chapter 14
Noorurrahman✔
Washe gari tafito zata makaranta yatareta a kofar gida"
Lapia shine abunda tafara tambayarsa dan bata tunanin lapia"
Eh lapia Ki shigo na sauke ki makaranta"
Makaranta kuma"
Eh makaranta bazakije bane.
Da kansa ya bude mata gaban mota ,
Ba musu ta shiga tana mamakin sabon salon yaya nas wanda tasan dole akwai wani motive a karkashinsa "
Koda suka yi parking cikin makarantar da kansa yazo ya bude mata kofa ,
Fitowa tayi still tana mamaki"
Nagode shine abunda ta tsinci kanta da fada masa "
Har tajuya zata tafi ya kamo hannunta "
Look noor wata alfarma nakeso kiyimun ,
Dan Allah Ki tsaya udaysah ta zo kitayani bata hakuri akan abunda ya faru kinga idan na auro miki ita ai abun alfaharinkine gaki ga kawarki mijinku daya.
Fincike hannuta tayi dan wannan tana tunanin shayeshayen da yake ya fara taba masa kwakwalwa.
Kokawan kwace hannuta take amma ta kasa lokaci guda kuma dan kanshi ya cikata ,
DA sauri ya tafi gurin udaysah dake tafiya sannu a hankali a gefen fayyaz,
Da hanzari ya isa garesu baiyi wata wataba ya kaima fayyaz naushi a fuska yana huci"
wato dan uwarka kaine kake hanata saurarata ko"
Ba noor ba hatta udaysah saida tayi mutuwar tsaye "
Fayyaz kuwa wanda baiji ba bai gani ba yasamu saukar naushi da sassafen nan gefen bakinsa ya taba yaga jini.
Kallon nas yayi da mamaki,bayyi kama da mahaukaci ba kuma baya tunanin yama taba ganinsa"
Wani naushin nas yake kokarin kaimasa ,
Cikin zafin nama ya rike masa hannu ya daukesa da mari "
Kafun kace me Security suka zo gurin da gudu"
Who let this mad man in"
Ransa a bace yake tambayar security din,
Bakowanne mutum ne zakuga yayi shigar kirki ba mai hankali"_
Eh eh din ni mahaukacine akanta ,akan udaysah zan iya yin komai so kafita harkarta wallahi kar nazama ajalinka"
.
Ai bama zaaje nan ba security ku kama mun mahaukacin nan,
Wayarsa ya ciro yakira yansanda ,
Kutafi dashi ku kulle idan yan sanda sunzo ku damka musu shi"
Ke kuma wuce muje zaki mun bayanin inda kika sanshi"
Sai a lokacinne idanun udaysah suka sauka akan noor wadda ta mutu a tsaye tama kasa yin komai babu abinda ke fita idanunta sai hawaye,
Da gudu tabi udaysah da sir fayyaz,
Office din fayyaz suka je ,
Suna shiga itama ta banka office din tana maida numfashi.
Lapia,
KO kema wata sabuwar kamun haukan ne zaki shigo ma mutane ba nutsuwa
Fita yanzu ko nayi maganinki sosai a gurinan banasan hauka"
Brother fayyaz please tanada duk wani right akan fadan nan sabida mutumin da kasa a kama mijinta ne.
Wani iri yaji kalmar ,mamaki da takaici,
Mijinta "??
Eh brother mijinta "
Wata dariya yasaka "now I understand ,wato ita makaryaci mijinta mahaukaci to zanyi maganinsa daga yau bazai sake dukan mutane randomly ba fice mun daga gani kin biyo ni ne kimun me "
"Dan Allah sir fayyaz kayi hakuri kar kasa a kama ya nas,
Nasan abinda yayi bai dace ba amma dan Allah kayi hakuri dan Allah.
Wani kululun haushi ne ya cika zuciyar udaysah ,
Shin noor wacce irin zuciyace Allah ya bata"
Idan baki fitaba wallahi har dake zan hada a kulle "
Ba musu ta fita a office din tana jin bakin cikin wannan wulakancin da ya nas ya jawo mata "
.
Back to you udaysah kin gani ko ,kingani irin jayejaye abunda ya jawo ko just kalli yarda ya fasa mun gefen baki ,
Just take a look,
Idan banda haukama ya zaayi ki ringa kula mijin kawarki wannan wane irin rayuwa ne ,
Duk bama wannan ba bai dameni ba ,ba ruwana da wani haukanku amma umma'ah have to know this ,
Dole tasan wannan abun and that man I promise zaigane kurensa,
Kuma waccan yarinyar mai ikirarin matarsace idan bata shiga hankalinta ba itama zata shiga ruwa .
Wama yasani ko hadaka sukayi ita ta nemi ta shiga jikinki shima ya bayyana yanzu dan su sace ki su samu ransom,ki dai cigaba da yayibo jaraba
Nonsense.
Brother fayyaz will you just listen to me"
Na saurareka ka gama naka so nima ka saurareni please,
Noor is innocent beside itace villain a cikin duk wannan abun"
Mijintane amma ta auresa sabida biyayya amma brother biyayyanta bai biyaba sabida duka yake mata baya ganin wani mutuncinta ,idan yana ganin mutuncinta kana tunanin zai biyo kawartane,
Last time fa nida ita ya hada ya zane "
Rufe baki tayi data yi realizing abunda ta fada ,
Shit"
Ya zane ku ,
Fayyaz ya maimaita cike da mamaki"
Ke a ina ya ganki har ya hada dake ya zane?
ehm dama dama ranar munje gidanta ne tare"
Gidanta ,ke har yaushe kukayi sabonda har zaki bita gidanta,
Wato ya zane ku amma sai yanzu kike fada,
Wait don't tell me abunda yasaki cuta kenan?
God is great "
Ficewa yayi a office din yana waya ".
Wayar noor ta kira amma bata dauka ba sai a kira na biyu"
Kina ina noor"
Ina bayan library"
Kashe wayan tayi ta tafi dan ganin halin da noor din take ciki"
zaune ta ganta kan step din da suka saba zama ,
DA sarsarfa ta karasa gareta"
Noor dan Allah kibar wannan kukan baida amfani please"
Udaysah mai zaisa bazan kuka ba ,
Kalli fa abunda ya nas yayi kuma nice sila ni na jawo komai yanzu gashi yanasan ya damu rayuwarki ,idan banda hauka ma ya zaayi kawai daga ganin mutum ka hau naushinshi,
I thought sabida ya gane yana abunda bai kyautuwa ne yasaka ya kawoni makaranta ashe sabida ke ne .
Kalla abunda ya jawofa
Ina yakeso nasaka rayuwata .
Noor dan Allah kibari just this once ya gane kuransa ,
And ni kisani bazan taba san mijinki ba bazantaba cin amanarki ta wannan hanyarba"
Dariya cikin kuka noor tasaka "
Kina tunanin damuwata dan ya nas yace yana sanki ne"
Ina alaka dakene sabida Allah sannan miji na gari ake kishi kuma kisani koda kin yarda kina san ya nas misali ni zan tsaya ne kar alakar ku ta tabbata sabida ya nas da kike gani ya wuce duk yarda zan miki bayani"
He is a monster ".
Udaysah na shirin sake magana wayarta tai ringing
Fayyaz ke kiranta ,
Daga wayan tayi dan jin ko menene"
Kuzo da kawarki station din dake bayan health school din Chan
,dif ya kashe wayar"
Kalan noor tayi wadda itama kallan nata take danjin mai ke faruwa*
Kamo hannuta tayi tace tashi muje"
Zaune suka hango fayyaz cikin station din yansandan na ta masa fadanci kamar sunga wani governor,
Karasawa ciki sukai jikin noor na karkarwa kadan kadan dan gabadaya tsoro ya kamata wannan ne farkon zuwanta guri irin wannan".
Yauwa Asp
Ga kanwata nan da ya daka,
Udaysah speak"
Kallonta noor tayi,
Udaysah nayi tunanin mun gama maganan duka ba "
Yi mana shiru please udaysah nace bake ba"
Idan ke ya dakeki iyayanki basu daukar miki mataki ba mu ba shashashai bane da wani katon banza zai daketa mu barsa,
Hala kudi keda danginki kuka gani kuka aureshi shiyasa suka barshi ya kashe ki"
Dama idan da kwadayi ai da wahala"
Babu abunda ke fita idanunta sai hawaye yau yaya nas ya jawo mata komai,
Kasa zama tayi ta fice daga station din shida ya ja ya biya "
Brother abunda ka fada yayi yawa and beside cousin brother dintane "
Allah ya kyauta iyaye na sakacin aura ma yayansu wadanda basu gama sanin halayyarsu ba idan ba hakaba ai ko cousin brother dintane sa binciki halayyarsa cewa Asp adnan.
Manta da ita Asp mai tasani na rayuwa ,kara biyu na kawo akansa ya dakar mun kanwa sannan ya dake ni babu hawa babu sauka ,sannan inaso kafin afara tambayarsa dalili a mai lilis tukkuna .
Ai ranka ya dade tunda ka kira waya yake shan lillisa.
Menene sunan matar tasa zan rubuta a statement tunda ai ita taja udaysah gidan .
Amma asp ai babu ruwanta itama villain ce .
Cewar udaysah"..
Kinasan in bata miki ko"
Bata fuska tayi amma brother ...
Will you keep quite my frnd menene full name dinta "
Noorurrahman muktar dala "
Tsayawa da rubutun asp yayi"
Badai Alhaji muktar dala dana sani ba shahararren dan kasuwar nan.
yo asp Allah na tuba yanzu karyar sunan masu kudi ai tazama ruwan dare kar kayi mamaki acikin irin wadanda yake bama taimako ne koshi ya sata makaranta take using sunansa ni kwata kwata ban yarda da yarinyar ba.
Bayan sun gama komai fayyaz ya cika Asp da kudi akan a daka masa nas sosai kafun gobe anema iyayansa suzo dan shi bai bukatar akaisu kotu.
Ware idanu udaysa tayi bayan sun fito ko zataga noor amma babu ita babu alamunta*
Brother fayyaz ko "kayi ma noor mumunar fahimta and i can understand sabida karyarda tayi makane kuma tayi makane dan kare karatunta and nice na jawo komai,
Noor ta dauki karatun nan rayuwarta shiyasa a lokacin ta tsorata dan tayi tunanin zaka iyasakawa a koremu and she couldn't afford it
Amma bakaji yarda take bakin cikin karyar datayi maka ba be understandable bakowane yake samun yarda yake so a rayuwaba noor abun a tausaya matane ba a zageta ba,
Tafiya tayi dan hawa adaidaita sahu,
Barinshi tayi yana juya zancen lokaci guda kuma yanajin wani irin yanayi wanda baisan menene ba.
Chu chu jay✍️
Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top