chapter 12

Noorurrahman✔

A tare sukayi mutuwar tsaye ganin ya nas gabansu kar ma ace noor wadda ita tasan kwanan batun amma udaysah kuwa mamakine ya cikata ganinsa tsaye da bulala dorina a hannunsa ".

Ya nas yaushe kadawo.

Amsarta itace saukar dorinar da taji jikinta ,
Kokarin gudu take amma ya tare ta ya cigaba da zuba mata bulalar ta ko ina yana zaginta "
Cikin karfin hali udaysah ta shiga tsakaninsu tana fadin "kai kuwa ko mai tamaka ka rufeta da duka haka daga shigowarta "

Kamar jira yake ya hadasu biyu ya hau jibga
Babu abunda kakeji sai ihunsu ,haji nas kuwa idanunsa sun rufe"
Saida ya tabbatar yayi musu lilis kafun yafita a gidan yana ta huci batareda ya damu da bakuwar da yahada da matarsa ya zane ba"

Kuka sosai noor take ,chan gefe ma hajiya udaysah ganin kwakwaf da jikinta yayi jawur tana nata kukan dan tunda uwarta ta haifeta ba'a taba mata duka irin na yau ba ,

Tashi noor wadda idan da sabo tasaba tayi ta dosa gurin udaysah
"Dan Allah udaysah kiyi hakuri this is not like yaya nas
Bansan menene yazo kanshi ba yau kiyi hakuri dan Allah laipina ya shafeki"

Wani bakin cikinta ne ya sake kama udaysah da ta fahimci tabbas yaya nas din shine mijin noor"
Daukar jakarta tayi ta kalleta da jajayen idanunta ,
Oh wato kina kareshi ma yaza'ayi ace mijin aurenka na sunnah yana maka irin wannan dukan sannan ya hada harda bakonka kuma ki fada mun wai ba haka yake ba"
Babu yarda zaayi mutum yafara irin wannan abun rana tsaka ,
I thought da iliminki amma kin ban mamaki da kike zaune cikin toxic marriage ,
To wallahi dukan nan da yayi mun bai ci bulus ba idan ke yaci bulus sai nasa an kulesa wallahi".

Jin ana batun kullewa yasa noor sake tsorata ,bazataso abunda zai taba mutuncin gidan su ba ,duk kuwa abunda yaya nas yake mata ai shi da ita jini daya ne,ganin udaysah ta doshi hanyar fita fuuu yasaka noor saurin binta ta kamo,

Dan Allah udaysah idan kika sa aka kama yaya nas wallahi mutuncin gidan mu zai baci yaya nas cousin brother nane idan kikasa yansanda suka kamashi na taba mutuncin mahaifinsa kuma na tona asirin gidan aurena ,
Dan Allah udaysah kiyi hakuri ba danshi ba domin ni ki yi hakuri ina kyautata zatan yanzu haka yana maye ne if not bazai hada dake ya dake mu ba"

Maye"
Wait do you mean he's also a drunkard?
Kuma kike zaune dashi ,ina hankalinki kina kiran wannan sirrin aure ,
sabida kawai dan uwankine sai ki bari ya kasheki?
Gyara dan Allah kar ki kara bata mun rai yanzun nan "_
Ficewa tayi tana mamakin rashin hankalin noor dan wannan rashin hankaline "

Da gudu noor ta bita tana kiran sunan ta amma ta mata banza ta fice ,
Mai gadi ne ya taso "
Hajiya ina taso na fada miki oga ya dawo ganinki da bakuwa kuma a yanayin yarda yashigo komai zai iya faru amma kikace na bari kifito"
Jitayi kamar ta rufe sa da duka"
Mai ya hanaka katseni ta hanyar fadamin simple maigidan ya dawo"
Fuu ta wuce ciki gida tana wani saban kukan"_

Wannan wane irin wukanci ne ,anya nas bashine zaizama ajalinta ba,ya Allah ga baiwarka ka kawomin dauki ina cikin wani hali,

Hajiya udaysah kuwa tana zuwa gida dakinta tashige bata tsaya bi takan kowa ba dan muddin yanzu wani ya zo inda take zata fada masa mai ke faruwane"
Zurfafa tayi cikin tunanin rayuwar da kawarta take ciki ,anya rayuwa zata tafi a haka ,tabbas da ita ke samun wannan dukan a gidan miji da tuni ta dade da hadashi da human right "
Amma gaskiya yau nas ya tsallake rijiya da baya yaci saar matarsa amma wallahi yau da sai yayi kwana station"

Wanka tayi ta dan gasa jikinta dan tafa daku ba karya had it been lokacin da noor tafada mata tana da aure da kawai ta yarda ba sai ta zurfafa bincike ba, gashi san a saninta ya jawo mata ganin abunda bata tunanin zata iya yin shiru har abada".

Washe gari a gidan su fayyaz kowa ya fito breakfast amma banda udaysah wadda kullum itace gaba gaba wurin tashi da wuri"

Nikam diyata lapia najita shiru "cewar alhaji umar"

Nimafa ban jitaba jiya duk da ban dawo da wuri ba, da naje gidan su hanne motana ya samu matsala a hanya nasamu delay karshe fayyaz ya dauko ni ,sanin halinta na idan bata shigaba kar kashigar mata nata yasa ban nemetaba amma harira ta ce mun ta dawo.

Tabe baki fayyaz yayi,
"Wanene ya Kai wannan neman attention kamar kullum yauma shi take nema"

Aikuwa yarda take neman attention din ta Samu tashi kaje ka gano ta lapia kar ta makara zuwa makaranta".

Amma umma'ah nikuma '

Eh kai ko bazaka bane natashi naje da kaina "
Mikewa yayi ya wani cin magani duk yarda udaysah zatayi tashiga rayuwarsa ta iya "_
Knocking ya fara yi a bakin kofar dakinta amma shiru daga ciki baayi magana ba "
Murda handle din yayi yaji a bude "
Budewa yayi ya shiga yana ware idanun inda zai ganota"

Kwance ya tarar da ita tana rawar dari cikin bargo"
Ke lapia "
Ganin bata kulashiba ne yasa ya koma dan sanar ma umma'ah halinda ya tsinceta ...

Bangaren noor kuwa kamar ma bai daketaba dan tasaba bata tunanin da akwai wani duka na yaya nas da zai saukar mata zazzabi,
Jikinta dai yayi tsami amma bayan gasa jikin da tayi taji dadi sosai".

Dakinsa yau ya kwana taji dadin hakan dan dama tarasa  balain dayasaka ya dawo dakinta gabaki dayansa ya tare dan balai"
Jitayi bazata iya zuwa makaranta ba dan haka kawai tayi kwanciyarta ta cigaba da juye juyenta tana ta tunane tunane wanda yazamar mata jiki"

Batareda sallama ba ya banko kai cikin dakin nata ,
Zama yayi bakin gado"
Ehm noor yarinyan dana baku kashi tare a ina take ne dan jiya sai bayan na kwanta fuskarta ta ke dawo mun gaskiya tana da kyau yazaayi nasameta na bata hakuri dan ta kwanta mun wallahi"

Kai yaya nas a cikin yan iska ma shi na daban ne,bata taba ganin mara kunya irinsa ba "

Banza tamishi saida ya kara jadada mata abunda yace,
Dake fa nake"

Tashi zauna tayi "
Yaya nas duk wani abun da kakeyi kasanifa Allah yana kallan ka sannan Allah bazai taba barin azzalimiba kuma kasani shifa  hakkin aure tun a duniya Allah yake fitar dashi and ni nasan tunda mukai aure ban taba cutar da kaiba koda sau daya ne amma kaifa ,
Baka kishina ,bakasan darajata ba,bakasan mutunci naba ,baka da aiki sai buguna wanda halayyace irinta jahilan farko ,babu abinda kasaka agaba sai duk wani abu wanda Allah ya hana kaji tsoran Allah sannan kaji tsoran haduwar ka dashi domin idan ka mutu yanzu wallahi tallahi bazakaji da dadi ba ko kadan"

Allahu akbar ,
Kin idar ?
To idan kin idar ni zan wuce sannan idan har kishi kikeyi akanta to ki daina danni naga guri,

Menene abun kishi akanka ya nas "ta tsinci kanta da fada"
To kaje maybe watan tozartar kane ya kama idan ni kamin kaci bati sabida yan uwantaka ita kasani gidan yari zakaci".

Bari idan nadawo sai ki kara maimaita abunda kika fada kiga yarda zamu kare .

****
A kidime umma'ah da Alhaji umar suka nufa dakin udaysah dan dubata suga ko lapia"
Yanzu ta tashi daga ka gadon ta dauko doguwar riga da zata rufe mata jikinta tasaka ,dan tasan tabbas sukaga shatin bulalai a jikinta to mijin noor ya kade har ganyensa "

Maike damunki sweetheart"
Umma'ah fever ne kawai "
Amma kika kasa zuwa ki fadama kowa ko waya ai kya kira"

Aa kalthume da laipinki kamata yayi ace tun jiya kin zo kin duba yarinyar nan da kika dawo dan ki tabbatar kalau take "
Fayyaz maza kira doctor edress ,
Abba ya bashi umarni ,
Babu musu ya kirasa a waya amma ya shaida musu baya gari amma su bawa udaysah ta fada mishi ya take ji,

Gaba daya yarda take jin jikinta tafada masa ,
Prescribing magani yayi mata fayyaz yaje yasiyo"

Bacci ta koma lokacin da tagama shan magungunnata .
KO Zata dan samu relief din abunda take ji.

Chuchujay

Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top