bayan ba mijin arziki bane"

Fayyaz ina ruwanka wata zuciyar ta tunatar dashi,
Mene naka nashiga abunda babu ruwanka ,
Ba haka kake ba kuma bazaka fara yau ba abu daya kasani shine yagane kuransa na offending dinka dakuma dukan udaysah babu gaira babu dalili.

.............................................................................
Tunanin inda zatayi tafara tasan muddin idan ta fadawa abba nas zai shiga cikin babbar matsala ,
Gidansu tayi kai tsaye tunda dama baba alhaji na tsaya mashi yanzu ga abunda zai tsaya masan ai ya taso ,

Gaba daya a kidime take fadawa mami abunda ya faru,

Mahammadu auwal da ya dawo daukar file ne yakalle ta"
to ke menene naki inace iskancinsa ne ya kaishi sai a rabu dashi ya gane kurensa tukunna and beside both abba da baba alhaji suna kaduna sai dare zasu shigo garinan nikuma banida connection din fito dashi kodama ina dashi bazan fito dashi din ba.

Amma yaya kasan abba bazaiji dadi ba"
Bai tsaya bi ta kanta ba ya fice mami kuma jinjina kyan zuciya irin na noor take dan kuwa ko itace duk da kawaicinta sai ya kwana biyu tukkunna zata fada"

Kalli noor je ki watsa ruwa kici abincin ni da kaina zan sanar ma babanku amma yanzu dole nas sai ya kwana sabida kinga yayanku yamayi tafiyansa ,

To mami Allah yasa kwananne alkheri ni ina tsorone dan kinsan halin baba yanzu sai ya fito da laipina acikin wannnan abun..

Koda muhammadu auwal ya fita direct police station din Da aka kulle nas yaje ,
Dafari sun dage akan bazai ganshi ba amma jin ya ambaci muktar dala agaban sunansa yasa Asp yace su barshi ya gansa amma gaskiya bazasu bada belinshiba sai wadanda suka kawo kararsa sunzo kuma ya kira sunce basu da lokaci yanzu.

A rana daya nas ya gama ganne cewa bashi kadaine dan iskaba .
Yana ganin muhammad yafara matsar kwalla ".
Muh please get me out of this place dan Allah"

Dan murmushi muhammadu auwal yayi ,
Katuba kenan inace yar mutane ka kama ka daka ,
Dukan noor is not okay talk less of ka hada harda bakuwarta ,to gashi ka tabo inda akafi karfinka inace santa kuma ka koma kanayi bayan ka daketa ,
Babu komai ni sai nama baba Alhaji magana a shiga a nema maka aurenta itama ka kawo  ka ringa duka kagani idan zakasha,

Noor din ma da kake duka kasani darajar yan uwantaka kakeci da kuma darajar samun mace ta gari wadda bata san bankada sirrinta ,
Nasan kana azabtar da noor amma noor bata taba koda sau daya takawo kararka ba illai yanzu haka neman mai fito da kai take wallahi nasir kaci amanar yan uwantaka"

Muh shikenan mutum kuma bazaiyyi kuskure ba,
Shairin shaidanne fa
Ni danasan haka abunnan zaifaru ma da wallahi bazan yarda na fara santa ba amma ya zanyi muh san ya riga ya shiga "

Babu fa yarda zakayi aikam gashinan kasha walmakalifati"
Ga bakinnan kamar shaida zata sha ruwa .
Anyways ni ba wannan ya kawoniba nazo domin darajar yanuwantaka naga ko zaa sake ka ka kwana gida amma abun ya ci tura dan wanda ya kawo kararka yace bashida lokacin zuwa yanzu .

Kana nufin yayantannan ,wallahi muh na zata saurayintane fa idanuna suka rufe na kai masa hannu da nasan yayantane ai da kamun kafa zanyi dashi.

Mamakin sabon nas din muhammad auwal yake ,
Juyawa yayi zai tafi dan takaicinsa bazai barshi ya kara magana dashiba .

Yanzu dan uwa anan zaka barni na kwana duk saurayen nan su cinyeni ,haba kamar wani mara gata hala baka fadama baba Alhaji halin danake ciki ba,
Muh please kar muyi haka da kai"

Zanyima doctor magana before hand idan yaso sai ya dubaka bayan ka fito,

Har bakin mota Asp ya rako shi
"Yallabai Ko zan baka number din wanda ya kawo case dinnan ne ku sasanta naga alamun na cikin cell din dan babban gidane "

No baka da damuwa Asp abarshi din ya kwana".

******************
Sai wuraren ishai su baba Alhaji suka dawo"
Koda yaga noor baice komaiba dan haka itama sai ta saki jikinta ,
Wani dadi takeji zata kwana gidansu yau dai wata zuciyar ta fara tunanin dama yaya nass ya wuce jail daga nan,
Lokaci daya wata zuciyar ta naushe ta *
Noor wannan mumunan fata ne mara kyau koda kuwa kafirine kar kiyi masa mumunan fata"
Okay to Allah yasa na dawo gida kenan nayi duk abunda zanyi dan kare ka yaya nas amma wautarka ta jawo maka tonan asiri .

Washe gari bayan sun gama breakfast ne baba alhaji ya tambaya kan mai noor ta zo yi gida,
Zayyana masa duk abunda ya faru mami tayi"
Shiru yayi na wani lokacin kafun yace"
Yanzu muhammadu auwal kana cikin garinnan dan uwanka ya kwana a police station,

Baba alhaji wallahi naje fa amma bansamu bail dinsa ba sabida ga dukkan alamu wadanda ya buga din manyan mutane ne"

Kana nufin shi nas din ba babban mutum bane ,har lalacewa tayi ace ya kwana a station dan kawai mu bamu gari har kuma kayi bacci cikin kwanciyar hankali da bacci mai dadi shi yana chan yana fama"

Shiru muhammadu auwal yayi dan idan ya sake magana bazaiji da dadi ba dan shima ba mai dadin zai fada ba"

Kallan noor Baba alhaji yayi"
Ke kuma kiyi addua Allah yasa kar na sameki da laipi dan idan na sameki da laipi ko da karamine zakisha mamakin yarda zanyi dake"

Kafun tace komai sallamar Abba ta ceceta"

Bayan sun gaisa da mami ne su noor kuma sun gaisheshi ya kalli yayansa"

Yaya muje ko "
Wannan sakaran yaran bazai taba dene nema mana magana ba ,idan ba iskanciba ace kadaki matarka harda bakuwarta ,
Ashe dama dukan ta yake yi ,
Ni ai naso yaya a kyalesa har sai lokacin da sukaga damar sakinsa ,
Shasha kuma noor indai ba ita ta yarda zata koma gidansa ba ta gama zama dashi.

Umaru zancen fa barin aure bai tashi ba ina kyautata zatan akwai wani bayanin a saman wanda ita tayi muje dai station din tukunna amma maganar noor tagama zaman gidan nas bai taso ba".

Haka suka fice muhammad auwal na ta cika yan batsewa dan shi har ga Allah baiso komawa station dinan ba "

................
Yau sai naga wanene uban yaronnan da har yakeda guts din saka bulala ya zane udaysah "
Daddy naji baka ta tawa cewan fayyaz".

Kai kana da karfin ramawa itafa ,yau zanga wanene ya tsaya masa "

Nine na tsaya masa "
Muryar baba Alhaji ta cikia gurin .
A tare Alhaji umar saraki da fayyaz suka juya dan ganin wanene mai magana"

,Alhaji muktar dala,A'a kace tare kake da Alhaji umar dala,
Yaushe gamu .

Ikon Allah yau ido wayake ganemun kamar Alhaji umar saraki,cewar baba Alhaji"

Shine fa ,

Kallonsu fayyaz da muhammadu auwal suke kowa da abunda yake sakawa a zuciyarsa inda iyayen kuma ke ta murnar ganin juna ,

Yaushe rabo cewar Baba Alhaji '
Tun ina siyan audiga a gurinka shekaru da dama ashe dai rai kanga rai"

Ashe yaron gurinkune sabanin nan ya shiga tsakaninsa da fayyaz.

Abba na shirin magana Baba Alhaji ya taresa dan yasan bazai taba magana a alfarmar nas ba"
"wallahi Alhaji ,yaran yanzune ka haifesu baka haifi halinsu ba ,
Kallan fayyaz yayi,
Masha Allahu yaran gurinka ne ya zama babban mutum haka ,
Ina tunawa wajen tsaran su muhammadu ne ,

Haka akayi kam lokacin ina tunasu su uku ,muhammad da nasiru, kar dai kace min nasiru ne aka kulle"

Kallan Aspn da yazama dan kallo Daddyn fayyaz yayi"
Kai maza a je a ciro nasiru ashe abun ma na gida ne"

Ba musu asp yabada umarni akaje aka taho da nas wanda kwana daya jikinnan yaci ubansa da cizon sauro"

Sulhu akayi inda nas yabawa fayyaz da mahaifinsa hakuri akan tsautsayine "

Shide fayyaz yace ya hakurane amma deep down yasan babu yarda zaayi yayi abota da nas kamar yarda iyayen nasu sukace .

Sallama sukayi kowa ya kama gabansa,
Fayyaz ba haka yaso ba kwata kwata amma babu yarda zaiyyi Daddy ya shiga zancen,
Tunda suka hau titi daddyn ke basa labarin irin amincin dake tsakaninshi da iyaye biyun amma shifa ba wannan ke gabansa ba "
Daddy nas din chan fa dukan matarsa yake i don't think this is right ,
Ya tsinci kansa da fada"

To in banda abunka fayyaz nasan iyayen zasu dau mataki dan tsayayyune a sanin da nayi musu ,
Abun nasu ma ai duk gidane tunda yarinyar Alhaji muktar din shi nasirun yake aure"

Shiru fayyaz yayi yana tuna cin mutuncin da yayima noor .
Shit "
Bai kyauta ba and yakamata ace yabata hakuri tinda shine mai laipi..

Chuchujay✍️

Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top